Showing 24001 words to 27000 words out of 88290 words
ta shiga babu abun da babu a cikin shi,komai da mara lafiya zai buƙata a kwashi a ciki,girmanshi zai kai clinic.
glass drawer dake ɗauke da nau'in magunguna ta nufa,side ɗin da magungunan zazzaɓi dana ciwan kai ta buɗi maganin zazzaɓi dana ciwan kai ta ɗauko mata, mai da ƙofar tayi ta rufe, ƙofar fita ta nufa light ɗin ɗakin ta kashe haɗi da ficewa.
da mom taci karo zata part ɗin dady hannunta riƙe da tea cup wanda ta haɗa ma dady herbal tea.
“ke kuma daga ina?” mom ta faɗa, in da take ta ƙaraso.
“magani na ɗauko ma Nainarh”
“ya Allah!, kinga shaf namanta IRFAN ɗin bai zo ba, gashi yanzu dare yayi da na sa dr lelah ya dubata, jikin nata yayi zafi ne sosai?”
“A'a da sauƙi, damuwace tayi mata yawa”
“dole damuwa tayi mata yawa, yanzu tafi da maganin ki bata” mom ta faɗa tana nufar part ɗin dady.
Kitchen Yumnah ta nufa,hot milk da coffee ta haɗa mata,saman ɗan madaidaicin tray ta ɗaura da maganin,ruwa ta ɗauko mata cikin fridge, ɗaukar trayn tayi ta ficewa zuwa bedroom ɗinta.
kamar yanda ta barta haka ta same ta zaune,ku sa da ita ta zo ta ajiye mata tryan, ɗaya daga cikin chairs ɗin dake ajiye bakin sliding door dake ɗakin ta jawo,zama tayi tana tasa Nainarh gaba.
“gashinan ki sha ko ɗaya daga cikin su ne sai kisha magani”ruwa ta ɗauka da nufin su zata sha,da sauri Yumnah ta girgiza mata kai.
“kar muyi haka dake Nainarh,ki daure kisha hot milk ɗin nan ko da baki sha coffee ba” jinjina mata kai tayi tana ajiye ruwan data ɗauka ta ɗauki milk ɗin ta kafa a baki,da kyar tasha rabin cup ɗin shima Nainarh ta tursasata har ta sha kamar haka.
yumnah da kanta ta shiga miƙa mata maganin tana sha,bayan data kammala tashi tayi ta kai kayan kitchen.
Toilet Nainarh ta shiga,ruwa ta watsa dan taji daɗin jikinta,tana fitowa Yumnah na shiga,wata ƙofa ta nufa,tanƙamemiyar glass drawer ce gari guda,daga waje kana hangen cikinta shaƙe take da sutura kala kala,kowace sutura wajenta daban.
ɓangaren pajamas ta buɗe tsaye tayi tana kallon kayan har Yumnah ta shigo, girgiza kai tayi yayinda take ƙarasowa ciki.
“please Nainarh ki riƙa abu da hanzari,yanzu ɗauko kayan ne ki ka ɗauki lokaci haka”
da kallo kawai Nainarh ta bita har ta ɗauko ma su kayan da zasu sa,riga da wando na saƙa farare ta miƙa mata saboda zazzaɓin da take ne yasa ta ɗauko mata su.
fita Nainarh tayi daga ɗakin,ƴar gown ɗin data ɗauko ta zura a jikinta,baby bant tasa ta ɗauke kanta,ficewa tayi daga ɗakin,samun Nainarh tayi har ta kwanta,itama bed ɗin ta nufa, laptop ɗinta dake ajiye saman night stand ta ɗauka,opreting ɗinta ta shiga yi, video call ne ya shigo ta laptop ɗin.
murmushi ta saki tana faɗin “yanzu nake shirin kiran ka saiga kiran naka” picking call ɗin tayi, a shagwaɓe tace “hey” tana yarfa yatsun hannunta irin na gayu.
Yana daga zaune saman Leather chair,da alama a office yake, Army shirt ce a jikinshi haɗe da trouser ɗinta,sosai rigar tabi shape ɗin broad chest ɗinsa ta bayyanar da strong arms ɗinsa,kallo ɗaya za kayi mashi ka tabbatar da jinshi turawa ne,kyakkyawa ne na gaske,hancinshi a tsaye yake ƙem, blue eyes ɗin shi sai ɗaukar ido su ke, kwantaccen sajenshi baƙi wul sai sheƙi yake,sumar kanshi ta sauka har saman neck ɗinshi,daga yanayin zanen tattoo ɗin dake saman neck ɗin shi da ear ring mai alamar Cross ɗin dake a ƙunnanshi zai tabbatar maka da Addinin shi.
