Showing 18001 words to 21000 words out of 88290 words

Chapter 7 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

409

Alhmdllh” ta faɗa, gaishe da laatifa tayi cikin kulawa laatifa ta amsa mata Balqis tunda su ka shigo parlorn kallo ɗaya tayi ma nainarh ta ɗauke kai
“amma kin sha magani kuwa?” laatifa ta faɗa cikin nuna kulawa
“A'a” nainarh ta faɗa tana nufar rug carpet zata zauna saboda wani jiri da take ji, da sauri momy ta nuna mata kusa da ita tace ta zauna.

sannu su ka shiga jera mata mom na faɗin“bari idan IRFAN ya shigo ya duba ki, yumnah kira man shi a waya kice nace idan ya taso daga aiki ina son ganin shi”


da to yumnah ta amsa tana ɗaukar wayar ta ta shiga contact, number Irfan ta shiga nema, dialing number tayi ringing ta shiga yi har ta katse bai ɗaga ba, sake kira tayi sai da ta kusa katsewa ta samu sa'a yayi picking,sallama tayi tana gaishe da shi babu wanda ya amsa mata daga ciki sai cewa yayi“ lafiya ki ke man irin wannan kiran?”


shagwaɓe fuska yumnah tayi kamar tana a gaban shi
“dama mom ce tace idan ka ta so daga aiki ka shigo gida tana son ganinka” rejecting kiran yayi kawai ba tare da yace komai ba, taɓe baki yumnah tayi.

masu aiki ne su ka shigo hannun su ɗauke wooden tray, soft drinks ne da ruwa masu sanyi haɗe da glass cups, cikin parlorn su ka ƙaraso bakin su ɗuke da sallama, amsa masu sallama su kayi,ajiye tryas ɗin su kayi saman glass round table ɗin dake parlorn, ficewa su kayi, fa'iza ce ta shiga zuba masu ruwan da lemu ta miƙa masu.


masu aikin suna fita daga parlorn ɗaya kitchen ta nufa yayin da ɗaya ta nufi elevator, da sauri ƴar uwarta tace“munirat ina za kije?”
“part ɗin mamy ”wacce aka kira da munirat ta faɗa, girgiza kai wacce ta kira munirat ɗin tayi tana faɗin


“munirat ina rabaki da kiwan kyalla kina akuya ta haihu, wallahi ki daina shishige ma mamy, dan wallahi za kiyi da kin sani dan ita ba'a mata gwaninta ina guje maki ranar da zata shuka maki rashin mutunci”


“banji bakin ki ba, kuma ni bani ke shishige mata ba itace ke jana a jiki”
“na dai faɗa maki dan idan baki san abun da ya faru da baaba jummai ba gara tun wuri ki sani”

“ni dai naji,yanzu zan dawo” ta faɗa tana daddana madannan dake jikin elevator, girgiza kai kawai ƴar uwar tata tayi tana nufar kitchen...


_*Episode 9_10*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘


______________________________






A kishingiɗe take saman makeken king size bed ɗinta ta ɗauki wankan rantsatsiyar shadda white color anyi mata aiki da red color ɗin zare, fuskarta tasha make_up a ko wane lokaci zaka samu hannuwanta da wuyanta da ƙafarta cikin adon gold ko zinari, kanta babu ɗan kwali gashin Attachment ɗin dake kanta ya sauka har gadon bayanta,wayarta ce a hannunta tana aikin daddanawa.



Nocking ƙofar bedroom ɗin a kayi,yamutse fuska tayi cike da izza tace “waye?”


ɗan ɗaga murya munirat dake tsaye bakin ƙofar tayi “munirat ce mamy”
“ke da waye ne?” mamy ta faɗa
“ba kowa ni kaɗai ce”
“ok shigo”mamyn ta faɗa.


a hankali munirat ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama,ƙaremata kallon mamy ta shiga yi tun daga sama har ƙasa, a bakin bed ɗin ta tsaya,cike da girmamawa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da mamy.


ƙin amsa mata mamy tayi sai ma cewa tayi “ina sauraronki mi ya kawoki ɗakina?”ta faɗa tana wani yamutse fuska.


