Showing 45001 words to 48000 words out of 92177 words
Chapter 16 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
tace" ko in bawa Asma'u wayar ne." ? Girgiza kansa yayi kamar tana kallonsa yace." K'yaleta kawai Momyna zamu gaisa idan anjima OK."
Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayar yana jin wani mugun daci a bakinsa, ko wane ango yana farin ciki ranar d'aurin auransa mussaman idan ya tuna amaryar sa, amma shi ranar d'aurin sa ta zame masa ranar bakin cikinsa Asma'u ta cuce shi, bai ta tunanin zai fada rudani na so irin wannan ba.dole yayi kokarin sa Mimi cikin zuciyar sa, ko don ya haddasa Asma'u ciwan zuciya kamar yadda take kokarin haddasa masa, wannan itace shawarar da ya yanke.
****
Mimi ta dawo fuskar ta cike da walwala da farin ciki, tace"Asma'u yace." Mu shirya bayan sallah magariba zai turo a dauke mu akwai walima da a bokanshi suka hada masa, da har nace ko in baki wayar Ku gaisa yace A'a in k'yale ki." 'Yan dakin suka kwashe da dariya tare da fad'in"Haka kurrum yana jin zakin muryar ki, zaki had'a shi da masifaffiya mai saurin baki, mai zai fuskanta ya burgini da ya gwale ki." Dariya suka kwashe da ita har Mimi din, wani irin b'acin rai ne ya kamani lokaci guda, ganin yanda suke min dariya sai naga kamar da gayya suke yi min har ita Mimi din, raina ya b'aci mutuka, Mimi tace. A bani wayar yace baya bukata lallai ma guy nan, cikin jin haushin su nace banzaye 'yan iska kawai baku da aiki sai iskanci da dariya Ko wacce ta rasa mashinshini don Allah a daure ayi aure ko kwa rage zumudi da tsiyayar da kuke yi." Ihu!! Suka sanya kamar wasu shashasha, Maryam tace"Dallah malama yi mana shiru ke akwai wacce ta fiki zuba, daga an fara zancan aure zaki hau lumshe ido idonki har ja yake yi "yar iska, hahahahaha " ta k'arashe maganar tana dariya Tare da bawa ta kusa da ita hannu suka tafa tsaki naja me k'arfi nace "Kanku a keji, kun dai ji Abunda Mimi tace ko, gaskiya Ku kintsa sosai bana son shirme a gurin ku zama manyan baby's kar Ku bani kunya shegu." Munnu tace"Dole ne ai nasan gurin zai had'a had'addan Samari gaskiya
Dariya muka kwashe da ita nace"Munnu ta Shamsu kenan" Hararata tayi, ni ko na cigaba da shiryawa ta ina mata dariya, aunt Hauwa ce ta lek'o dakin tare da kiran Mimi hannunta taja suka futa, nace"Mimi yau kin bannu a gurin aunt Hauwa.
****
K'arfe takwas dai-dai gurin Walima ya k'ayatu, nan cikin Estate din aka shirya komai guri Tasha decoration, haske ko ta ina ga wasu shegun kujeru an ajiye guda biyu na ango da amarya ne, su uku ne kacal cikin Estate din, Ma'aruf Mujahid Hafiz sai Amjadu din, dukanin su ma'aikata ne, Hafiz yana aiki a babban banki najeria, shi kuma Ma'auruf yana aiki a babban Asibiti na nasarawa Mujahid yana aiki a Company d'angote cement shine manager dukaninsu suna da aure da yara biyu Hafiz ne me D'a d'aya tunda shi bai jima da yin auran ba, sai Amjad da yayi aure yanzu, suna zama na fahimtar juna a tsakaninsu, kasamcewar su Ma'aikata yasa basa haduwa sosai sai weak end suke had'uwa su gaisa da junansu sai kuma lokacin azimi suke shan ruwa tare, yau idan an sha ruwa gidan wannan gobe a sha gidan wancan, Amjad sai dai yaje domin shi bashi da matar ma, sunyi ciwon baki har sun gaji, Matar Hafiz me suna Samina ita ce ta dinga nanika masa k'anwar ta yana basarwa da ta lura ba auran zaiyi ba kawai sai ta hak'ura, amma dukaninsu sun yi mamaki da suka ji labarin auran sa katsaham! Shine suka shirya masa walima domin taya murna, amma da ba don haka ba , shi babu wani shiri da yayi domin murnar ranar.
