Showing 30001 words to 33000 words out of 92177 words
Chapter 11 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
ganinshi wahala ce,kaso Wanda bai San kana yi ba, bai tab'a tunanin son da Mimi take masa ya kai haka a zuciyar ta, sai yaji zuciyar sa tana ce masa da ma wannan Soyayyar daga gurin Asma'u ka same ta daka ji dad'i. Amjad mutum ne mai mutukar son a dunga tattashin sa da rarrashin sa kulawa da soyayya, shiyasa yake addu'ar Allah ya bashi mace wacce take da wannan azanci domin matan ma suna suka tara.
Yafi minti goma a tsaye a kanta yana kallonta, kokari yake yaji wani abu wanda ya shafi so ya darsu a zuciyarsa a game da ita, bai ji komai ba sai dai tausayin da taye mata da kuma kaunar da yake mata saboda sunan Maman shi, Wanda ba ita kadai yake wa wannan kulawar ba, mutukar A kace kina da suna Aisha to zaki samu kulawa sosai a gurin shi.
A gogon dake daure a hannunsa ya kalla hud'u shaura na Asubah. Gyad'a kansa yayi ya bude kofar dakin a hankali ya futa, har yanzu suna zaune a inda suke sai dai sun matso cikin wata rumfar kwano dake gurin saboda sanyin asubah. Sosai suka bashi tausayi mussaman Asma'u da ya ganta tayi wujuga-wujuga da ita ga idanunta sun kode. daga nesa ya tsaya tare da fadin "Umma ni zan wuce Allah ya bata lafiya."
Umma tace"Ameeen suma ameen mun Gode k'warai da kulawa." Kallona naga yayi a fakaice sai kuma ya kalli Aminu dake dauke dauken kai ya mik'a masa hannu domin suyi sallama.
Da kyar Aminu ya bashi hannunsa, Amjadu ya wuce yana mamakin abunda Aminu yake yi sai kace jahili in banda dalili ya kai dalili Aminu ya Isa yaga inuwar shi ma ballanta ya hada hannu dashi, duk sanadin Asma'u ne.
Sai da ya shiga motar sannan ya kira ta a waya, ina jin wayar na ringing naki dauka Munnu ta karba daga hannuna tana dubawa. Mik'a min tayi tare da fadin"Shine." Aunt Hauwa tace" Sai ki tashi kije mybe akwai abunda zai ce miki."
Kallon da Umma tayi min ne yasa na mike da sauri na bi hanyar da naga ya bi.Na gane motar shi tunda duk inda suke basa b'uya bayan haka kuma gurin da haske.
Kallonta yake yana daga cikin motar har ta k'araso. Ajiyar zuciya ya sauke babu wasa a tartare dashi ya bude motar tare da fadin"Shigo muyi magana dake ta fahimta."
K'in shiga nayi na tsaya ina kallonshi. Shima ya kalle ni babu fara'a yace." Time d'in sallah ya kusa ki shigo muyi abunda zamuyi in tafi gida Ok."
A hankali na shiga motar na zauna ina kauda fuskata. Ya kalle ni na minti uku, kana yace." Wannan kukan da kike yi Sam! Ba zai miki maganin komai ba sai dai ma ya kara sanya miki damuwa da ciwon kai, Yanzu shawara zamu yanke dake idan kin amince ni mai sauki ne."
Kallonshi nayi ina d'an ya mutsa fuskata nace"Ina jinka." Shiru na minti biyu bai ce komai ba yana kallona, na dago kaina hade da watsa masa harara nace"Kace lokacin sallah ya kusa amma kuma ka sanya ni a gaba kana kallo kamar tv."
Ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe idonsa, k'asa-k'asa naji yace." Asma'u Allah ne kadai yasan ita a dadin kaunar da nake miki a cikin wannan zuciyar tawa, tun da nake a rayuwata ban tab'a furta wa mace WANNAN Kalmar ba sai ke, duk da cewar nayi rayuwa da 'yan mata iri-iri masu kyau da kudi Asali nasaba da wayewa amma babu wacce ta samu wannan Kalmar sai ke."