“dama zuwa nayi na sanar dake hajiya maimunatu matar yallaɓai hashim ta zo ita da ƴaƴanta suna part ɗin madam zulaihart”


“mi su ka zo yi”mamy ta faɗa tana wani tsuke fuska
“nima ban sani ba amma ina tunanin sun zo yima madam jaje ne”


jinjina kai mamy tayi“naji daɗin jin wannan labari da ki ka zo man dashi, abunda nake so dake ki sa man ido akan kowa dake part ɗin komai ki ka gani ki sanar dani, komai ƙanƙantar abu ki sanar da ni”


“in sha Allah madam” jinjina kai mamy tayi“yawwa haka nake son ji, tashi ki tafi bana son janar ya shigo ya sameki, zan tura maki saƙon ki ta waya” miƙewa munirat ɗin tayi “nagode sosai Allah ya ƙara girma”ta faɗa tana nufar ƙofar fita ta fice.


tsaki mamy taja tana faɗin“munafuncin banza ko miye abun zuwa jaje in ba tsabar tsugudidi ba” mamyn ta faɗa tana sake jan wani tsakin.


wayarta ta ɗauka tayi dialing wata number, bugu biyu a ka yi picking, murmushi ta saki yayin da take kara wayar a kunenta.



“Allah ya taimaki first lady,hutawar ki lafiya hajiyar yallaɓi Ahmad”mamy ta faɗa ta na sakin dariya,on the other hand ta cikin wayar itama dariya ta saki.


“kullum da kalar tsokanar da ki ke zuwa MABARUKA, yau kuma ni ki ke ma wannan kirarin?”
“ai kin can canta ne, ya ki ke ya kwana biyu?”
“Alhmdllh, fatan kema kina lafiya, ina madam ɗinki take?”


taɓe baki mamy tayi “tana nan kamar yanda ki ka santa,ban ma baki labari ba”


“ina jinki mi ya faru?”
“uhmm ina wannan shari'ar da suke akan ƙawarta wannan munafukar hajiya Asma'un?”


“eh na gane ,ɗazu naji WASEEF na mata jaje wai an yankema hajiya Asma'u hukuncin ɗaurin rai da rai”
“eh ashe kinji?”


“naji waseef na mata jaje kin san ni ba ma'abociyar bibiyar labarai bace”
“ai kuwa kamar yanda ki ka ji an yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai”



“tab! Allah ya kyauta gaba,ki ce yau ku baku ba walwala”
“bata ba walwala dai, kema kin san babu abun da zai hanani walwala dama abun da na daɗe ina jira kenan dan wallahi ba ƙaramin jin haushin Asma'un nan nake ba”


dariya mai ɗan sauti ta cikin wayar ta saki “duk da haka da kinyi mata kara ai zaman tare baice haka ba”


“wa ni? Allah ya ki ya ye dama ta dawo magana na samu na nannausa mata na san sai ta da ɗe tana damunta”

dariya ta cikin wayar ta sake saki “gaskiya mabaruka baki da kir ki, mai makon ki taya ta ja je shine zaki ɓige da gaya mata magana”


“Allah ya ki ya ye ai ga abokan cin mushenta can ɗayar har ta zo wai ja je ɗayar munafukar ma na san tana nan zuwa anjima”


“baki da dama mabaruka, nima anjima ko gobe zan shigo nayi mata ja jen”


taɓe baki mamy tayi“ai da yake ke akwai kara a tsakanin ku”

“to ya zanyi tunda Allah ya haɗa Auratayya a tsakanin ƴaƴan mu dole ne zumunci ko bama so”


“Allah ya kawo ki lafiya” da Ameen ta cikin wayar ta amsa, sallama su kayi.

wata number mamy ta sake dialing, ringing wayar ta shiga yi, sai da kiran ya kusa katsewa sanann a kayi picking, murmushi mamy ta saki tana faɗin


“kaga abun gidan janar, halama bacci ki ke nake kira ba'a picking in time”

on the other hand ta cikin wayar tace “ina fa na shiga kitchen ne wurin masu aiki, kin san idan baka sa masu ido sai suyi maka shirme”

murmushi mamy ta saki“ kice kina can kina gasa masu aya a tafin hannu dan na san halinki ba sauƙi ne dake ba”


“duk rashin sauƙina na kai ki ne?”

“ai wallahi masu aikin ne sai da jan ido, idan kayi sanya sai su kawo maka raini”

“haka ne kam,to ya gidan, ya kwana biyu fatan kina lafiya??”


