Showing 69001 words to 72000 words out of 88290 words

Chapter 24 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

424

rasa laifin mi su ka aikatama wanda yayi masu haka.



Adu'arta a kullum Allah ya toni asirin wanda yayi silar rushewar farin cikin su, shima Allah ya rusa nashi farin cikin, ya tozarta rayuwarshi kamar yanda ya tozarta ta su, sosai tayi nisa a duniyar tunani ringing ɗin wayar Yumnah ne ya dawo da ita hayyacinta, a jiyar zuciya ta sauke tana jawo jakar, wayar ta ciro, duba sunan mai kira tayi,ya Naeem ta gani.


da sauri ta ɗan bubbuga kafaɗar Yumnah “ki tashi ya Naeem na kira” juya kwanciya Yumnah tayi
“please ki ɗaga kice mashi bacci nake” picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunenta


“Assalamu Alaikum” ta faɗa, on the other hand ya Naeem ya amsa mata sallamar
“ya Naeem ina wuni”
“lafiya lau Yumnah, kun dawo ne ko har yanzu kuna school?”
“ba ita bace, Nainarh ce” Nainarh ta bashi amsa
“yawwa Nainarh dama ke nake nema, kun dawo daga school ɗin?”


“eh” ta bashi amsa
“ok,meet me in the garden now” a sakale ta amsa mashi,mamaki ne ya cikata, neman mi yake mata

“right now” ya sake jaddada mata haɗi da rejecting ɗin call ɗin


“ni kuma, neman mi yake man” ta faɗa da tsantsar mamaki, ajiye wayar tayi ta nufi toilet, bata wani jimaba ta fito, dressing room ta nufa, hijab ta ɗauko,ficewa tayi daga ɗakin.


bata samu kowa a parlorn ba, tun daga nesa ta hango su saman chairs shi da ya Adnan a garden ɗin, waya ce kare a kunen ya Naeem ɗin da alama waya yake, tunda ta tunkaro su ya Adnan ya kafeta da ido yana kallota harta ƙaraso in da su ke, sallama tayi masu ya Adnan ne ya amsa mata ya Naeem kuwa hannu kawai ya ɗaga mata.


Cike da ladabi tana ɗan rissinawa ta gaishe da Ya Adnan ɗin, da kulawa ya amsa mata yana sakar mata murmushi ya nuna mata chair dake fuskantar wacce su ke zaune dan ta zauna, murmushi ta saki “nagode” ta faɗa tana zama.


“ya school,fatan kun dawo lafiya?”
“lafiya lau Alhmdllh” masha Allah ya faɗa, hankalin su ne ya koma kan ya Naeem dake waya


“it's a favor i'm asking for, please ka taimaka ranar birthday ɗinka ka zo,ya ɗauki ranar birthday ɗinka rana mai daraja da mahimmaci, ka daure a wannan karon ka tabbatar mashi da darajar ranar,the anger u have with him is enough, dan Allah ka kawo ƙarshen wannan guje mashin da ka ke”

ɗan dakatawa yayi da magana ya can ya cigaba

“kayi shiru ba kace komai ba, ka sa ni yanda ya ke sonka ko mu dake tare dashi baya mana son da yake maka, baka tare dashi amma duk wani abu daya shafeka baya wasa dashi,ka sani duk abunda zaiyi mana a rayuwa sai yayi maka,more than u think,wasu har gani suke kamar ya samu taɓin hankali a kan ka saboda wasu abun da yake hankali ma bazai ɗauka, please yaci albarkacin wannan ƙaunar da yake maka kayi haƙuri ka daina wannan fushin da shi” sosai ya Naeem ya kwantar da murya yana bashi haƙuri duk dan ya sauko.


zuba mashi ido Nainarh da ya Adnan su kayi, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai waye wannan ake haɗashi da Allah irin haka amma yaƙi yayi abunda ake so.


“shikenan kayi duk abunda ka ke ganin shine dai dai, amma ka sani haƙƙin  baƙin cikin da kake cusa mashi bazai barka ba, he's ur father, ko wane irin laifi zaiyi maka aduniya he didn't not deserve to be anger with him” yana gama faɗar haka yayi rejecting call ɗin.


haka nan Nainarh ta tsinci kanta da rashin jin daɗin abun, bata san ko waye ba amma bai kyauta ba mahaifa ba abun wasa ba ne.