ƙayataccen murmushi ya sakar mata wanda ya ƙara bayyanar da kyawun fuskarshi yana maida mata martanin sallamar da tayi mashi, a shagwaɓe cikin harshen nasara tace “mi yasa baka kirani ba duk yau?”
in a cool voice yace“Am sorry, yayan ki ne yau duk yabi ya takura man” murmushi ta saki
“ko dai ka takura mashi,kai ma fa na san..” murmushi ta saki ba tare data ƙarasa ba,wani irin killer smile ya sakar mata,shagwaɓe mashi fuska tayi kamar za tayi kuka.
cikin shauƙin soyayya su ke waya Nainarh na daga kwance tana sauraronta sama sama kafin bacci yayi awan gaba da ita.
Yumnah ba itace ta gama waya ba sai wajen ƙarfe uku na dare, kusan kullum haka take ɓata lokaci suna waya saboda shi lokacin ne ya ke samun sararin kiranta saboda banbancin lokaci dake tsakanin ƙasashen guda biyu.
*WASHE GARI*
Alhmdllh jikin Nainarh zazzaɓin ya sauka sai ciwan kai da take fama dashi har lokacin gashi har time ɗin Irfan bai zo ba.
kwance take saman bed ita ka ɗai a ɗakin,babu yanda Yumnah ba tayi da ita ba ta zo su fita tayi breakfast tare da su amma taƙi sai dai a kawo mata a ɗaki.
turo ƙofar ɗakin a kayi aka shigo, Yumnah ce ta shigo jikinta sanye da riga da wando masu taushi peach color ta yafa farin mayafin a saman kanta.
cikin ɗakin ta ƙaraso “ki tashi ki shirya mom tace mu tafi hospital Dr Faawar ya dubaki tunda ya Irfan bai zo ba”
yumnah ta faɗa yayinda take nufar toilet,tashi Nainarh tayi tana bin bayanta da ido,bata motsa daga inda take ba har Yumnah ta fito sanye da bathrobe.
“tashi ki shiga” Yumnah ta faɗa,sauka Nainarh tayi daga saman bed ɗin toilet ɗin ta nufa
“ki fa yi sauri kar mom tace tare da wani za ku tafi ko ya Irfan ya shigo”
Dressing room ta nufa,shaf shaf ta shiga shiryawa duk tana wannan saurin ne dan kar wani abu yasa a fasa fitar ko Irfan ɗin ya shigo dan da ƙyar ta samu mom ta amince akan za su je hospital ɗin dan cewa tayi kawai su tafi clinic ɗin dake cikin Estate ɗin ko ta kira dr Faawar ɗin ya zo har gida ya duba Nainarh.
Nocking taji anyi,da sauri ta ƙarasa zura rigar data fara sawa,ficewa tayi zuwa cikin bedroom ɗin har time ɗin Nainarh bata fito ba,ƙofar ta nufa tana faɗin waye.
shiru taji wanda ke Nocking bai Bata amsa ba ba'a kuma fasa Nocking ɗin ba,buɗe ƙofar tayi da ɗan faɗa faɗa tace “wai waye ke neman fasa ma mutane kunne da noc.......”
bata ƙarasa ba ganin wanda ke tsaye,wani kyakkyawan matashi saurayi ne tsaye yana sanye da wandon suit a jikinshi tare da shirt long sleeve mai maɓallai gaba,hannunshi riƙe da briefcase ɗin shi tare da rigar suit ɗin da bai sa ba.
tun daga ƙafafunshi dake sanye cikin leather shoes masu masifar kyau ta shiga kallo ,dogo ne ɗan dai dai fatan jikinshi fara ce tas,yanada broad chest tana iya hangen six pack ɗin shi saboda maɓallan rigar da bai sa duka ba ,hancinshi a tsaye yake ƙem ga wasu idanuwa masu jan hankali farare tas da su,launin ƙwayar idonshi ash color ce, pink lips ɗin shi ba ƙaramin ɗaukar ido su ke ba,yanada ɗan tsayin fuska ga wani kalar kwantaccen saje sai sheƙi yake,kwantacciyar sumar kanshi har saman neck ɗin shi ta sauka, fuskar shi a ɗaure take kamar wanda aka aiko ma saƙon mutuwa.
Tsuke fuska yayi ganin irin kallon da take mashi
“ya Irfan kai ne!!?” Yumnah ta faɗa
“ban sani ba,zaki ban hanya na wuce ko sai kin gama kallon nawa?” da sauri ta matsa mashi,wani wawan tsaki yaja yana kunna kai zuwa ciki.