Dukaninsu sun gayyaci abokanan su shiyasa guru ya tsaru domin duk manyan 'yan boko ne samari masu kwalisa gayu kenan, ango kuwa babu wani abokan shi da ya gayyata, to yawanci ma shi bai fiye sakewa da mutane ba, kuma abokan shi da suka shak'u da juna turawa ne, 'yan gari daban-daban shiyasa sam bai da abokai a najeria sai Wanda ba'a rasa ba.
Shigar wani irin yadi suke yi baki Wanda bantab'a ganin irin shi ba, dinki iri daya huluna iri daya takalman su iri daya kai hatta da agogon hannunsu iri daya ne, sunyi kyau sosai da sosai, Amjad ya futo ango dashi sai gaisawa yake da jama'a fuskar shi babu yabo babu fallasa.
****
To muma namu b'angaran haka take mun shirya sosai ko wacce ta k'ure kwalliyar ta, ni da Mimi kayan mu iri d'aya, cikin Wanda ya aiko Rambo dasu ne jiya muka dauki wani masifaffan les ruwan Zuma, anyi mishi wani irin dinki mai tutoci gaba da baya dinki Riga da siket ne rigar kuma bata da girma babu abunda yafi burge ni da dinki sai yanda aka kaya ta hannun rigar d'aya dogone d'aya kuma gajere gajeran anyi masa wani falmaran a saman sa cif rigar tayi min amma duk da haka saman k'irjina sai da suka futo k'aida ne dama indai zan sanya Riga pitatd to sai saman nonuwana sun futo har tsagar su, saboda Allah yayi min baiwar su, sai nayi amfani da gyale mai Dan fad'i inda na samu ya rufe min mazaunai na, amma yana da sharara dole sai an ga komai nawa, hakan ma dai dashi gwara babu, ni kuma bazan yi kwalliya ta in sanya babban mayafi ba.
Mimi kam net ta sanya kamar yanda amare suke yi muka futo waje muna ta d'aukar hoto, wayar na hannuna naga kira, shine na daga kaina ina Neman Mimi tana can suna hoto, a dake na daga wayar nayi sallama.
Zuciyarsa yaji dam!! Jin muryar ta, dake namiji ne sai ya maze cikin wata 'yar iskar murya yace." Mommahh ga motoci nan sun tawo d'aukar Ku, na k'agu naga fuskar ki, wallahi naji k'amshin ki, humm! Ina fatan zan same ki, a yanda nake tsammani, sai kunzo."! Kashe wayar yayi ba tare da ya bari tace komai ba, ya maida ita aljihunsa, ya cigaba da sabgar shi da jama'a.
Saroro nayi da waya a hannuna gwiwa tayi sanyi sai naji duk wani karsashi da kuzari na, yayi kasa, tunanin guy nake, dama can yana son Mimi Ashe yake pretending ko kuma yanzu ya fara sonta, ni dai tunda nake dashi ban tab'a jinshi da irin wannan muryar ba, gashi yana fad'a mata kalamai na so, zuciyata ta shiga zullumi da wasi-wasi, gashi tayi min wani nauyi ina jin bakin ciki a cikinta da kyar na dai-dai ta kaina na shiga cikin jama'a muka cigaba da hoto amma lokaci lokaci sai inji fad'uwar gaba idan na tuno guy din.