“in wuni ya Naeem”
“lafiya lau Nainarh, ya school”
da Alhmdllh ta amsa ma shi
“dama akwai wasu maganganu da nake son zamu tattauna game da abunda ya faru da dadynki”
tunda ya faɗi haka yanayin fuskarta ya canza, fahimtar hakan ne yasa shi cewa

“karki damu ba wani abu bane kawai ƴan tambayoyi ne zanyi maki,in dai ki ka bani haɗin kai in sha Allah za muyi nasarar gano wanda su ka kashe shi”

“in sha Allah zan baka haɗin kai, duk wani abu dana sani zanyi ƙoƙarin sanar da kai”

“yawwa haka nake son ji,
da na so muyi maganar yanzu,but bana da time, zuwa ranar Saturday za muyi magana ko kuje can gida keda Yumnah ku same ni”

“to shikenan, Allah ya kaimu”
“Ameen ya Allah, za ki iya tafiya kawai” to tace ta na tashi daga chair, sallama tayi masu ta koma cikin gidan, ranshi ya rigada ya gama ɓaci bayajin zai iya maganar da za suyi shiyyasa kawai ya sallameta. 


tunda Nainarh ta fito daga gidan ta nufo garden yake tsaye bayan pillar da waya a hannunshi, da alama video yake  ɗaukar su, baƙaƙen kaya ne a jikinshi ya rufe ko ina na jikinshi banda idanun shi babu wani abu da ake iya gani daga jikinshi.


Nainarh na tunkaro ƙofar shiga gidan yayi saurin ɓoyewa yana zura wayar Aljihun wandon jikinshi, kowaye da alama leƙen asiri yake masu.


ɗan dukan kafaɗar ya Adnan ya Naeem yayi ganin ya bi Nainarh da ido
“ya dai,lafiya ka kafe yar mutane da ido ka ke binta da wannan kallon ƙurillar?”

kauda kai gefe  ya Adnan ɗin yayi yana sakin murmushi 
“ba komai, kawai dai tana burgeni ne she's so innocent” murmushi ya Naeem yayi
“ka tsaya dai iya haka”

dariya ya Adnan ɗin yayi yana girgiza kai “ya ku ka yi da SAM ɗin ya amince kuwa?” ya Adnan ya faɗa yana kallon fuskar ya Naeem, tsaki ya Naeem yaja

“ka kyale SAM kawai Adnan,na rasa gane  wane irin bauɗaɗɗan mutum ne shi, Allah ma muna mashi laifi ya yafe mana sai shi ne bazai yafe ba, na rasa a wajen ubanwa ya gaji wannan baƙar zuciyar da idan ya juyama abu baya ya juya mashi kenan?”

“uncle Mustafa shi ka manta tashi kalar zuciyar ne?”
“uhmmm Allah gara uncle Mustafa dashi, tsawan shekara nawa kenan ana fama dashi amma ya maida mutane shashashu, ka du ba fa ka ga irin haukan da dady keyi a kan shi wannan bai isa ba ace ya yi haƙuri,bawan Allah nan sau nawa yana taka ƙafa ya bishi amma haka zai ƙaraci zamanshi ya dawo bazai taɓa ganinshi ba haba” ya ƙare maganar cikin fushi


“Allah ya kyauta, amma SAM lamarin shi sai shi, ni kaina sai na kusa haɗa shekara banji muryarshi ba” ya Adnan  ya faɗa
“wallahi zanyi mashi maganin abun da ke damunshi ne” murmushi ya Adnan ya saki
“ai da yake kunfi kusa, dama da kai yake uban ba da dady ba” tsaki kawai ya Naeem yaja.


*Queen Kainart💫*


tafe take kwata kwata bata lura da mutum dake tahowa ba duk da ƙofar ta glass ce,shima hankali shi baya gaban shi yana a kan wayarshi da yake latsawa.

saurin ja da baya tayi dalilin karon da su ka yi,wayar dake hannunshi ta faɗi ƙasa, dafe goshinta da ya bigi broad chest ɗin shi tayi,wani irin zafi ne ya ziyarci kwakwalwarta, a masifance ta ɗago tana kallonshi ido cikin ido

“dallah malam baka gani ne or are u blind da ka ke tafiya baka kallon gabanka??” ta faɗa tana wani zazzare mashi ido, wani irin haushin shi da tsanar shi take ji a ranta.


kasa magana yayi saboda mamaki daya rufe shi, ta bugeshi har ta yar mashi da waya ƙasa amma ta rufeshi da faɗa kamar wani sa'anta,mamakinshi ma a ina ta samu confidence ɗin yi mashi rashin kunya.

harara ta sake watsa mashi haɗi da  jan tsaki,raɓawa tayi ta gefenshi zata wuce, rai a ɓace ya fisgo Arm ɗinta, gaba ɗaya ta tafi taga taga zata faɗin, riƙota yayi sosai, idan da abunda ya tsana a rayuwarshi tsaki, ya tsani tsaki musamman ace mace ce tayi mashi shi.