“lafiya lau Alhmdllh, ya naki gidan”

taɓe baki mamy tayi“ yana nan yanda ki ka san shi sai ma abunda ya ci gaba” murmushi ta cikin wayar ta saki
“ki ce kina nan kin hana dangin nasara masu jan kunne sakat”


“mi za'a fasa, ai in dai ina raye ta shiga uku”
“Allah ya shirya man ke ƙawata, ki zo ki samu mata a har gidan mijinta ki hanata rawar gaban hantsi”


“tama isa, wanda yace tayi sakacin da mijinta yayi mata kishiya”
“kina sha'aninki ta wajena, wai ni kam ɗazu nake gani a TV an yanke ma ƙawarta hukuncin ɗaurin rai da rai”


“eh Allah yayi maganin ɗayar munafukar saura manyan, kin san kuwa ɗayar harta kwaso ƙafa ta zo jaje??”


“wa ki ke nufi?”

“wacece kuwa ban da uwar ƴan tausayi maimunatu” tsaki ta cikin wayar taja

“munafukan banza kawai, na san ɗayar munafukar ma tana nan zuwa”


“wannan a rubuce take sai ta zo”
“wallahi haushi hajiya maryam ke bani, sai girman kan masifa”


“ai wallahi bake kaɗai take ba haushi ba, wani lokacin idan tana hura hanci tanama mutane kallon banza ji nake kamar na rufeta da duka”

“ke dai ki bari mai abun duniyar ma batayi ji da kai ba sai ita”


“za ki shigo anjima?” mamy ta faɗa
“mi zan zo nayi”
“ai nayi tunanin ko zaki zo mata ja je”


“wa ni? Allah ya ki ya ye, lokacin da hajiya Asma'un zata kashe mijinta shawara tayi dani da zan zo mata ja je, ai in kin ganni lahira to kaini a kayi”


dariya mamy ta saki “shiyyasa nake sonki ƙawata, yanzu na gama waya da hajiya SALIMA ta ce zata zo”


“ita ki ka ce ji tayi zata iya”
“ai kin san so akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin su”

“wace alaƙa?, daga ɗanta na Auren ɗiyarta shikenan ko dan IRFAN na hannun mijinta, ni ba NAEEM bane ke Auren NAFISAT, ke ni bazan iya ba alaƙar Aure ma dake tsakanin nafisat da naeem dan bani da yanda zanyi ne amma wallahi da ba'ayi Auren ba”



“nima dai haka na gani”
“rabu da ita kawai sai mun haɗu ranar juma'a a part ɗin Abba”
“ok Allah ya kaimu” da Ameen matar ta amsa sallama su kayi.



𝑸𝒖𝒆𝒆𝒏 𝑲𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒕💫




Mom da momy ne kawai babu a parlorn, Yumah na kusa da laatifa sai zuba mata zance take yayin da balqis da fa'iza ke zaune saman sofa suna firar yaushe gamo.


tashi Nainarh tayi ta nufi bedroom ɗin Yumnah,da sannu su laatifa su ka bita balqis kuwa banda binta da kallon tsana babu abunda take, haka nan taji bata son Nainarh ita kanta bata san dalili ba amma taji ta tsaneta.



Sallama su ka ji daga bayan su da sauri su ka kai duban su ga matar dake shigowa, ta ɗau wanka baƙar Abaya tayi rolling da gyalenta,da gudu Yumnah ta nufeta hugging ɗinta tayi tana faɗin“momy kema ashe kina hanya” murmushi matar ta saki tana raba jikin su



“wani ya zo kenan da har ki ke tunanin nima ina hanya” murmushi Yumah ta saki “momy ma ta zo tare da su Aunty laatifa” ta faɗa yayin da su ke ƙarasowa cikin parlorn, cike da girmamawa su laatifa su ka shiga gaishe da matar tana amsa masu cikin kulawa yayinda take hugging ɗin su ɗaya bayan ɗaya.




