Showing 45001 words to 48000 words out of 88290 words
Chapter 16 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
sabo a idonta amma duk wanda ke parlorn yasan cewa babu jituwa tsakanin mama Ameenah da mom kwata kwata bata sonta.
Mama Ameenah matace ga Abbah,ita ta haifi Aunty Adama,ita ka ɗai ta rage a matan Abbah,kwata kwata bata ƙaunar mom.
“mun same ku lafiya?”
“ga zahiri kuwa kin gani” mama Ameenah ta faɗa tana nuna kanta da hannu, murmushi ne ya bayyana akan fuskar mamy da su Hajiya fatilah da alama abun yayi masu daɗi.
shiru mom tayi ba ta sake cewa komai ba,gaishe da mama su Yumnah su kayi, a taƙaice ta amsa masu tana sauke idonta kan Nainarh da duk tasha jinin jikinta.
“ita kuma wannan ina aka sameta?” mama Ameenah ta faɗa tana nuna Nainarh da hannu,faɗuwa gaban Nainarh yayi,gaba ɗaya parlorn duban su suka kai ga Nainarh.
“ɗiyar Aminiyata ce Hajiya Asma'u” mom ta faɗa,jinjina kai mama tayi
“ziyara ta zo maki ko mi?”
“A'a wani iftila'i ne ya faɗama mahaifiyar ta,to shine na daw...” bata ƙarasa ba mama tayi saurin dakatar da ita
“to sai aka yi yaya,zama mi take cikin zuri'ata,ita mahaifiyar ta ta bata da dangi ne da bazaki barta a hannunsu ba,?”
“ba haka bane mama,zaman...”
“dan Allah dakata mana Zulaihart, wai sau nawa zance karki sake kirana da mama,banda jaza masifa ina ni ina haihuwar dangin sheɗan wanda Allah ya tsinemawa,ko nayi maki kama wannan tsohuwar banzar mai yawo ƙwauri waje??”
ƴar dariya mamy tayi tana kallon su Hajiya gaje
“Allah ya huci zuciyarki” mom ta faɗa tana tashi, ta nufi ƙofar fita daga parlorn, Yumnah idanunta har sun cika da hawaye bakomai yasa bata son zuwa part ɗin Abbah ba idan ba ranar Friday ba sai dan saboda wannan cin mutuncin da mama kema mom,tashi tayi tana kama hannun Nainarh da duk jikinta yayi sanyi.
Fa'iza ma ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba,tashi itama tayi ta bi bayan su da kallon mamaki mamy tabita har ta fice daga parlorn.
rai a ɓace Aunty Adama ta kalli mama Ameenah
“gaskiya wannan abun mama da ki ke a gaban ƴaƴa da jikokin ki bai dace ba,haba dan Allah da shekarunki zaki zauna yara na zugaki kina abu irin haka”
“kamarya yara na zugata, mi kike nufi Adama?”mamy ta faɗa rai a ɓace
“da mahaifiyata nake magana ba dake ba,karki ƙara sa man baki,kuma duk abunda take akwai mai zugata sama da ku ne?”
tsantsar mamaki ne ya bayyana a kana fuskar mamy wai yau ita Adama ke faɗama haka “lallai Adama Ni kike faɗa ma haka saboda Zulaihart?”
“fiye da haka ma sai ta faɗa maki mabaruka,gaba ɗaya ku babu mai hankalin data san abun da ya kamata,mama shekarunta sun ja tunaninta baya yake komawa,maimakon ku zama masu bata shawara idan kunga za tayi abun da ba dai dai ba amma saboda son zuciya kullum cikin birkita mata tunani kuke,babu wanda yafi bani haushi a cikin kuka sama da ke Safeenah” Aunty Mariya ta faɗa rai a ɓace tana kallon Aunty Safeenah
“ni mi nayi Aunty mariya,babu ruwana fa a cikin wannan abun?”
“dama zaki ce haka mana,akwai wanda ya ɗaure masu gindin yin abunda su ka ga dama sama dake,kina ƙanwar mazajensu ko kunya bakiji”
“da Allah ya isa haka mariya,ni ya kamata Ku rufe da faɗa ba su ba,kune za ace ma ko kunya ba kuji,kun fifita bare sama da ƴan uwanku musulmai,ko da yake ke barewa ai baza tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba”
“ko mi zaki ce mama a shekarunki wanan abun da ki ke bai dace ba” Aunty Mariya ta faɗa tana nufar wata ƙofa,da harara mamy ta bita har ta shige ɗakin,tsaki Aunty Adama taja tana bin bayan su mom.
