Showing 78001 words to 81000 words out of 88290 words
Chapter 27 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
ƴata, gaskiya A'a, to in bashi ma tayaya yaronda ma baya tare dani”
“he will come back ai”
“ni gaskiya bazan bashi ba koda yana so”
“to shikenan sai kiba Naeem ko Adnan”
“Allah ya kiyaye ƴata ta Auri mai mata” dady baisan sanda ya saki dariya ba jin furicin mom
“ke nan bazaki iya ba mai mata ƴarki ba?”
“koda kuwa yana so, haka kawai da ƙananun shekarunta a hana mata zaman lafiya”
“to ai shikenan, yanzu dai kin haƙura da maganar Auren Irfan ɗin ko?” turo baki tayi kamar ƙaramar yarinya “idan hakan Alkairi ne Allah ya tabbatar, idan kuma akasin haka ne shima ina fatan ya kasance Alkairi” dariya dady ya saki yan jan dogon hancinta “That's why I'm proud of u because of ur patience, i love u my baby katte”
“ni karka sake kirana da wannan sunan” zaro ido dady yayi yana riƙe baki“ki rufa mana asiri idan ba so ki ke momy tace rashin kunyata ta kai har na canza maki sunan data sa maki, ko so ki ke tace na dawo mata da ƴarta?” dariya su ka saki gaba ɗayan su
“momy, i luv her” dady ya faɗa, murmushi mom ta saki, wayar dady ce ta fara ringing tashi mom tayi ta miƙo mashi ita, duba sunan mai kiran nashi yayi, saurin nuna mata screen ɗin yayi, my friend ta gani,zaro ido tayi, murmushi dady ya saki yana picking call ɗin “hello, how are u” on the other hand na cikin wayar yace “am fine my friend,long time,how is ur family?”
“they are fine,guess what?” dady ya faɗa yana kallon mom
“what?” na cikin wayar ya faɗa, murmushi dady ya saki
“I'm with ur daughter”
“really, please give her the phone” murmushi ya sake saki yana miƙa ma mom wayar
“hello uncle”
“hi katte,how are u, where's my children??”
“they fine,how was mom Natasha and james?”
“their all fine” kallon dady tayi tana canza harshe zuwa Spanish,yanyin fuskarta ne ya canza zuwa tsantsar damuwa “El tío SAM todavía no cree que volverá?, su padre estaba muy preocupado”
_Uncle har yanzu SAM bai amince zai dawo ba, mahaifin shi ya damu sosai_ ajiyar zuciya ya sauke
“Él todavía no está de acuerdo, pero intentaré que venga a su fiesta de cumpleaños”
_Har yanzu bai amince ba, amma zan yi kokarin sa shi ya zo da birthday ɗin shi_
“okay,El tío Irfan se casará”
_shikenan,uncle Irfan zaiyi Aure_
“cuando! pero por qué no me lo dijiste?”
_yaushe,amma miyasa baki sanar dani ba?_
“Ahora he's padre que me lo dice,but uncle, no me gusta la chica con la que se va a casar, pero él no me entiende”
_yanzu dadyn shi ke sanar dani,amma uncle bana son yarinyar da zai Aura,amma yaƙi ya fahimce ni_
“Por qué no la amas?Quién se casará?”
_mi yasa baki sonta, wacece zai Aura_
“tío es hija de su hermano menor, sabes que no todas las esposas de su hermano menor me aman, ella mother no me ama.”
_Uncle ‘yar kaninsa ce, ka sani ba duka matan kanensa ke so na ba, mahaifiyarta ba ta so na._
“Irfan la ama y ella lo ama?”
_irfan ɗin yana sonta,itama tana sonshi?_
“si se aman, solo que a su madre no le agradamos”
_eh suna son juna, mahaifiyarta ce kawai bata sona ni da Irfan_ murmushi Uncle ya saki
“No es nada, es la boda de Naeem y dices que su madre no te ama, y se casaron y viven felices, no te preocupes, esto también estará bien”
_karki damu,lokacin Auren Naeem ma haka ki ka ce mahaifiyarta bata sonki,kuma sunyi Auren suna zaune lafiya,karki damu shima wannan lafiya za'ayi_ turo baki tayi jin abunda uncle ɗinta yace
“uncle por qué siempre apoyas a Tahir?”
