Showing 30001 words to 33000 words out of 88290 words
Chapter 11 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
wacce su kayi Auren soyayya bana ƙiyayya ba,wasu zafafan hawayen ne suka sake wanke mata fuska.
da jan jiki ta sauko daga saman bed ɗin,blanket ɗin dake shimfiɗe taja ta rufe jikinta,a daddafe ta nufi ƙofar fita, ficewa tayi daga ɗakin, a hankali take tafiya tana ƴan waige waige gudun karta haɗu da wani ko masu aikin gidan su ganta a irin wannan yanayin, Allah ya taimaketa har ta kawo bakin ƙofar wani ɗaki bata haɗu da kowa a hanyar ba, tura ƙofar ɗakin tayi ta shige,mai da ƙofar tayi ta rufe da key,a jikin ƙofar tabar key ɗin,yara ne ƴan maza guda biyu kwance saman makeken bed ɗin dake ɗakin cikin shigar PJ white color, sai sharar baccin su suke hankali kwance.
Ƙofar toilet ta nufa, tsarkake jikinta tayi,sannan ta gasa jikinta da yayi mata tsami, bathrobe ta zura a jikinta ta fito,zuwa tayi tsakiyar yaran ta kwanta bayan ta kashe light ɗin ɗakin,hugging ɗin yaran tayi ajikinta yayinda hawaye ke sintiri zuba daga idanunta, tsawan shekara goma kenan da yin Auren su,shekara ɗaya kawai su kayi suna shan soyayya amma tun daga nan komai ya lalace kullum cikin fuskantar azaba take daga Zaabith duk wasu munanan halayenshi babu wanda bai nuna mata ba, ya fita gida sai sanda yaga dama zai dawo,idan ya koma wajen Aiki Lagos sai yayi wata da watanni bai dawo ba duk ranar da zai dawo a buge yake dawo mata kuma a ranar ta shiga uku, iyayenshi sunyi faɗa sunyi faɗan sunyin jan hankalin amma a banza,duk da fara tara iyali da su kayi bai sa ya canza halayen shi ba.
tayi tunanin zaman su a gidan gomnati zai sa ya canza ɗabi'un shi kodan gudun zubar mutuncin mahaifin shi da siyasarshi a idon duniya,amma a banza saima abun da yaci gaba gashi duk wannan uƙubar da take ciki ta kasa sanar da iyayenta duk dan gudun lalacewar zumunci dake tsakanin su saboda mahaifin Zaabith yaya ne ga mahaifinta uban su ɗaya.
ta jima tana saƙawa da kwancewa har baccin wahala yayi awan gaba da ita rungume da ƴaƴanta, lokacin da ya fito daga toilet ɗin ƙugunshi ɗure da towel, kallon gadon daya barta a kwance yayi, ganin wayam bata nan me yasa shi jan wani mahaukacin tsaki yana faɗin “zan kamaki ne yarinya”.
ƙofar fita shima ya nufa, ficewa yayi daga ɗakin zuwa master bedroom ɗin shi, yana shiga ɗakin a saman gadon shi ya faɗa rub da ciki babu Adu'a babu komai,cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi.
*WASHE GARI*
Tunda Asussu ba ta koma ɗakinta ta gyara gudun masu aiki su ganshi haka bata son su zargi wani Abu,duk da irin azabar da take sha a wajen shi har kawo wannan lokaci tana son shi tana kuma yi mashi kallon uban ƴaƴanta, Adu'arta a kullum Allah yasa ya gane kuskuren da yake aikatawa.
shaf shaf ta gama kauda komai,toilet ta shiga wanka tayi haɗe da Alwala,fitowa tayi ta nufi cloth set ɗin ta,doguwar rigar Abaya ta ɗauko ta zura a jikinta,da ƙyar ta zura rigar a jikinta saboda ciwukan da taji a dalilin dukan da yayi mata duk ya faffasa mata baya,sawun duka har saman wuyanta ga marin da yayi mata, ta san dole sawun hannunshi ya fito.
a saman kai ta ɗaura mayafin Abayar tukun ta ɗauko hijab,ficewa tayi daga ɗakin dan ta san a kowane lokaci zai iya dawowa.
Bedroom ɗin yaranta ta koma,a kwance ta same su kamar yanda ta barsu, tashin su ta shiga yi domin lokacin sallah yayi,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga toilet su ka ɗauro Alwala,jallabiya ta ɗauko masu cikin kayan su, cire PJ ɗin dake jikin su suka yi suka zura jallabiya.