“aikin banza dana wofi, kullum da an taɓa wannan dangin sheɗan ɗin sai su rufe mutane da faɗa kamar wasu ƴaƴan cikin su” Hajiya Gaje ta faɗa tana sake jan wani tsaki
“gaba ɗaya zanyi maganin su ne daga su har ita” a cewar mama Ameenah
“wallahi mama karki bari yarinyar nan ta zauna,ta maidata can dangin uwarta,haka kawai zata jajubo ma mutane gayyar tsiya inji ba uwarta bace ta kashe mahaifinta ba” Aunty Safeenah ta faɗa sai wani huci take.
“rabu da ita ai Tahir ɗin zai zo ya same ni,zanji idan shi ya bata damar ajiye wanann annobar a gidan shi”
mamy ranta fes kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,dama ta san muddin mama Ameenah taga Nainarh sai tasa an koreta daga Estate ɗin gaba ɗaya.
first floor mom ta koma, bedrooms ɗin dake floor ɗin ta nufa, toilet ta shiga yayin da Yumnah da Nainarh su ka zauna saman arm chairs ɗin dake bedroom ɗin, Nainarh hankalinta duk a tashe yake da abunda ya faru a part ɗin mama Ameenah,tunaninta yanzu wace irin rayuwa za tayi idan ta koma hannun dangin mahaifinta,kwata kwata basa sonta musamman yanzu da suke zargin mahaifiyarta da kashe mahaifinta,bare ace dangin mahaifiyar ta da ba nan suke ba,yanzu ita ya za tayi kenan...⁉️ _*Ep 21_22*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘
______________________________
sosai tayi nisa a duniyar tunani har mom ta fito daga toilet yumnah ta shiga bata sani ba,prayer mat Fa'iza ta shimfiɗa ma mom ɗin, wurin da Nainarh take ta nufo.
dafa kafaɗarta Fa'iza tayi, saurin kallon fa'izar tayi,murmushi Fa'iza ta sakar mata “ ina ta magana kinyi nisa a tunani baki ji,karki damu da maganar mama Ameenah babu in da za kije kina nan a tare da mu, ki kwantar da hankalin ki kinji”
murmushi kawai Nainarh ta sakar mata ba tare da tace komai ba, turo ƙofar ɗakin Aunty Adama tayi ta shigo,duban su suka kai gareta, cikin ɗakin ta ƙaraso, zama tayi kan chair ɗin da yumnah ta tashi tana fuskantar Nainarh, fuskarta ɗauke da murmushi tace
“kiyi haƙuri da halin kakar taku wasa take babu in da za kije, kina nan tare da mu har Allah ya kubutar da mahaifiyarki kinji”
murmushi Nainarh ta sakar mata
“nagode sosai Aunty, Allah ya bar zumunci”
“kar ki damu,ai yanzu munzama ɗaya, zansa yumnah ma ta kawoki gida ki zo man ziyara, ai zaki zo ko”
“Eh in sha Allah, nagode sosai Aunty”
“shikenan, tashi ki shiga toilet ki ɗauro Alwala ki zo kiyi sallah” da to ta amsa mata, tashi tayi ta nufi toilet ɗin, kusa da Yumnah ta zo ta kabbar sallah, bayan fitowar Nainarh Fa'iza ta shiga,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga gabatar da sallar zuhur, bayan da su ka kammala ne su Yumnah su ka fice aka bar mom da Aunty Adama a ɗakin.
main parlorn su ka nufa,a zaune su ka samu kairiyyah da Noor,ƙarasawa su kayi cikin parlorn, kusa da kairiyya yumnah da Nainarh su ka zauna.
suna a nan zaune parlorn Aunty Nafeesa da Aunty Nadiya su ka shigo,sun ɗau wanka Abaya maroon color yayinda Enaaya da Aneesarh su kayi ankon Pakistan dress riga da wando white color ,rigar da wandon sun sha adon sparkling stones,sunyi rolling Veil ɗin kayan a kan su,simple makeup ne a fuskarsu, kamar ko da yaushe eyes ɗinsu manne suke da sunglasses mai shegen kyau.
basu jima da shigowa ba Laatifa da Balqis su ka shigo tare da mom maryam da mom maimunatu, suma ankon Abaya su kayi yayinda mom maryam da mom maimunatu suka ɗau wankan tsadadden Swiss less naji da faɗa.
mom maimunatu ta so su shiga part ɗin mama Ameenah Amma mom maryam tace babu inda za ta sai dai mom maimunatu taje ita ka ɗai,duk yanda mom maimunatu ta so su shiga su gaishe da mamah ƙin zuwa mom maryam tayi sai ma tashi da tayi ta nufi bedroom ɗin da su mom su kayi sallah, itama sallah tayi.