_uncle mi yasa ko wane time ka ke goyan bayan Tahir ne?_ kallonta dady yayi jin ta ambaci sunanshi
“No lo apoyo, cálmate y todo irá bien”
_ba goyan bayansa nake ba,ki kwantar da hankalin ki komai zai tafi dai dai_ ƴar dariya yayi cikin hausar sa da sai a hankali yace “ke da nake so ki samar ma SAM mata anan” turo baki kawai tayi tana kallon dady without saying anything,zuba mata ido dady yayi har su ka kammala wayar, sallama tayi mashi tana miƙama dady wayar, kara wayar yayi a kunnenshi cike da zolaya yace “wato abun ƴar wariyar launin fata ce, shi ne za ku canza man yare dan kar naji abunda ku ke faɗa ko??” dariya Uncle Jonas ya saki, cikin hausarshi da bata gama daidaita ba yace “baruwana laifin matarka ne ita ta fara”dariya dadyn ya saki, sun ɗan jima suna waya kafin su ka yi sallama, kallon mom dady yayi
“maganar mi ki ka yi mashi?”
“i talk to him about SAM and Irfan's marriage”
“shine sai kin canza harshe dan kar naji”
“ai kaine ka ƙi ka koyi spanish”
“it's too hard, that's why” murmushi kawai mom ɗin tayi.
*UNITED STATE❤*
_*Las Vegas (Nevada)*_
Around 10pm Miss Malika ta koma gida, saboda jikinta daya rikice dan sosai jininta hau,Dr Daniel ya so ya bata gado amma tace A'a, magunguna kawai ya bata,da baza ta tafin ba ma sai dai dan ganin har time ɗin Nailarh bata farka ba ne yasa ta tafi, Aunty sophia ma har time ɗin bacci take.
bayan tafiyar Miss Malika da 30 Minutes Aunty sophia ta farka,luna na kan sofa tana bacci,da sauri Nures ɗin dake kula da ita ta nufo bed ɗin ganin tana shirin sauka
“sorry,how do u feel now?”kallonta Aunty Sophia tayi “Nailarh,Please take me to her place,I want to see her” ajiyar zuciya nurse ɗin ta sauke kafin tace ok,ficewa tayi daga ward ɗin,bayan kamar five minutes sai gata ta dawo.
kallon Aunty Sophia tayi
“we can go” kamar jira take tace haka,da sauri ta shiga ƙoƙarin sauka daga saman bed ɗin, taimaka mata tayi ta sauko,slippers ɗin dake bakin bed ta zura a ƙafarta,ficewa su ka yi daga ward ɗin, direct office ɗin doctor Daniel su ka nufa.
A bakin ƙofa su ka tsaya,nocking nurse ɗin tayi kafin aka basu iznin shiga,tura ƙofar tayi ta shiga Aunty Sophia na biye da ita,a zaune su ka samu Dr Daniel yana duba wasu files dake gabanshi,cikin office ɗin su ka ƙarasa,sallamar nurse ɗin yayi,ficewa tayi daga office ɗin,kallon Aunty Sophia yayi da tsantsar kulawa yace “how do u feel now?”
“am feeling better, please Dr I need to see her” jinjina mata kai yayi kafin,ya ɗauki landline ɗin dake ajiye kan table ɗin shi,wasu numbobi yayi dialing,kara wayar yayi a kunne bayan anyi picking,alfarma ya shiga nema kan a bar ta taga Nailarh,Aunty Sophia dai na kallonshi,can ya katse wayar,miƙewa yayi yana faɗin“we can go”
Ficewa su ka yi daga office ɗin zuwa ward ɗin da Nailarh take,Ward ɗin tsit yake baka ganin gifcin kowa sai na nurses jefi jefi,da kallo kawai Aunty Sophia ke bin wurin,a bakin ƙofar wani ɗaki su ka tsaya, nocking Dr yayi kafin aka bashi iznin,ƙofar ya nuna ma Aunty Sophia yana barin wajen.
tsaye tayi ta kasa shiga sai kallon ƙofar take,rabinta glass ne kana iya hangen cikin ɗakin,ɗan leƙa cikin tayi,ba komai yasa ta kasa shiga ba sai fargabar halin da za ta ga Nailarh,a hankali ta shiga bin ɗakin da kallon kafin ta sauke idonta a kan Nailarh dake kwace,yana daga tsaye bakin bed ɗin ya ɗan rissinar da kanshi saitin fuskarta,still face mask ne a fuskarshi,sosai ya zuba mata ido kafin ya ɗan lumshe idonshi yana motsi da bakinshi kamar mai shirin furta wani abu,can ya buɗe idonshi,tafukan hannayenshi ya kai saitin baƙin shi,da alama Adu'a yayi mata kafin ya shafa mata a fuska,still da oxgyen a hancinta,Aunty Sophia dai na tsaye da tsantsar mamaki take kallonshi,to miye hakan yake ma Nailarh.