“momy Dady ya dawo ko??”faɗuwa gabanta yayi dalilin tambayar da yaron yayi mata.
“Eh ya dawo tare ma za ku tafi masallaci,yana ɗakin shi kuje ku same shi”
“momy shine ya dake ki ko” faɗuwa gabanta ya sake yi
“shine ko momy??” yaran su ka sake jefa mata tambayar
saurin ƙaƙalo murmushi tayi tana girgiza masu kai alamar A'a
“shi ne mana momy,ga sawun duka nan a fuskar ki”
“faɗuwa nayi Ammar ba duka bane”
“duka ne mana,gashi nan sawun hannunshi ne a saman fuskar ki”
“momy mun gaji da dukan ki da dady yake,sai mun rama maki dukan da yake maki yaji shima idan da daɗi,kuma sai mun sanar da grandfa har yanzu bai daina dukanki ba”
duk yanda take daurewa kasawa tayi hawaye ne su ka wanke fuskarta,tun tana ɓoye masu yanzu yaran babu abunda ba su sani ba game da irin zaman iyayen na su.
hanyar fita su ka nufa suna sai sun faɗama grandfa Aman har ya fara zubar da hawaye,da sauri tabi bayan su,jawo su tayi zuwa jikinta, hugging ɗin su tayi.
“kuyi haƙuri Aman kar ku sanar da dady Ahmad,dadyn ku bada gangan ya mareni ba ya bani haƙuri bazai sake ba”
“momy kullum haka yake faɗa,amma har yau bai daina ba,kinga da gangan yake dukan ki”
“duk da haka Ammar shi ɗin fa mahaifin ku ne,idan baku rufa mashi asiri ba waye zai rufa mashi,kuyi haƙuri kunji ko,ku yafe mashi nima na yafe mashi”
sake shigewa su kayi jikinta suna sakin kuka,wasu hawaye ne itama su ka wanke fuskarta,ɗan bubbuga bayan su ta shiga yi
“ya isa haka ku daina kuka kun ji,zai daina wata rana” raba jikin su ta yi,hannu tasa ta shiga goge masu hawayen fuskar su.
“kuje yana ɗaki ku same shi” maƙe mata kafaɗa su kayi
“mu dai tare da grandfa zamu tafi da su uncle Waseef”
“ki bar mu kawai momy muje tare da grandfa”
“shikenan sai kun dawo,Allah yayi maku Albarka”
da Ameen su ka amsa suna nufar ƙofar fita,turo ƙofar ɗakin da a kayi ne ya dakatar da su,gaba ɗayan su suka kai dubansu gare shi.
farar jallabiya ce a jikinshi,jikin shi da alamar danshin ruwan da yayi alwala,cikin ɗakin ya ƙaraso,hannuwan shi biyu ya buɗe ma yaran alamar su zo gareshi fuskar shi a sake.
tsuke fuska su kayi suna bin shi da wani irin kallon tsana,lamarin yayi matuƙar ɗaure mashi,da sauri ya kai duban shi ga kainart dake tsaye tana kallon su,saurin kauda kai tayi kamar ma bata ga abun da su Ammar ɗin su kayi mashi ba.
ta gefen shi su ka zo za su wuce,saurin kamo hannun su yayi,wayancewa yayi irin kamar ma bai fahimci mi yaran su ke nufi ba “ fushi ku ke da dady saboda bai dawo da wuri ba,kuyi.....” bai ƙarasa ba saboda fisgewa da su kayi daga riƙon da yayi masu,ƙofar fita su ka nufa ba tare da ko sun kalli inda yake ba,baki ya saki kamar saka rai wai yau shine su Aman su kayi ma haka,mi hakan ke nufi mahaifiyar su ta fara hure masu kunne ke nan.
yana nan tsaye har su ka ɓacce ma ganin shi,jinjina kai yayi yana nufo in da take,da sauri ta ɗauki hijab ɗin ta zata zura a jikinta,a zafafe ya fisge hijab ɗin yayi jifa da ita,damƙara sumar kanta yayi,rintse ido tayi saboda zafin daya ziyarci kanta.
