Showing 81001 words to 84000 words out of 88290 words
Chapter 28 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
kenan” bata yi mamakin jin cewa SAM ne,dan tunda taga photo a part ɗin dady da yanda Yumnah ke ja mata aji ta fara zargin shine,sai gashi zarginta ya tabbata
“ya SAM” ta furta a hankali,jinjina mata kai Yumnah tayi,wani irin ƙayataccen murmushi ne ya bayyana a fuskarta ba tare da ta shiryama hakan ba,kallonta kawai Yumnah take ba tun yau ba take zargin akwai wani abu a zuciyar Nainarh game da yayan nata dan kusan kullum ne sai tayi mata maganar shi,maida dubanta tayi kan system ɗin,a hankali ta ɗaura hannunta kan keyboard ɗin kamar mai tsoron taɓawa,cikin photo ɗaya ta shiga,ɗaya bayan ɗaya ta shiga kallon pics ɗin,zuba mata ido Yumnah tayi tana sakin murmushi,sosai ta shagala da kallon pics ɗin wasu a cikin mota aka ɗaukeshi,wasu yana a cikin jirgi wasu a gym room ne,mafi yawan photo an ɗauke su ne ba tare da sanin shi ba,duk kyan photon babu wanda aka ɗauka yana dariya,fuskarshi a ɗaure take sai dai hakan bai ɓoye kyawun fuskarshi ba.
saurin janye system ɗin Yumnah tayi tana faɗin “kallon ya isa haka baby,karki cinyeshi mu shige su” da sauri ta kalli Yumnah can kuma ta saki murmushi tana kifa kanta saman pillow,dariya Yumnah ta saki tana leƙa fuskar Nainarh
“wai kunya ki ka ji”sake ɓoye fuskarta tayi da pillown,hakan da tayi ba ƙaramin sa Yumnah nishaɗi tayi ba,dan sosai take mata dariya tana ƙoƙarin zame pillown data cusa fuskarta,dariya take itama Nainarh tana sake ɓoye fuskarta a jikin pillown.
hayaniya su kaji sama sama da yake ƙofar bedroom ɗin a buɗe take,da sauri Nainarh ta ɗago tana kallon Yumnah,sauka Yumnah tayi daga saman bed ɗin tana nufar ƙofar fita,da sauri itama Nainarh ta sauka daga saman bed ɗin tana bin bayanta,turus su ka tsaya a parlorn mom suna kallon su mom fatilah daketa fama ɗura ashar kamar wasu maguzawa,mom da mom Maryam na tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin mom su na kallon su
“ehe warning nake bige maki,tun wuri Irfan ya fita harkar ƴata, idan har ta hanyar halak ki ka haifesa ba shege ne shi ba daga yau ya rabu da ƴata,inba ma jaraba ba ko wane shege daya ta so bashi wacce zai maƙalemawa sai ƴaƴan mu,idan abun arziƙi ne dan mi bazasu nemi danginki ba sai ƴaƴan mu,to wallahi tun wuri ya fita safgar ƴata dan ban haifama wani ƙaton banza dangin nasara masu jan kunne dangin sheɗan ƴata ba ehe,ƴata tsarkakakkiya ce gaba da baya,babu ta idan take da abun faɗe,jinin musulunci ce gaba da baya ba sabbin tuba ba”tunda mom fatilah ta fara zazzaga rashin mutuncinta babu wanda yace mata ƙala daga mom har mom Maryam da mamaki ya gama kasheta,jikin Nainarh duk ya yayi sanyi,wani irin tausayin mom ne ya rufeta, Yumnah tuni ƙwalla sun cika idanunta dama ta san dole hakan ta faru muddin mom fatilah ta san da maganar soyayyar Irfan da Noor
“idan ba so ake mu shuka rashin mutuncin da har a koma ma Allah ba'a manta damu ba to tun wuri
yaje can ya nemi wata,amma ba ƴar mu ba”hijaya Zainab ta faɗa tana wani jijjiga jiki
“wallahi har gobe takaicin haɗa zuri'a nake da wannan dangin sheɗan ɗin,dan da yanda zanyi da wallahi ba'ayi Auren Nafisat da Naeem ba,har gobe Adu'ar abunda zai tsige wannan tsinanniyar igiyar Auren nake” mom Halima ta faɗa cike da takaici
“wallahi ke ki ka so,Ni ba'ayi ɗan iskan da zaiyi man wannan ba,dan wallahi ko ubanta bai isa ba bare wani can ƙanin ubanta da ko kallon banza bai ishe ni ba” a cewar mom fatilah, kwashewa mamy tayi da wata ƴar iskar dariya tana guɗa kamar zata fasa parlorn
