Showing 12001 words to 15000 words out of 88290 words

Chapter 5 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

405

aikin ta bita har ta ɓacce ma ganin ta,taɓe baki tayi tana komawa kan aikin dake gabanta, a bakin ƙofar wani ɗaki ta tsaya, tura ƙofar tayi ta shiga,wani haɗaɗeb bedroom ne ta shigo komai na cikin shi ɗan dai dai babu haya niya, ciki ta ƙarasa tana kiran sunan
“Aunty laatifa! am home where are u” matashirya mata ta hango zaune kan study chair yayin da laptop ke a saman desk tana operating.


“Aunty nah sarkin aiki,a gidan ma baki huta ba, gaskiya mijinki ya shiga shiga uku na san a daren ku ma nafarko kwana za kiyi kina aiki, shiyyasa momy ke ce maki agogo sarkin aiki”

juyowa tayi masha Allah na faɗa da ganin wannan madarar kyan, laatifa kyakyawa ce ajin farko,riga da wando ne a jikinta masu taushi, kanta babu ɗan kwali tayi parking gashinta a tsakiyar kai, medical glass ɗin dake idonta ta cire.


“ƙanwata idan ban yi aiki ba mi ki ke so nayi?”
“gaskiya kina aje wa kina hutawa”
“shikenan, ya gajiyar aiki?” ya mutse fuska tayi yayin da take samun wuri bakin bed ta zauna

“aiki babu daɗi” murmushi laatifa ta saki wanda ya ƙarama kyakyawar fuskarta kyau

“gaskiya Balqis kin cika raki, miye abun gajiya a wannan aikin ke da kina bayan mota kina shan iskar Ac”

“haka za kice mana tunda ke kin saba, duk ranar dana sha court za kice haka”
“ba wai zan ce ba haka ne ma, kawai dai kin cika raki”
“shikenan naji ina alƙawari na?”
“yanzun nan na gama tura mashi saƙo ta email kin san baya ɗaukar kira ba tare da ka fara tura mashi saƙo ba”
“haka ne, amma ai ke naga kuna waya”
“wannan ai shi ke kirana, amma duk lokacin da ni nake son magana da shi sai na fara tura mashi saƙo tukun” taɓe baki Balqis tayi
“shi dai komai nashi na daban ne”

“classic boy ake faɗa maki dole komai nashi ya kasance unique,ke dai kawai ki dage da Adu'a dan akwai aiki a gabanki”

“ni kaina na sani Aunty laatifa abun har tsoro yake bani”
“karki damu nima zan tayaki da adu'a ”
“in sha Allah, bari na tafi ɗakin momy bata san na dawo ba, nan na fara shigowa”
“ok anjima zaki bani labarin yanda ƙarar ta kasance”


“kin ma tuna man, wallahi dady ya ganni ba kiga harar da ya watsa man ba kamar ƴan hanjin ciki na su faɗo” dafe ƙirji laatifa tayi
“nashiga uku!! dan Allah da gaske ki ke”laatifa ta faɗa da tsantsar tashin hankali
“wallahi kuwa na san dole yaji ba'asin abun da ya kaini, amma zanyi duk yanda zanyi ganin bai gane ke ki ka tura ni ba”
“yawwa dan Allah kice ra'ayi ki ka yi ba ni nace kije ba”
“in sha Allah karki damu”
“yawwa na gode” ƙofar fita Balqis ɗin ta nufa tana ƙara jaddadamata karta damu.



zama tayi bakin bed dafe kanta“ya Allah” ta furta,da alama hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin dadyn su yaga Balqis.