“su mom na garden ita da momy” Yumnah ta faɗa
“ok bari na ƙarasa wajen su” ta faɗa yayinda take nufar sliding door dake parlor wacce daga nan kana iya hangen cikin garden ɗin da kusan zagaye yake da gidan.





shuke shuke ne a cikin a garden ɗin masu matuƙar ɗaukar hankali da ban sha'awa,ga grass carpet dake malale a cikin garden ɗin,ƙaton swimming pool ne a cikin garden yayinda aka ƙawata gafe da gefenshi da lounger chairs da deck chair masu kyan gashe domin zama,ducks ne ke shawagi a cikin swimming pool ɗin farare tas da su,daga can gefen swimming pool ɗin wasu rukunin bishiyu ne masu matuƙar ɗaukar hankali sunyi rukuni,peacocks ne masu kyan gaske ke yawo tsakanin bishiyun,babu kalar tsuntsun da babu a cikin garden ɗin.


A tsakiyar bishiyun mom Maryam ta hango mom da momy kishingiɗe saman rug sun yi matashi da tum tum yayin da aka cika masu gaban su da fresh fruit cikin kwandon kaba haɗe da snacks da soft drinks masu sanyi.


Momy ka ɗaice ta ɗan gatsi Apply yayin da mom ta zuba ma ducks ɗin dake shawagi cikin ruwa ido,damuwar halinda Aminyarta take ciki ce duk ta isheta ,bata so duniya ta juya mata baya lokaci guda ba.


“ki kwantar da hankalin ki barisster in sha Allah babu abun da zai faru da Asma'u,ina sha Allah zata kuɓuta su kuma wanda su kayi silar jefata cikin wannan halin da izinin Allah asirin su zai tonu”


Ajiyar zuciya mom tayi

“babu abunda yafi ɗaga man hankali sama da yanda jami'an tsaro da mutanen gidan su ka kafe akan ita ta kashe shi, ni na san wacece Asma'u ko dabba bazata iya kashewa ba bare ɗan Adam”


“nima a iya sani na da ita bazata iya aikata wannan babban laifin ba amma in Sha Allah gaskiya za tayi halinta”
“ina fatan haka”



fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso in da suke, sallamarta su ka ji daga bayan su ,da sauri su ka kai duban su gareta, murmushi su ka sakar ma juna yayinda su ka miƙewa, hugging ɗin juna su ka shiga yi cike da kulawa suke gaishe da junan su,kalar ta su gaisuwar kenan a duk lokacin da su ka haɗu da juna.

saman rug ɗin su ka koma su ka zauna,sake gaisawa su kayi

“ya kuma mu ka ji da abun da ya faru da Asma'u” mom Maryam ta faɗa
“sai godiyar Ubangiji” momy ta faɗa
“Allah ya kuɓutar da ita”
“Ameen ya Allah” mom ta faɗa yayin da take ɗaukar sherry glass cup ta zuba ma mom maryam drink mai sanyi, miƙa mata tayi , murmushi mom Maryam ta saki ya yinda take amsar cup ɗin.


shiru ne ya gitta a tsakanin su,kowa da abunda yake saƙawa a ranshi ba kamar mom da kwata kwata bata cikin walwala,mom maryam ce ta katse shirun na su.


“amma barisster kin ɗauki wani mataki a kan shari'ar nan?” ta faɗa ya yinda take ajiye cup ɗin dake hannunta.


“ban fahimci ya ki ke nufi ba ,wane mataki zan ɗauka??”
mom ta faɗa cikin rashin fahimtar Abun da mom maryam ɗin take nufi.


“ai nayi tunanin zaki sa ayi maki bincike na daban akan case ɗin,idan Allah yasa aka dace kinga ba sai a tada shari'ar ba tunda hukuncin ɗaurin rai da rai ne”

“wane bincike zan sa ayi bayan wanda barisster Hashim yayi”

yana yin fuskar mom maryam me ya canza “uhmm barisster hashim fa ki ka ce?”


“eh shine lawyer dangin marigayi ,duk wani bincike da ya kamata ayi yayi”

“kenan kin yarda ita ta kashe mijinata?”


“A'a sai dai na san barisster ba zai faɗi abunda ba shikenan ba, kuma bana zargin zai haɗa kai da kowa dan kawai yayi nasara a kaina”

girgiza kai mom maryam tayi,mom Maimunatu na kallon su ƙala ba tace ba


“am sorry hajiya Maimunatu ba wai ina zargin barisster ba ne” murmushi kawai mom Maimunatu tayi ko zargin barisster su ke ya za tayi halin mijin nata ne dole a zargeshi.