Raba idanu ta shiga yi a fuskarshi, ba ƙaramin tsorata tayi da yana yin shi ba,cike da mugunta ya sake matse hannunta,saurin rintse ido tayi saboda wani zafi daya shigeta.


Murya a kausashe yace “wa ki ke ma tsaki?” banza tayi da shi ƙoƙarin ƙwace kanta kawai take daga riƙon da yayi mata, tsawa ya daka mata “tambayarki nake wa ki ke ma tsaki??” ya faɗa yayin da yake murɗe hannunta

fashewa tayi da kukan azaba, murya na rawa tace “ai ba da kai nake ba”
“dawa ki ke” ya faɗa fuska a ɗaure
“dan Allah kayi haƙuri”
“tsaran wasanki ne ni?” girgiza mashi kai tayi hawaye na bin cheek.


“bani wayata” ya faɗa yana nuna mata wayarshi dake yashe a ƙasa
“ka sakar man hannu to” sakin hannunta yayi, duƙawa ƙasa tayi ta ɗauko mashi wayar
“gashi” ta faɗa tana turo mashi baki.


amsar wayar yayi yana sake riƙe hannunta “this should be the first and last time da za kiyi gigin yiman rashin kunya if not, sai na ɓaɓɓalaki a gidan nan useless”

“IRFAN” su ka ji an faɗa a bayan su.

saurin sakin hannunta yayi yana juyawa bayanshi,dady ne da uncle hashim,tun lokacin da su ka yi karo su ke tsaye suna kallon su.

hannunta da Irfan ɗin ya riƙe ta shiga murzawa saboda zafin da yake mata

“Irfan mi ya haɗaka da ita?” dady ya faɗa
“babu komai, ina wuni Uncle”
“lafiya lau” uncle hashim ya faɗa, saurin barin wajen Irfan yayi ya nufi garden wajen su ya Naeem.


“zo nan Nainarh”dady ya faɗa yana mata alama data zo, nufo su tayi har time ɗin hawaye na bin kumatunta, hannu dady yasa ya shiga share mata hawayen
“kukan ya isa haka, mi yasa ki ka yi mashi rashin kunya?”
“babu komai”
“he's ur elder brother, kar na sake gani,kina jina ko”
“eh dady in sha Allah bazan sake ba”


“haka nake son ji, ga Uncle ɗin ku nan ku gaisa” ya faɗa yana nuna mata Uncle hashim dake tsaye yana kallonsu
“in wuni Uncle”
“lafiya lau, ya ki ke, ya school??”
“lafiya lau Alhmdllh”
“masha Allah, Allah ya taimaka”
da Ameen ta amsa tana barin wurin ta nufi bedroom ɗin su.

tana shiga bedroom ɗin saurin zame hijab ɗin jikinta tayi tana kallon hannunta da Irfan ɗin ya riƙe wurin har yayi ja.


wasu hawaye ne su sake taruwa a idonta “mugu kawai” ta faɗa tana turo baki.



*Queen Kainart*💫


“muje ko” ya dady ya faɗa yana kallon Uncle hashim
“gida zan tafi”
“tafiya dai hashim, ai ka shiga ku gaisa da Zulaihart ko?”
“A'a yaya tafiya zanyi, idan na sake dawowa mun gaisa”
dady ya faɗi haka ne kawai amma dama ya san uncle hashim bazai tsaya ba in dai dan su gaisa da mom ne
“shikenan ka gaishe da mutanen gidan”
“za su ji, sai anjima” jin jina mashi kai dady yayi yana nufar sama zuwa part ɗin shi.


ficewa uncle hashim ɗin yayi amma instead of ya fice daga gidan baki ɗaya sai ya nufi part ɗin Mamy, bai samu kowa a falonta ba, masu aiki na part ɗin su Fa'iza na gidan shi wurin Balqis.


direct bedroom ɗinta ya nufa, bai sameta a ciki ba sai ƙarar ruwa da yaji a cikin toilet alamar tana ciki.


