Showing 75001 words to 78000 words out of 92177 words

Chapter 26 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

gurin cutar shi da izgilanci ga Allah ga manzon sa, yana nan ya sanya matakan tsaro ko ta ina yayi lamfu bunkice yake sosai aka mutanan da suka kulla masa sharri, maganar company kuma tunda sun rusa shi babu wasu kudinsa da zai futo dasu ya saka tada wani, suje kawai Wanda bai ji bari ba zai ji hoho.. Loptop ce a kan cinyar shi yana duba sakkonin da Anthony ya turo mishi tsawon lokuta dama wasu ya bashi amsa wasu bai bashi ba, ya bari ne in yaje can sai suyi maganar. Granny CE ta futo daga dakin ta ta zauna kusa dashi.. Hankalinsa na kan Loptop din bai dago ba yace." Ina Sweetheart yau banji motsin ta ba." Granny tace"Tana gurun Iyami tun safe da tayi mata wanka take bacci." Dariya yayi yace." Wannan Aishar ai rigamammiya ce tafi uwarta fitina." Granny tace"Mai suna Aisha kuka ne da ita ai." Yace." Granny ina tunanin cikin satin nan Zan tafi Chana kuma zan kai wata uku a can insha Allah, amma ina tunanin tafiya in barku fa."

Granny tace"Allah ya taimaka ni kam babu wata chana da zan biki to kaji."!! Dariya yayi yace." Shikkenan zamu je da sweetheart d'ina OK." Hararshi tayi tace"Kaje ka bawa wa ita wannan garin ai ku da ku ga zaku iya zuwa." Murmushi yayi kawai ya cigaba da duba lptop d'insa.
A hankali tace"Ni ko nace dama akwai wata magana da na yanke a kanka." Gyada kansa yayi tare da fadin"Ina sauraren ki." Tace"Mai zai hana ka nemi auran Hafsatu. Da zan ce ko yarinyar nan Asma'u to amma naga wannan yaron Dan albarka Mujahid yana nemanta ana barin halas Dan kunya ko ba haka ba ne."? Bata fuska yayi had'e da ya mutse ta yace."granny ki k'yaleni in huta tukkuna ni kam yanzu babu maganar aure a gurina sai an kwana biyu sannan. " Tace"Aikuwa dole kayi aure domin shine cikar mutum ka kai munzali kace baza kayi aure ba, baka Isa ba."
'Yar dariya yayi yace." Granny nayi aure har na samu riba mutuwa ta rabani da mata ta, ki k'yale ni na huta tukkuna zanyi amma ba yanzu ba." Tace." Ni kam bazan ta kallon ka a haka ba dole ni nayi maka aure. " dariya yake yana mamakin rigimar ta, yace." Ok kiyi min aure sai in barki da matar wallahi inyi tafiya ta tunda bani na saki ba." Granny ta hau zuba masa masifa, dafe kansa yayi yace." Ina aiki kin hani oh my god."!!! Iyami ce ta shigo da Baby Aisha a goye a bayanta tana motsi, alamun ta tashi. Granny tace" Ta tashi ne."? Iyami tace"Gashinan fa da alama Dadynta take so." Rufe loptp din yayi yana kokarin karb'a baby daga hannun granny sai murmushi yake, yarinya tayi mulmul da ita tayi wata irin kib'a hasken fatarta ya kara futowa Iyami ta iya raino gaskiya sai wani kamshi take yi, tana cikin kayansu na jira jira abun gwanin sha'awa, leb'anshi ya manna a kumcinta yana sakin ajiyar zuciya yace." Momyna 'yar rigima hummmm! Yau ba kuka kenan. "? Kamar yana da magana da babban mutum haka yake yin magana da baby Aisha.