“wato raini ya fara shiga tsakanin mu ko,har kin fara tara yara kina gaya masu ina dukan ki ko,a tunaninki dan kin sanar da su hakan zai canza wani Abu ne,ki sani a duk faɗin duniyar nan babu wani wanda ya isa ya hanani abun da nayi niyya ko da kuwa mahaifina ne,dan na san shi ki ke tunanin zai iya hanani??”
cikin ƙunar rai tace “a tunanin ka ya Zaabith su Ammar ba su san abun da ka ke aikatawa ba ne?,ko a tunaninka ba su da wayan sanin abun da kake aikatawa ,karka manta kasha dukana a gaban su dan mi baza su ji haushin ka ba,nifa mahaifiyar su ce”
fisgar kanta yayi kamar zai cire shi gaba ɗaya “to sai mi dan sun sani,ke baki isa ki shiga tsakani na da su ba saboda ni ɗin mahaifin su ne ko suna so ko basa so”
fashewa tayi da kuka
“kaji tsoron Allah ya Zaabith,ka sani alhakin mu bazai barka ba,Allah zai saka m...” tsawa ya daka mata
“ya isa haka” ya faɗa yana sakin gashin kanta,idan da abun da ke tada hankalinshi ta furta Allah zai saka mata baya son tana barin shi da Allah, yana tsoron ranar da Allah zai tashi saka mata.
ƙofar fita ya nufa,da kallo ta bishi har ya fice hawaye sai sintiri suke a fuskarta.
hijab ɗinta ta zura, prayer mat ta shinfiɗa,gabatar da sallah ta shiga yi,ta jima zaune tana kai ku kanta ga Ubangiji sammai da ƙassai.
Tana a nan kwance a kayi Nocking ɗin ɗakin, tambayar waye tayi ba tare da ta tashi ba.
“saraj ce dama madam Salima ce tace ki fito time ɗin breakfast yayi,takuma ce anjima za ku je can family house ɗin ku”
“bana jin daɗi sarah,ki kawo man nawa breakfast ɗin nan kawai”
“to shikenan,ya zance ma Madam ɗin?”
“ki faɗa mata bana lafiya”
“to shikenan” mai aikin ta faɗa tana barin wajen,bayan kamar minti biyar mai aikin ta dawo.
iznin shiga Kainart ɗin ta bata,a hankali ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta ɗauke da tryan data haɗa mata breakfast ,saman ɗan table ɗin dake ɗakin ta ajiye mata.
“sannu madam,Allah ya baki lafiya”
“Ameen sarah,su Ammar na wajen dady ne?”
“eh suna can harda yallaɓai Zaabith”
“ok shikenan zaki iya tafiya”
“ok Allah ya ƙaro sauƙi” da Ameen kainart ɗin ta amsa,ficewa mai aikin tayi.
* Big Daddy's house*
Mom da ya Naeem ne zaune a saman gondola chairs dake cikin garden ɗin gidan,ɗan madaidaicin glass table ne a gaban su an cika masu shi da fresh fruit haɗe da snacks, yayin da mom ke riƙe da wasu takardu a hannunta sai jujjuyasu take,
kallonta ya Naeem yayi “mom kinyi shiru ba kice komai ba?”
ɗan sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon ya naeem ɗin daya kafeta da idanu,takardun dake hannunta ta miƙa mashi
“ban san ta in da zan fara maka bayani ba ne naeem”
“koma ta yayane ki fara mom Zan fahimce ki in sha Allah”
jinjina kai mom tayi “wani taimako nake so kayi mana game da case ɗin Asma'u”
“umarni za kice mom,Dan kinfi ƙarfin neman taimako a gare mu,mi kike buƙata nayi maki a kan case ɗin?”
“yawwa,ina so ka sake wani sabon bincike a kan case ɗin bayan wanda jami'an tsaro su kayi”
“amma mom saboda mi?”