*Queen Kainart💫*
A jere danƙara danƙaran motocinsu su ka shigo cikin estate ɗin yayinda motocin securitys Armys ɗin su suka sako su a tsakiya,katafaren parking space ɗin dake part ɗin Abbah suka nufa, daidaita parking ɗin su kayi, durowa security Armys ɗin su ka shiga yi daga motocin su,cikin girmamawa su ka shiga buɗe masu car doors, motar farko
Abbah ne ya fitowa hannunshi riƙe da sandarshi mai shegen kyau sai ɗayan ɓagaren dady ya fito, motar bayan su dady Ahmad ne da dady mustafa su ka fito bayan ta su sai tasu Uncle ubaid da Uncle mutallaf su ka fito daga nan sai Uncle hashim.
bayan motocin su sai na jikokin Abbah,a mota ɗaya ya Naeem da zaabith su ka fito motar bayan su ya Adnan da ya usman, ya Ahmer ne su ka fito bayan tasu ne sai ta su Irfan da Waseef su ka fito waseef riƙe da hannun Jamal a front seat na motar da su ka fito Aman da Ammar su ka fito su ukku sun sha ankon white jallabiya harda Arb turban a kansu ba ƙaramin kyau su kayi ba kamar ka sace su ka gudu, motar bayan su Fa'iz da Yazdan ne su ka fito sun ɗauki wankan farar shadda kamar sauran, kawunan su a sanye su ke da huluna hakan ya ɓoye tarin sumar dake kansu.
gama fitowar su kenan daga motocin su motocin her excellency salima suka kunno kai cikin estate ɗin,da katawa su kayi har motocin su ka ƙaraso parking space ɗin, sai bayan da su ka gama daidaita parking ɗin tunkun ɗaya daga cikin securitys ɗin ya buɗe mata car door ta fito,masha Allah na furta a sanye take da lafaya white color ta yafa gyale saman kanta, fuskarta ɗauke take da simple makeup kyawawan eyes ɗinta a manne su ke da farin shade mai shegen kyau.
wurin Abbah ta nufo cikin takun ƙasaita yayinda PA ɗinta ke take mata baya, cikin girmamawa ta gaishe da Abbah, da kulawa ya amsa mata
“ina ki ka baro man Amaryata na ganki ke ka ɗai?”
“ bata jin daɗi ne”
“subhanallah, mike damunta?”
“ta dai ceman zazzaɓi na damunta, da tare zamu zo to sai da muka shirya kuma taji bata iya zuwa jikin ya ɗanyi zafi”
“ya salam, to Allah ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane” gaba ɗayan su da Ameen su ka amsa
“dr ya dubata kuwa?” uncle Mustafa ya faɗa
“eh dr James ya dubata”
“mike damunta yace?”
“zazzaɓin ne kawai” mom salima ta faɗa
“zazzaɓi kawai ne a wajenki?,ni dama na san Zaabith bazai iya kula man da ƴata ba,idan baza ku iya kula da ita ba ku dawo man da ita zan sa ƙwararren likita ya duba man lafiyar ɗiyata” ya faɗa yana zaro wayar shi daga Aljihun wandon shaddar shi.
Uncle Ahmad har ya buɗe baki zaiyi magana Abbah yayi saurin dakatar da shi dan ranshi ya ɓaci ya rasa miyasa Almustafa yake mashi haka, kullum gazawar su yake gani a wajen kula da ƴarsa,gaba ɗaya zuba mashi ido su kayi suna kallon ikon Allah, Zaabith duk yasha jinin jikinshi yasa bazai wuce rashin mutuncin da yayi mata bane ya haddasa mata zazzaɓi.
dialing number dr fawar yayi, bugu biyu yayi picking “hello fawar kana hospital ne?” on the other handa dr fawar ya amsa mashi da “Eh sir, kana buƙatar wani Abu ne?”
“kainart ce ba lafiya nake son kaje ka duba man ita”
“ok sir”
“thank u” ya faɗa yana rejecting call ɗin.