“musluncin rahama ne”ta faɗa tana wani rausaya kai
“duk kun gama ƴaƴan malamai jikokin malamai,mahaddata Alqur'ani,masu tafiya harrufa na zuba?” mom Maryam ta faɗa,kyaɓe baki MOM halima tayi“A'a uwar mu ke muke jira” Hajiya Zainab ta faɗa,tsawa mom maryam ta daka mata rai a ɓace “kee dakata tsaya matsayinki da yayarki nake dan ke baki isa nayin dake,dan ko kallon banza baki ishe ni ba” shewa su ka yi kamar wasu karuwai suna tafa hannu, girgiza kai Nainarh tayi a ranta tana faɗin “tayama Noor za tayi tarbiyya bayan mahaifiyarta ma ba ita gareta ba,sai yanzu ta fahimci ta inda rayuwar Noor ɗin ta samu matsala,tausayi ma uncle mutallaf da Ubaid su ka bata dan ance mace ta gari jarice amma su kam ba suyi dace ba”
“da ku ka zo kuna cika ma mutane kunne da hayaniya sai kace wasu ƴan dandi, a haka Musluncin da ku ke iƙarari yake?,inji dai duk wannan hauragiyar da haukan kuna yi ne akan Noor,to me Noor ɗin take dashi da har namijin arziƙi zaiyi fatan kasancewarta uwar ƴaƴanshi,mi Noor ɗin take dashi banda tsagwaron rashin tarbiyya da jahilinci???”mom Maryam ta faɗa tana bin su da idanu
“ke Hajiya Maryam tsaya matsayinki,ba dake muke magana ba da ita muke,kuma da ki ke magana,idan har bata da tarbiyya mi yasa ɗan naku ya maƙale mata,yaje ya nemi mai tarbiyya mana” a cewar mom Halima, murmushi mom Maryam ta saki tana girgiza kanta “bari ku ji na faɗa maku,babu wacce a cikin ku ta kai matsayin da Zulaihart za tayi musayar baki da ita,Aure tsakanin Noor da Irfan tun kafin zuciyarki ta raya maki kizo kiyi rashin mutunci ki sake tabbatar ma da Uwarshi ba'a baki tarbiyya a gida ba bare har kiba taki ƴar tayi ma tufkar hanci,ki sani tasan darajar ɗanta baza ta so abunda zai ruguzar rayuwar shi ba,Noor ba Macen arziƙi bace da za'a so haɗa alaƙa da ita,dan haka ku tattara ƙafafuwan ku kufuce ku ba mutane wuri”
“kan bala'i lallai Hajiya Maryam,ke har kin isa ki faɗama mana haka,idan ba macen arziƙi bace uban mi yasa ɗan nata ya maƙale mata,wato an baki kin tada kai har kinyi ƙwarin shiga gaba, wallahi kinji kunya” a cewar mom Halima
“wannan ku ta shafa,mara tarbiyyar ƴar ku dai bata gurbi anan sai ku ƙara gaba,gayyar tsiya”
carb Mamy tace “shishshigi shiga dangin miji da gana masgo,shi ɗan naku da ku ke cika baki tarbiyyar gareshi,yaron da duk daran Allah yana yawan mashaya,kullum idon shi akan tsiranci yake,ko da yake ba baƙon abu bane a wajen Uwarshi bare shi”tunda mamy ta fara magana gaban mom ya faɗi ta rasa miyasa duk wani abu ya haɗasu saita danganta Irfan da yawan mashaya abun yana ɗaga mata hankali,juyawa Yumnah tayi da gudu tana fashewa da wani sabon kuka
“ko kwana yake a cikin kwalbar giya ba mashaya ba,ƴarku dai nan ƙwalelenta,tai makon da aka yi ma na baya bazata samu ba” mom Maryam ta faɗa,wani irin mugun ɓaci ran mom Halima yayi wato da ƴaƴan su take
Sosai su ka shiga musayar baki kamar zasu kaima juna duka, maganganu su mom Fatilah ke faɗa ma mom amma ƙala batace masu ba mom maryam ke aikin maida masu da maratani, Nainarh tausayi ma su ka bata su duka,kowa na ƙoƙarin ganin ya kare nashi, kowa iƙirarin nasha nada tarbiyya yake, to ita dai a iya fahimtarta da Noor da Irfan ɗin bataga wani wanda yafi wani tarbiyya ba amma suna cecekuce da junansu, a ganinta barinsu su Aure juna kamar rufin asirinsu ne baki ɗaya dan tayi imani kaf a cikin iyayen su babuwanda yasan kalar soyayya da su ke.