“naeem zuciyata ta kasa yarda cewa Aminiyata zata iya aikata wannan laifin ,duk da ɗan Adam yana canzawa akan yanda ka san shi amma ita ina kyautata mata zato”
“shikenan mom in Sha Allah zanyi yanda ki ke so ,amma dole sai na samu wasu ƙarin bayanan sama da wannan da ki ka bani”
“wanann ba damuwa bace,ko a wajen yarinyar ta zaka iya samun wasu baya nan,sannan akwai masu aikin gidan da masu gadi duk da sun bada bayanan su a court da wurin ƴan sanda sai dai bayanan na su ban gamsu da su ba, ina ji a raina kamar sun ɓoye wani ko wanda su ke da alhaki a kan kisan su suka hansu faɗar gaskiya”
“shikenan ba damuwa mom ko da sun ɓoye wani Abu nayi maki alƙawarin sai sun magantu dole za su faɗi gaskiya”
“yawwa haka nake son ji,amma ina so ya zama sirri kai ka ɗai nake so kayi aikin sai wanda ka yarda da dashi daga cikin yaran ka wanda kasan bazai yaudareka ba”
“karki damu da wannan mom,komai zai tafi yanda ki ke so in sha Allah”
jinjina kai mom ɗin tayi “bayanan komai yana a cikin takardun nan”
“zaka samu komai a ciki,tun daga tarihin rayuwar su, sunayen mutanen da suke mu'amula da CP lokacin da yana raye da ita kanta Asma'u da duk wani ma'aikacin su,hatta ƙasashen da su ke yawan zuwa da garuruwa da wurare da su ka fi yawan zuwa a faɗin ƙasar nan zaka samu, Naeem kar kayi sakace da su duk da na san ba halinka bane amma ka kula da su sosai akwai baya nan da ko Court bata san da zaman su ba naƙi bayyanar da su ne a gabanta saboda wasu dalilai nawa, dan Allah ka maida hankali a kan su Naeem”
ɗan dariya ya Naeem yayi “dama na daɗe ina zargin tsakanin ke da dady wa SAM ya gado naci da bin ƙwaƙwafi case Ashe ke ce?”
murmushi mom ta saki “bana son shashanci Naeem,wannan case ɗin karka manta Aminiyata ce a ciki kaga kuwa dole na nace akan shi”
“haka ne in sha zan baje gaba ɗaya ilimina akan wannan case ɗin,zanyi ƙoƙarin ganin munyi nasarar fitar da momy in sha Allah”
“haka nake son ji,ka ko yi waya da SAM?”
“A'a,mun kwana biyu ba muyi waya ba,kin san ɗan naki sarki ne sai ya sha iska yake neman mutane gashi ko ka kira shi a banza idan ba yana free ba shine zai ɗaga ko idan yaga missed call ya kira”
“nima kwana biyu bai kirani ba,amma Alyar da James sun kira ni kuma sun shaida man yana lafiya,aiki ne yayi mashi yawa”
“nima Alyar ya kirani harma ya ke sanar dani suna nan zuwa ƙarshen shekarar nan shi da James,na dai ce su lallaɓa SAM ɗin nima zan gwada sa'ata ko za'a samu wannan karan ya biyo su”
“duk lokacin da mu kayi waya dashi sai na roƙi Alfarmar ya taimaka ko kiran dadyn ku ne yayi a waya ko ya tura mashi message ko da bai zo ba amma ina,baƙar zuciyar dana rasa awajen wa ya gadota taƙi barinshi,harda momy da Uncle Jonas nasha haɗashi saboda yafi jin maganar su sama da tawa amma a banza sunyi sunyi yaƙi, ko da picking call ɗin dadyn ku ne yayi idan ya kirashi amma ina”
“in sha Allah mom wata rana da ƙafarshi zai tako ya zo har ƙasar nan saboda dady,komai zai wuce”
“bana tunanin SAM zai yafe ma dadyn ku,ya riƙeshi sosai a zuciyar shi,tsawan shekara 18 fa kenan”
“mom ki daina wannan tunanin in sha Allah zai yafe mashi wata rana,koda shekara 50 ne,ke da ma yayi ma laifin ki ka yi haƙuri bare shi SAM ɗin,zai dawo da kanshi saboda dadyn in sha Allah”
“Allah yasa haka Naeem”
“in sha Allah mom,wata rana komai zai wuce har jikokin SAM ɗinki za ki gani a gabanki dan na san burinku kenan ke da Dady”
murmushi ta saki “Allah yasa haka,da kuwa nayi farin ciki mara misaltuwa”
“Ameen mom,ni zan wuce gida”
“ok muje nima zan koma ciki” tashi su kayi, jerawa su kayi a tare su ka nufi ƙofar cikin gidan.
part ɗin dady su ka nufa,a kishingiɗe su ka same shi saman rug carpet yana duba wani littafin addini,bakin su ɗauke da sallama su ka ƙara da ciki,ɗagowa dady yayi yana amsa masu sallamar.
kusa da shi ya Naeem ya zauna mom kuma ta zauna saman kujera
kallon su dady yayi fuskarshi a sake yace “uwa da ɗa daga ina haka,wani abun daɗin ya faru ne”
murmushi ya Naeem yayi “barka da hutawa dady”
“barka dai Naeem,ya Aiki yau ba ku shigo tare da Adnan ɗin ba?”
