Showing 51001 words to 54000 words out of 92177 words

Chapter 18 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

shiga ko kallonshi Banyi ba, yaja motar da sauri muka bar gurin.



Mintuna ashirin ne suka kaimu unguwar ta Jambulo sosai na murtuke fuskata hade da futowa daga motar, Kai tsaye kofar parlor na nufa.
Rambo dake tsaye bakin kofar ya bude min ba tare da nace masa komai ba na shiga.

Yana zaune a farlor da cup din tae a hannunshi yana kurb'a kad'an-kad'an nayi sallama na shiga, kanshi ya d'aga yana kallonta har ta k'araso ciki sosai.

Babu yabo babu fallasa nace." Ina kwana." Shiru yayi yana binta da wani kallo shi ba na tsana ba shi ba na so ba, mugun haushi ya bani ana gaidashi shi kuma yans faman kallon mutane tsaki naja na nufi bedroom din Mimi, wani irin kallo ya bita dashi, wato shi take wa tsaki lallai ne. Cigaba yayi da kurbar tea d'insa hankalinsa kwance.


Halin da naga Mimi a ciki ya d'aga min hankali kuma ta bani tausayi mutuka hawaye na fara yi sosai ta rike hannuna tana kuka take fadin "Asma'u ciwo nake ji a gabana na kasa daga k'afafuna." Cike da takaici nace "Mimi kina nufin kice har ya kwanta dake ko d'aga k'afa babu ki gama warware gajiyar biki."
Rikeni tayi tana yunk'urin tashi zaune tace." Gashi kuwa kingani Asma'u sau hudu yayi min zafi wallahi."! Naji wani irin bakin ciki cikin zuciyata wai wannan guy wane irin Dan iska ne, budurwa ba bazawara ba, kayi sau hudu sai kace wani bunsuru.
Cike da takaici nace"Kinyi ruwan zafi ko."?
Gyada kanta tayi tare da fadin"Sau biyu ma nayi.
Nace"To yanzu kiran me kike min ne."?
"Kawai kizo in ganki." Tafad'a muryar ta na rawa."
Ajiyar zuciya na sauke nace." Tom gani shikkenan ko." Rike ni tayi ni kuma ina tunanin
taimakon Da zan yi mata

Shigowa dakin yayi cikin tafiyar shi ta jarumai ya k'araso kusa damu hannunshi rike da cup din tea dinshi, ya kalleni fuskarsa dauke da murmushi yace." Ina ganin ki had'a mata ruwan zafi ta gasa jikinta sosai tun jiya take kiran ki sunan ki, duk ts hanani sakewa da ita, a matsayin ki na makusanciyar ta, ki tamaka min ki gasa mata jikinta ba sai na dauko dector ba, idan kuma da matsala ta fada miki sai a dauko dector ya duba ta OK."

Ji nayi ina nema in kifa daga zaune zantukan shi suka dinga yi min yawo aka wai in hadawa Mimi ruwan zafi jiya tana kiran sunana me yake nufi guy nan ne." Tambayar kaina nake yi babu me bani amsa.
Zama tayi kusa da k'afafunta tare da janye bargon dake rufe a jikinta, da sauri na mike na bar gurin jin zuciyata tana wani irin bugawa toilet Din na nufa bana kallon gabana.

Tsayuwa nayi cikin toilet din narasa me ma zanyi shikkenan ta tabbata Mimi matar Amjadu tunda gashi har ya kwanta da ita ya raya sunna shikkenan ita dashi sun haramta da junnan su, wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa daga idonna jingina nayi jiginayi jikin garo ina wani irin kuka me Sosa zuciya lokacin ji naka yi gwara in mutu in huta da wannan bakin cikin.
Motsin bude kofar toilet din naji firgit na dawo hayyacina ina goge fuskata ya shigo toilet din, sauri nayi na juya baya na soma had'a ruwan zafi da na sanyi jikina sai b'ari yake.