bed ɗinta ya nufa, zama yayi yana kwantar da kanshi jikin head board, wayarta dake ajiye kan nightstand ya ɗauka, babu password a wayar hakan ya bashi damar shiga contact da messages ɗinta.



turo ƙofar toilet ɗin tayi ta fito tana yarfe hannunta da alama alwala tayi, da mamaki take kallonshi bata san yaushe ya shigo ba, mamakin ganinshi a irin wannan lokacin ne ya hanata ƙarasawa gare shi.


wayarta dake hannunshi ya ajiye yana zuba mata mayatattun idanunshi “ƙaraso mana ki ka tsaya nan” ya faɗa ganin tayi tsaye kamar an dasata.


cikin ɗakin ta nufo kamar yanda ya umarta “yaushe ka shigo, baka tsoron wani ya ganka a irin wannan lokacin??” jin jina mata kai yayi alamar eh
“eh fa kace, baka gudun yayanka ya shigo gidan?”
“tare mu ka shigo da shi, yana part ɗin shi”
“amma shine ka shigo part ɗin, baka tsoron ya shigo part ɗina??”


“wait mabaruka kinyi farin cikin gani na ko na tashi na kama gabana?” ya faɗa yana ɗan tsuke fuska alamar rashin jin daɗin tambayoyinta
“kaima ka san am really happy to see u but kawai dai bana son abunda zai jawo mana matsala”


sauka yayi daga saman bed ɗin ya nufo inda take, kama hannunwanta yayi ciki nashi
“naga hankalinki bai kwanta da zuwana ba,lee me go” ya faɗa yana sakin hannunta, saurin kamo hannunshi tayi
“tunda har kai hankalinka a kwance yake bana da wata matsala”


“are u sure?”
“really sure, kai da kazo ma baka damu ba sai ni daka iske”
a jiyar zuciya ya sauke yana wani lumshe ido
“why did u not pick my call yesterday?”
“am with u brother, ka san jiya a wajena yake”


“mi yarinyar can take har yanzu bata bar gidan nan ba?”
tsaki taja “hmmm ka bari kawai u know ur brother yanda yake da matarshi komai tayi dai dai ne a wajansa, duk wata hanya na bi dan ganin ta bar gidan nan har mama Ameenah na sanar mawa tace za tayi mashi magana amma shiru, dama nayi mashi maganar sai shata man layi yayi akan yarinyar, wani mugun sonta yake ga yarinyar da ɗan banza kilibibi, duk wata hanya data san zata bi danta samu shiga a wurinshi sai da tayi”


“alright, amma dole yarinyar nan ta bar gidan nan kema kin san da haka?”
“i know,  in sha Allah zanyi iya bakin ƙoƙari na ganin tabar gidan nan” jawota yayi zuwa jikinshi, cikin wata irin shu'umar murya yace
“alright, yaushe zaki bar ya Tahir ki dawo gare ni, na gaji da wannan raba dai dan da nake dashi” ya faɗa yana wani lumshe ido


“ko a yanzu a shirye nake, umarninka kawai nake jira” sake matso da ita yayi jikinshi, hannunshi ya zura bayanta, zip ɗin rigarta ya shiga zugewa, a hankali ya furta “har yanzu burinmu bai cika ba mabaruka”

“don't worry about that, nan da wani lokacin komai zai zo ƙarshe”
“are u sure?”
“am sure, Fa'iz da Fa'iza ne kawai nake ganin za suyi man cikas”


“karki damu da wannan sun riga da sun girma, kuma ko baki nan Zulaihart zata kula da su kamar yaranta, kuma da sunyi Aure ai shikenan”
“haka ne, amma maimunatu fa kasanfa bana son zama dakai tare da kowa?”


“maimunatu is not ur problem ni na san yanda zanyi da ita” ya faɗa yana wani kashe mata ido ɗaya, murmushi ta saki itama tana maida mashi martani.


saurin manne bakinshi yayi da nata, a zafafe ya shiga kissing ɗinta ba ƙaƙautawa,sun jima a haka har ƙafafunsu suka fara gajiya, ganin tsayuwar baza tayi masu bane yasa shi sakin bakinta,ida unzipping rigartar daya fara yayi, he slipping her all and throw it away, sake manne bakinsu yayi yana ɗaukarta,a haka ya nufi bed da ita.


*UNITED STATE❤*


_*Las Vegas (Nevada)*_


*THE PRESENT DAY*


Aunty sophia da Chefs ne a kitchen suna shiri akan celebrating dinner da za suyi zuwa anjima,suke aikin tana kula da su,tunda miss Malika ta dawo ta koma kitchen duk da ba girki take ba.