“mu duka mun san cewa barisster baya ƙaunar zulaihart tun fil'azal, ni bana zargin zai iya haɗa kai da wasu dan dai kawai ya cika burin shi akan barisster,amma ƙara binciken da za kiyi yanada matuƙar amfani ni a nawa tunanin amma ya ku ka gani”


shiru mom tayi tana tsunduma duniyar tunani ta wani ɓan garen hajiya maryam na da gaskiya sai dai bata son ta binciko ma kanta abunda zai hanata zaman lafiya duk da har zuciyarta bata zargin Aminyarta zata aikata laifi makamancin haka.


“maganarki gaskiya ce hajiya maryam,ƙara binciken yanada amfani,sai dai waye zaiyi binciken?” mom Maimunatu ta faɗa


“haka ne ƙara binciken yanada amfani, Allah yasa ya zama sanadiyyar tonuwar asirin duk wanda ke da sa hannu,sai dai ta maganar Maimunatu wa zan sa yayi man binciken?” mom ta faɗa

“yawwa burina dama ku fahimce ni, maganar kuma wanda zaiyi binciken ba matsala bace karku manta gidan nan cike yake da jami'an tsaro kala kala samun wanda zaiyi bincike ba abun bane mai wahala NAEEM ma zai iya tunda dama aikin shi ne”

jinjina kai su kayi da alama sun aminta da maganar mom maryam

“shikenan zan samu lokaci mu zauna da shi,zanyi mashi bayanin yanda case ɗin yake” mom ta faɗa


“yawwa hakan yayi ,sai dai fa ya zamana cikin sirri zaiyi shi, kuma kar ya sanar a wajen aikin su yayi shi parsonal,duk da na san aikin su dama na sirri ne sai dai wannan ya ɗauke shi a matsayin na gida bana aiki ba” mom maryam ta faɗa


“in dai wannan ne ba matsala”a cewar mom , murmushi mom Maimunatu ta saki


“shiyyasa nake sonki hajiya maryam akwai kawo shawara mai ɓullewa” murmushi su ka saki gaba ɗayan su


“abun ne wallahi ya taɓa zuciyata,baiwar Allah nan babu ruwanta amma ace lokaci guda wani ya dabaibayeta da sharri,su barta mana taji da zaluncin kashe mata miji da su kayi mana ba sai sun manna mata kisan a kanta ba”


“gaskiya ko waye ba ƙaramin cutar da ita yayi ba” firar su suka shigayi suna alhinin abunda ya faru da ƙawar mom.



𝑸𝒖𝒆𝒆𝒏 𝑲𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒕💫



A tsaye take a gaba motar ta ƙirar honda Black color, blue black ɗin Abaya ce a jikinta ta yafa gyalen saman kanta,hand bag ɗinta ce riƙe a hannunta,cikin faɗa faɗa take faɗin
“Enaaya wai zaki fito ne ko sai nayi tafiyata?”


daga cikin motar naji Muryar yar ƙaramar yarinya tana faɗin “momy gani nan fitowa hand bag ɗina zan ɗauka”


tsaki matar taja “ko uwar mi za kiyi da hand bag,ni kinga tafiyata idan kin gama kilibibin naki kya shigo” matar ta faɗa tana nufar entrance ɗin gidan.


da sauri wata ƴar ƙaramar yarinyar ta fito, Black ɗin abaya ce a jikinta tayi rolling da gyalen, simple make_up ne a fuskarta yayin da kyawawan idanunta ke manne da ɗan sunglasses dai dai idonta mai butterfly,ƴar hand bag ɗinta ce riƙe a hannunta,highills ne a ƙafarta ba ƙaramin kyau tayi ba.



bayan mahaifiyarta ta tabi tana wani tako ɗai ɗai kamar wata uwar mata,a main parlor part ɗin ta samu mahaifiyarta tana jiranta,glass elevator dake part ɗin mom yarinyar ta nufa da sauri mahaifiyarta ta tace.


“ENAAYA ina kuma za kije?” ya mutse fuska yarinyar tayi tana faɗin “part ɗin mom mana”ta faɗa cike da yanga
“muje mu fara gaishe da mamy tukun” mahaifiyar ta faɗa tana nufar part ɗin mamy,juyawa yarinyar tayi tana faɗin

“ni gaskiya bazanje part ɗin mamy ba,haka nan kawai ta rufe mutum da faɗa ba abunda yayi mata,kuma Ni dady nake son nunama wannan kwalliyar dan karma sister ta rigani,sai kin dawo kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login