Showing 39001 words to 42000 words out of 92177 words

Chapter 14 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

tare da fad'in "Idan ban da ka tsaurara bunkice a kan al'amarin da sai dai muyi ta tafiya a haka domun idanun mu sun rufe akan al'amarin ta inda muka mance da wannan alak'ar saboda haka yanzu zab'i na gare ka, Kaine zaka zab'awa kan ka matar aure cikin su biyun."

Ranshi babu dad'i yace." Matar aure tuntuni na zab'e ta Kawu Asma'u ita na zab'a Insha Allahu ina fatan ta zama Uwar 'yayana." Kamar yanda Kawu yayi tsammanin haka daga gareshi hakane ya tabbata hamdala yayi a fili yace." Insha Allahu baza kayi nadamar auran d'iyar mu ba Allah ya sanya alkairi.." Ameen suma ameen Yanzu dole kaje ka Sanar da Umma halin da ake ciki na janye auran Mimi tunda bai hallasta ba." Kawu yace." Yanzu kuwa zan bar kasuwa inje in Sanar da ita, kuma maganar d'aurin aure tanan jibi insha Allahu." Sallama suka yi da juna, Amjad ya kashe wayar zuciyar sa na sak'a masa abubuwa da dama jikinshi na bashi kamar akwai wani Gagarimin al'amari da zai faru nan gaba.


Kai tsaye gidan Granny ya wuce domin ko ya koma gida yanzu yasan mutane baza su bar shi ya huta ba, to zancan kenan itama Granny fad'a tayi ta yi tana fadin dama Ashe basu da Asali yaran haka kawai zai jawo wa kansa zuvewar mutum ci to itama ba ta yadda da wannan auran ba, yana kwance cikin kujera yana jinta bai ce mata komai ba, duk abun duniya ya dame shi, daga zarar ya tuni Asma'u sai yaji faduwar gaba, abunda bai ta faruwa dashi ba.


******
*Innalilhi wa inna ilahi raji'un* shine abunda Umma take nanatawa lokacin da ta gama sauraron maganar da Kawu Yunusa yake tafe da ita, tashin hankalin ta sai ya ninka na da tana fargar bar Mimi taji wannan mummunan labari tsakanin ta da Amjadu babu aure tunda dai ya zab'i Asma'u a cikin su, ga jikinta ya rikice tun d'azu take kuka an kasa shawo kanta. Cikin yanayin damuwa da tashin hankali Tace." Kawu wannan k'addara Allah ya ije mana ita naso yaron nan ya zab'i Mimi domin ceto ranta, rai shine abun dubawa Mimi marainiya ce kuma tana dauke da ciwo mai mutukar hadari kuma kaga ta dalilin sa ta Sam......... Bata k'arasa ba Kawu Yunusa yayo kanta da bala'i yace." Baki Isa ba Mariya wallahi tallahi baki Isa ba!!! Arziki yana neman mu kina korarsa awwo!! Bakin ciki kike mana? Ko kuma bakin halin ki zaki nuna mana wanda kika saba, 'yarinya dai 'yarmu ce muna da ikon mu aura mata duk Wanda muke so ke!! Baki Isa ki hana mu ba 'yar bakin ciki kawai." Tsakanin Kawu da Umma dama ba a shiri tun Asali, basa jituwa a cewar sa itace take zuga Babanmu lokacin in ya dauki albashi baya taimaka wa mahaifiyar su lokacin tana Raye.Umma ta fusata! Ranta ya b'aci sosai wato har Yunusa yana da bakin magana akan 'yayan ta, mutanan da suka wofin tar da ita bayan mutuwar mijinta suka watsar da zuri'ar shi, wahalar duniya babu wacce bata sha ba, akan 'yayan ta, sai yanzu da suka ga sun zama mutane shine zasu yi wata magana har da gadara cewar 'yayan su saboda kwadayin abun duniya to har indai itace ta haifi Asma'u zata nuna masa iko a kanta. Ranta a mutukar bace tace." Yunusa ni kake d'agawa murya har kana kokarin kai min duka akan 'yaya na, Yanzu kai kana da bakin magana akan Asma'u wacce baka San cin ta ba baka San shan ta ba, sutturarta karatun ta duk baka San wannan ba, sai yanzu daka ga ta zama mutum sannan zaka yi wata magana akanta."? Ta k'arashe maganar cike da mamaki, Kawu Yunusa ya mike tsaye a fusace! Yana a matsayin wan mijinta take kiran sunan sa kai tsaye, ransa ya b'aci sosai yace." An fad'a miki nace na fad'a miki magana Mariya kiyi abunda zakiyi dama ai baki da kunya nasan halin ki d'an uwana yayi hakuri zama dake, kina maganar suttura da sauran su, ki fad'i kud'in wahalar da kikayi sai a biya ki, wacce bata gaji arziki ba, mu bama haihuwar 'yayan banza d'an uwana ya iya haihuwa koma komai abunki sai anyi wannan auran."!!!