“da ki ke tada jijiyoyin wuya mi yasa ke baki haifa mata mai tarbiyyar ba, kinga ai da sai ki bashi ƙarewa shigema uwarshi faɗa”mom fatila ta faɗa tana kallon mom Maryam, ƴar dariya mom Maryam tayi “mai tarbiyya dai sai mai tarbiyya, dan haka kija gayyar tsiyar ki ku ba mutane wuri ko wallahi nasa ayi waje da ku”mom maryam ta faɗa
“ke har kin isa kisa a fitar damu, karki manta yanda yake gidan mijinta haka yake gidan mijina, ke kinyi kaɗa kisa a fitar damu wallahi” mamy ta faɗa tana huci
“dallah jacan kilaki kawai” mom Maryam ta faɗa tana aikama mamy da harara,da mugun gudu mamy tayo kanta dan ranta ba ƙaramin ɓaci yayi da kalaman mom Maryam ba,bata ƙarasa gareta ba a dalilin muguwar tsawar da aka daka masu,babu ƴan hanjin cikin wanda basu kaɗa ba a cikin su dan Nainarh barin wajen tayi ta nufi wurin Yumnah,gaba ɗaya su ka kai dubansu ga dady, uncle Mustafa, uncle hashim,ya Naeem da ya Adnan da sun ɗan jima da shigowa parlorn,kusan rabi da kwatar faɗan a kunen su,kallo ɗaya mom tayima dady ya kafeta da idanu ta nufi bedroom ɗinta,juyawa mom Maryam tayi zata bita,wata irin gigitacer tsayawa wacce tafi ta ɗazu uncle Mustafa ya dakata mata
“zo ki wuce kafin ranki ya ɓaci”
“zan ɗau jakana ne” tsawa ya sake daka “i said get out” ƙofar fita kawai ta nufa ba tare da ta ɗauko jakar ba.
murmushin mugunta su mamy su ka saki dan hakan da Uncle Mustafa yayi ba ƙaramin daɗi su kaji ba,tsuke fuska yayi fiye da ɗazu yana kallon su mamy “U,what are u waiting for,get out before i deal with you” da sauri sumi sumi su ka nufi ƙofar fita dan ba ƙaramin shakkarshi su ke ba ko mom fatilah dake cika bakin ko uban Noor bai isaba bare wani can ƙanin ubanta ta faɗa ne kawai dan ba'a gabanshi bane ba,yanzun ma Adu'a take Allah yasa baiji lokacin da tace hakan ba dan ba su kaɗai ba hatta ƴan uwanshi shakkarshi su ke,kallon dady yayi, tsantsan ɓacin rai ne kwance a fuskarshi,haka su ya Naeem babu wanda ranshi bai ɓaci da wannan abun da su mamy su ka yi ba,kallon ya Adnan uncle Mustafa yayi yace ya ɗauko mashi jakan mom Maryam dake ɗakin mom,da to ya amsa mashi yana nufar bedroom ɗin mom,fitowa yayi da jakan a hannu,amsa uncle Mustafa yayi,ficewa kawai yayi without saying anything,dan rashin a ɓace yake,a parking space ya samu mom Maryam jingine jikin motarshi sai wani cika take tana batsewa,tun daga nesa ya shiga aika mata harara,yana isowa driver seat ya buɗe ya shige without looking at her,jefa jakatar dake hannunshi back seat yayi,front seat mom Maryam ta zo buɗe saiƙara ɗaure fuska take ganin ko kallon inda take baiyi ba,key yayi ma motar su ka fice daga gidan,tsit motan tayi can dai yayi breakin silet ɗin
“dama abunda ke kawo ki gidan ya Tahir kenan ko?”
wani kallo tayi mashi da kamar baza tace komai ba sai kuma tace “shine zaka wulaƙantani gaban wann...”