Balqis tana fita daga ɗakin wani ɗan corridor ta nufa, wani ɗan madaidaicin parlor ta shiga,a zaune take saman sofa mai mazaunin mutum biyu les ne a jikinta ɗinkin half bubu da zani, hannunta da wuyanta sun sha adon zinari, wayace kare a kunenta da alama waya take
“lamari ai baiyi daɗi ba, in sha Allah anjima idan Barrister ya dawo zan tambaye shi naje nayi mata jaje ai abun ayi jaje ne” murmushi Balqis ta saki tana ƙarasawa cikin parlor.


faɗawa tayi saman jikinta“momy na dawo” da sauri ta janye wayar daga kunenta “ja'irar banza kin girma amma baki san kin girma ba, ba ki gani waya nake, karya ni ki ke son yi?” tashi tayi zaune tana turo baki“momy daga nayi kewarki zaki rufe ni da faɗa”
“an rufeki da faɗa, dan gidan ku haka ake kewa kina shirin karya ni”
“ke momy haka ki ke daga abun arziƙi sai ki rufe mutum da faɗa na san da dady ne bazai ce man komai ba”
"ai shi ki ka ce ƙashin shi ƙwari ne gare shi” ficewa Balqis ɗin tayi daga parlorn tana gungunai.


Mai da wayar tayi a kunne “kina jina da wannan ja'irar yarinyar tana neman karya ni”bana jin mi na cikin wayar ke faɗa
“to shikenan idan Allah yasa mun haɗu anjimar to shikenan, idan kuma bamu haɗu ba sai ranar friday kenan idan mun haɗu a part ɗin Abbah” jinjina kai tayi kafin daga bisa ni su kayi sallama.





*UNITED STATE*


_*Las Vegas (Nevada)*_


_*Nailarh Racing Track (N.R.T)*_



Ƙaton track ne gari guda wanda girmanshi zai kai girman wani babban ƙauyen,kallo ɗaya zaka ma wurin ka hango tsirarar dukiyar da aka kashe wajen gina shi,
ta ko ina ka duba mutane ne zazzaune a saman chairs gaba ɗaya hankalin su naga wasan da ake gabatarwa,kowa burinshi nashi yayi nasara,duka mutanen dake wurin suna sanye ne da polo shirt white color wacce a gabanta a kayi rubutu da ɓakin fenti in da aka rubuta QUEEN da manya haruffa daga saman shirt ɗin logo ne na sunan center ɗin ( N R T) sai p_cap da hat wanda suma aka rubuta QUEEN a jikinsu kamar na shirt ɗin,maza ke sanye da p_cap yayin da mata ke sanye da hat wacce aka yi mata kwalliya da gashin tsintsaye a samanta, Al'adar wurin wasan ce duk wanda zai shiga sai an bashi wannan shirt da cap ya sa wanda kyauta ce daga mamallakiyar wurin wasan.


dawakai ne kyawawan gaske ke gudu a tsakiyar filin,yayin da mamallakansu ke saman su jikin su sai salƙi yake yana ɗaukar ido,color uku ne dawakan wasu brown yayin da wasu su ka kasance baƙaƙe doki ɗaya ne a wurin ya kasance white color,daga yanayin tsarin dokin zaka san na musamman ne, a jere su ka fara gudun,cikin ƙwarewa da karsashi dawakan ke gudun abun gwanin ban sha'awa,abun dai sai wanda ya gani,rabuwa su ka fara yi da junan su, dawakai uku ne su kayi gaba yayin da su ka bar sauran a baya harda wannan farin dokin yama fisu yin baya sosai sama da sauran dawa kan,sosai su ke gudu dan kaiwa ga matsaya,miƙewa tsaye mutane su ka fara yi da alama dawakan nan gudu uku na daban ne, mutane na da buri a kan su.


Wasa fa ya fara ɗaukar zafi dawakan kansu su ukun sun rabu da juna yanzu biyu ne a gaba ɗayan a baya.


“da alama dai yau tarihin N R T zai canza, ban taɓa ganin wasa irin wannan ba” cewar wani bature dake zaune cikin ƴan kallo, murmushi gefen baki mace dake gefen shi ta saki tana faɗin

“ba abu bane mai yuwuwa canza tarihin N R T cikin sauƙi, a ko wane lokaci da sabon salo take zuwa, kana tunanin wannan baya bayan da tayi babu wata a ƙasa?” taɓe baki yayi yana ɗaga kafaɗa
“i don think,tazarar tayi yawa duba kiga in da su Ryder su ke kalli in da king yake”murmushi matar ta saki
“dear sai kace yau ka fara zuwa kallon wasan N R T”
“ba yau na fara zuwa ba, but wasan yau ne ban taɓa ganin irinshi ba”
“to ka zuba ido za kace na faɗa maka”
“okay” ya faɗa yana mai da glass ɗin shi daya cire.