Umma ta fashe da kuka Wanda yasa na futo wuf!! Daga cikin dakinmu Allah yasa na samu Mimi tayi bacci duk irin tujarar da Kawu yake wa Umma a kunne na kuma duk naji zancen da suke yi, rai na a b'ace na futo INA kallon Kawu dake tsaye kan Umma yana ta surfa mata masifa! "Ita yarinyar da kike so ya aura yace. Ba yaso saboda rashin galihu ya fi son 'yar Asali me cikkakiyar nasaba, bayan wannan kuma sun sha nono d'aya babu yadda za'ayi ya aure su duk su biyun, in banda kidahumanci irin naki Mariya 'yar ki zata auri mai kudi Wanda duniya ta San dashi ke kanki kin bar kangin talauci ki nuna ba kya so Allah yayi wadaran ki Mariya."! Ya k'arashe maganar sa a harzuke.



Kuka na fashe dashi jin irin cin mutumcin da Kawu yake wa Umma tana kuka ko tausayin ta baya ji, idanuna sun rufe ta inda nake ganin girman shi ya zube a gurina, tunda nasan da me yake wannan tashin hankali, duk dan kudi da soye-soyen rayuwa yau da talaka ne Amjad Kawu bazai tako cikin gidan mun ba ko dan kar ace yayi kayan daki, amma yanzu dubi yadda yake tada hak'arkari da jijiyar wuya.



Ina kuka nace." Kawu wannan ba dai-dai bane kar ka manta da cewar har gidan ka naje munyi magana dakai cewar mutukar Amjadu bai auri Mimi ba nima bazan aure shi, to yanzu duk naji abunda kuke magana akai ni da Mimi mun sha nono d'aya, Amjadu ya zab'e ni a matsayin matar auran sa ya bar Mimi, Kawu kayi hakuri da hukuncin da na yankewa rayuwa ta, idan shine ya aiko ka ka koma ka fada masa cewa ni Asma'u d'iyar Sulaimanu mai madara, bazan aure shi ba, idan son gaskiya yake min ya karb'i Mimi 'yar uwata a matsayin matarsa ta sinna domin mu ceto rayuwar ta, daga halaka."
[11/14, 6:35 PM] .: Cikin tashin hankali da damuwa Kawu yake kallon Asma'u, yace." Asma'u kina da hankali kuwa kike fad'ar wannan maganar cewar ke baza ki aure shi ba kin barwa wata."! Gyada kaina nayi rai na a dagule nace"K'warai kuwa Kawu na rantse bazan aure shi ba, sai da ya hak'ura tunda babu halin ya hada mu mu biyu idan kuma da gaske kaunata yake tsakani da Allah to sai yazo yayi abunda nace." Kawu yace." Baki Isa ba wato Bakin Ku d'aya da Uwar ki ko."? Da sauri! Nace"Ko daya Kawu wannan ra'ayi na ne, kuma don Allah ina Neman alfarmar ka daina zagin Umma haka, kayi hakuri kar kace nayi maka rashin kunya, a matsayin ka na babba bai dace ba da abunda ka keyi ka daina don Allah."


Kawu yayi mamakin abunda yarinyar tace wato suna so suyi musu bakin ciki suga samu suga rashi,babun bad'ulahu kenan abunda bazai yiwu ba wallahi ko gawar Asma'u ce sai an kaita Gidan Amjadu sai dai idan shine yace ya fasa auran.


A fusace ! Yace." Duk wani iya shege da zakuyi ke da uwarki a tafin hannuna kuke, kuma ku rubuta Ku aje, jibi I war haka kin zama matar Amjadu kin zama Mallakin sa, in dai nine wakilin ki." Ya futa a fusace. !!



Umma naje na rungume da kyau! Ina kuka ina share mata hawaye nace"Umma ki kwantar da hankalin ki duk yanda kike so haka za'ayi ki zab'a min miji Wanda kike so Amjadu na bar wa Mimi ."


Umma tace." Asma'u kina jin abunda Kawun Ku yake fada ko akan ki kina jin irin cin mutumcin da yake min ko.? Nace" Umma duk naji kiyi hakuri ki kyalesu dama ba yau suka saba miki cin mutum ci. Ni nasan yanda zanyi insha Allahu Mimi bata da miji sai Amjadu ki kwantar da hankalin ki."