Bayanta ya k'ura ido da lumsassan idanun sa, kamar na mashaya sarai ya fahimci kuka take yi tunda ya gan hawayen a fuskar ta tana gogewa, murmushi yayi yana shafa siririn sajan shi, a hankali ya k'arasa har inda take, saura kad'an jikinsu ya had'u, gyaran murya yayi tare da fadin "Jimana."! Tun sanda ya iso kusa dani nake addu'ar Neman tsari dama nasan Neman fitina ne ya sanya aka dauko ni a daga gidanmu, fuskata a mugun hade da juyo k'irjina da nasa suka sad'u hakanan fuska ta da tashi ta had'u dogon hancin shi na tab'a goshina,
Zame wa nake kokarin yi ya babbake gurin, fuskar shi na kalla da tawa fuskar wacce take a mutukar daure!! Wannan d'an iskan murmushin nasa ya saki tare da tsare ni da fitinanun idanuwan sa, da babu d'igon kunya ko kad'an a cikinsu yace." Kukan me kike yi uhumm."? Wani irin masiffafan fleengs naji yana taso min a lokacin sai na fara addu ar neman tsari daga sharrin shi, cike da jarumta kamar ko da yaushe nace." Ina kuka ne kawai saboda rashin imanin da ka gwada akan Mimi Wallahi baka da Imani."!!
'Yar dariya yayi as'usuel ya shafa sumar shi hade da sajan shi, yace." Wane irin rashin Imani humm? Ko ke na samu haka zanwa tunda hakkina ne kuma sadaki na ne, mallakina ne, yanzu ma na kiraki ne kawai ki gasa min amarya ta, zuwa dare idan ta warware in lallab'ata in kwashi gara yanda ya kamata." Cike da iskanci yayi maganar.

Wani irin haushin sa da takaicin sa nake ji a lokacin sai na rasa me zance masa, kawai na buge k'irjinsa da mugun k'arfi na futa daga tsaka insa tare da fad'in"Dan iska kawai."
Mamakin ta yake yi wai d'an iska take kiran shi a kan hakkin shi, ya gano kishi tsagwaron sa a idanunta dama so yake ya tunzurata, babu wata damuwa a tare da shi yace." Ni kam babu mahalukin mutumin da zai kirani da wannan Kalmar a kan HAKKINA, kawai Dan nayi marking love da Matata sai a ce min d'an iska, kin ci albarka cin My Wife Mimi na da sai kin gane kuran ki."
Yana gama maganar shi ya futa daga toilet din ba tare da ya saurari abunda zata ce ba.

Zamewa nayi na zauna dab'as! Kan tayal din dake kasan toilet din na hada kaina da gwiwa ta wani irin kuka ya kufce min Wanda nayi ta kokarin danne shi, kuka nake sosai da sosai ina addu'ar Neman samun sauki daga Allah, wani irin sabon sonshi da kaunar shi naji yana taso min a zuciyata take jikina ya kama rawa duk narasa me zanyi inji dad'i a rayuwa ta.
Motsin bude kofar naji na mike zumbur domin na dauka shine ya dawo sai naga Mimi ta shigo tana bin bango, da sauri naje na kama ta, ita kuma ta dinga bin fuskata da kallo bakinta a bushe tace"Habibty kukan kike yi ko." Babu karya domin ga hawaye ne nan tana gani a kwarmin idona nace" Mimi kukan tausayin ki kawai kawai nake yi." Murmushi kawai tayi min tana fyada kanta, ruwan ha hada mata cike wani baho na zuba detol kad'an a hankali na zaunar da ita ciki. Kara ta k'walla ra tana rike hannuna nace" Mimi ki zauna ki Dade a ciki ZAKIJI dad'i jikin ki." Gyda min kai tayi tana rintse idonta, futa nayi daga toilet din na barta.

Babu kowa a dakin, na hau cire bedshirt din shina duk ga d'igon jini nan, gashi duk ya cukurkude raina babu dad'i ko na kwabo na cire shi hade da aje shi gefa guda, wani na ciro kai kyau na shimfid'a kan bed din, na Ciro mata kaya masu kyau na aje gefan gado, zama nayi ina jiran futowar ta,

Minti ashirin tayi ta futo yanzu tafiyar ta ta sauya ba kamar d'azu ba, na kalleta naga duk ta rame lokaci guda.
Zama tayi kusa dani tana fadin,"Kinga yanzu naji dad'i wallahi."
Nace "Dole haka zaki dinga yi in anjima da yamma ma ki kara shiga ruwan zafin."
Tace"To."
Shiru mukayi tana kokarin sanya kayan ta, ina taya ta. Nace"Kin San me."? Girgiza min kai tayi. Nace"Duk sanda ya kara zuwa yace zai yi sex dake Wallahi kar ki yadda har sai kin warke in ba haka ba tafiya ma zata gagare ki, domin na lura ba imani ne dashi ba."
Karaf!! A kunansa lokacin za yake shigowa dakin yaji Hud'ubar da Asma'u take wa Mimi.