Granny tace"Aiki ya same ka kana magana kamar kana magana da babban mutum." Dariya yayi hade da kamo bakin baby yana Dan tsotsa yarinyar ta fara mamular leb'an shi da sauri.
'Yar dariya yayi ya cire bakinsa ya kalli Iyami dake zaune kusa da granny yace." Allah Iyami zanci tarar ki sweet heart dina yunwa take ji ga alamu nan na gani." Iyami tace"Afuwa Uban gida dama yanzu nake so in dama mata madarar ta, kaga ai bacci take kuma sweeh Hart din naka ci ne da ita Wallahi ." Dariya ya kyalkyale dashi jin yanda Iyami take fadi wai sweeh hart. Yace." Ungo ta ki bata bana so tayi kuka yanzu dai kin San halinta." Iyami ta karb'e ta da sauri ta futa...... Wayar shi tayi k'ara yana dubawa yaga Jahid ne, murmushi yayi hade da daga wayar sallama yayi Jahid yace." Kana gida ne." ?
"Eh ina Gida yanzu amma k'arfe biyar dai-dai zanje government house." Jahid yace." OK ganinan zuwa nima ina Gida kasan yau Sunday muna Hutu. " Amjad yace." OK sai ka shigo din." Kashe wayar yayi ya cigaba da abunda yake yi.

Minti goma tsakani sai ga Jahid ya shigo parlor yana zama yace." Ina baby Aysha take." Amjad ya rufe loptop tare da fad'in"Tana gurin me raino yanzu kuwa ta dauke ta suka bar gurinan granny ma yanzu ta tashi." Jahid yayi Dariya tare da fadin "Babu wasa cikin al'amarin muna so ka bamu baby Aysha fa."" ! Amjad yace." Ai gatanan ga kanan Aboki baby Aysha taku ce kai da Madam." Jahid yace." Thank you my friend, wallahi Asma'u ce tun jiya ta dame ni lallai a basu ita shine nace zanyi maka magana nasan dai baza ka hana ba." Tunda ya ambaci sunan Asma'u ranshi ya b'aci don har sai da fuskarsa ta nuna ya kalli Jahid din babu alamun wasa a tare dashi yace." Babu wannan maganar my friend babu Wanda zan iya bawa sweet heart gaskiyar magana." Jahid yace." Kuma yanzu kace ka bani ita."
"Yes Ni nace na baka ita saboda nasan muna tare da Kai har abada, naji ka sanyo min zancan wata Asma'u ne, am sorry my friend Asma'u bata da haleyan K'warai Wanda zata iya tarbiyan tar da d'an wani. Bana jin Zan iya bari baby Aysha ta yini a gidansu ma balle har ta kaita ga kwana gudun ta d'auko d'abiun yarinyar." Jahid ya sha kunnu mutuka yace." Kayi dai-dai Asma'u kake ciwa fuska a gabana ko."? Dariya Amjadu ya sanya tare da fad'in"Sorry halin ta ne fa, amma da baka yimin wannan maganar ba ni babu ruwana." Jahid ya bude hannunsa dake kan kafad'un sa yace." Wato kana nufin matar da zan aura bata da tarbiya ko me."? Hannu Amjad ya d'aga cikin sigar bada hakuri fuskarsa da murmushi yace." Ban fad'i haka ba my friend.........................








*26/11/2019*
[11/26, 9:01 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*64*