Shiru nayi sauraron shi. Ya cigaba da cewa "Ina da kudi sosai Wanda ban San iya a dadin su ba kuma kullum karuwa suke yi ina zakka da duk wani Abu da Allah yace kayi da dukiyar da ya baka amana, Abu guda ya rage min mata, kuma na samu insha Allah." Shuru Yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Mimi ta bani tausayi mutuka nasan illar so, tabbas tana so na, Wanda naji a zuciyata dama kece kike min irin son da take min da babu namijin da ya kaini dacewa a duniyar nan."
Kallonshi nayi jin abunda yake fada.
Dauke kaina nayi hade da d'an ya mutse fuskata nace"Me yasa ka yaudari Mimi kasan baka son ta."
Shiru yayi yana nazarin magana ta can naji yace." Da farko da wasa nake yi, amma daga baya na d'aura niyyar auranku tare domin in cuzguna miki dalilin yin haka kuwa shine Rashin mutumcin da kika je kikayi gurin pary Ku ya bani haushi shiyasa na yanke wannan shawarar."
Murmushi nayi me ciwo nace"Idan domin ka bani haushi kace zaka auri Mimi a lokacin wallahi da baka wahalar da kanka,saboda kasan shi so sai ana kishin mutum ake yin sa, Mimi tana sonka tana kishin wani ya rab'e ka ciki kuwa har da ni, Mimi ita yafi da cewa ka aura bani ba."
Fuskarsa ya Dan hade yana kallona tare da k'ankantar da idanunsa yace." Gashi ni kuma ba Mimi nake so ba ke nake so, sai dai idan kin yarda in hada ku, Ku biyu in aura amma duk abunda ya biyo baya kar kiyi kuka dani."
Ba tare da tunanin komai ba nace"Ni dama akan wannan k'adami nake, Ya Aminu dole ya janye maganar auran Mimi idan yak'i janjewa nima nace bazan aure ka ba, sai dai duk mu hak'ura dama ni ban damu ba, itace abar damuwa."
Gabanshi ya fad'i jin abunda take cewa, tana nufin idan Aminu bai janye maganar auran Mimi ba itama baza ta aure shi ba? Lallai a kwai badakala anan gaba, idan Aminu yak'i janje maganar shima ya kusa fadawa chakwakiya kenan, yanzu zai canza salo domin ya risinar da zuciyarta iya zaman shi da ita ya fahimci yarinya ce me mugun taurin kai da kafiya.Dole ya nema wa kansa mafuta domin bai San abunda zai je ya dawo ba nan gaba.
Shiru motar tayi bayan na gama magana ta. Yace." An sanya wata uku na auranmu ina ganin za'a kara sauko da lokacin k'asa saboda gudun wata masifar, ki San yanda zakiyi a gida ki ga Aminu ya janye kudirin sa daga kan Mimi ni kuma zan aure Ku ga ba d'aya."
Motar nake kokarin bud'ewa ina fadin"Kai kake damun kanka da lallai sai ka aure ni, nifa idan Ka aure duk d'aya idan baka aure ni ba ma duk d'aya ne, mutukar ka aure Mimi da ka sanya ta fad'a komar ka shikkenan bukata ta tabiya domin likita yace zuciyarta daf take da ta buga."
Ina gama magana ta na bude motar hade da fucewa a fusace.!! Kallo ya bita dashi cike da mamakin gaud'ancin ta yarinya mai baud'andan ra'ayi shi a yanzu ma ya rasa in da ta dosa. Jikinsa babu kuzari yaja motar ya tafi zuciyarsa na masa wani irin ciwo idan ya tuno kalaman ta wai bata son sa, wannan kalma ta nayi masa mugun ciwo ya za'ayi ya auri macan da zata dinga gasa masa magana ko wace iri CE, da Alama Asma'u baza ta kula dashi. Mimi ita ke son sa sosai da sauran 'yan matansa tabbas a gurin su zai samu irin kulawar da yake buk'ata.