“i hope Miss Nailarh enjoyed this Burger more than the previous one”
ɗaya daga cikin chefs ɗin ya faɗa,riƙe ƙugu wanda ke gaban oven yayi “i also wish this cake is better than the last celebration”

murmushin Aunty Sophia ta saki tana jin kowa da abunda yake buri
“ni dai ba komai ke burgeni ba except how we can relax today,har Adu'a nake shekara ta zagayo because of this celebration,i like how Nailarh allow us to do what we want on this day” ɗaya daga cikin chefs ɗin ta faɗa tana sakin murmushi.

Aunty Sophia na sauraron kowa sai faɗar albarkacin bakinsa yake ƙala bata ce masu ba,amma tana jin daɗin yanda su ke yabon Nailarh.

maida hankalinsu su ka yi kan aikin da suke,ƙarar fashewar wani abu su ka ji daga waje
“ba ku jin wata ƙara kamar fashewar nockout?” ɗaya daga cikin chefs ɗin ya faɗa

“ko dai sun dawo ne ,naji kamar hayaniya ƙasa ƙasa?” wani ya sake faɗa daga cikin chefs ɗin,tashi Aunty Sophia tayi daga saman chair ɗin da take zaune
“ku ci gaba da aiki,lee me check” Aunty Sophia ta faɗa tana nufar ƙofar fita.


sauran ƙiris suyi karo da luna ta shigo kitchen ɗin da gudu,da sauri Aunty Sophia taja baya tana kallonta ganin yanda ta shigo kitchen ɗin kamar wacce aka koro
“lafiya!?” Aunty Sophia ta faɗa tana leƙen bayanta ko za taga abunda ya biyota.


da mamaki Aunty Sophia ta dawo da dubanta gareta dan ba taga komai ba “are u okay?”
ƙofar fita ta shiga nuna mata tana sauke numfashi da sauri sauri alamar na wanda yayi gudu ko yaga wani abun tsoro.

“minene wai,i don't see anything?” da ƙyar luna ta fisgo kalma daga bakinta tace “Na..i..larh” zaro ido Aunty Sophia tayi,da sauri ɗaya daga cikin chefs ɗin ya miƙa mata ruwa,hannunta har rawa yake wajen amsar ruwan,kafa kai tayi ,tas ta shanye ruwan tana maida numfashi “Miss Nailarh shot Alex with a gun!”

wani mummuna faɗuwa gaban su yayi,gaba ɗaya su ka zaro ido suna kallon luna da tayi maganar,Aunty Sophia bata tsaya jin abun da luna zata sake cewa ba ta fice daga kitchen ɗin da sauri ta nufi main parlor,tana shiga parlorn Nailarh na Kunno Kai da gun a hannunta yayin da miss Malika ke biye da ita kamar mahaukaciya tana mata magiya akan ta ajiye gun ɗin.


cikin parlorn security ɗin su ka shigo da Alex hannunshi sai jini yake,ba ƙaramin tashi hankalin Aunty Sophia yayi ba,da sauri tasha gaban Nailarh “baby are u out of mind,what are u planning to do like this?”

ɗago idanunta tayi ta kalle Aunty Sophia,da sauri ta kauda kanta gefe ganin yanda idanun Nailarh su ka yi jawur wutar ɓacin rai ce kawai ke ci a cikin su, fuskarta tayi jawur musamman cheek ɗin ta.


“if u dont move of on my way,I will kill u!”
Kamar saukar aradu haka Aunty Sophia taji maganarta

“Nailarh are you saying that you will kill me?” tsawa Nailarh ta dakata mata tana zaro mata ido
“i said move or I will shoot u!” gaba ɗaya parlorn babu wanda hankalinshi bai tashi ba yau Nailarh kema Aunty Sophia tsawa har take faɗin zata kashe ta lallai ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba.

wasu irin hawaye ne su ka wanke fuskar Aunty Sophia cikin ƙunar rai tace“bazan matsa ko ina ba kill me Nailarh”

“sophia are out of mind or u forgot who's Nailarh when she's angry?”miss Malika ta faɗa tana zazzare ido

“babu inda zan matsa taje ta illata kanta,Nailarh just kill me if that can calm u're mind”Aunty Sophia ta faɗa babu alamar tsoro,nuna ta Nailarh tayi da gun ɗin,rintse ido Aunty Sophia tayi,wani irin wahalallan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login