*18/11/2019*
[11/19, 10:01 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*56*





Cike da mamaki yake kallon Asma'u wacce tayi tsili-tsili da ita tasan tabbas yaji maganar da take fadawa Mimi ga yanayin kallon da yake mata.
K'araso wa yayi dakin sosai hannun shi rike da wata Leda har ya zauna gefan Mimi idanunsa na kàn Asma'u yana tuhumar ta da idonsa, sunkuyar da kaina nayi kamar wacce tayi wa sarki k'arya.

Gyada kansa yayi hade da rungumo k'afafun Mimi yana kallona yace." Manene hujjar ki, na bata wannan gurguwar shawarar.?
Kunya ta hanani in d'ago kaina na kalleshi.
Dariya naji yanayi kasa kasa yace." Saboda mugunta kike zugata ta bujere min a shimfid'a kina mata bakin ciki tafi ki ta ko wane fanni, ga lada ga dad'i zata kwanta a kirjin mijinta shi kike wa bakin ciki ai na gane yanzu."
Kaina na dago in kallonsa yanda ya wani matse Mimi a jikinsa yayi mugun bani haushi a zuciya ta nace "Wannan guy wai wane irin tantiri ne?
Ba tare da nace komai ba na mike tsaye hade da gyara hijab dina INA kallon Mimi dake lumshe ido a ka fad'ar sa, nace" Ni Zan tafi idan kin dauki shawara ta kan ki kika yiwa Allah ya bamu alkairi."
Kofa na nufa da sauri.!

Mimi ta yunk'ura da sauri ta mike ta biyo bayana cikin dingisa k'afafu shima bayan ta ya biyo lokacin har na Isa parlor Tarar gabana tayi hade da marairaice fuska tace "Don girman Allah kar ki tafi yanzu ki bari sai gobe."
Kallon baki da hankali nayi mata wai in Bari sai gobe lallai Mimi, ni idan nabar gidanan nayi rantsuwar babu Wanda zai sanya ni na kara dawowa cikin shi, kokarin bude kofa nake in futa yazo ya bake kofar Yana min wani kallo kasa-kasa yace." Malama Madam tace ki bari sai anjima kya tafi kin ji, yanzu ki shiga kicin kiyi mana girki ni da ita."
Hararsa nayi a lokacin sai ya bani dariya saboda nasan duk abunda yake yi domin ya bani haushi pretending yake ina kallon wani Abu boyayye a k'wayar idonsa.
Nace"Wallahi da Kai da Mimi babu Wanda zan yiwa girki Kaji na fada maka ma."
Babu yabo babu fallasa yace." Wato kinanan da Wannan gantsarar taki ko? Na hanani sanya Wannan bakin hijab din kinki ji ke gaki da baki kamar shuni."!!

Naji haushin ba'ar da yayi min sosai na kalleshi fuskata a daure nace",Bani hanya na wuce." Ki yayi ya tsira min ido, Mimi ta k'araso gurin jikinta a sanyaye tace."My heart ka k'yaleta ta tafi tunda baza ta zauna ba."
Kallonta yayi yace." Ok tunda kince a k'yaleta ta tafi kar ki k'ara kiramin sunan ta, idan anjima, dama don kin damu a dauko ta ne."
Hannunsa ta rike tana murmushi,
Matsawa yayi daga jikin kofar na bude na futa ko kallonsu ban yi ba.
Harabar gidan na tsaya INA waige-waige karaf ! Muka hada ido da Mujahid ya futo daga part din shi, jikinshi sanye da kayan kwallo shi da wani boy da bool a hannunsa suna bugawa a filin gurin.
Saurin dauke kaina nayi na fara tafiya
Da sauri Mujahid ya mik'ewa yaron shi, boll din ya Isa gurin ta fuskar sa dauke da kayattacan murmushi.