Bayan munyi sallah gari yayi haske sai ga Babansu Munnu ya shigo a sibitin cikin motar sa, dama jiya gida ya koma saboda b'acin ran Aminu.
Da sauri muka mike ni da Munnu muka karasa gurin da yayi parking din ya futo muka gaishe shi hade da karb'ar kayan dake hannunshi, k'aton Fula's din tea ne sai wata Leda babba cike da bread da kayan shayi dangin su madara da Milo gaba yayi muka bishi a baya.
Cikin mutum ci suka gaisa da Umma aunt Hauwa ta gaida shi Aminu baya nan domin ana idar da sallahr ya tafi gida, kai tsaye..... Ciki ya shiga gurin dector
Ni da Munnu ne muka had'a wa kowa tae d'in shi ga manya manyan bread nan kowa ya dauki Wanda yake so, Ni kam tea din kawai nake kurb'a bakina babu dad'i fargabar rashin lafiyar Mimi da tunanin maganganun Amjadu na d'azu, nayi mamakin yanda yake k'aryar min da kai da sanyayyar murya yake fadin Yana sona, mutum me kudi kyau mukami izza da ginshera duk ya na dasu, amma d'azu duk ya aje su gefe, gaskiya na gazgata maganar shi, tab'e bakina nayi kawai na cigaba da kurbar tae din amma lokaci zuwa lokaci sai in ji gabana ya fad'i tsigar jikina ta mike idan na tuna shi.
K'arfe Takwas dai-dai wata nursa ta futo tace"An futa da Mara lafiyar yanzu zaku iya shiga Ku ganta duk da cewar ma yanzu za'a baku sallama." Da sauri muka mike dukaninmu muka fara turereniyar shiga duba Mimi.
Tana zaune kan gado tayi wani firgai-firgai da ita fuskarta ta kode ta kara wani ufan haske Mimi da ma ba jikin arziki ba tayi wata irin rama lokaci guda. Umma na ganin ta sai hawayen ta ya dawo ta zauna kusa da ita hade da iri hannunta tana fadin"Mimi ke ce kika dawo haka lokaci guda." Ganin Umma na zubar da hawaye Mimi ma ta fashe da kuka kamar zararriya ta hau dukan k'irjinta tana fadin"Umma k'irjina ciwo da nauyi na rasa wace irin masifa ce wannan? Umma na rasa me yake damuna gwara in mutu in hutaa!!!!! Aunt Hauwa ta buga mata tsawa Cikin jin haushin ta tace"Don Allah ki daina wannan kukan da kike yi kiyi tawakkali mana ita rayuwar ai duk hakuri ake yi, kina kuka kina bugun k'irji dole hankali Umma ya tashi, ko me kike ji a zuciyar ki sai ki dinga fadin "Innalillahi Allah zai miki magani."
Leb'anta na rawa tace"Aunt Hauwa baza ki gane ba ne, bana fata Allah ya dora wa wani masoyina abunda nake ji a zuciya ta, gwara in mutu da wannan rayuwar."
Hankalina ya kai k'oluluwar tashi jin abunda Mimi take fad'a ban tsaya naji Abunda Ummansu Munnu take cewa ba na futa daga d'akin. ba tare da sun ganni ba.
Diri-diri nake harabar a sibitin kamar wata sabuwar mahaukaciya nayi waje da sauri na, bakin titi na tsya na tari a dai-dai ta sahu, na fad'a mishi idan zai kaini. Har kofar gidan Kawu Yunusa ya aje ni, nace"Bari in shiga ciki in karb'o maka kudinka." Kallo kawai d'an a dai-dai ta ya bita dashi.