a hankali ya ɗago da kanshi yana kallon ƙofar jin anyi nocking kuma ba'a shigo ba,da sauri Aunty Sophia ta turo ƙofar ta shigo,tashi yayi daga bakin bed ɗin ya nufi
Ventilator machine,cikin ɗakin ta ƙarasa,a bakin bed ɗin Nailarh ta tsaya,wani irin tausayin Nailarh ne ya rufeta,tuni hawaye sun cika idonta,saurin kamo hannun Nailarh tayi cikin nata,hannunta ɗaya ta kai ta shafa fuskar Nailarh, muryar shi ta tsinkaya a cikin kunnenta“how was ur body,I hope u feel better now??” ya furta without looking at her dubanta ta kai gareshi,haka nan muryarshi tayi mata kama da wacce ta sani,a hankali tace “am feel better”jin jina kanshi yayi,kafin ya ɗauki wa su pepars ya fice daga ɗakin baki ɗaya,da kallo kawai Aunty Sophia ta bishi har ya fice,dubanta ta kai ga Nailarh dake fitar da numfashi a hankali,kwantar da kanta tayi saitin kanta tana jin wani iri a zuciyarta,ji take inama zata iya yaye mata ciwan,cike da tausayi take kallon Nailarh har bacci ya sake ɗaukarta ba tare da ta sani ba.
Miss malika lokacin data koma gida,wanka ta samu tayi da ƙyar chefs su ka samu tasa ma cikinta wani abu kafin tasha magani,kwanciya tayi duk da ta san da wuya bacci ya ɗauketa,hakanan dai ta kwanta ta lumshe idonta,wani iri take ji a zuciyarta ga tsanar wannan bawan Allah da tayi mata kane kane a ƙahon zuciya,tun tana hospital ta bada umarnin a kawo mata shi ko a ina yake ,har yanzu ba taji feedback daga gare su ba,ta ɗau alwashin sai tayi mashi azaba mai raɗaɗi saboda halin da ya jefa Nailarh a ciki,sosai ta lula duniyar tunani, ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, ajiyar zuciya ta sauke tana ɗan jan tsaki dan a yanda take bata jin zata iya waya da kowa,jawo wajar tayi da nufin rejecting amma ganin sunan mai kiran nata ne yasa ta fasa, picking call ɗin tayi tana ɗan tsuke fuska,kara wayar tayi a kunne ba tare da tace ƙomai ba,on the other hand na cikin wayar yace “hello wife” ɗaure fuska tayi“don't ever call me with that name again”
ajiyar zuciya ya sauke
“i know u are angry with me,am so sorry,where is my baby?” rai ɓace tace “which baby,dama kana da baby ban sani ba?”
“u know who I mean,where is Nailarh” tsaki taja “Nailarh da baka damu da ita ba ko wa?”
“am sorry Malika,U know I love her and I care for her”
“a yaushe ka ke son nata,tunda kayi ma US ƙaura ka taɓa kira dai dai da rana ɗaya kace naba Nailarh ko ka tambayi lafiyarta?”
“am sorry Malika,kinfi kowa sanin yanda Nailarh ke treating ɗina, Nailarh Bata so na Bata san gani na a tare dake,Ni kuma da shekaruna da matsayina bazan zauna yarinya ƙarama ƴar cikina na treating ɗina like that ba”
“Nailarh yarinya ce danmi zaka biyeta?”
“to ai kema harda laifinki,kema nunawa ki ke tafini a wajenki,kulawar da ki ke bata tafi ƙarfin ta uwa da ƴa”
“kaima ai kanada wanda ka nuna sunfini mahimmanci a rayuwarka,tunda na bar Australia baka sake ɗaga waya ka kirani ba almost 5 days kenan,kana can wurin matarka wacce duniya ta shida Aure tsakanin ku”
“ba haka bane Malika,ni ban fifita kowa sama dake ba”
“haka ne mana,ko dan babu ƴaƴa tsakanin mu yasa baka ɗauke ni da mahimmanci ba”
“ko ɗaya Malika,kiyi haƙuri na san nayi kuskure amma na maki alƙawari hakan bazata sake faruwa ba,yanzu ina Nailarh ina son magana da ita”
“she in serious sick, she had an attack”
“what,attack” ya faɗa cikin tsantsar tashi hankalinki,ɗaga mashi kai tayi kamar yana gabanta“amma taya hakan ta faru?” kaf ta kwashe abunda ya faru a N R T da yanke jikin da Nailarh tayi ta faɗi ta faɗa mashi
“zan shigo US ɗin next week,Ina mata fatan samun lafiya”
“mi yasa sai next week,kai da nayi tunanin zaka ce gobe”
“akwai wani ɗan issue ne nan da ya riƙe ni,kiyi haƙuri zan shigo next week ɗin”
“shikenan”
“yanzu a wane hali Nailarh take ciki?”