Motoci uku ya turo masu zafi dama ba mu fi mu bakwai ba, muka shiga sai Jan bolo gurin parking motocin suka k'arasa da mu sannan ko wacce ta futo, haske ko ina da ina kamar rana ga wasu manya manyan motoci a fake a gurin, k'amshin turare kuwa na wannan yana wane wancan, can hango shi ya tawo abokanshi biyu a bayan shi, gabana ya dinga bugawa tun kafin su k'araso nake kokarin nemo jarumta ta tana guduwa yayi min masifar kyau! Farin mutum cikin bak'aken kaya, sai ya zama kamar wani tauraro cikin abokan nasa abun mamaki tunda ga nesa nake hango wani kwantaccan murmushi k'ayattace a fuskar sa, Suna karasowa gurin ya rike hannun Mimi tuni abokan shi da masu d'aukar hoto suka fara aikin su, suka fara tafiya mukuma muka rufa musu baya, na lura bani kadai ce na shiga halin d'imuwa ba har da k'awayemu suma duk jikinsu yayi sanyi ganinshi narasa me yasa yake wa mutane kwarjini haka,mussaman mata.
Addu'ar Neman
nake cikin zuciyata, *"Wallahu galibun ala'amri."* wannan addu'ar nake yi cikin zuciyata domin ina ganin zuciyata zata iya tona mun asiri, a gurin, shiyasa na dauki alk'awarin bazan k'ara kallon inda yake ba, suna. Tafiya ana musu vedio da hotona har suka Isa gurin zaman su, muma muka samu guri muka zauna, sannan guri yayi shiru mai gabatar wa ya tashi ya gabatar da malamin da zai fad'a kar kam zaman aure da abunda auran ya kunsa
Wa'azi yayi kyau kuma ya fad'ar kar sosai bayan ya gama. Masu rabo suka shigo suka fara raba wasu manya-manyan ledoji komai cikin nutsuwa akeyin shi, ko da wasa naki kallon inda suke zaune, hira ma muke yi da Maryam tana k'ara fada min Yanda Mimi tayi dace da miji tana fadin"Dole sai tayi da gaske domin akwai 'yan matan shi da suka d'aura arinyar akanta mussaman Alina." Nace"Dole kuwa Alina kinga ko zuwa bata yi ba." Maryam tace"Yaushe zata zo matar da tunda taji abun take tada Aljanu." Dariya nasa Ina rufe fuskata da hannuna kawai sai naga hasken flash dago kaina nayi da sauri, naga d'aya daga cikin abokan shi Wanda suka sanya kaya iri daya yana tsaye a kanmu nida Maryam sai daukarmu a hoto yake mussaman ni. Bata fuska nayi ina kallon shi, murmushi ya sakar min, tare da kashe min ido daya. Dauke kaina nayi ina Jan tsaki k'asa-k'asa. Gurin ya bari yana duba wayar shi, hotona yake dubawa
Duk abunda yake faruwa tsakanin Mujahid da Asma'u a kan idonshi, yasan halin Mujahid akwai son matan tsiya gashi dai da auran shi, amma in yaga mata jikinsa har tsuma yake, yaji wani iri a zuciyarsa amma kallon da yaga Asma'u na watsa ma Mujahid din ya ji dad'i a zuciyarsa yace." Mata masu daraja kenan."
Mik'ewa nayi daga gurin ina waige-waige Su Munnu na can baya an had'u da samari ana hira da ciye-ciye ganin na mike yasa Maryam mik'ewa muka fara ratsa jama'a tafiya zamu yi tunda dai an gama ango ya kawo amaryar sa gida domin na tsani kallon da maza suke min. Aikuwa ido yayi caaaaa! A kanmu ni kaina a jikina nasan kallona ake yi, cikin sauri sauri nake tafiya inda sassaan jikina yake motsawa, sai tsaki nake.
Amjadu kuwa tun lokacin da ta mike tsaye ya karewa jikinta kallo kuma yaga yanda shatin jikinta ya futo ta cikin sharara din mayafin ta, sai yaji kamar ana soka masa kibiya a kahon zuciyarsa, mussaman. Yanda yaga maza da dama sun raja'a a kanta, gumi ya tsinke masa, lips d'insa ya tura a baki yana ji kamar ya hadiyi zuciyarsa ya huta da wannan bakin ci, Mimi ya kalla a sace ya ga Sam ita babu wani abun assha da dinkin ya futo mata dashi, ya rasa wace iri ce Asma'u me karuwan jiki, ko wane irin kaya tasa sai sun tona mata asirin jiki. Innalillahi wa'inna'ilah raji'un. " shine abunda yake nanatawa cikin zuciyarsa ko ya samu sassauci.