Hannun d'iyar tata ta rike tare da fad'in"Ubangiji Allah yayi miki albarka Asma'u Yanda kike min biyyaya Allah ya baki 'yaya masu biyayya kema, yanda kike ceci rai ubangiji Allah yasa Annabi ya cece ki kema." Wasu zafafan hawaye na hau sharewa lokaci guda tausayin kaina ya kama ni, wani irin hali na shiga a lokacin ta inda naji gwara min mutuwa da rayuwa Allah-Allah nake naga Mimi a gidan Amjadu ko ma samu hankalin mu ya kwanta, Alluma ajirin fi musibati wa aklifni kairan minha itace addu'ar Dana ke ta maimatawa a zuciyata tare da Innalillahi wa inna ilahi raji'un, lokaci guda naji zuciyata tayi sanyi na kalli Umma tare da fadin"Don Allah Umma kar a kara tayar da maganar nan domin I Dan Mimi taji to wani tashin hankalin ne, Umma kija kunnen Ya Aminu a kan hakan." Umma tace"Nima abun ya soma damuna Asma'u Insha Allah zan ja kunnen sa, ke dai Allah yayi miki albarka insha Allahu yanda kika sanya ni farin ciki kema 'yayan ki zasu sanya ki."




Bacci ne ya soma fizgar sa kad'an-kad'an yaji ringing din wayar sa, cikin kunnen sa, dalili airpic din dake manne a kunnen sa, a hankali ya dauki wayar dake saman k'irjinsa yana dubawa. Mik'ewa yayi da sauri ganin numbar da ta kirashi.



Ba tare da ya cire airpix din ba ya latsa wayar tare da fadin"Salamu alaikum." Murya Asma'u yaji sama-sama ta amsa da wa'alaikasalm. " gabansa ya fad'i sosai lumshe idonsa yayi hade da cije leb'anshi fargabar abunda zaiji daga bakin ta yake."



Kai tsaye yaji tace"Barka da yamma." A hankali yace." Barka ya kike Husnah."!!
"Lafiya.'! Tafad'a babu wani sassauci ta cigaba da cewa " Yanzu Kawu Yunusa ya bar gidanmu bayan ya Sanar damu sak'on ka."

"Owk" shine abunda Yace yaja bakinsa yayi shiru yana sauraran ta. Ta cigaba da cewa" Allah ya kadddara ni ba matar ka bace, ina yi maka fatan alkairi idan son da kake min na gaskiya ne, to a madadina da aka zab'a akan Mimi ni na hak'ura ka mai da maganar auranmu kan 'yar Uwata domin ceto rayuwar ta.".



Wani irin gumi ne yake tsayaya daga jikinsa bakinsa yayi wani irin daci ya soma Jin zazzab'i na shigar shi, jin abunda take cewa, amma da yake NAMIJIN duniya ne, muryarsa a tsaye yace." Meye hujjar ki ta fad'ar haka, shin nine bakya so ko kuma akwai wata manufa taki."? Cike da dakiyar zuciya tace." Eh duk biyun ne bawai bana sonka ba ne, Mimi tafi ni sonka bayan haka kuma kayi mata alk'awarin aure ka yaudare ta da kalaman ka hade da zakin bakin ka, kayi kwance kwance ka lasa mata Zuma a baki daga baya kuma kace ka fasa auran ta, shin baka tunanin halin da zata shifa ko kuma kana so mu rasa ta, son da Mimi take maka zai iya kashe ta."!



Wani irin yammm!! Yake ji a jikinsa tsigar jikinsa tana Mik'ewa jin abunda yarinyar take fada, a kausashe yace." Shine Hujjar ki."! ?
"Eh shine Hujja ta." Ta fada babu wasa a cikin maganar ta."

Ajiyar zuciya ya sauke minti uku tsakani yace."Shikkenan tunda haka kika Zab'a mana ni dake muyi rayuwa na karb'i Mimi a matsayin mata kamar yanda kika bukata, Allah ya sa haka shi yafi alkairi.".
Da sauri nace"Ameen auran Mimi alkairi ne a gare ka insha Allahu." Kashe wayarsa yayi ba tare da yace min komai ba.



Lokacin naji damuwar da ke cikin raina ta ragu burina kawai inga Mimi gidan Amjadu mu huta da wannan masifar, duk abunda ya faru tsakanina dashi na Sanar da Umma ita ma taji dadin yanda ya amunce lokaci guda.




Hannusa ya sanya ya dafe kansa dashi lokaci guda kansa ya shiga Sara masa wani irin bakin ciki da damuwa sun taro sun tsaya masa a mak'ogwaro da kyar yake had'iyar yau!! Sosai yake jin bakin ciki da takaicin zafafen maganganun da yarinyar ta watsa masa lallai inda ranka kasha kallo wai shine yau 'ya mace take furta cewa bata son sa baki da baki yarinyar ma k'arama irin Asma'u.







