Showing 27001 words to 30000 words out of 92177 words

Chapter 10 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

rufe gaban rigarta duk ya b'aci da jini
Wani ma'aikacin gurin ne ya k'araso gurunmu da sauri da wani keke dama mun San ka'idar asubitin Mimi muka Dora kan keken ya ja ta da sauri ya shiga ciki da ita.
Tsayuwa muka yi bakin kofa duk jikinmu a sanyaye.
Umma tace"WANNAN kukan da kike bashi ne zai bata lafiya ba, addu'a zakiyi mata kawai."
Nace"Umma Mimi na bani tausayi haka kurrum zata jawo mana abunda baza mu iya ba."
Tace"Itama ba ita ta dorawa kanta ba Allah ne saboda haka sai dai mu bar masa.
Yaya Aminu kuwa kai wa yake yana kawowa a filin asibitin idan ka kalli fuskarsa sai ka rantse da bai taba dariya ba tunda uwarshi ta haife shi, shi a ganinsa zuwan guy gidan ne ya dawo da Mimi ciwon ta sabo ta inda har ya tsananta ta fara zubar fa jini dole ya mike tsaye a kan al'amarin domin yana ganin Ana so ayi masa tsakiyar da babu ruwa wani irin haushin guy yake ji da tsanar sa a cikin zuciyarsa

K'arfe goma saura sai ga aunt Hauwa ta shigo asubitin hankalinta a tashe take tambayar abunda ya sami Mimi Umma ta dinga fada mata tun farkon al'amarin
Jama'ar gidansu Motar Babansu Munnu ce ta shigo asubitin Aminu ya karasa da sauri ya bude masa motar
Ya futo tare da Ummansu Munnu da ita Munnu duk babu nutsuwa a tartare dasu.
Su k'araso kusa da mu suna gaisawa da Umma jiki duk babu nutsuwa
Yace." Ina Aishatu take." ? Dake da haka yake kiranta
Umma tace." Tana ciki tun d'azu dector yana dubata."
Jin Gina yayi jikin bango yana sauke ajiyar zuciya Mahaifin yarinyar ya tuno da yanda yake kaunarta da irin amanar da ya bashi kafin ya tafi Wanda har yanzu ba a San a wace duniyar yake ba, tun bayan rasuwar mahaifiyar Mimi din yaji duniyar ta isheshi ya hada ina sa ina sa, yayi sallama da 'yan cewar ya tafi Neman kudi tunda ga ranar har yanzu basu sake ganinsa ba amma labari na zuwan musu cewar yana cikin koshin Lafiya, kuma bashi da zance dai na d'iyarsa Aishatu.
[11/10, 6:49 AM] Binta U Abbale: Umma da Ummansu Munna zancan suke yi cikin jimami ni da Munnu kuwa babu abunda muke yi sai aukin kuka

Kusan awar Mimi daya a ciki sannan wata narse ta futo tace"Waye mahaifin yarinyar nan da aka wo ta yanzu emergency. " Kawu yace." Ganinan." Juyawa tayi tana fadin"Muje dector yana son ganinka ".
Dukaninmu sai mukaji kamar mu bi Kawu muji me dector zai ce masa.

Kawu da dector ne a ofis a hankali Dr ya cire farin gilashin dake idonsa ya kalli Kawu suka gaisa a mutumce yace." Kaine mahaifin yarinyar nan ko."?
Jiki a sanyaye Kawu yace." Nine Dr Allah yasa naji alkairi."
Dr ya gyada kansa tare da fadin " I'm sorry to say yarinyar ka tana cikin garari rayuwa domun zuciyar ta ta Riga ta tab'u sakamakon tunani da damuwa da ta sanya a ranta bayan haka kuma da akwai a Abunda take mutukar so Wanda aka hanata shi shine mussababbin ciwon nata idan ba 'ayi gaggawar kwantar mata da hankalin ba, to ana iya rasa ta a ko wane lokaci."


Kawu ya share zufa da take tsatstsafo masa a goshi yace." Dr yanzu wane irin taimako za'ayi mana."?
Dr ya gyada kansa cikin nazari yace." Taimakon da zan fara yi shine, kuje gida Ku rarrasheta sosai Ku lallame ta tayi kokarin fada muku abunda take so Wanda ta sanya a ranta ya dame ta, idan kun San abun to sai kuyi gaggawar bata shi domin samun zaman lafiya da d'orewar lafiyar ta, bayan haka kuma zan d'aura ta a kan magani insha Allahu mutukar aka bi doka zata samu lafiya, yanzu dai mun dakatar da zubar jinin insha allahu babu matsala."