Sosai Jahid yaji babu dad'i saboda yana k'aunar Asma'u tsakani da Allah kuma sam baya kaunar yaji wani ya fad'i mummunar magana a kanta, kokarin mik'ewa yake Amjad din ya mai dashi ya zaunar, gyara fuskar shi yayi babu alamun wasa yace." Karfa kayi magana ta wata fahimta ta daban, ba wai na fad'i wannan maganar bane domin ranka ya b'aci ko kuma kaji wani fargaba a game da k'udirin ka kan yarinyar kace zaka janye auran ta. No kawai na fad'i iya abun da nasa ni a kanta, kuma kasan ko wane mutum Tara yake bai cika goma ba, amma hak'ika ka cancanci yabo da godiya a gare ni abokina babu abunda zaka nema a gurina na kasa yi maka shi, misali kace min in baka Baby Aysha zaka had'a ta da Salim ka rike min, wallahi babu abunda zai hanani in baka saboda nasan Maman Salim macace da take da nutsuwa gami da tarbiyya sai ince maka ma kusan halayen su d'aya da Mimi Allah ya jikanta, amma maganar In bawa Asma'u baby ka aje ta gefe guda a halin yanzu babu ita." Jahid ya Dan ji sanyi a ransa, amma duk da haka bai hak'ura ba saboda kwata kwata baya son b'acin ran Asma'u yace." Yanzu idan Allah ya kaddara auramu da Asma'u zaka bamu ita ko ? Tunda kana ganinta a kusa dakai sai kayi mata tarbiyar da kake so." Amjad yayi Dari hade da Sosa kansa yace." Mai zai hana kuwa zan baku wannan nasan muna kusa kuma kai ma zaka samin ido sosai." Jahid yaja tsaki tare da mik'ewa tsaye yace." Baza ka fasa ba kenan ? Ni kaga tafiya ta." Amjad ya mike tsaye shima yana dariya ya rufa masa baya. To kafin suyi sallama ma sai da suka d'an jima a tsaye sannan suka rabu, dama kuma tun Asali cikin makotan sa, sunfi shiri da Mujahid din saboda saukin kansa.

****
K'arfe takwas dai-dai Mujahid ya kirani a waya cewar gashinan a waje yana jirana, a shirye nake saboda nasan da zuwan sa, cikin motarsa na same shi, Duk sanda zai zo gurina da sabbin kaya a zuciya nace Jahid ba dai gayu ba, budewa nayi na zauna sosai ya sakar min murmushi tare da fad'in "Yau kin futo da Wuri."
'Yar dariya nayi nace"A shirye nake dama ya maganar mu da kai." Fad'uwar gaba yaji amma dake namiji ne sai ya dake yace." Kya bari mu gaisa ko."?

Rife fuska ta nayi da tafin hannuna ina dariya, shima dariyar yake yace." Ke kinfi baby Aysha rigima ma." Bude idona nayi har yanzu da murmushi a fuskata nace"Wallahi na damu na ga babyn ne." Yace." Kina da gaskiya amma kin san me."? Girgiza kaina nayi, yace." Babanta ya hana wallahi yace ki Bari tukkuna muyi aure zai bamu ita." Raina a bace nake kallon Jahid din nace"Ban gane ya hana ba."? A hankali yace."Shima baya so tayi nisa dashi a yanda na fahimta yana kallonta baby ne yaji sanyi a ransa duk lokacin da ya tuna matarsa.
Nace." Jahid abun da bangane ba shine, shi kad'ai ne yake da hakki da yarinyar? Mu da muke a matsayin iyayen ta bamu da amfani kenan Jahid gani ba ci ba, dama baby 'yar shi waye yace ba tashi ba."! A zafafe na k'arashe maganar.
Jahid ya gyad'a kansa ya San zai fuskanci haka daga gurin ta, yace." Matsala ta dake saurin d'aukar zafi kiyi wa magana ta kyakyawar fahimta mana." Cikin takaici da jin haushin sa nace"Na lura kamar bakin Ku d'aya Jahid baka San yanda nake ji ba Wallahi tallahi tunda naji kuna fadin baby suna kama da Mimi naji ina mugun kaunar ta." Cikin rawar murya ta karasa maganar, cike da tausayin ta yace." Kiyi hakuri dai yanzu dai kar kiyi min kuka Jahid UA fad'a cikin rarrashi. Nace"Wallahi na saki jiki zangan ka da tare da ita." Cikin shagwaba take maganar,Jahid yaji kamar zai suma a gurin hannunsa na rawa yace." Bari kiga hotonta hankalin ki ya kwanta, nima dai kin kusa bani nawa babyn ko."?

