Showing 72001 words to 75000 words out of 88290 words

Chapter 25 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

416

yawu miss Malika ta haɗe kamar ita aka nuna da gun ɗin.

magiya parlorn su ka shiga yima Aunty Sophia kan ta matsa amma ko gezau ba tayi ba.

hawayen da suka taru idonta tun ɗazu sai yanzu su ka samu damar zubo,wani irin Shaking jikinta ya shiga yi,canza direction ɗin gun ɗin tayi zuwa sama, crystal Chandelier ɗin dake ceilling tayi shooting,gaba ɗaya ya ruguzo ya faɗa kan center table dake parlorn,toshe kunnuwansu su ka yi in ka cire Aunty Sophia data kafe Nailarh da idanu hawaye na zuba.

hawaye ne su ka shiga sintiri a fuskar Nailarh,ita kuka Aunty Sophia kuka ga wani irin rawa da jikinta ke yi,jifa tayi da gun ɗin da gudu ta raɓa ta gefen Aunty Sophia ta nufi sama.

zubewa Aunty Sophia tayi kan gwiwoyinta,bin bayan Nailarh miss Malika da sauran masu aikin su ka yi,kallo su Alex Aunty Sophia tayi tace su tafi hospital,ficewa su ka yi dashi har time ɗin jini ke zuba.


tashi tayi tabi bayan su jiki a sanyaye dan taga halin da Nailarh take ciki,daga nesa ta hange su a home bar kasancewar glass wall ne a wurin,da sauri ta ƙarasa
a tsaye ta same su sunyi cirko cirko idanunsu a kan Nailarh dake tsaye ta ɗaga kwalbar wine tana ɗurama cikinta.

da mugun sauri Aunty Sophia ta faɗa ɗakin har tana bangaje wanda ke bakin ƙofa,a zafafe ta fisge kwalbar daga hannun Nailarh tayi jifa da ita nan take kwalbar ta fashe.


“mi yasa ki ka yi haka sophia?,atlest idan tasha zata samu relief” Malika ta faɗa, ko kallon inda take Sophia bata yi ba kamar ma bata san tana magana ba,cikin raunannar murya tace

“Nailarh idan rai ya ɓaci hankali baya gushewa,wannan abun da ki ke is not a solution,ko kin manta alƙawarin da ki ka yi man,mi yasa ki ke son maida hannun agogo baya,tell me mi ke damunki sai muyi solving matsalar tare???” cike da kulawa Aunty Sophia ta faɗa.

hannu biyu Nailarh tasa ta kama kwalar rigar Aunty Sophia,zaro ido su kayi gaba ɗayan su da mamaki su ke kallon Nailarh,Aunty Sophia ma da tsantsan mamaki take kallon Nailarh.

jijjigata Nailarh tayi cike da karaji tace “who is he,kalamanki na ranar da momy zata dawo sun tabbatar man dasa hannunki,tell me who's he??” ta ƙarashe maganar tana daka mata tsawa.

wani irin mugun tashi
hankalin Aunty Sophia yayi dan kwata kwata bata fahimci inda zancen Nailarh ya dosa ba “baby what are u talking about, please kiyi man bayani?”


“i said who is he answer me” Nailarh ta faɗa tana wani zare mata ido, hawaye ne suka wanke fuskar Aunty Sophia,girgiza mata kai ta shiga yi “believe me Nailarh ban san akan mi kike magana ba” gani tayi ɗakin na juya mata ga wani irin ciwo da zuciyarta ke mata,dafe saitin zuciyarta dake barazanar faso ƙirjinta ta fito tayi tana faɗin “my chest”gaba ɗaya ta tafi zata faɗi da sauri Aunty Sophia ta riƙota jikinta,gaba ɗaya ta faɗa jikinta
“please Aunty Sophia waye shi” Nailarh ta faɗa a hankali daga haka kuma bata sake cewa komai ba, jikinta ya saki alamar suma tayi.


fashewa Aunty Sophia tayi da kuka kamar ƙaramar yarinya..