"Asma'u" sanyayyar murya shi naji yana ambatar sunana, tsayuwa nayi hade da sakin fuskata nace"Na'am kana lafiya."? Ya saki murmushi tare da fad'in"Lafiya Lou nake sai dai tunanin ki ya hanani Sakat! Jiya da kyar nayi bacci wallahi." Dariya na danyi nace"Ka fiye ban dariya har da rantsuwar ka."
"Am serious wallahi babu karya a magana ta jiya da kyar nayi bacci Allah ya Dora min so da kaunar ki kamar raina." Shiru nayi ina kallonshi fuskata a sake, yace." Kin lek'a amare har zaki tafi." Nace" Wallahi kuwa." Agogon hannunsa ya kalla tare da fadin"Gaskiya ana rana bari in futo da mota in kai har gida."
Nace"Aikuwa da ka kyauta." Juya wa yayi da sauri ya nufi part dinshi, kallo na bishi dashi ina murmushi guy yana da kyau da sanyin hali ga nutsuwa.
Mintuna uku naga motar shi na futowa daga nashi gurin, saurin dauke kaina nayi ganin shine yake driving din.
Kusa dani ya tsaya yana yi min Hon!
Banza nayi dashi ina kallon part din Mujahid aikuwa sai gashi ya futo cikin motar shi, ya k'araso gurimu tare da futowa.
Fuskar sa a sake ya mik'awa Amjadu Hannu tare da fad'in "Ango! Ango."!! Dariya suka yi a tare Amjadu ya Sosa kanshi As'usuel yace." Wato dama wayo kuka yi min Ashe haka ake Jin dad'i shine kuka b'oye min."
Mujahid ya bashi hannu suka tafa, tare suna kyalkyala dariyar shakiyan ci, Mujahid yace."Baka da wasa fa wato har an wuce gurin kenan. "
Amjadu yace." Tuntuni Alhaji yanzo sai jiran sakamako."
Dariya suka kece da ita a karo na uku suna tafawa.

Ji nayi tsayuwar gurin ta ishe ni, domin gani nake yi duk abunda yake yi kamar da hujja yake yi, motar Mujahid na fufa jikina duk babu k'wari ,wai ni guy nan yakewa wannan tozarci, wallahi babu abunda zai kara kawo ni gidansa
Bude motar nayi na shiga na zauna abuna.
Amjadu yana kallonta a take ya gimtse fuskar sa daga dariyar da yake yi, kafin ya Ankara Mujahid ya saki hannunsa tare da fadin"Bari i n kai wife dina gida insha Allah."
Fuska ya had'e sosai yana kallon bayan Mujahid da yayi gaba, har ya bude motar sa ya shiga idonsa na kansa yana mamaki yaushe suka shaku shi da Asme yasan halin yarinyar da girman kan tsiya.
Duk yanayin da ya shiga ina kallon shi, tunda motar Mujahid tana gefan tashi, naji dadin ganin yanda ya shiga halin damuwa
Kawai sai na shiga dariya babu gaira babu dalili, shima Muhajid din dariya yake yana kallona cike da so ya kunna motar shi muka wuce motar Amjad din da sauri.

Gumi ne yake tsiyaya a jikinshi wato wulakanci. Da yarinyar nan zata yi mishi kenan, da kanshi ya futo domin ya kaita gida, Dalili ya aiki su Rambo shine zatayi masa wannan cin mutumcin ya lura fa Mujahid da gaske yake ganin yanda yake zak'ewa akan yarinyar bude motar yayi a fusace! Ya nufi part dinshi yana wani taka k'asa da k'arfi sai huci yake yana jin wani irin kishin ta a zuciyar sa.