Kawu yace." Insha Allahu komai zai zo cikin sauk'i zamu bi doka zamu kuma zauna da yarinyar domin mu tuntube ta muji meye Matsalar.

Dr ya gyda kansa tare da fadin"all right." rubuce-rubece yayi jikin wata takarda ya mik'a masa tare da fadin idan ka futa zaka ga pharmacy sai ka shiga ka siyo wad'annan magungunan insha Allahu, amma ba yau zamu sallame ta ba sai zuwa gobe dole zamu ga dai-dai tuwar numffashinta."
Kawu ya karb'i takardar da sauri ya futa.

Yana futowa muka mike da sauri dukaninmu tambayar sa muke jikin Mimi
"Da sauk'i yake cewa kawai ya nufi dakin magani Aminu ya bishi a baya.
Ofis din Dr suka nufa har Aminu Dr Ya kalli Aminu tare da Kawu yace." Wannan fa."?
Kawu yace." Shine Wanda zai aure ta." Dr yace." Zauna muyi magana da Kai. "
Aminu ya zauna kan kujera jikinsa sanyi k'alau!
Dr yace." Kaine kafi kusanci da sosai Kaine zaka fi sanin abunda yake damunta domin sai ta fada maka abunda yake damunta bata fadawa Iyayenta ba, saboda haka Kayi kokarin rarrashinta ta Sanar da kai meye matsalarta domin magance ta kada ka rasa kyakyawar matarka Cikin lokaci kankani."Ya Aminu yayi shiru yana sauraran Dr da abunda yake fada
Ba sai yayi masa dogon sharhi ba, yasan kome ye yake damun Mimi bai wuce soyayyar Amjadu ba, Wanda yake ganin a kan ya sadaukar masa da ita gwara Mimi ta mutu in yaso kowa ma yayi asara.
Shiru kawai yayi har Dr ya gama maganar shi suka mike da niyyar futa Aminu ya tsaya tare da fadin" Dr babu halin ganinta a yanzu."? Dr ya gyda kansa tare da fadin" ta samu bacci yanzu sai dai gobe insha Allahu da safe sai Ku shiga Ku ganta kafin a sallame Ku."
Jiki babu k'wari ya futa daga ofis din.
Fuskarsa na kalla naga yayi kucin-kicin gabana ya fad'i nayi saurin kallon Fuskar Kawu nan ma naga babu sauk'i tuni kukana ya tsananta nace"Ku fada mana ko menene k'afafun Babansu Munnu na rike ina kuka.
Ummansu Munnu ta janye ni tana rarrashinna ni a lokacin sai nake ganin kamar zasu ce Mimi ta mutu ne Sabuda yanda muka kawo ta a sibitin ta futa daga hayyacin ta.


Can gefe guda suka tsaya suna magana. Kawu yace." Aminu ni a iya fahimta ta nafi tunanin Mimi ta sanya soyayyar wannan Yaro da zai auri Asma'u a cikin ranta ne Wanda yake kokarin haifar mata da WANNAN gagarumar Matsalar shine Abunda nake tunani."

Aminu ya gyara tsayuwarsa babu sassauci a muryarsa yace." Dama ni tun kafin muzo gaban likita ya fada mana meye na gane komai, a gaskiya Baba babu mahalukin da zan iya barwa Mimi domin nima idan nayi haka zan iya shiga cikin tashin hankali watak'ila ma nawa yafi nata tunda kowa ya shaida nafi sonta ita bata sona saboda haka ni ina gani kawai daga nan zuwa jini a d'aura mana aure da ita ba sai an jira lokacin da aka sanya ba, idan taji labarin haka nasan dole zata hak'ura ta fawwala Allah kasan dama ance kiyyayyar 'ya mace bata tasiri ina ganin Mimi zata hak'ura ta zauna dani."!