Murmushi kawai nayi masa ina Allah-Allah ya mik'o min wayar in gani.. Da sauri na karb'a ina dubawa sosai baby Aysha take kama da Mimi sai da tafi ta haske kamar yanda naji suna fad'a ta murmure sosai da gani ma hoton tana jikin babanta aka dauka don ga jikin shi nan ya futo da hannunshi guda da ya rike ta, Dole in gane saboda manya manyan azurfan dake bisa yatsun sa.
Wayar na rungume a k'irjina ina sakin ajiyar zuciya nace"Jahid baby Aysha na kama da Mimi wallahi ka bani wayar nan yau ta kwana a hannuna in kwana ina kallonta kaji. " dariya yayi yace." Kece kin ki ki bude whatsp da sai na turo miki hoton." Da sauri na mik'a mishi wayar nace "Bari in dauko wayar tawa ka tura min wsp din don Baby Aysha amma da na daina yi." Dariya yake min har na futa daga motar. A tsakaice dai sai da Jahid ya bude min wsp dina da na rufe tun bayan rasuwar Mimi ya tura min dukanin. Hotonan baby Aysha, yace" kullum zai dinga d'aukar ta sabbin pictures Yana turo min sosai naji dadin haka na saki jikina sosai muka yi shirarmu nan yace insha Allahu a karshen wata yake so ya turo magabatan sa gurin Kawu Yunusa nace"Allah yasa nan mukayi sallama dashi ya tafi.


Ko da Umma taga hoton baby Aysha tayi ta mamaki sosai sai taji sha'awar ganin yarinyar a zahiri tace." To tunda ya hamu ita ni zanje da kaina in duba ta ai hakan ba laifi bane." Umma da kin kyaleshi dai komai abunda baby Dole ta nemi dangin uwarta wallahi." Umma tace"Ai baza'ayi haka ba, domin bamu San munufar sa tayin haka ba, to koma dai menene abar shi da d'iyar shi yayi yanda yake so da ita." Shiru nayi ina raya wani Abu a raina

Abunci naci nayi wa Umma sallama, kai tsaye dakinmu na nufa, na tube kayan jikina wata duguwar Riga na sanya a jikina mai uban kyau da tsada duk cikin kayan Mimi suke, hula na sanya a kaina na kwanta kan katifa, hade da rufe k'afafuna hotan baby na tsurawa ido ina murmushi nima wallahi na damu inga yarinyar a zuciya ta.

Wsp na shiga na d'ora pic dinta kan df na, wsp din dake amfani a waya ta mai Gb ne ya nuna min Amjad na online wata zuciyar tace kiyi masa magana kawai tunda gashi a onile da sauri na shiga gurin shi naga ya sauka akai. Yanzu Df shi na kamo da sauri ina dubawa, pic dinshi ne da baby Aysha ya d'aga ta sama yana dariya hat tada dimple dinshi sai da ya futo saboda dariya itama babyn dariya take naji sun bani sha'awa, zuciya ta tace min "Shi yana Cikin jin dad'i har da dariya gashi ga 'yar shi hummm! Ai in da mutumci Amjad bamu cancanci haka daga gurin shi ba, message na tura masa kamar haka

_" Duk d'an halak baya bance alkairi kuma tilas! Ace da mijin iya baba, duk talaucin mu, baby na tabbata sai ta neme mu, domin mune dai dangin uwarta."_

Tura masa nayi na kashe data ta, tsawon mintuna ashirin, na k'ara bud'e datar, ina dubawa naga har ya gani, sai naji wata fad'uwar gaba, messenges na cigaba da dubawa ina sauraron amsar sa, shiru kusan minti talatin kuma duk dubawar da zanyi sai inga yana online, bakin ciki da takaici suka ishe ni, abunda na tsana a rayuwa ta shariya guy nan yaga sakona zai wulakanta ni, lallai ya sanja sabbin halaye, ji nayi wasu zafafan hawaye na nema su kufce min. Kira ne ya shigo wayar tawa ina dubawa naga shine.....