“amma kasan cewa gidan gomnati ba wurin shigar kowa bane haka kawai ?” Uncle Ahmad ya faɗa yana kallon Uncle Mustafa da yayi kicin kicin da fuska
“Irfan kaje kayi mashi rakiya zuwa Villa ɗin,idan kun isa ka kira ni ina son na san mike damunta da gaggawa”
“in sha Allah Uncle” Irfan ya faɗa yana nufar ɗaya daga cikin motocin da suka dawo,driver seat ya shiga, suna anan tsaye yayima motar key ya nufi main gate ɗin estate ɗin.
babu wanda Uncle Mustafa ya kalla a cikin su ya nufi ƙofar shiga katafaren garden ɗin gidan, murmushi kawai hajiya salima ta saki,Uncle Mustafa yanda mataƙar tsaurin akan ƴaƴan sa, bai haɗa soyayyar da yake masu da komai ba, zai iya ɓatawa da kai saboda ƴaƴan shi shikuma tashi ƙaddarar kenan son ƴaƴa,shiyyasa Kainart ke mugun tsoron ya san irin zaman da suke da Zaabith dan ta san muddin ya sani abun bazai yi kyau ba.
“bari na shiga ciki Abbah”
“to salima” Abbah ya faɗa, enterence ɗin shiga part ɗin Abbah ta nufa
“muje ko Abbah”dady ya faɗa
“kuje gani nan zuwa” da to suka amsa mashi,ƙofar shiga garden ɗin su ka nufa, dakatar da Uncle Ahmad Abbah yayi.
“zo Ahmad” dawowa yayi in da Abbah yake tsaye, kamo hannunshi Abbah yayi cikin nashi, wata ƙofar shiga garden ɗin su ka nufa daban da wacce su dady su kashiga,wasu irin shuke shuke ne a wajen masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali,ga wasu tsuntsaye masu ban sha'awa dake kai komo a cikin garden ɗin.
wasu ƙayatattun benchs dake ƙarƙashin wasu rukunin bishiyu su ka nufa,zama su kayi suna fuskantar wasu killatattun ruwa,kai tsaye baza'a kira su da swimming pool ba ga wasu tsuntsaye dake shawagi saman ruwan abun gwanin ban sha'awa.
“na san ba kaji abunda ɗan uwanka yayi maka ba,amma ina so kayi haƙuri kayi mashi uzuri” Abbah ya faɗa
“Abbah amma mi yasa kullum Al'mustafah yake ganin gazawata akan ƴar sa,ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin wani abu bai faru da ita ba”
“haka ne Ahmad,amma kafi kowa sanin halinshi,yanada saurin fushi ga zuciya musamman akan ƴaƴanshi shi kalar tashi ƙaddarar kenan shiyyasa nake son kuriƙa yi mashi uzuri idan yayi wasu abubuwan,yanzu na san yana can hankalinshi duk ba'a kwance ba saboda rashin lafiyar ɗiyarshi,da ƙyar yau yayi bacci mai daɗin,kayi haƙuri da ƙaddarar ɗan uwanka”
“shikenan Abbah komai ya wuce a wajena, Allah ya bashi ikon cinye ƙaddarar shi”
“Ameen ya Allah,ya fama da mutane,ina fata komai yana tafiya daidai??”
“Alhmdllh Abbah komai yana tafiya yanda ya kamata”
“masha Allah,labari yana samuna har gida daga mutane daban daban,suna kawo man labarin yanda komai ke tafiya,kuma Alhmdllh naji daɗin yanda kowa daya buɗe baki yake faɗin Alkairi a kanka,Na yarda da tarbiyyar ka da gaskiyar ka da riƙon amanarka,nasan yanda kake da tausayin talaka ina so Ahmad ka ƙara fiye da haka, kazama adalin shugaba kamar ɗan uwanka,ina fatan yanda ɗan uwanka yayi ya gama lafiya har yau ƙasar nan bata manta da ayyukan Alkairin sa ba,ina so kaima kowa ya buɗe baki ya faɗi Alkairin ka ko bayan saukar ka”
“in sha Allah Abbah zaka sameni fiye da yanda kake tunani”
“haka nake son ji,Allah yayi jagora”
“Ameen ya Allah” fira su ka shiga yi Abbah na ƙarfafa mashi gwiwa akan mulkinshi da bashi shawarwari.