Kawu ya gyada kansa yana Nazarin maganar Aminu Yaro Yaro ne, murmushi yayi yace." Aminu kenan, kamar ka manta abunda Dr yace akan Aishatu, Jin labarin d'aurin auranku zai iya sanyawa zucuyarta ta buga gaba daya ta mutu lokaci guda, kaga kuwa wannan sha'awar taka ba abun dubawa bace."

Aminu ranshi ya b'aci da jin abunda Kawu yake fada murysrshi a kaurare yace." Kai ya kake ganin za'ayi."
Kawu ya kalleshi cike da mamaki jin yana yi masa magana kazar-kazar babu Wani ladabi.
Yace." Abunda za'ayi shine mu samawa Aishatu abunda take so domun samun ta da tabbatuwar lafiyar ta.

Aminu ya watsa masa wani kallo tare da fadin"Kawu in na fahimce ka anan shine kana so kace min in hak'ura da Mimi in yaso Ku bats Wanda take so kome."?

Kai tsaye..... Kawu yace." Shine abunda nake Nufi."
Aminu ya guda kansa yana murmushi me ciwo yace." Impossible, bazai tab'a yiwu wa ba Kawu Mimi 'yar kace nima inda kara d'an ka ne nasan baza ka bawa Mimi bare ba gani a zaune, ina so saboda haka yanda aka karb'i kud'in aure na da Mimi to babu mahalukin da ya Isa ya hana tabbatuwar auramu idan ba Wanda ya hallice mu ba."
Cike da d'umbun mamaki Kawu yake kallon Aminu ganin yanda yake wani irin huci!! Yace." Aminu ka fahimce ni mana ba wai ina k'in ka ban......... Kafin ya karasa Aminu ya daga masa hannu a fusace.!!! Yace." Kawu ga magana nan ta futo kanunamin bakai ka haife ni b.... Cike da b'acin rai Kawu yace." Rashin kunya zakayi min Aminu. "
Daga kafad'a yayi tare da fadin "Babu maganar rashin kunya anan Kawu gaskiya ce ni nayi rantsuwar babu Wanda ya Isa ya hanani auran Mimi."

Ganin tsageran cin da Aminu yake masa ne yasa ya fusata shima yace." Aminu indai nine waliyin Aishatu to baza ka aure ta ba."
Aikuwa sai ya ingiza Aminu ta inda ya shiga sirfa masa rashin kunya wanda ya jawo hankalimu Kansu dukanimu mu k'araso gurin tare da tambayar ba'asi
Abunda Aminu yake yi yayi bala'in konawa Umma rai ta cire hannunta ta zabga masa mari cikin tsawa tace"Na kara jin bakinka a gurinan Aminu sai na tsine maka, a tunanin ka wannan tsagerancin da rashin kunyar da kake yi shine zai sanya a baka auran Mimi ko meye."?

Kawu yace." Kyaleshi ya zage ni son ransa lokacin sa ne."
Wuce mu yayi tafi can bakin get ya zauna tare da masu gadi

Fada sosai Umma take wa Aminu Tace" Haka ake soyayya da hauka Aminu ka futo da son zuciyarka a fili kana ganin mawuyacin halin da yarinyar nan take ciki shine zakaje gwara ta mutu a kan ka janye kudirin ka a kanta, me yasa ita lokacin da ka fad'i har ka kwanta a asibiti tace"Zata aure ka alhalin ga Wanda zuciyar ta take so Mimi yarinya ce me ladabi da gudun b'acin rain wani ta so ta faranta maka ta faran wa zuciyata ba tare da ta damu da nata farin cikin ba, shine yanzu tana cikin halin rai da rayuwa kake mummunan magana a kanta Aminu wannan ba soyayya bace."!!!!
Umma ta karasa maganar ta tana haki! Kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin b'acin rai da damuwa
Cikin kuka na futar hayyaci nace"Wallahi tallahi Umma mutukar Ya Aminu bai janye kudirinsa ba nima bazan aure shi ba, sai dai mu zauna a haka, kawai a aura mata Wanda zuciyarta take so ta huta da wannan azabar da take sha."
Umma tace." Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Mimi bata da Miji sai Amjadu dole a bawa zuciyarta hakuri abata abunda take so."
Ya Aminu ya kalleni ya kalli Umma zuciyarsa nayi masa wani irin ciwo yace." Umma don bani da kudi bani da aikin yi bani da mota bani da babur bani da keken hawa kana bani da kudi a banki kuke mun haka,? Meye laifi na meye? Aibuna anan Zan kula da Mimi zan tsare mutumcin ta zan sanya ta farin ciki! Umma kar Ku kware min baya akan Mimi Ku duba halin da zan shiga a kanta soyayyar ta tana iya kashe ni!!!!! Umma ni danki ne baza ki so wani bayan ni ba, Umma ki dube ni da idanun rahama!! Ki tuna so da kaunar da kike min Umma ki bani Mimi domin itace farin cikin rayuwata."!!!!!!!! Ya k'arashe maganar sa hawaye na zubowa daga idanunsa