*****
Hira sosai muke da Mujahid sai yanzu na kare mishi kallo kyakyawa ne sosai yana da d'an kiba amma ba sosai ba fari ne amma ba kai Amjadu ba, fuskar sa kullum a sake, take naji ya kwanta min domin duk cikin samari na babu Wanda na tab'a sakarwa fuska kamar shi, a yanda yake fada min shi da gaske yake aurena zai yi kuma, baya so aja wani dogon lokaci, to nima gaskiya ya kwanta min a rai naji zuciya ta ya kwanta min shiyasa na bashi numbar wayata da zamu rabu, tare da yi min alk'awarin zai kirani da daddare mu sha shira nace masa ina sauraren sa.

Ko da na koma gida a lokacin aunt Hauwa ta tafi gidan sai Umma kadai tana gyare-gyaren abunda ba'a rasa ba, tana kallona cike da mamaki take fadin ",Har kin dawo kenan."? Nace" Eh Umma zaman me zanyi"
"Lafiya dai ko."? Umma ta fada tana kokarin futa daga dakin, ta San dai ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki.
Shiru nayi mata domin ina jin nauyin fada mata dalilin kiran Mimi di.

*****
Rayuwa kenan yau kwanan Mimi biyar a dakin mijinta, inda Umma kullum ya zauna zancan Mimi take yi, duk da cewar kullum sai sunyi waya da ita, wani lokacin ta bani wayar mu gaisa ta k'araci korafin ta ta gama , sai dai in ce mata kawai tayi hakuri zan zo. Wani lokacin kuma idan ta kira wayar kin karba nake yi ko in tashi in bar gurin.

Ya Aminu da Babban su Munnu sune suke mana cukucukun makaranta nan FCE Babban su Munnu yake sha'awar muyi mu samu ko Diploma ne tsakanin Munnu da Ya Aminu soyayya tayi k'arfi domin Babansu ya kori Shamsu tunda yayi da shi ya turo manya a yi magana shikkenan ya gudu daga ranar be kara zuwa ba.

Gaskiya naji dadin koma wa makarantar da zamu yi ina mutukar son in ga nayi karatu me zurfi a rayuwata.
Ni da Munnu sai shirye-shirye muke yi wacce tayi tayi dani muje gidan Mimi naki zuwa, ita kuma tace baza taje ita kadai ba.


********

Rayuwa suke da Mimi babu yabo babu fallasa Shine me Dan shige mata jiki ita kuwa kullum kamar suruka take a gurin shi, idan yana guri ta dinga b'oye-boye kenan shi dai sai dai yayi dariya kawai yana mamakin me zata b'oye masa Wanda be gani ba.
Tun ranar da ya kwanta da ita kwamciyar aure bai kara takar ta ba, sai dai duk daran duniya yana ragewa kansa zafi da ita, amma bai kara gangancin yin sex da ita saboda baiji da dad'i ba a farko.


Misalin k'arfe goma sha biyu da rabi na ranar Asabar Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu gidan Amjadu, tana zaune a parlor ita kadai lokacin ya futa zuwa company sa kuma dai shirye-shiryen tafiya Chana yake yi shiyasa kwana biyu baya zama sosai.
Kallo take yi ita daya kamar tsuntsuwa, sai ta soma jin takun takalmi za'a shigo parlor da sauri ta kallo kofar shigowa, suka Had'a Ido da Alina ta shigo cikin wasu 'yan iskan kaya fuskar ta tasha make up sai taunar cingum take, hannunta rike key din motar ta tana kar kad'a shi, tazo ta tsaya kan Mimi tana girgiza jikinta, cikin shigar raini.
Mimi tace" Alina babu sallama kika fado min gida."
Wata irin mahaukaciyar dariya Alina ta kwashe da ita tare da fadin"Su Mimi masu gida!!!! Hahahahaha.'' Mimi ta bita da kallo cike da mamaki.
Wani irin tauna tayi wa cingum din bakinta tayi kwai dashi ta kalli Mimi a d'age tace."Ina sugar Boy yake yi."?
Alina ce kawai take kiran shi da wannan sunan."
Mimi tasha kunu tare da fadin "Ban sani ba ni Zak........ Kafin ta karasa Maganar tata Alina ta wanke ta da mari tare da fadin" Kinyi ganganci Wallahi!! Kinyi gangamcin shiga gona ta, shigiya 'yar mutsiya ta, kar ki ce bam san abunda yake faruwa tun daga farkon auran Ku har karshen sa, duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login