Idan muka koma ɓan garen su dady wani ƙaton dinner hall su ka nufa dake cikin garden ɗin,gaba ɗaya zagaye yake da glass daga waje kana iya hangen abunda ke ciki,wasu irin zungura zunguran luxury dinner tables ne guda biyu masu ɗauke da chairs guda ashirin akan kowane table,daga saman floor ɗin wasu irin manyan crystal chandelier ne masu shegen kyau dogayen da su kamar za su sauko ƙasa,gaba ɗaya hall ɗin a zagaye yake da manyan curtains masu matuƙar kyau an zuge su.
hall ɗin an ƙawatashi da wasu tukwanan ƙasa dake ɗauke da furanni masu matuƙar jan hankali,chefs ne maza da mata da a ƙalla zasu kai su goma sai aikin jera warmers suke a saman tables ɗin,cikin hall ɗin dady su ka shigo bakin su ɗauke da sallama.
da sauri chefs ɗin su ka dakata da abunda su ke,cikin girmamawa su ka shiga gaishe su,da kulawa suke amsa masu,tunda su ka shigo suka sauke idon su a kan uncle Mustafa dake can zaune saman ɗaya daga cikin kujerun dinner table ɗin,ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai aikin jijjigata yake,bini bini yake kallon wayar shi haɗi da jan tsaki.
dinner table ɗin su ka nufa kwanansu kujera yaja ya zauna dady ne kawai bai zauna ba ya nufi uncle Mustafa,kujerar dake kusa da wacce ya zauna yaja ya zauna,dafa kafaɗarshi yayi,saurin kallonshi uncle Mustafa da baisan da zuwanshi wajen yayi ba.
“yanzu Mustafa duk dan saboda ƴarka ka shiga wannan yanayin?,
rashin lafiya ne ba wani abu ba amma duk kabi ka tada hankalin ka?”
“bazaka gane bane ya Tahir,ni ka ɗai na san yanda nake ji”
“taya zan gane tunda ni ban haifa ba, Al'mustafa ka rage wannan mugun son ƴaƴan da kake,duk kabi ka ɗaurawa kanka damuwa saboda ƴaƴa sai kace kai kaɗai Allah yaba ƴaƴa,akan ƴaƴanka ba kaji baka gani,haba!?” ɗan dakatawa dady yayi yana kallonshi kafin ya ɗaura da cewa
“yanzu abunda kayi ma matar Ahmad kana ganin ka kyauta kenan,karka manta yanzu kainart ta tashi daga ƙarƙashin kulawarka ta koma hannunsu,sun fika iko da ita,sannan ina so ka sani ko babu Aure a tsakanin su Ahmad mai iya riƙe kainart ne haka Zaabith,ka zamo mai kawaici a kan ƴaƴanka”
tunda dady ya fara magana ƙala Uncle Mustafa bai ce ba sai yanzu
“kayi haƙuri ya Tahir in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba,hankalina ne ya tashi ban san wane irin ciwo take na”
“koma wane irin ciwo take Adu'a ya kamata kayi mata ba abunda kayi ba”
“in sha Allah zan kiyaye,kayi haƙuri”
“shi zaka ba haƙuri ba ni ba” Dady ya faɗa,waige waige uncle Mustafa ya shiga yi ko zaiga Uncle Ahmad
“yana waje tare da Abbah,kaje ka bashi haƙuri”
“to” uncle Mustafa ya faɗa yana miƙewa ya fice daga hall ɗin.
tun suna ƙananansu suna matuƙar girmama umarnin dady har kawo yau da su ka mallaki hankalin su kuwa.
tashi dady yayi ya nufi in da su uncle Ubaid su ke ya zauna,matan ne su ka fara shigowa hall ɗin,Mama Ameenah ce a gaba yayinda su mamy ke biye da ita a baya,sai da su ka gama shigowa mom da mom maryam da mom Maimunatu su ka shigo bayan sun shigo ne yaran su ka fara shigowa.
Su Yumnah ne su ka shigo hannunta riƙe da hannun Ammar da Aman yayinda da Jamal ya maƙalƙale hannun Nainarh sai turo baki yake shi adole fushi yake yumnah bata riƙe hannunshi ba.
ɗaya bayan ɗaya su ka shiga shigowa, kowannan su ya shigo wajen zama yake nema ya zauna, table ɗin da su dady ke zaune su mom su ka zauna, kowaccen su na fuskantar mijinta yayinda mamy da su hajiya fatilah su ka cure waje ɗaya su da Mama Ameenah bako ta mazajen na su suke ba, sai hura hanci su ke sunama mutane kallon tara saura kwata.
ɗayan Table ɗin su Yumnah su ka zauna da sauran jikokin Abbah, a tare Abbah da Uncle Ahmad da Uncle Mustafa su ka shigo, suma wajen zama su ka nema su ka zauna,saida kowa ya gama samun wurin zama