Umma ta zube a gurin Tare da dafe k'irjinta tana salati aunt Hauwa da Ummansu Munnu suka rike ta hawaye ne ya fara zirarawo daga idanunta muryarta na rawa tace"Ya Allah ka ije mun wannan masifa da ta tun karo ni, Allah ka sanyaya min kasa kawo karshen wannan badak'ala!! Sai hawaye sharrrrrrrr-sharrrrrrrr suka fara zuba a kuncinta.
Duk taurin zuciya irin ta aunt Hauwa hawaye ta fara sharewa ganin Umma tana kuka abunda zai sanya Umma kuka ba Karami bane hakuri kurum suke bata

Ni ko da sauri na bar gurin bayan na warce wayar Munnu dake tsaye, wani d'an korido na nufa dake Cikin asibitin na fara Neman numbar sa, sai da tayi ringing sai uku ba a dauka ba,

Sai ana hudu ne ya dauka muryarsa da yanayin bacci yayi sallamsa da sauri nace." Kanwa ta kar tsami! Kwarna fi ya kwanta. "!!!! Jin muryar yarinyar ya sashi mik'ewa zaune da sauri hade da yaye blanket din jikinshi na ci gaba da cewa " Yanzu haka muna babban asibiti na zana Mimi a kwance rai a hannun Allah bayan tafiyar ka, jini ya tsinke mata ta baki ta hanci!!!! Ta galabaita mutuka duk ta dalilin ka!!! Ina kara fada maka duk abunda ya same ta Kaine sila Kaine! Mujaza!! Mahaifiyar mu ta zubar da hawaye akan haka, mun zubar da hawaye a kan haka, duk wani mai imani ya kalli Halin da Mimi ta shiga a yanzu sai ya tausaya mata, insha Allahu duk wani sharrinka sai ya koma kanka ka cuce mu, ka yaudare mu, Ka azabatar da zuciyar Mimi akan sonka kullum kana fada cewar zaka aure ta, alhalin karya kake!!! Wallahi mutukar ka bari Mimi ta mutu baka yi Wani Abu akai ba nima sai na kashe ka."!!!!!!!!!!! Kamar wata mahaukaciya haka na k'arashe maganar..... Wata irin zufa ce ta keto masa duk da cewar akwai AC a dakin Muryarshi sanyi k'alau yace." Asma'u.!!! " saurin kashe wayar nayi na zube a gurin hade da fashewa da kuka mai cin rai.

Mik'ewa yayi da sauri ya duro daga bed din toilet ya nufa ya dauro alwala ya futo yana kallon agogo bango uku shaura na dare,
Jallabiya ce a jikinsa sai garan wando ya dauki wata rigar sanyi sa mai hula ya sanya kai a gogonsa ya d'aura ya dauki key ya futa da sauri.

Rbow suka ji ana kokarin tada mota hankali a tashe suka futo daga gurinsu, suna tambayar sa yace." Su koma kawai shima yanzu zai dawo jikinsu duk babu k'wari suka tsaya a gurin har sai da suka ga futar shi Daga gidan.

Kai tsaye......Asibitin Zana ya nufa zuciyarsa kwata-kwata babu dad'i abun yana mutukar bashi mamaki shi dai yasan babu wata Kalmar so da ya tab'a fadawa Mimi wacce har suke zargin sa da ya yaudara ta, maganar auran ta kuwa ya fada ne saboda son da take masa gami da ganin yanda suka shak'u da Asma'u yana ganin ko ya aure su su biyu ba za a samu matsala ba, yanayin dabi'un Mimi da nutsuwar ta gami da kunyar ta suna bashi sha'awa amma zallah so gangariya babu Wanda yake wa sai Asma'u duk cikin 'yan matansa babu wacce ta samu wannan matsayin kamar ta hak'ika Asma tana da babban matsayi a zuciyarsa.