A tsakiyar ɗakin ya tsaya
“ina yarinyar take?”
“tana toilet” ta bashi amsa,tsaki yaja yana juyawa ya nufi ƙofa
“idan ta fito ina parlorn mom ku same ni a can”
har ya kai bakin ƙofa, Nainarh ta turo ƙofar toilet ta fito jikinta ɗaure da towel iya gwiwarta ta saki sumar kanta har gadon bayanta.
“yawwa gata nan ma ta fito” Yumnah ta faɗa,sai a lokacin Nainarh ta lura da mutum a tsaye,juyowa yayi karab idanunsu suka shiga cikin na juna,tun daga kan shantala shantalan ƙafafunta farare ya fara kallo har izuwa kan pro khaki eyes ɗinta,kafe juna da ido su kayi kamar sun samu TV Yumnah na daga tsaye tana kallon ikon Allah.
Nainarh ce ta fara janye ido ta gabanta na wani irin mummunan faɗuwa,ƙaton namiji a gabanta gashi daga ita sai towel,da sauri ta nufi dressing room ɗin har tana tuntuɓe,da kallo kawai ya bita har ta shige cikin ɗakin,wani irin yanayi yake ji a tattare da shi wanda bai san minene ba.
Tsaki yaja,duk sai yaji haushin kanshi ya rufeshi ko miye a jikin yarinyar da ya tsaya yana kallo shi da kullum cikin ganin ƴan mata yake daban daban wanda su ka fita komai nesa ba kusa ba,duk sai yaji ya tsani kanshi,a zafafe ya juya ya fice yana sake jan wani tsaki.
da kallon mamaki Yumnah ta bishi har ya ɓace ma ganinta, dariya ta kwashe da ita tana nufar dressing room ɗin da sauri, a tsaye ta samu Nainarh gaban clothset ta kasa taɓuka komai jikinta har wani rawa rawa yake.
“wai da baki sa kayan ba,ya Irfan fa baya son jira yana iya tafiyar shi”
shiru Nainarh tayi, girgiza kai Yumnah tayi “na lura ba ƙaramar wahala zan sha ba wajen dawo dake dai dai”
Yumnah ta ɗauko mata kayan da zata sa,ficewa tayi ta bata wuri,shaf shaf ta shirya ta fito,ficewa su kayi daga ɗakin.
parlorn mom su ka je,wayam su ka samu parlorn ba kowa,hakan yasa su ka ƙarasa bedroom ɗin mom ita ka ɗai su ka samu.
“mom ina ya Irfan ɗin?”
“ya fice,ga magani nan ya bata,zo Nainarh,ya jikin naki?” ƙarasawa tayi gaban mom ɗin
“da sauƙi”
“Allah ya ƙara sauki,mi Irfan ɗin yace yana damunki?”
“mom ya Irfan fa bai dubata ba cewa yayi mu same shi a parlorn ki”
“amma yace ya dubata,ɗauko mata ruwa tasha maganin to”
da to Yumnah ta amsa tana ficewa daga ɗakin,dawowa tayi hannunta riƙe da glass cup na ruwa, Nainarh ta miƙamawa,mom ta Bata maganin tasha.
“kwanta ki huta kinji” mom ta faɗa, a saman bed ɗinta Nainarh ta kwanta Yumnah sai complain take ma mom akan Nainarh ta cika sa damuwa a ranta.
*UNITED STATE*
_*Las Vegas (Nevada)*_
*10:00 pm*
A hankali ta zuro ƙafarta dake sanye da flip-flops masu gashi gashi, bathrobe ce a jikinta yayin da kanta ke naɗe cikin short towel da alama daga wanka take.
masu aikinta ne su ka shigo su biyu,juyawa tayi ta nufi ƙofar HOME BEAUTY bin bayanta masu aikin su kayi.
Ɗakin ya haɗu sosai,yana da girma ba laifi,komai na cikin shi unique ne,beauty shelf ne manne jikin bangon ɗakin an jera kayan gyaran jiki kala kala dana gyaran gashi harda foot care product da skin care product masu tsadar gaske,ga wani faskeken mirror a jikin bango tun daga sama har ƙasa ,daga gabanshi tulip chairs ne guda biyu, daga can ɓangaren da skin and foot product su ke lounger chair ce.
nufar lounger chair tayi ta zauna miƙar da ƙafafuwanta tayi tana kwantar da kanta saman head ɗin chair ɗin haɗe da lumshe ido.