“Eh kila sai anjima zai shigo”
“Allah ya kaimu anjimar lafiya,na shiga wurin Abbah ɗazu yace kwana biyu bai saka a idon ba ina fatan dai lafiya?”
“Ayyuka ne su ka ɗan yi man yawa kwana biyu shiyyasa ban shiga ba na bari sai ranar juma'a”
“duk da haka Naeem tunda har kana samun lokacin shigowa nan ai ka ɗan leƙa ku gaisha ko da da dare ne”
“in sha Allah daga nan zan shiga”
“yawwa hakan yayi,Allah yayi maku Albarka”
“Ameen dady” ya Naeem ɗin ya faɗa yana miƙewa,sallama yayi masu ya fice.
*Main Parlor*
da sauri yaja baya saboda karon da yayi da mutum,duban shi ya kai ga matashin saurayin dake tsaye a gaban shi sai layi yake kamar zai faɗon mashi,da tsantsar mamaki yake bin saurayin dake neman ya raɓa ta gefenshi ya wuce,a wani zafafe ya fisgoshi baya,saukar maruka matashin saurayin yaji a saman fuskar shi wanda su kayi sanadiyyar dawowar shi cikin hayyacin shi,da sauri yasa hannuwanshi ya dafe kumatunshi.
ɗan uwan shi dake bayan shi ganin irin marin da ya Naeem ya sauke ma ɗan uwan nashi ne yasa shi komawa baya cikin sanɗa ya koma parking space ya shige motar da su ka zo,mai da ƙofar yayi ya rufe a hankali,shiru yayi yana baza ido a hanya ko zaiga wucewar ya naeem.
tun daga kan crazy short ɗin dake jikin shi da ƴar iskar shirt ɗin dake jikinshi mai kama da rariya zuwa ɗan iskan askin dake kanshi ya Naeem ke kallo,ga wani chain dake manne a wuyan shi kunnenshi ɗaya a huje yake ya saka ear ring.
wani marin ya Naeem ya sake kifa mashi,dafe kuncinshi yayi sai ga hawaye shar da alama marin ya shige shi sosai
“dan Allah second father kayi haƙuri,wallahi bangaka bane shiyyasa na bigeka” saurayin ya faɗa yana watso ido kamar tsohun kwarto a kan ya Naeem.
“daga gidan ubanwa kake haka?” ya naeem ya faɗa yana cakumo wuyan rigar shi
cikin rawar murya yace “wallahi daga islamiyya muke Ni da YAZDAN,yazdan dan Allah ba daga can muke ba” ya faɗa yana waigawa bayan shi wayam ya gani babu yazdan
“wallahi daga can muke” ya sake faɗa yana kallon ya naeem,dariya ma maganar tashi ta so ba ya naeem in ba ya ɗauke shi ɗan iska kamar shi ba taya zaice mashi daga islamiyya yake da irin wannan shigar ya yarda,ta ina ma yayi kama da mai zuwa islamiyya.
“saboda ka ɗauke ni shashasha kamar kai ko”
“wallahi ka tambayi yazdan daga can muke mun shiga gida ne muka canza kaya”
“in tambayi abokin cin
mushenka ko,zan kamashi ne shima”
“Allah ba ƙarya muke ba”
“to naji, karanta man abun da aka koya maku yau ko ka kwana kana frog jump”
da ƙyar ya haɗe yawu jin abunda ya naeem ɗin yace,raba ido ya shiga yi kamar wanda yayi ma sarki ƙarya
“oya kai nake saurare” ya naeem ɗin ya faɗa fuska a tsuke yana harɗe hannuwanshi a ƙirji
nan fa ido ya raina fata,ƴan kame kame ya fara,ran ya naeem ne ya fara ɓaci,cakumo kwalar rigar shi yayi yaja shi ƙiiii zuwa waje,yazdan na ganin haka yayi saurin kwanciya cikin motar sai zare ido yake.
ɗaya daga cikin sojojin dake shawagi cikin Estate ɗin ya Naeem ya kira,da sauri sojan ya ƙaraso,ƙato ne bana wasa ba,daga bakin parking space zuwa bakin