Da wannan tunane-tunanen ya Isa asubitin, Madi suka bude masa kofar ya shigo cikin sauri suka biyo motar da gudu yana parking suka bude masa kofa suna yi masa barka da zuwa.
Amsa musu yayi babu yabo babu fallasa, ya wuce ciki.
Suka tsaya suna binshi da kallo tare da tunani wane dalili ne ya kawo shi asibitin ? Suna zargin yau ya zagayo su ne duba marasa lafiya da. da bada tallafi kamar yanda ya saba, murna suke sosai yau zasu cika aljihunansu.

Wayarsa ya futo da ita yana laluben numbar da ta kira shi da ita yanzu....








*10/November/2019*
[11/11, 9:19 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*




*Mallakar_BINTA UMAR*




*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*




*48*




Ringing d'in wayar ne ya dawo dani cikin hankalina wayar na duba sai naga numbar sa, da kamar kar in dauka wata zuciyar tace"Dauki kiji me zai ce miki.
Jin alamun ta daga wayar ne yasa yace." Gani cikin hospital din ki futo kiyi min jagora har inda kuke."
Bai saurari Abunda zata ce ba ya kashe wayar sa.
Futowa nayi daga gurin da nake.
Har yanzu suna tsaye kan Umma sun yi mata rumfa Aminu sai fiffita yake mata.
Aunt Hauwa ta kalle ni tare da fadin"Da ina kika shiga tun d'azu. "
Cikin wayan cewa nace"Futsari naje nayi."
Raba ido nake yi a gurin ko Allah zai sanya I n hango shi
Da yanayin tafiyar shi na gane shi.
Shiru nayi har ya k'araso gurin.
Cike da mamaki suke kallonsa.
Ya mik'awa Aminu Hannu su gaisa.
Da kyar ya mik'a masa nasa hannun kamar yanda yayi masa jiya.
Umma ya kalla yace." Umma Ashe bayan tafiya ta jiki ya rike CE."
Umma ta gyara zamanta hade da gyara mayafin ta tace"Wallahi kuwa aman jini take sosai."
Gaban shi ya fadin jin abunda Umma tace, Yace." Bari in ga dector babu matsala insha Allahu komai zai zo da sauki."
Binsa mukayi da kallo har ya shige ciki abun mamaki babu Wanda ya hana shi shiga cikin ma'aikatan sai ma da d'a gyara masa hanyar wuce da suka yi.

Kamar yanda dector ya yiwa Kawu Baya ni haka yayi Amjadu baya ni Wanda ya gamsar dashi kuma shima ya gane kan ciwon Mimi kamar yanda Asma'u take fada cewar ciwon sonsa ne yake damunta.


Yace." Doctor yanzu kun gama komai ko."? Gyada kai Dr yayi tare da fadin"Mun gama komai dasu domin har sunje sun karb'o magani a pharmacy kuma yanzu na sanya nurse ta bata maganin babu matsala insha Allahu mutukar an bi doka."

"Yanzu sauransu biyan kudi domin yanzu nake cewa Narse ta zo mik'a musu rasit." Yace." Kar ka damu insha Allah ka bani numbar accont din Ku na hospital din sai a turo maku hakkin Ku.


Da sauri Dr ya dauki 'yar k'aramar ta karfa da biro ya rubuta masa hade da mik'a masa, ya San ba iya kacin kud'in su zai tura musu ba Dole sai yayi musu kari, tunda dama ya saba kawo musu ziyara a sibitin.

Har ya mike zai futa sai kuma ya tsaya tare da fadin"Yanzu babu halin a ga yarinyar. " ? Dr ya mike da sauri yana fad'in"A'a Yallab'ai kai zaka iya shiga ka ganta."


Tare suka shiga room d'in da Mimi take kwance bacci take sosai sai dai har yanzu nuffashin ta bai gama dawo wa normal ba. Dr ya futa hade da jawo masa kofar , ido ya tsura mata sosai yake kallonta mace har mace tana Neman ta jefa rayuwar ta a wahala.


Domin shi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login