“abunda na tambayeki kenan?” ya faɗa babu alamun wasa
“to dan mi suna ci mata matuncin naƙi shigar mata,dan kawai sunga bata da son fitina” kallonta uncle Mustafa yayi “ke me son fita ko?” murmushi ta sakar mashi “ni bazan iya zuba ido a wulaƙanta ta a idona ba”
“da kyau,idan na riƙa ki zaki san bazaki zuba ido a wulaƙanta ta ba” ƴar dariya kawai tayi without saying anything to him.
uncle Hashim ma sallama yayi ma dady,motarshi dake parking space ya shiga,shima ficewa yayi daga gidan zuwa nashi,tun a main parlorn gidan ya shiga kiran sunan Balqis da ƙarfi, har amsawa parlorn sai da yayi,da gudu balqis ɗin ta fito tare da mom maimunatu da Laatifa,da sauri balqis ta nufeshi ai kuwa Unexpected taji saukar mari a cheek ɗinta,da mugun sauri ta dafe cheek ɗin ta tana kallonshi cike da mamaki
“barrister lafiya?” a cewar mom Maimunatu,nuna balqis yayi “wannan yarinyar har ni zata kai ƙara wajen ya Tahir,tasa su tasani gaba shida ya Mustafa suna man faɗa kamar wani ɗan cikin su”
“wane irin ƙara kuma,ke balqis lafiyar ki kuwa??” kuka balqis ta fashe da shi “momy Ni nace mashi hospital ɗin yaya SAM nake so ba nasu ba,amma yace s...” ai bata ƙarasa ba ganin ya yo kanta,da gudu tayi bayan momy ta ɓoye
“kina tunanin dan kin kai ƙarata wajen ya Tahir shine zai sa na haƙura,wallihi kinji na rantse babu ke babu hospital ɗin wacan yaron” wani kallo mom Maimunatu ta shiga yi mashi “wai kai barrister miye matsalarka da SAM ne,dan mi bazaka barta ba,sai kace SAM ɗin ma yana nan ne”
“ina ruwanki da ƴata nake magana,aiki ne dai wacan hospital ɗin baza tayi ba” fashewa balqis ta sake yi da wani sabon kuka
“dan Allah dady kayi haƙuri,momy d...” bata ƙarasa ba saboda tsawar da momy ta daka mata “kar bakin ki ya sake kiran sunana,if not saina tsintsinka maki mari” tana faɗin haka ta tureta daga jikinta, kitchen ta nufa laatifa na bin bayanta,da kallo kawai uncle hashim ya bita dan baƙarim haushi yaji ba data bangaje balqis,yasan ba komai yasa tayi haka ba sai dan yace ba ruwanta,to ai shi ba wai yana nufin karta sa masu baki ba ne.
kuka sosai balqis ɗin take,har cikin ranshi yake jin kukanta,kwata kwata baya son abunda zai ɓata ranta amma bazai iya amincemata tayi aiki a hospital ɗin SAM ba,kallo ɗaya yayi mata ya nufi part ɗin shi.
hawaye ne ke zuba idon mom lallashinta dady yake kan abunda su mamy su ka yi mata amma kamar ba da ita yake ba,kuka kawai take taƙima ta saurareshi
“haba Zulaihart dan Allah kiyi haƙuri kibar kukan nan,su basu isa su tada maki hankali ba,dan Allah kiyi haƙuri”
“yallaɓai yanzu inace kaga abunda nake gudu ko,ina zaman zamana mata ta tada man hankali haka kawai,dama dan saboda su ci man mutunci yasa ku ka dage akan dole sai kun haɗa alaƙa tsakanina da su”
“kinfi kowa sanin bana son ganin ɓacin ranki,wallahi na amince ne saboda ƙara danƙon zumunci tsakanina da ƴan uwana”
“a rayuwata ban san miyi matsala ba ko na nemi abu na rasa,amma mi yasa tunda na Aure ka nake fuskantar matsaloli,laifi ne dan na cika burin soyayya ta,ko laifi ne dan nabi addinin mijina??”