ran wani magidanci ne daga cikin ƴan kallo ya fara ɓaci,sign matar wannan baturen tayi mashi, duban shi ya kai ga mata da majin
“bazan taɓa ƙyale Anthony ba idan har kuɗina su ka lalace” ya faɗa da alamar ranshi ya ɓaci“but why?” matar shi ta tambaya

“babu alamun zanyi nasara,kin kuma san dama ba da san raina na zuba kuɗi na a wasan nan ba, idan har kuɗina su ka salwanta bazan ƙyale shi ba”

“just bcox of five hundred thousand dollars kake wannan maganar akan brother nah?”
kallonta yayi da mamaki“its not a money?”
“no it's money, but ai kafi ƙarfin su, kuma banyi tunanin zaka iya furta wannan maganar akan Anthony ba”
“it's not my concern,kuɗina kawai na sani”

“sai ka bari idan kaga ba kayi nasara ba sai ka faɗi duk abun da zaka faɗa,ai har yanzu wasan ake”

murmushi takaici mutumin ya saki
“oh wai kina nufin har yanzu kuna da sa rai a wannan wasan,ƙazamin tunani kawai” ya faɗa yana kauda kanshi gefe, haɗa ido su kayi da wannan matar da mijinta, a tare su ka sakar mashi murmushi suna ɗaga mashi hannu, shima hannun ya ɗaga masu yana maida kanshi ga wasan.


Murmushi matar tayi“mi na faɗa maka kowa ya san cewa canza tarihin N R T ba abau bane mai sauƙi, ka dai ji wance magidanci ya saduda ta ƴan kuɗaɗen shi kawai yake” ta faɗa tana sakin murmushi, murmushi shima mijin nata yayi yana jinjina kai da faɗin“na tabbata...
_*Episode 7_8*_


*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘

_____________________________




Murmushi matar tayi“mi na faɗa maka kowa ya san cewa canza tarihin N R T ba abau bane mai sauƙi, ka dai ji wance magidanci ya saduda ta ƴan kuɗaɗen shi kawai yake” ta faɗa tana sakin murmushi, murmushi shima mijin nata yayi yana jinjina kai da faɗin“na tabbata”




mai da hankalin su su kayi akan wasan,wasan ne ya fara canza salo kamar walƙiya sai ga dokin dake baya sama da ko wane doki ya zama shine a tsakiyar dawakai biyun dake gaba, kamar a mafarki masu kallon wasan ke kallon ikon Allah,tashi wannan magidanci yayi yana jan tsaki ya kalli matar shi


“kin dai ji abun dana faɗa maki sisi na ban yarda tayi ciwo ba” yana gama faɗa ya bar wurin gaba ɗaya, taɓe baki matar tayi ita har a lokacin ba taga wani alamar rashin nasara ba tunda dai ba'a gama wasan ba.


fita dokin yayi daga cikin jerin dawakai biyun daya shiga ya zama shine ke biye da dokin dake gaba sai dai akwai ƴar tazara a tsakaninsu,sosai dawakan ke gudu cike da karsashi suna tunkarar matsayar wasan in da ya kasance nan ne ƙarshe duk wanda ya riga isa shine ya lashe gasara.


hankalin mutane dake sa ran cin gasar ne yayi matuƙar tashi, tuni zufa ta shiga wanke wasu daga cikin su saboda maƙudan kuɗin da su ka zuba wanda suke ganin suna gab da yin asara,seconds Biyar ya rage a kammala wasan,bai wuci taku kaɗan ya ragema dokin dake gaba ya isa matsayar wasan, kamar walƙiya wannan farin dokin ya gita ta gabanshi ya riga shi isa matsayar, da sauri ma hayin dokin yaci birki rai a ɓace ga ci yana gani amma ya rasa.