“har yanzu bata farka ba”
“ok idan ta farka let me know”
“ok I will let u know” sun ɗan jima suna waya kafin su ka yi sallama.
Aunty Sophia sosai bacci ya ɗauketa a ward ɗin da Nailarh take,nurse ɗin dake kula da ita ne ta shigo ward tashinta tayi daga bacci ta sanar da ita Dr yace a bar Nailarh haka ta koma ɗakinta,ba dan ta so ba ta tashi, kissing forehead ɗin Nailarh tayi kafin su ka fice.
*ABUJA NIGERIA*
“amma gaskiya abun nan ya bani mamaki da haushi,Irfan ya rasa wa zai so sai Noor Fisabilillahi,to wai ma mi ya gani a jikinta da har yayi sha'awar Aurenta,yarinyar da kwata kwata bata da tarbiyya” mom Maryam ta faɗa rai a ɓace, ajiyar zuciya mom ta sauke “ni ba ma duk wannan ba,Hajiya Fatilah kin san halinta,kwata kwata bata da mutunci,ina tsoron duk wani abu da zai hanani zaman lafiya,anyi na Naeem ya wuce gaskiya yanzu bazan iya ɗaukar tashin hankalin dana ɗauka lokacin Auren Naeem ba”
“ni wallahi da ki ka kira kina faɗaman ban ɗau maganar mai mahimmanci ba sai da yallaɓai ya dawo yake faɗa man,haba dan Allah sai kace Idanun Irfan ɗin rufewa su ka yi ,ga ƴaƴan arziƙi ya rasa wacce zai so sai Noor”
“dama ya san bazan amince ba bai taɓa faɗa man ba,sai dai ya samu iyayenshi ya faɗa masu”
“ya san zaki hanashi ne,amma duk da haka ya kamata ayima tufkar hanci tun kafin maganar ta kai ga Abbah dan Noor ba mace da zai sha'awar zaman Aure da ita ba ne”
“babu yanda ban nunama janar ba amma yaƙi fahimtata,saima gani yake saboda ƴata yasa naƙi amincewa”
“shi dama bazai ƙi amincewa ba saboda ƴar ɗan uwan shi ce,kuma duk abunda za kice gani zaiyi kin ƙi ƴan uwanshi,amma maganar gaskiya Irfan baiyima kanshi zaɓi na gari ba”
“ni yanzu tashin hankalina abunda zai biyo baya idan fatilah ta sani”
“karki wani tashi hankalinki, mata ta hana maki zaman lafiya,in sha Allah ma wannan Auren bazai yiwu ba,zan ga Irfan ɗin ne”
*Tashin sense Irfan da Noor wane irin rayuwa ne wannan kowa baya farin ciki da Auren ku?*
A kishingiɗe take saman rug carpet da ke katafaren parlorn ta,shigar alfarma ce a jikimta kamar koda yaushe, fuskarta tasha makeup kamar wata amarya,hannunta riƙe da fork tana shan fruit salad,time to time take sakin murmushi kamar wata zautatta,bakomai ke sata nishaɗin nan ba sai time ɗin da su ka ɓata ita da barrister hashim, wani irin shauƙi take ji, ji take inama ace sun dawwama a lokacin,ta ƙosa komai yazo ƙarshe su kasance a inuwa ɗaya,tundaga main parlor ɗinta taji ana kwaɗa sallama kamar tashin hankali.
zambur ta miƙe tana dafe saitin zuciyarta dan baƙaramin tashi hankalinta yayi ba, mom Fatilah ce tare da mom halima da ƙanwar mom Fatilah hajiya zainab su ka faɗo parlorn kamar an jehosu, da sauri mamy taja baya tana faɗin
“innahu min sulemanu wanna innahu bismillahi, ku kuma daga Ina haka abu kamar tashin duniya?”
“wallahi yau tashin duniyar ne ma za'ayi” hajiya zainab ta faɗa, gwalo ido mamy tayi waje jin furucin hajiya zainab
“Auzubillahi, mi yafaru?”