“ko ɗaya ba laifi ki ka yi ba,basu san ciwan kansu bane shiyyasa su ke maki hakan,amma kiyi haƙuri”
hawayen dake zuba daga idanunta ta share
“i want to go US tomorrow”da sauri dady ya kalleta jin abunda tace“why Zulaihart,saboda wannan ɗan saɓanin zaki tafi?”fashe mashi da sabon kuka tayi kamar ƙaramar yarinya mom tana da raunin zuciya abu kaɗan ke ɗaga mata hankali “i said I want to go,I want to see my mom”
“please Zulaihart karki man abunda baki taɓa ba a zaman mu”
“I need my mother's shoulder to cry on, I want to hug her and tell her all my problems” kusa da ita ya matsa, jawota yayi zuwa jikinshi “as long as that will make your mind calm,cry on my shoulder” zame hannunta tayi daga cikin nashi “mamana nake son gani, Please ka barni na tafi gobe”
“haba Zulaihart miyasa za ki man haka,at ur age kin wuce zuwa gida da sunan wai ranki ya ɓaci a gidan mijin ki,duk abubuwan da ki ka fuskanta a baya baisa kinje ba sai yanzu,kinfi kowa sanin momy bawai tana son Auren mu ba ne,miyasa zaki man haka,ko kin gaji da zama da ni ne??” ɗan dakatawa yayi kafin ya kwantar da murya yana sake kama hannunta
“Please kiyi haƙuri komai zai wuce,in dai son ganin momy ki ke nayi maki alƙawarin zamuje tare lokacin birthday ɗin SAM,sai kar muyi celebration a nan sai muje can, Please kiyi haƙuri kinji”lallashinta ya shiga yi dan ta bari sai lokacin birthday SAM su je,amma kamar ƙaramar yarinya taƙi saurarenshi ta kafe akan dole itafa sai taga momynta har cewa dady ta kirata video call amma fir tace itafa ganinta take son yi a zahiri,kallonta kawai yayi,shi kanshi yasanta tanada matuƙar haƙuri yanzunma kasa jurewa tayi ne,dan abunda ake mata a familyn shi da watace da tuni ta rabu dashi,amma tayi haƙuri tsawan shekaru,sosai ya sake kwantar da murya yana bata haƙuri
“please i want to see my mom” iska dady ya fesar,ganin dai ba daina maganar tafiyar za tayi ba ne yasa shi tashi ya fice ya barta,a parlorn ya samu su ya Naeem in da ya barsu zaune,kallo ɗaya yayi masu ya wuce sama, bedroom ɗin momy su ka nufa,suma kwantar mata da hankali su ka shiga yi,su ka yi mata alƙawarin tunda har bata son Auren dole shima Irfan ya haƙura,ta ɗanji sassauci da kalaman su amma bata fasa maganar tafiya gobe ba,suna nan dady ya shigo da waya kare a kunnenshi,miƙa mom yayi,amsa tayi takai wayar kunenta tana kallon shi, Muryar uncle Jonahs ce daki dodon kunnenta “katte mi yasa za kiyi haka da girma ki,ur not a kid fa,dan mi zaki tada hankali shi,idan kin zo taya zaiyi solving matsalar??”
“momy nake son gani Uncle”
“yace nan za kuyi celebration birthday SAM why baza kiyi haƙuri ba,kefa ba yarinya bace ko Carol da ace tana nan baza tayi abunda ki ke ba,yara nawa ne a tsakanin ku?” ɗan kallon dady tayi kafin tace “five”
“five kids amma ki ke wannan abu like Yumnah,you should be patient, everything will be fine”
“thank u uncle”
“bey take care of ur self” jinjina mashi kai tayi,miƙama dady wayar tayi bayan tayi rejecting amsa kawai yayi ya fice.
*UNITED STATE❤*
_*Las Vegas (Nevada)*_
A round 1:30Am ta shiga buɗe idanunta da su ka yi mata nauyi sosai,ta jima da farkawa ta kasa buɗe idanun ne saboda nauyin da su ka yi mata,a hankali ta sauke idanunta kan ceilling,kallon ɗakin ta shiga yi,biji biji take gani,buɗe idanunta ta ɗanyi sosai tana son tuna abunda ya faru da ita da kuma ina ne nan ,idanunta ne suka sauka akan mutum dake zaune saman sofa, scrub suit ne a jikinshi,ya ɗan jinginar da kanshi jikin head ɗin sofa, fuskarshi har time ɗin da facemask,idanunshi ne kaɗai a waje,ɗan lumshe idanunta tayi kafin ta sake buɗe su akanshi,wayace kare a kunnen shi yayinda hannunshi ke riƙe da wani littafi,zuba ma littafin dake hannunshi ido tayi kamar Bible sai dai kuma rubutun dake jikin littafin sun banbanta dana Bible,saurin kallon fuskarshi dake manne da facemask tayi,idanunshi a lumshe su ke kamar mai bacci,kauda kanta tayi zuwa Ventilator machine da drip ɗin dake hannunta,sai a time ɗin hankalinta ya kai ga oxgyen ɗin dake hancinta,fahimtar a hospital take ko medical room ɗin su ne yasa ta fara tuna abunda ya faru,a hankali ta lumshe idanunta zuciyarta na mata wani irin zafi
“she wakeup now I will call you later” ya faɗa yana rejecting call ɗin,bed ɗin da take ya nufa yana ajiye book ɗin hannunshi da waya saman Centre table dake gaban sofa,ventilator machine ɗin ya fara kashewa kafin
a