Ganin duk sun mike ne suna kokarin futa daga gate sai hakan yayi masa dad'i mutuka wayar sa ya dauka yana kiran Rambo yace." Maza'a maida su gida shi da kansa zai kawo Mimi gida aikuwa haka aka yi, muna kokarin shiga mota ne sai ga Muhajid ya k'araso gurin, hade da kure ni da ido yana sakin wani murmushi, yace." Asma'u." Nayi mamakin yanda ya San sunana haka, babu yabo babu fallasa nace." Na'am ya kake."?
Murmushi yayi Wanda na lura hakan d'abiar shi yace." Lafiya amma ba Lou ba, tunda na ganki na rikice na gigice na dimauce na rasa nutsuwa ta, Asma'u ina kaunar ki fisabillah." Ya k'arashe maganar sa har da kwantar da kansa, Su Munnu kuwa dariya suke masa, yace." Ina da mata da yara biyu ni ma'aikacin lafiya ne, ina aiki a nasarawa hospital ina fata zaki so ni kar kice na miki tsufa." Yanayin barkwancin sa da yanda yake da sakin fuska da wasa da dariya yasa na saki fuskata nace"Ashe dai ka sani ni kam kayi min tsufa bazan auri me mata ba." Marairaice fuska yayi hade da fadin "Don Allah kinji. " sai na tsinci kaina da sakin dariya har fararen hak'ura na suka bayyana Wanda yayi dai-dai da zuwan Amjadu gurin Hannunshi rike da na Mimi, ina ganinshi na dauke kaina da sauri gaba na lugude, ko kallonmu bai yi ba nida Mujahid ya fara magana dasu Rambo Wanda suke kokarin saka mutane a mota, Ina jin Mujahid nace "Aboki nifa nayi mata a gurin nan gaskiya naji dadin wannan ranar wallahi na tsinci dami a kala."
Babu yabo babu fallasa ya kallemu dani dashi yayi wani killer smile As'usuel ya sosa kanshi tare da fadin"Kayi dace Aboki amma bakayi gaggawa ba, kuwa." Mujahid yasa dariya tare da fadin" Wane irin gaggawa kuma in tsaya kallon ruwa kwad'o yayi min k'afa."
Kamar babu abunda yaje damunsa ya sanya dariya tare da fad'in"OK ni babu ruwana wallahi kai da Madam."! Mujahid din yace." Shareta ai ba da ita kadai zan zauna ba." Shiru yayi masa ya cigaba da magana da Rambo, ko da wasa ban kalli shi ba sai ma sauri da nayi na bude motar na shiga.
Ina kallonshi ya rungume kafad'un Mimi a jikinshi lokaci-lokaci yana sumbatar goshin ta, hade da yi mata magana k'asa-k'asa, da sauri na kauda kaina dama tsautsayi ne yasa na kalleshi, Yanzu kuwa Allah Allah nake motar ta tashi mubar gurin.