*Ya Allah mike shirin faruwa dake Nailarh,mi ya faru a N R T*


*Back to N R T Dan muji abunda ya faru*

Track ɗin a cike yake maƙil ,ta ko ina ka duba mutane ne zazzaune a mazauninsu da aka tanada,Track ɗin ya cika Masha Allah,mutane ne daban daban daga garuruwa daban daban wasu ma ba daga ƙasar su ke ba.


kamar ko wane lokaci suna sanye da shirt da cap na track ɗin kamar yanda ya kasance al'adar wajen.


daga gefe manyan baƙi ne da, wasu daga cikin ƙasar su ke wasu kuma daga wajen ƙasar,suna zaune a mazauninsu na musamman wanda akatanadar masu,miss Malika na cikin manyan baƙi ta ɗau wankan Sheath gown kamar wata yarinya kanta sanye da haɗaɗirya hat mai net daga gabanta anyi mata ado da bird feather,su luna na daga gefenta tsaye,kiɗa da bushe bushe ne ke tashi a cikin Field ɗin.



dawaki ne aƙalla guda ashirin a cikin field ɗin,suna a killace cikin ɗan cage ɗin su a tsaye,kowa wane doki akwai mutum a saman shi,a shirye su ke umarnin fara gudu kawai su ke jira, Nailarh na daga tsakiyar dawakan saman dokinta.


wani baƙin doki ne a hannun damanta sai sheƙi yake yana ɗaukar ido,kallon wanda ke kan dokin tayi,daga yanayin shigarshi ta fahimci sabon ɗan wasa ne dan komai nasa daban yake da nasu hatta suturar dake jikinshi da helmet ɗin dake kansa,sosai ta zuba mashi ido tana kallo, banda idanunshi bata iya hangen komai daga fuskarshi,saurin kauda kai tayi ganin yana ƙoƙarin juyowa alamar ya fahimci ana kallonshi,kallon inda Nailarh take yayi,kallon ƴan seconds yayi mata ya ɗauke idonshi.


lokaci na cika aka basu damanr far gudu ta hanyar hura whistle,cike da karsashi dawakan su ka shiga gudu a cikin babban field ɗin, a tare su ka fara gudu abun gwanin ban sha'awa,sosai suke gudu kowa burin shi ya kai ga matsaya.


rarrabuwa dawakan su ka yi,shidda su ka yi gaba yayinda aka bar sha huɗu a baya,dawaki biyu ne cikin shidda su ka yi baya a dalilin karon da su ka yi da juna,hakan yasa suka koma bayan huɗu yayinda sha huɗu ke biye da su,sosai Dawakai biyu dake cikin sha huɗun su ka dage har sai da su ka cimma biyun dake gaban su suka zama su huɗu, huɗu na gaba huɗu na tsakkiya sha biyu a baya.


A wannan karan Nailarh ba tayi baya ba kamar na last wasan da su ka yi,tana cikin huɗu dake gaba,sosai ta dage dan ganin tayi nasara a wannan karon kamar ko yaushe.


Mutane kowa sai baza ido yake dan ganin yanda wasan zai kwashe,da yawan mutane na fatan Nailarh tayi nasara kamar ko wane lokaci yayinda wasu ba haka bane a zuciyar su burin su ta faɗi ko za su rage raɗaɗin kuɗaɗen su da suke asara a wajen wasan, murmushi kawai miss Malika ke saki cike da ƙwarin gwiwa take kallon wasan ta san cin galaba akan babyn tata abune mai wahalar gaske.


sosai su ka dage da gudun gashi har sun kusa isar ma matsaya amma dawakan nan uku na tare dana Nailarh, hankalin ta ne ya fara tashi ganin duk iya bakin ƙoƙarin da take dan ganin tayi masu zarra abun yaci tura, data ta samu ta kere masu sai su sake cimma mata.


duka ta kaima king dan a ganinta sakacinshi ne yasa har ta kasa tsere masu,ganin dai idan ba tayi wani abu ba komai zai iya faruwa ne yasa cike da dabara yanda alƙalan wasan bazasu lura da abunda take ba ta matsa kusa da dokin dake kusa dashi,cike da mugunta taja igiyar dake jikin dokin ta tarɗe ƙafar dokin,mahayin dokin baiyi auneba ba sai jinshi yayi ya tafi ƙasa har ya shafi dokin dake kusa da shi,gaba ɗaya su ka kifa ƙasa daga su har dawakan nasu,nan su ka shiga birgima a ƙasa,hankali tashe mutane su ka shiga miƙewa ganin abunda ya faru.