Ihu da sowa ne ya fara tashi a wurin wasan haɗe da kiɗe kiɗe, a fusace ɗai ɗai kun mutane su ka fara tashi suna barin wurin wasan,birki dokin yaci cike da kuzari mamallakin dokin ya sauko, da sauri wasu matasan ƴan mata su biyar suna sanye da riga da skirt iya gwiwar su, rigar white color yayin da skirt ɗin ya kasance black color aƙalla kowace a cikin su zata kai kimanin shekara 28 zuwa 30,cikin filed ɗin su ka nufa a gaban wannan dokin su ka tsaya ɗaya na riƙe da water bottle yayin da wata ke riƙe da ɗan ƙaramin towel wacce tafi kowa girma a cikin su ce take goye da backpack sauran biyu babu komai a hannun su sai sakin murmushi su ke, wani matashi sauarayi ne ya amshi dokin, helmet ɗin dake kanta wacce aka rubuta Queen a jikinta ta zame tabarakallahu ahsanul kaliƙin na furta da ganin wannan maƙurara kyan.


fara ce tas doguwa kyakyawar gaske wacce idan akace kyau to fa anazuwa kanta an rufe babin kyau,tana da idanuwa masu matuƙar jan hankali launin Acme white grey sai sheƙi su ke ga zira ziran eye lashes ɗinta da su ka ƙara ƙawata su,tana da siraran laɓɓa launin light pink masu matuƙar taushi tana da ɗan tsayin fuska hancinta a tsaye yake kem,tana da cikar gashin gira sai dai ba sosai ba,kanta ta ɗan girgiza yayin da take zame ɗan ƙaramin ribbon ɗin data ɗaure gashin kanta nan take wavy hair ɗinta launin light golding brown ta tarwatse a gadon bayanta ,tana da shape mai matuƙar ɗaukar hankali skin ɗinta sai sheƙi take tana salƙi kamar hasken rana bai taɓa raɓarta ba.


kissing neck ɗin dokin tayi tana ɗan sakin murmushin gefen baki har sai da dimples ɗinta su ka lotsa sosai murmushin ya ƙarama kyakyawar fuskarta kyau
“madam water”ɗaya daga cikin matan ta faɗa tana miƙa mata water bottle ɗin dake hanunta mai kyan gaske wacce a jikinta aka rubuta Queen, ya mutse fuska tayi ba tare da ta ko kalli in da matar take ba,wacce ke riƙe da towel a hanunta ce ta matsa kusa da ita daddaɗan ƙamshin turaren ta ne ya daki hancin matar har sai da ta lumshe ido duk da zufar da tayi haka bai hana dawwamamman ƙamshinta fita ba, a hankali ta shiga goge mata zufar da tayi,jefi jefi mutane su ka shiga ƙarasowa cikin field ɗin suna mata congrat yayin da take ya mutse masu fuska ba tare da ta amsa masu ba hakan bai dame su ba saboda sanin halinta sunma samu sa'a yau da har ta tsaya harma take yamutse masu fuska.



barin wurin matashi yayi da dokin, ɗaga ma dokin hannu ta shiga yi tana faɗin“ i miss u” murmushi matan su ka saki,fly kiss ta ma dokin tana sakin murmushi,bata bar wurin ba har sai da ta daina ganin dokin tukun ta bar wurin yayin da matan ke biye da ita har gaban wasu motoci guda bakwai,guda shidda rang robbers ne yayinda su ka saka wata farar Rolls Royce tsakiyar su sai ɗaukar ido take,body guards ne tsaye a bakin motocin Aƙalla za su kai su biyar ban da drivers ɗin da da su kayo driving motocin,cikin girmama su ka shiga gaishe da ita suna tayata murnar lashe wasan, babu wanda ya samu arziƙin data amsa mashi sai ma nufar wannan fara rolls royce ɗin dake tsakiyar motocin tayi, da sauri ɗaya daga cikin su ya buɗe mata back seat ta shiga,komawa su kayi cikin motocin harda wannan matan,a jere su ka hau wani dogon titi a cikin wurin wasan.