*16/November/2019*
[11/17, 1:56 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*54*
Sai ya tabbatar da motocin su sun tashi sannan yaja hannun Mimi suka bar gurin, cikin sauran abokan sa ya koma masu hoto suka dinga d'aukar shi da Mimi sai sunkuyar da kanta take cike da kunya shi kuwa rumgumeta yake jikinsa fuskar sa a sake, 'yan jaradi ma ba a bar su a baya na sai da suka zo ganin k'waf tare da d'aukar amarya da ango hoto da vedio walima tayi kyau sosai kuma ta k'ayatu, k'arfe 11:30 gurin yayi sauki jama'a duk sun a watse a gajiye yake sosai amma babu yadda ya iya dole ya maida Mimi gida. Hannunsa rike da nata babu um bare umum suka shiga mota tare Doh! Yazo da sauri, sai ya daga masa hannu alamun a'a baya ya matsa, yana d'aga masa hannu yaja motar suka futa daga Estate din.. Sai da ya hau kan kwalta sannan ya kalleta a fakaice yace." Momy kin gaji wannan idon naki akwai bacci a cikinsa."? Mimi tayi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace." Wallahi na gaji sosai hankalina yayi gida." Cike da tsokana yace." Da har ina cewa kinzo kenan baza ki koma gida ba." Kauda kanta tayi cike da kunya, hira sama-sama suke yi da ita kamar wasu surukai har suka Isa badawa yayi parking a inda ya saba, kallonta yayi da lumsassun idonsa saurin dauke kanta tayi, ya saki murmushi tare da fadin "Kije ki huta kinji ko gobe ina jiran ki, kiyi min tanadi me kyau." Kofar motar ya bude mata hade da sumbatar hannunta guda, Mimi ta futa a hankali tana d'aga masa hannu, motar yaja ya bar gurin, dake da wutar NEPA a unguwar yasa matasa basu watse ba. Mimi ta tsallaka ta shiga lokonsu cikin sauri
Hira muke da su Munnu amma hankalina da tunani na nakan Mimi gamin har k'arfe goma sha biyu saura bata shigo gidan nan ba, Umma ma ta leko dakin kusan sau uku tana tambayar ta shigo, aunt Hauwa ce ta kwantar da hankalin ta, tunda dai tana gurin mijinta,Ni da Munnu hirar muke Mimi ta shigo da sallama, duk muka bita da kallo, 'yar dariya tayi tare da fadin'Meye daga shigowa ta zaku zuba min ido."? Tsaki naja ina d'an hararata nace." Mimi dubi lokaci fa ke ko tsoro bakya ji, bakya ce masa dare yayi." Maryam dake danne-danne a waya tace "Wane irin tsoro tana tare da mijinta." Munnu tace "Nima dai abunda na gani kenan." Tab'e bakina nayi kawai ina kallonta ta tsallako har inda nake zaune k'amshin turaran sa ya buge ni, domin duk jikin Mimi k'amshin masifaffan turaran sa take, d'an rungume ta da yayi, sai naji zuciya babu dad'i wani irin kallo nake mata cike da zargi ina tunanin ko wani Abu ya shiga tsakanin ta dashi, tunda nasan halinsa ba hakuri ne dashi ba, mik'ewa nayi na futa daga dakin domin ji nayi wani irin fleelings na taso min jin k'amshin turaran sa sai na dunga tuno da salon soyayyar shi, Uwar dakin Umma na shifa duk mutane kwance a rumfa na tsallake su, kwanciya nayi kan gadon ta, gefan aunt Hauwa wacce take bacci sosai nasan gajiya ce." Lumshe idona nayi ina addu'ar kar Allah ya dora min tashin sha'awa ta a wannan daran nasan zan shiga mugun hali ga jama'a a gidan.
****
Shima bashi bangaran damuwa da tsanani gajiya su suka dame shi, don haka yana shiga part dinshi yayi wanka ya futo parlor ya kwanta kan doguwar kujera lokaci guda bacci ya dauke shi, mai cike da mafarkai bar katai.
****
Washe gari da kuncin zuciya na tashi har 'yan buki suka so su gane ganin naki walwala kamar jiya yasa suka dame ni da tambaya dole na sake na cigaba da wurda da mutane kamar yanda na saba.
K'arfe bakwai dai-dai motoci sun fi ashirin kofar gidanmu da bakin layinmu duk na d'aukar amarya ne da 'yan uwanta kowa sai da ya samu guri wasu ma basuyi niyyar zuwa ba, mussaman makotanmu amma saboda su kashe kwarkwatar idonsu yasa suka dinga futowa daga gidan jansu su da gayyar 'yayansu suna fadin"Hali Yayi yau Dole suje suga gidan *Young millionaire* Estate din sai da ya kusa cika da mutane sai hauka suke da ihu hade da k'auyanci aikuwa karnuka na rufe a gurinsu suka dinga haushi sosai, saboda ganin sabon Abu.
Kowa fadin albarka cin bakinsa yake game da kyau da tsaruwar gidansa ni da Munnu da ita kanta Mimi gidan ba bakonmu bane, saboda haka bamu damu ba, amma dai naga sauye-sauye a parlor ba kamar zuwana na baya ba.
Mimi