da gudu emergency officers
suka shigo cikin Field ɗin ɗauke da stretcher,ɗaukar wanda su ka samu rauni su ka yi suka ɗaura a stretcher su ka fice da su,juyawa Nailarh tayi tana sakin wani wicked smile ko a jikinta,yanzu ya rage saura su biyu daga ita sai wannan baƙin dokin,tunda yaga abunda tayi ya kafeta da ido yana kallon ta cikin helmet ɗin dake kanshi, fingers biyu yasa yayi saluting ɗinta,tsuke fuska tayi tana kauda kai.



haka aka cigaba da gabatar da wasan duk yanda Nailarh ta so yima wannan mai baƙin dokin mugunta kamar yanda tayi wacan abun ya faskara, ƙoƙarin kereta ma yake hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba gashi sun kusa isa Wining line,hankalin wasu daga cikin ƴan kallo ne ya fara tashi yayinda wasu ke fatan a karya tarihin N R T,ƙus ƙus ne ya fara tashi wasu na son sanin waye wannan dake neman yima Nailarh zarra dan da yawan mutane basu san shi ba.


hankali Nailarh sosai ya ƙara tashi, zufa duk ta wanke jikinta,tun tana ganin abun kamar wasa sai ga dokin nan ya ƙetare Wining line kamar a mafarki,wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi ba shiri taci birki tana haki,abunda bata taɓa kawo ma ranta ba ya faru da ita,miss Malika ma zabura tayi daga inda take zaune tana kallon field ɗin.



Ihu da sowa ne ya fara tashi a filin wasan, mutane da dama hakan yayi masu,da gudu securitys ɗin wajen suka shigo cikin field ɗin, tai maka ma duk mahayan dawakan su ka yi su ka sauko daga kan dawakan,tsaye Nailarh tayi a wurin kamar idol, ta kasa motsawa in a shock take kallon field ɗin dan har yanzu ta kasa yarda da hakan gaskiya ne.


Murna wajen mutanen da su ka daɗe suna jin haushin Nailarh ba'a magana, dama da yawan su irin wannan ranar su ke fata gashi kuwa ta riske su.


cikin field ɗin mutane su ka fara shigowa suna nufar wannan mutumin da har yanzu yaƙi cire helmet ɗin dake kanshi haka ma Nailarh,hannu mutane su ka shiga bashi suna taya shi murna wasu kuma na hugging ɗin shi.



tunda ya sauka kan dokin idanunshi ke kan Nailarh ko ƙiftawa bayayi ganin mood ɗinta, walking majestically ya nufo inda Nailarh take still he's eyes on her kuma har time ɗin bai zame helmet ɗin dake kanshi ba,tunda ya tunkarota take kallon shi, yana da tsayi sosai dan ya kereta sosai duk da tana da tsayi, ƙaƙƙarfa ne na gaske yanada broad chest dan tana iya hangen shatin six pack ɗin shi ta jikin polo shirt ɗin dake jikin shi, ga wasu strong arms dake a murɗe, kallo ɗaya za kayi mashi ka gane gym product ne, bazaka iya tantance kalar fatar jikinshi saboda jikinshi dake a rufe.


saurin ɗauke idonta tayi daga kallonshi tana tsuke fuska, har inda take ya ƙaraso, ɗan rissinawa yayi dai dai saitin kunnenta ya kai bakinshi, whisper ya shiga yi mata, bazaka iya jin mi yake cewa ba, a hankali yake magana kamar baya son buɗe bakinshi,wani irin kishi ne ya turniƙe miss malika ta tsani taga wani ya raɓi Nailarh, wani irin kallon wulaƙancin ta shiga binsu dashi zuciyarta na wani irin tafarfasa.



sun kai five minute a haka kafin ya janye bakinshi daga kunnenta, saurin kallonshi Nailarh tayi, from head to toe yake kallonta ta cikin helmet ɗin kafin yayi saluting ɗinta a hankali yace “nice to meet u cutie,see u next time, have a nice day” ya faɗa yana ɗaga mata hannu,barin wurin yayi wani irin ƙara ɓaci ran Nailarh yayi.



da sauri Luna da sauran maids suka nufota Miss Malika na bayan su, hannu luna ta kai da nufin cirema Nailarh helmet ɗin kanta, saukar wani irin azabebben mari taji,saurin dafe cheek ɗinta tayi tana kallon Nailarh data mareta,a masifance ta zame helmet ɗin kanta tayi jifa dashi, jiki na ɓari malika ta nufota, kafin ta ƙaraso Nailarh har ta bar wurin ta nufi motocin su maganganunshi na yawo a brain ɗinta.