ɗaya daga cikin matan ce ta matso ɓangaren skin product ta buɗe, mayuka masu matuƙar tsada ta shiga fito da su,gyaran jiki ta shiga yi mata,cikin ƙanƙanin lokaci fatar jikinta ta riƙa wani glowing tana fitar da wani daddaɗan ƙamshi.
A hankali ta buɗe idon ta,sauka tayi daga saman kujerar ta nufi mirror dake ɗakin,ƙarema kanta kallo ta shiga,ta ɗan ɗauki tsawan mintoci tana kallon kanta a mirror kafin ta nufi ɗaya daga cikin kujerun dake gaban mirror ta zauna.
ɗayar matarce ta nufo inda take,warware mata short towel ɗin dake saman kanta tayi ,nan take sumar kanta ta zubo har saman bayanta,hairdryer ta jawo, busar mata da kan ta shiga yi,bayan data kammala ne ta ɗauko smoothing serum haɗe wide tooth comb,shafa mata ta shigayi tana taje mata kan,saidata tabbatar ya shartu tukun ta shiga kwarara mata hair oils masu daɗin ƙamshi tana cuɗa kan yanda oil ɗin zai shiga ko ina.
Nan take color ɗin kanta light gloden brown ya ciza sai ƙyalli yake da ɗaukar ido ga wani daddaɗan ƙamshi dake fita daga cikin shi.
Straightener ta ɗauka ta shiga miƙar mata da gashi,bayan data ta gama miƙar da gashin,half up half down style tayi mata a kan, ba ita da ake yima gyaran ba hatta su kansu masu gyaran ba ƙaramin tafiya da su kan yayi ba.
Kallon kanta tayi a mirror,ita kanta ta san baƙaramin kyau tayi ba,side smile ta saki, simple make_up su kayi mata,baƙaramin kyau tayi ba.
miƙewa tayi ta nufi wata ƙofa a cikin ɗakin wacce za ta sadaka da dressing room ɗin ta.
Masha Allah na furta a yayin da nayi arba da dressing room ɗin wanda idan ba an faɗa maka a gida ne ba zaka yi tunanin boutique ne,duk wani nau'i na sutura a kwaishi a cikin, hatta jakunkuna da takalma babu abun da babu.
Ƙatuwar wall drawer ce mai ɗauke da sliding door zagaye da ɗakin,daga waje kana iya hangen tarin suturun dake ciki,ɓangaren pajamas da ban,ɓangaren gwon da ban skirts, shorts, underwears, trousers,shirt, sweaters komai da ku ka sani nadaga ɓangaren sutura an ware mashi wajen shi,idan muka koma ɓangaren takalma da jakunkuna abun sai ya baka tsoro,takalma ne da jakunkuna iri iri ga su na.
daga tsakiyar ɗakin half drawer ce ajiye ƙasa doguwa wacce itama marfinta ya kasance na glass, tsawanta ya kusa tsawan ɗakin ta kwance,an kakkasata kashi kashi wanda bakomai ne a cikinta ba sai gold jeweleries,wristwatch, watch chain, watch glass, sunglasses,links,neak chain,rings,babu abun da babu na adon ƴa mace,komai na ciki daga gold sai zinari.
bango ɗaya na ɗakin mirror ne,daga gaban shi stool ne guda biyu masu kyan gaske,zama tayi kan ɗaya daga cikin stool ɗin,masu aikin ne su ka shiga zaɓo mata kayan da za su dace da fitar da za tayi,sun jima wajen ganin sun ɗauko mata kayan da su ka dace,kafin su ka dawo in da take zaune hannunsu riƙe da sexy summer bodycon dress masu matuƙar jan hankali.
gwada kayan su ka shiga yi a jikinta,duk wacce su ka ɗaura saita girgiza kai alamar ba tayi mata ba,haka su ka shiga gwada kayan,aƙalla sun gwada yafi kala ashirin har sun fara gajiya da gwada mata kayan sai da ƙyar su kaci sa'a ta zaɓi wata White color mai one shoulder tana da baza daga ƙasa,bazar taji adon sparkling stones masu matuƙar ɗaukar ido.
A jiyar zuciya su ka sauke ganin sunyi nasarar samarta wacce ta dace don baƙaramar wahala su ka sha ba wajen ɗaukowa da maidawa, ɓangare takalma su ka koma nan ma jido mata su suka shiga yi,duk wanda su ka nuna sai ta nuna baiyi mata ba sai da ƙyar su ka samu ta ɗauki wani high hill Pump black color masu shegen tsini.