Ina shiga soron gidan naci karo da Musa zai futa yaci kwalliya cikin shaddar sa, gaishe shi nayi ya amsa yana was he min baki, tare da fadin "Husna kece a gidan nan da Safiya." ? Nace"E h Musa ga mai s dai-dai ta can bashi kudinsa don Allah." Da sauri ya futa ni kuma na shige gidan.
Muka gaisa da Baba Mariya a muntunce sai tsokana ta take da amarya amarya ni dai nayi mata shiru, tace"Na ganki duk a furgice ." nace"Kawu yanan ko."? D'aga kanta tayi tare da fadin yana sama tare da d'aya Kawun naki Idiris nasan maganar auran ki suke yi." Mik'ewa nayi ina fadin"Yawwa dama gurinsu Nazo."
Babu yabo babu fallasa nayi sallama dakin Kawun namu Wanda ya zame mana waliyi, daga ciki naji muryar shi yana fad'in "Shigo ko waye." Na shiga cikin mamaki suka Bini da kallo shi da Kawu Idiris na zauna muna gaisawa . Kawu Idiris yace." Daga ina kike da sassafe nan." ? Nace"Daga asibiti. " Kawu Yunusa yace."Waye babu lafiya."? Kuka na fashe musu dashi nace"Mimi ce ." Kawu Idiris yace."Mai ya same ta kiyi shiru kiyi mana bayani yanda zamu gamsu."
Cikin kuka nace"Aman jini take sosai da kyar likitoci suka shawo kan Matsalar kuma sun ce lallai a bata abunda take so idan ba haka ba zuciyar ta zata buga da ko wane lokaci."
Kawu Yunusa yace." To mu wannan ai bs hurumin mu bane zaki zo ki tayar mana da hankali da sanyi safiyar nan." Kawu Yunusa yace." Nima abunda na gani kenan kije ki Sanar da kanin mahaifin ta shine magana."
Kallonsu nake cike da mamaki dama halinsu ne rashin zumunci da rashin taimako Sam 'yan uwan Babanmu basu da kara basu da kawaici kowa kansa ya sani da iyalinsa, mun sha wahala sosai bayan mutuwar mahaifinmu shiyasa nake jinjinawa aunt Hauwa ta ko wane fanni domin ta taka muhimmiyar rawa a gare mu, kafin Umma ta tsaya da k'afafunta.
Nace." Kawu Wallahi nayi rantsuwa da Allah mutukar baku sanya Ya Aminu ya janye maganar auransa da Mimi ba to nima dole Ku warware nawa Ku mai da wa da Amjadu kudinsa, na aure da kuka karb'a, Mimi ba son Aminu Amjadu take so saboda haka yace. Zai auremu ni da ita Ya Aminu dole ya hak'ura tunda shi namiji ne idan yak'i hak'ura kuma to nima bazan aure shi ba."
Jikinsu ne yayi sanyi jin abunda yarinyar take cewa, Suna murna arziki ya shigo musu gida ai ba za su Bari wannan dama ta kubce musu ba shiyasa suka yi ruwa suka yi tsaki kan al'amari idan banda rashin hankalin Asmau da kanta ta zo nema wa kanta kishiya. Babu ruwan su su dai burinsu suga tabbatuwar auran ta da Amjadu ko banza zai kira su Waliyyanta Kuma zai dunga tunawa dasu, duk abunda zai biyo baya babu ruwan su."
Kawu Yunusa yace." Wannan ce matsalar taki."? Gyada kaina nayi ina share hawaye na, Yace." Kar ki damu zan samu Aminu in rarrashi shi tunda kinji kin gani shikkenan Allah ya sanya alkairi." Ameen nace na mike hade da yi musu sallama.
Tana futa suka cigaba da maganar cike da mamaki sukan ba damuwar su bace hakan burinsu tabbatuwar auran kawai.