*26/11/2019*
[11/27, 4:45 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*



*65*



Cikin fad'uwar gaba na mik'e zaune sosai ina k'ara duba wayar tabbas shine ya kira ni. Cikin zuciyata nace to me zai ce min lallai ma, kin d'agawa nayi har ra katse wani kiran ya k'ara shigowa ina kallon wayar nan ma ta katse band'aga ba, sai da ya kira sau uku nak'i dagawa sannan ya hak'ura, kwanciya nayi ina sak'e-sak'e a zuciya ta, data ta kara kunnawa aikuwa sak'on shi na farko hannuna na rawa na shiga ina dubawa. Ga Abunda yace.

_"Maganar ki gaskiya ne 'yan mata, Sweetheart bata da wani dangi sai ku domin kune iyayen ta, Abunda na kasa fahimta a maganar da kika ce duk D'an halal ba ya mance alkairi, shin wane alkairi kuka yi min da har na manta? Bayan nan kuma ina so in k'ara jaddada miki cewar Aysha d'iya tace domin nine k'ashin bayan Samar da ita, dukanin Ku baku da iko akanta, ni nake da iko akan kaya ta, so bana son damuwa don Allah daga yau sai yau karki kara yi min magana makamamciyar wannan, ina fatan kin fahimta? Kin turo min Jahid kan bukatar ki, to baki isa ba indai nine uban Aysha bazan tab'a Bari ki raine ta ba ballanta ki koya mata munanan d'abi'un ki, tabbas yanzu na tabbatar da cewa a baya nayi wauta da nake kokarin rabuwa da mace tagari a kanki , na tabbata Mimi alkairi ce a rayuwa ta, kuma duk macan da zan aura sai dai tabi bayanta wallahi,a halin da ake ciki yanzu soyayyar ta ta cika min zuciyata duk da bata Raye, ta inda nake yi wa mata kallon maza ciki kuwa har dake, saboda haka ki kiyaye fad'a min magana ko wace iri ce,ni Amjadu AbulAbbas ma nasara na shafe ki a babin rayuwa ta."_

~AMJD ABUL ABBAS~


Wani irin gumi ne yake tsiyaya a jikina take wasu zafaffan hawaye suka kece min, Dana San wad'annan mugayen maganganun guy nan zai fad'a mun da ban mishi magana ba, hannuna na karkarwa nake bashi amsa..... Da sauri na tura masa, na kashe data hade da jefar da wayar kan Katifa na rungume filo ina tik'ar kuka harda sharb'e majina,wato ni guy nan yake nunawa iyaka ta kan abunda Mimi ta tafi ta bari gashi Ubangji ya zuba min kauna da son baby Aysha a cikin raina, nafi awa guda ina kuka k'asa kasa don kar Umma taji fa kyar na rarrashi kaina tare da alk'awarin cewar bazan kara shiga harkar shi ba har a bada..Data na k'ara kunnuwa ina tunanin zanga sak'on shi domin nasan na fad'a masa bak'aken maganganu Wanda suka fi nashi abun mamaki, ko da na duba sai naga yayi bloking d'ina, sak'on Dana tura masa Yanan yanda yake, ajiye wayar nayi ina da na sanin bud'e whatsp din inda nasan wannan bakin cikin zan riske, da kyar bacci ya dauke ni mai cike da mafarkin baby Aysha da Mahaifiyar ta.

Ko dana tashi da safe sukuku na tashi jikina duk babu kuzari har Umma ta fahimci wan Abu amma bata ce min komai ba, saboda tana tunanin a jizanci ne irin na d'an Adam, sallama nayi mata na tafi makaranta. To ko A skull din ma kasa b'oyewa Munnu nayi sai da na fad'a mata komai kuma na nuna mata text din da ya turo min, Munnu ta dinga mamaki tsabar haushi da takaici yasa ta dinga zaginsa hotonan baby take dubawa sosai tana fad'in"Wallahi karya yake in Ku ya rabaku da ita mu bai isaba sai munje mu daukota Wallahi munganta ai wannan rashin imani ne ace kamar jinin Mimi sai dai mu ganta a hoto gaskiya bai isa ba."!!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login