da sauri Alex ya buɗe mata back seat ko jiran su malika ba tayi ba tace ya kaita gida,Malika suna isowa suma motocin su suka shiga, da mugun sauri su ka bi bayan su Nailarh, a kusan tare su ka yi parking,ko gama daidaita parking driver baiyi ba Malika ta fito ta nufi Nailarh, tana isowa Nailarh na fitowa da gun a hannunta, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, saita kanta Nailarh tayi da gun ɗin da nufin shooting kanta.


hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Malika yayi ba,umarni taba securitys da drivers ɗin dake wurin da su amshe gun ɗin, garin su amshe ne Nailarh ta harbi Alex.


*back to story*


Jijjigata Aunty sophia ta shiga yi tana kiran sunanta,miss Malika ma kamar za tayi hauka wajen kiran sunan Nailarh, ɗaya daga cikin chefs ne ya nufosu da ruwa, da sauri Aunty sophia ta amsa tana yayyafama Nailarh amma ko gezau ba tayi ba, tayi hakan kusan sau huɗu amma Nailarh bata farfaɗo ba,wani mummunan faɗuwa gaban Aunty sophia yayi haka ma miss Malika, tsoron kar ace ciwan Nailarh ne ya tashi ne ya mamaye zukatansu yaushe rabon da Nailarh ta samu Attack, dan suna kula da duk wani abun da zai ɓata ranta, komai ta buƙata yi mata su ke.

*Nailarh tunda aka haifeta take fama da haert Attack infact ma dashi aka haifeta, shiyyasa duk wani abu da zai faranta ranta miss malika na ƙoƙarin yi mata shi,haka Aunty Sophia bata wasa da lafiyar Nailarh duk wani abu da zai faranta mata tana ƙoƙarin yi mata tana kumakiyaye abunda zai ɓata ranta bare harya kai da ciwonta ya tashisai ta yi mi bata samu Attack ba dan duk abunda take so a rayuwa shi take samu*


hawaye su ka wanke fuskar Miss Malika, maids ɗin dake wurin wasu har sun fara zubar da ƙwalla

Jijjigata miss Malika ta shiga yi tana faɗin “please Nailarh wake up, I promised u to punish this man and sai ya girbi abunda ya shuka,sai yayi daya sanin shigar shi gasar nan, please wake up dear” kamar mahaukaciya haka take jijjiga Nailarh tana roƙonta akan ta tashi,Aunty Sophia banda hawaye babu abunda take.


“Please Nailarh, don't leave me, please wake up, I promised you, I promised u sai yayi daya sani,nayi maki alƙawarin zanyi mashi hukunci mai tsanani, don't leave me please wake up” Sosai take sambatu tana roƙon Nailarh,wani tausayin miss Malika ne ya rufe maids ɗin dan daga yanayin da take magana kamar bata cikin hayyacinta,da ƙar Aunty Sophia tayi ƙarfin halin faɗin


“Ma'am,I think she's on attack” Aunty Sophia ta faɗa tana share ƙwalla
ƙara rikicewa miss Malika tayi jin abunda Aunty Sophia ta faɗa.


zabura tayi da nufin ɗaukar Nailarh

“please tell Alex to bring the car, Sophia let's go to the hospital, I don't want to lose Nailarh” magana take tana ƙoƙarin ɗaukar Nailarh amma ta kasa,gaba ɗaya a gigice take har ta manta da abunda ya faru da Alex,da sauri luna ta fice dan sanar da NOAH saƙon miss malika,shima ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan ne.


da sauri William ya ƙaraso cikin ɗakin,hannu biyu yasa ya ɗauki Nailarh,a shoulder ɗin shi ya ɗaurata,gaba ɗaya jikinta ya saki kamar mattaciya,ficewa su kayi daga cikin ɗakin baki ɗaya,miss Malika kamar zata tashi sama,Aunty Sophia kuwa sai sharar hawaye take.


NOAH har ya shiga Mota yayi mata key,jiran fitowar su kawai yake,back seat ɗin motar William ya saka Nailarh Aunty Sophia ta shiga kusa da ita yayin da miss malika ta shiga front seat,reverse yayi suka nufi main gate ɗin gidan, securitys ɗin ma shiga motocin su su ka yi harda su luna su biyu,bin bayan motar su miss malika su ka yi.


komawa bakin aikinsu suka yi sauran securits ɗin da aka bari,cikin gida chefs ɗin su ka koma wasu na jimami yayinda wasu ke sharar ƙwallar tausayin halin da Nailarh take ciki.