Ɓangaren da jeweleries su ke su ka nufa,basu sha wata wahala ba wajen zaɓo mata ɗan kunne da sarƙa sai Agogo da chain ɗin ƙafa.
Turo ƙofar ɗakin a kayi aka shigo tun kafin ta ƙaraso ta san ko wacece ita ka ɗai ce a cikin ma'aikatan gidan ke da lasisin shigowa part ɗin ta ba tare da ta nemi izinin ba, su kansu na'urorin dake sarrafa part ɗin sun san da zamanta.
kyakkyawar matashiyar dattijiwa ce ta shigo,baturiya ce, sai dai duk da manyantar ta hakan bai nuna a fatarta ba,fatarta kamar ba ta tsohuwa ba, kyakkyawa ce ajin farko ,hancinta tsaye yake babu lanƙawasa bakinta ɗan dai dai, launin idonta sak irin na Nailar Acme white grey.
long sleeve shirt ce a jikinta tare da A_line skirt wanda ya wuce gwiwarta,sumar kanta dake da jefi jefi na furfura sai sheƙi take tana ɗaukar ido, simple make_up ne a fuskarta ba ƙaramin kyau yayi mata ba jikinta sai fitar da wani ni'imtaccen ƙamshi yake.
Aunty Sophia kenan ƴar ƙwalisar tsuhuwa ko budurwa bazata gwada mata iya ɗaukar wanka ba wasu abubuwan duk a wurinta masu Aikin Nailar ke koya,ta san ta kan fashion.
In da Nailar take ta ƙarasa fuskarta ɗauke da murmushi wanda yaba dimples ɗin ta damar lotsawa,ta cikin mirror Nailar ke hangenta, Murmushi itama ta sakar mata.
cikin girmamawa masu Aikin su ka shiga gaishe da Aunty Sophia,harara ta ɗan watsa masu da sauri su ka sadda kai saboda sanin laifin su na ƙin faɗa mata Nailar zata fita, hugging ɗin ta tayi ta baya.
“i miss U so much Aunty sopi,jiya shi ne kwata kwata baki nemi ni ba?” Nailar ta faɗa a shagwaɓe kamar ba ita ba, murmushi Aunty Sophia tayi tana miƙewa tsaye haɗi da juyo da stool ɗin da Nailar ke zaune.
“my baby na shigo fa kina bacci,bana son na takuraki ne shiyyasa na fice”
ɓata fuska Nailar tayi “dama na san babu wanda zai kashe man ear phone sai ke”
“nayi laifi kenan?” taɓe baki Nailar tayi“ dan kin san baki laifi a wajena shiyyasa ki ke yanda ki ka ga dama”
ƴar dariya Aunty Sophia ta saki wacce ta bayyanar da kyawawan haƙoranta.
juya mata baya Nailar tayi tana turo baki,kallon masu Aikin tayi da ido tayi masu alamar su fice,kayan dake hannunsu su ka ajiye saman table su ka fice.
cikin ɗakin Aunty Sophia ta nufa, ɓangaren underwears ta nufa,bandeau style top ta ɗauko mata haɗe boyshorts masu matuƙar jan hankali white color.
dawowa tayi wurin Nailar,miƙa mata tayi “am sorry idan na ɓata ran Queen,ga wannan kisa sai na idasa shirya gimbiyata da kaina” turo baki Nailar tayi
“ni bazan iya sawa ba” ɗan zaro ido Aunty Sophia tayi
“ƴata fa yanzu budurwa ce dole ta koyi wasu abubuwan da kanta ba sai masu aiki sunyi mata ba”
tashi Nailar tayi sai ɓata fuska take ta amshi kayan dake hannun Aunty Sophia, murmushi Aunty Sophia ta saki,cikin ɗakin ta nufa sai turo baki take.
saman ɗaya daga cikin stool ɗin Aunty Sophia ta zauna tana sakin murmushi ita ka ɗai ke kema Nailar haka a zauna lafiya,tana da matuƙar ƙima a idanun Nailar a kwai soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, Nailar ta ɗauketa tamkar mahaifiyarta tun tana ƴar ƙaramarta Aunty Sophia ke kula da ita Nanny ɗinta ce hakan yasa su ka shaƙu,wani lokacin har cewa masu Aikin gidan keyi suna kama.
Dawowa Nailar tayi in da Aunty Sophia take ta cire bathrobe ɗin pant da bra ɗin ne kawai a jikinta, a gaban Aunty Sophia tazo ta tsaya,da sauri Aunty Sophia tasa hannu ta rufe fuskanta hakan da tayi ba ƙaramin dariya yaba Nailar ba.
“baby ya kamata ki riƙa