Ko da na koma asubitin tashin hankali na tarar domin Ya Aminu ya dawo ya tadda Surutun da Mimi take yi tamkar me motsuwar kwakwalwa take sambatu tare da fad'in sunan Amjadu , fad'uwa yayi a gurin hankalinsa a tashe, yana dafe k'irjinsa haki! Yake sosai, likitoci suka shigo dakin suka dinga fada sosai suka yi kora waje, nan suka dauki Aminu da bai San a wace duniyar yake ba, cikin tashin hankali suka yi wani daki dashi ganin yanda yake jawo numfahi da kyar oxygen suka sanya masa.
Mimi jikin ya kara rike wa likitan ta kamar ya mammari su Umma haka yake ji ya dinga fada sosai da sosai itama Oxygen din aka sanya mata Dr din yana addu'ar Allah yasa kar jinin ya dawo mutukar jinin ya dawo da zubah to babu shakka sakamakon su ya nuna masa cewar zuciyarta zata iya daina aiki.
*11/November/2019*
[11/12, 11:13 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA*
*49*
Hankalin Umma ya kai k'oluluwar tashi inda ta dinga wata irin zufa!! Gabanta yana wata irin fad'uwa su biyu kawai iyayen su suka Haifa ita da k'anwar ta, Aisha maihaifyar Mimi kenan tabbas idan ta rasa Mimi bata da wani Abu da ya dangaci k'anwar ta, Mimi take kallo a matsayin Aisha k'anwar ta, Aminu danta ne dole zata iya sarrafa shi ya hak'ura da Mimi a bata zabin ranta, ko da kuwa Shi Aminu zai rasa tasa rayuwar wannan hukuncin ta yanke, ba tare da bata lokaci ba ta sanya aunt Hauwa ta kira mata Kawu a waya yace gasu nan zuwa asibitin.
Sunzo sun tadda badakalar da take faruwa Umma tace Ita ta Riga ta gama yanke hukunci Aminu ya janye auran sa a kan Mimi dole a aura mata Wanda take so.
Kawu Yunusa yace." Muma maganar da take tafe damu kenan domin Asma'u taje har gida ta Sanar mana saboda haka tunda taga zata iya shikkenan dama kuma shi yaron Neman auran mutum biyu yazo ita da Mimi saboda haka kan Aminu baza mu bari a rusa wannan auran ba domin mu abun alfarin mu ne, hada jini da Amjadu saboda haka zamu tattashi Aminu."
Wannan shawarar ita ce matsaya Babansu Munnu na tsaye bai ce komai ba sai da suka gama magana yace."Idan babu damuwa Aminu yazo ga Munnubiya na bashi sai a d'aura auran rana daya.
Kawu Idiris yace." Mungode da wannan karamci zamu jira ya dawo hayyacinsa muji ta bakinsa.
4:35 Aminu ya farka masha Allah nuffashin sa ya dawo dai-dai budar bakinsa "Ina Mimi take kar kice min ta mutu Innalillahi wa'ina ilahi raji'un."
Ya fada yana yunk'urin tashi zaune
Dr Yayi saurin mai dashi ya kwantar yana rarrashin sa fafur Aminu yak'i zama dole sai an kaishi gurin Mimi, Dr da kansa ya Dora shi keke saboda jikinsa babu k'wari kai tsaye dakin da Mimi take ya nufa da shi.
Mimi na kwance sambal hancin ta sakale da oxygen idanunta a rufe Aminu ya tsura mata ido zuciyarsa nayi masa zafi wai yanzu shi Mimi take gudu tafi son bare dashi, hak'ika Allah ya jarrabe shi da kaunar ta tun tana 'yar jaririyar ta, Ashe zan Ga wannan ranar ta bakin ciki, wasu zafafan hawaye ya share cikin zuciyar sa yace ."Ya zama Dole in hak'ura dake Mimi domin ko ns aure ki zuciyar ki na can gurin wani bazan samu kulawar da nake so ba."
Wasa-wasa har k'arfe goma na dare Mimi bata farfado ba, likita ya duba ta sosai ya tabbatar tana Raye kawai tayi dogon suma ne, nan ya rarrashin Aminu da ya