*Get well soon Nailarh,to be honest wannan bawan Allah baka kyauta ba😢*



*ABUJA NIGERIA*


*UNCLE MUTALLAF'S HOUSE*



saukowa yake daga saman stairs, walking gently yake taka stairs case ɗin,white suit ne a jikinshi,waya ce kare a kunnenshi.


“gaskiya I'm really happy yaya da wannan maganar,amma nayi mamaki da ban taɓa fahimtar hakan ba” saurin ɗaga kai mom fatilah dake zaune a parlor ita da Noor tayi tana kallon uncle mutallaf,kallo ɗaya za kayi mashi ka hango tsantsar farin cikin da yake ciki.


cikin parlorn ya ƙaraso,ɗaya daga cikin sofas ya nufa ya zauna “wallah da gaske nake yaya ban taɓa lura da hakan ba,kuma kasan duk rashin kunyar Noor Bata taɓa faɗa man ba” da sauri Noor ta tashi ta nufi dadynta jin abunda yace,saurin kai kunnenta tayi jikin wayar wai ko za taji dawa dadynta ke waya.


ture kanta yayi yana sakin dariya “kaji ja'iri wato shi mai kunya shine sai ya aiko maka abokinsa” ƴar dariya yayi yana gyara zaman shi

“to shikenan in sha Allah zuwa goben sai muyi magana,amma gaskiya nayi farin ciki da hakan Allah yasa ayi muna da rai,amma Abbah da yayan sun sani kuwa?”
ɗan jim yayi yana sauraron na cikin wayar can yace


“ok to shikenan Allah ya kaimu sai na shigo goben in sha Allah” sallama yayi da wanda yake wayar
“dady kai da waye ka ke waya?” Noor ta faɗa cike da shagawaɓa
“kawunki ne, maza je part ɗina ki ɗauko man glass ɗina yana Nan kan nightstand”


“to dady,amma maganar mi kuke kai dashi?”
“idan kin dawo zan faɗa maki” saurin tashi tayi ta nufi stairs case da sauri, girgiza kai kawai mom Fatilah tayi.


iska uncle mutallaf ya shaƙa tukun ya fisar,yayi ɗan shiru yana nazarin wani abu
“lafiya dai Dr?” mom fatilah ta faɗa tana leƙen fuskar shi, ajiyar zuciya uncle ya sauke kafin ya kalleta



“ya Ahmad ne ya kirani,kin san cewa Noor da Irfan soyayya su ke?” yana yin fuskar mom fatilah ne ya canza,tsuke fuska tayi
“mi ya faru,kiran mi yake maka to?”
“ya kirani ne ya sanar dani har ma sun tattauna maganar shi da su ya Ubaid, Abbah da ya Tahir ɗin ne kawai ya rage basu sanarmawa ba,amma yace zuwa gobe zai sanar da su dan a san yaushe ya kamata a sa bikin na su,amma fa nayi mamakin da ban taɓa lura da suna soyayya ba duk abun Noor ma bata taɓa sanar dani ba” tunda ya fara magana mom fatilah ta shiga binshi da wani kallon rainin wayau,Noor saukowarta kenan taji abun da dadyn nata ke furtawa,da gudu ta nufi ɗakinta ba tare da ta ko kawo masa glass ɗin da yace ta ɗauko mashi ba.


“gaskiya naji daɗin haka,kinga kafin mu tafi sai a tsaida ranar Auren na su zuwa bayan sallah sai ayi bikin,yara nata ƙara mana daƙon zumunci,saura Yazdan fatana shima ya daina wannan shashanci ya zama mutumin ƙwarai kinga sai mu haɗa su shi da Yumnah” kallon mom fatilah yayi jin tunda ya fara magana ƙalla ba tace ba



“naji kinyi shiru ba kice komai ba,magana nake kana Auren Noor f...” saurin katse shi mom fatilah tayi
“dan Allah dakata Dr,wallahi sam ba zai yiwu ba”
da mamaki yake kallonta bai taɓa tunanin wannan ce kalmar zata fito daga bakinta ba.


“fatila kin san mi ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login