A kishingiɗe take a cikin motar ta lumshe idanunta yayin da sanyin Ac ke ratsata, tafiya mai ɗan nisa su kayi kafin su ka nufo wani katafaren gate ga wasu irin jibga jibgan security guard a bakin shi, horn driver dake gaba yayi, babu ɓata lokaci security guard ɗin su ka buɗe masu gate,da gudu motocin su ka kunna kai ciki security guard ne ke kai kawo ta ko ina na wurin, titi ne su ka sake miƙewa shantal, wani ɗan ƙaramin gate na ɓakin ƙarfe wanda ya kasance shara shara kana iya hange ciki su ka nufo, wani remote driver dake gaba ya danna nan take gate ɗin ya buɗe ciki su ka kutsa kai ciki.

masha Allah na furta da ganin irin haɗuwar wurin ,ƙatafaren luxury skyscraper ne iya ganinka, ta ko ina ka kallah a jikin ginin gilasai ne masu matuƙar ɗaukar ido A ƙalla yana da sassa guda shidda,harabar gidan kanta abun kallo ce lion water fall ne a tsakiyar gidan yayin da yake fitar da ruwa da styel daban daban, security guard ne ke kai kawo a ko ina na harabar gidan.



A bakin skyscraper ɗin su kayi parking da sauri ɗaya daga cikin security guard ɗin ya fito ya buɗe mata car door,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa,gaba ɗaya matan gaban motar da take ciki su ka zo su ka tsaya, a hankali ta zuro ƙarta kafin ta fito gaba ɗaya, security guard ɗin dake kai kawo ne su ka shiga rissinawa suna gaishe da ita, hannu kawai ta ɗaga masu kafin a hanzarce ta nufi gidan matan nan na take mata baya,a bakin main entrance ɗin gidan suka tsaya,wata irin haɗaɗiyar ƙoface ta glass,sai ta fuskarta tayi a jikin wata na'ura dake manne jikin ƙofar wacce nake kyautata zaton face ID ne magana na'urar ta fara cikin harshen turanci
“welcome back home miss NAILARH”



zugewa ƙofar ta shigayi, kutsa kai su kayi ciki, wani katafaren parlorn ne su ka shigo,painting cikin shi sliver glod ne, an ƙawatashi da manya manyan sofas jigunannun gaske masu matuƙar taushi da daɗin zama set huɗu sai throw pillows dake kan ko wace sofa, daga tsakiyar parlorn round glass table ne an jera flower vase masu matuƙar kyau, daga saman ceiling ɗin ginin crystal chandeliers ne golding color masu girman gaske an ƙawata su da kwalliya, sai faskekiyar flat creen tv mai matuƙar girma ta mamaye kusan rabin bangon da take sai kayan sauti dake gefe da gefen tv, sparkling floor lamps ne ajiye a ƙasa suna bada haske mai launika daban daban, ga dogayen curtains wanda aka ƙawata da zanen furanni kewaye da parlorn an zuge su,idan ka kalli ƙasan parlorn wanda ya kasance na glass wasu irin kifaye ne masu launika a jikin su suke shawagi.


komai na cikin parlorn golding color ne hatta stairs case ɗin dake ciki,A ƙalla floor ɗin na ɗauke da parlor biyar harda wannan wanda ya kasance shine babba a cikin su kuma yake a tsakiyar su, daga cikin parlorn zaka iya hangen sauran falukan dake floor ɗin,masu karatu ba ƙaramar dukiya aka kashe a wajen haɗa wannan parlorn ba idan nace sai na fayyace maku komai dake cikin shi to tabbas anan book one zai ƙare,kawai ku ida ƙissma sauran a zuciyar ku.


ma'aikata ne ke kai komo a cikin parlorn, zubewa su ka shigayi akan gwiwowunsu suna kai gaisuwa gareta, ko kallon in da suke ba tayi ba.


glass elevator su ka nufa,ɗan yatsanta tasa a jikin na'ura dake jikin ƙofar elevator nan take ƙofar ta buɗe, ciki ta shiga tana lumshe idanunta alamar gajiya,mara mata baya ma'aikatan su kayi,ɗaya daga cikin ma'aikatan ce ta danna wasu madanni dake ɗauke da nombobi a jikin su,ƙofarce ta shiga zuge, sama elevator tayi da su, daga ta ciki zaka iya hangen manya manyan parlor kan da suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login