“miyema bai faru ba, zuwa za kiyi muje part ɗin waccan dangin sheɗan ɗin, yau wallahi sai mun nuna mata tantagaryar rashin mutunci” a cewar mom halima
“yo ni naga jaraba,shegun ƴaƴanta kowane mai tashen balaga daya ta so sai ya liƙe ma ƴaƴan mu dan mi baza taje can danginta ta nema masu Aure ba sai ƴaƴan mu saboda son zuciya” a cewar mom Fatilah
“to fa mi zulaihart ɗin tayi ne wai?” mamy ta faɗa
“ok bama ki san mi tayi ba”a cewar hajiya zainab
“A'a ban sani ba”
“idan munje can za kiji”mom halima ta faɗa, da sauri mamy ta nufi mayafinta dake kan sofa ta rufe gashin attachment ɗin dake kanta tana faɗin “ai ko dan naga yanda fuskar ƴar banza zatayi naje, muje mutanena ku nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makahu bane”
“wallahi yau sai ta yaba ma aya zaƙinta” hajiya zainab ta faɗa, ficewa su ka yi daga part ɗin kamar za su tashi sama...
*A dai yi a sannu mamy*
“please sister Yumnah ki faɗa man, wallahi ina so na sani ne amma ba dan wani abu ba” Nainarh ta faɗa tana kallon Yumnah dake mata dariya
“saifa kin faɗaman dalili,sannan zan faɗa maki”
“kawai dan kinga na damu da na sani ne ki ke jaman aji tun jiya”tun jiya take fama da ita ta faɗa mata waye amma sai ja mata aji take wai ta gano da kanta
yar dariya Yumnah tayi
“na tambayeki miye dalilin da yasa ki ke son ki sani kinƙi faɗaman gaskiya”
“haba Yumnah kema kin san babu wani dalili dayasa nake son sanin waye”
“ban yarda ba dan ina lure dake”
“shikenan tunda haka za kice,banama son ki faɗa man,zan tambayi dady shi na san bazai ƙi faɗa man ba,ke kuma kar Allah yasa ki faɗa man”ta faɗa yayinda take sauka daga saman bed ɗin
“yanzu ke sai ki tambayi dady?”
“sosaima kuwa” Nainarh ta faɗa tana murguɗa mata baki
“lallai abun naki azimun ne” juya mata ido Nainarh tayi tana nufar dressing room ɗin su,da sauri Yumnah ta jawo hannunta
“sorry,kema kin san zan faɗa maki,kawai ina son ganin react ɗinki ne,ai ban san haka ki ka damu ba”fisge hannunta tayi “ni sakar man hannu,banaso ki riƙe kayanki” da sauri Yumnah ta sauka daga saman bed ɗin tana kamo hannunta “sorry zan faɗa maki ba sai kin tambayi dady ba”tsuke fuska Nainarh tayi “nace maki bana so”
“ke wallahi sai kin saurareni,dallah can kawai” Yumnah ta faɗa tana murguɗa mata baki, murmushi Nainarh ta saki ganin yanda Yumnah ta murguɗa mata baki,jan hannunta Yumnah tayi,cikin ɗakin su ka nufa,zama Nainarh tayi kan bed, laptop ɗinta dake ajiye saman Nightstand dake chaji ta jawo,kunnata tayi,zubama laptop ɗin ido su ka yi harta gama searching, murmushi Yumnah ta saki lokacin da tayi ido biyu da photonshi dake wallpaper system ɗin,hannu tasa tana shafa kyakkyawar fuskarshi,kissing hannuta tayi tana shafa lips ɗinshi,da mamaki Nainarh ke kallonta ta rasa mike damun Yumnah duk ta buɗe system ɗinta sai tayi haka,ita dai in ba idanunta ne basa gani sosai ba kamar ba musulmi ba,shiru dai tayi ba tace komai ba tana kallon Yumnah,gallery ɗinta ta shiga,turama Nainarh system ɗin tayi yayin da ta shiga wata folder,zuba ma system ɗin ido tayi har ya gama loading,fotunanshi ta gani kamar an jehosu harda na part ɗin dady dama wasu daban,saurin kallon Yumnah tayi, murmushi ta sakar mata tana ɗage mata gira ɗaya
“kin san waye?”girgiza mata kai tayi alamar bata sani ba,yar dariya Yumnah tayi
“to wannan ba kowa bane face shalelen dady ya SAM