*14/November/2019*
[11/15, 10:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*52*




Yana zaune a gurin hannunsa saman goshin sa granny da Iyami me aikinta suka shigo parlor Iyami ta nufi daining tana gyara gurin, ita kuma Granny ta k'araso kusa dashi da sauri ganin yanda yake cije bakinsa yasa ta dafa kafadar sa, tare da fadin"Kar ka sake ka sanya damuwa cikin zuciyar ka har ta haifar maka da wani ciwon ni dai a ra'ayi na nafi so ka auri 'yar bak'ar yarinyar a cikin su biyun naga kamar tana da kunya da hankali." Ta k'arashe maganar ta a tausashe.


Da kyar ya iya bude bakinsa yace." Tace bata sona Granny. " Zama tayi kusa dashi cike da mamaki tace" Amma Wannan anyi 'yar banza ta samu namiji me zafi da kwarjini kamar tace bata so, in banda ma Matsalar ka nasan ko mata dozin aka aje maka zaka iya dasu, amma wannan yarinyar ta bani haushi wallahi. " Kwanciya ya gyara hade da lumshe idonsa shi kadai yasan abunda yake damun zuciyar sa. Granny kuwa mita take tayi tace"Tun farko sai da nace maka kaje ka nemi auran Hafsatu ka kiji kaga ni ai abunda nake guje maka."

A hankali yace." Granny magana ta wuce a halin yanzu insha Allah jibi za'a d'aura min aure da Ma ko wacece na yadda haka Allah ya shirya min." Tace"Tunda dai kayi niyyar auran mata biyu mai zai hana ka hada da Hafsatu nasan in kayi magana baza su ki ba."


Jajayen idonsa ya bude ya sauke su a kanta, fuskar shi a murtuke yace." Ki k'yaleni da wani zance Inji da guda d'ayan ma ni da ba cikkakiyar Lafiya ba."

Hararasa tayi tace"Au! Ashe munafurci ne yasa kace zaka hada mata biyu hummm! Kai dai ka sani ma kanka."


Shiru yayi cikin zuciyar sa Yace ." Granny in batayi wasa ba zai sauke fushinsa akan ta yanzu juya mata baya yayi ta gaji da mitar ta tashi daga gurin.
Wayoyinsa duk kashe su Yayi domin baya bukatar damu a halin da yake ciki ji yake zuciyarsa tana iya bugawa ta tarwatse.

Sai daf da magari ba ya tashi daga kwanciyar da Yayi kai tsaye masjid ya nufa yayi sallolinshi tare da addu'ar Neman zabin Allah ya futo daga massalaci Jama'a na ta mik'o masa gaisuwa Amjadu bashi da wulakanci sosai ya tsaya ya gaisa da mutane, cikin ikon Allah yana shiga gidan yaji zuciyar sa tayi masa sanyi, sakamakon karatun alk'uranin dake tashi a parlor Granny ta kamo tashar Saudiya tv Jama'a na ta kewaye dakin Allah *(Ka'aba)* zama yayi kusa da ita da carbi a hannunta sai da ta kammala tukkuna ta kalleshi cike da kulawa tace." Iyami ta girki dafaduka shinkafa da daddawa nasan kana son shi, tayi amfani da bussasan kifi yayi dad'i sosai. " Murmushi yayi yace."naji dad'i kuwa domin rabo na da cin abunci me nauyi har na manta. Granny ta mike hade da aje carbin NATA a kan kujera tace." Naga alama kazo kaci ka koshi naga alamun yunwa a tare da kai."
Mik'ewa yayi yabi bayan ta, yana 'yar Dariya domin ya kwantar mata da hankali shi kam a irin halin da yake ciki yanzu kome za'a bashi bazai faran ta masa ba Idan ba Asma'u aka bashi ba."


*****
Shirye shiryen aure ya kammala duk wani Abu da ake bukata akwai shi a aje idan da kud'in ka ka wuce Matsalar komai, Tun safe su Kawu Yunusa suka yo gayya 'yaya da jikoki suka zo suka kare mana zagi ni da Umma munji bakin ciki da ciwo Abunda suka zo suka yi mana a unguwa amma daga k'arshe muka hak'ura muka cigaba da sabgar mu. Duk Abunda. Amarya take yi nida aunt Hauwa mun sanya Mimi tayi domin me lallai har gida tazo tayi mata ja da baki, aunt ce ta sanya mata man shamfo a kanta, ta had'a kayan gyaran jiki na sanya Mimi a gaba na dinga mulka mata a jiki ina gogewa yinin ranar abunda muka yini kenan, lokaci guda Mimi tayi Wani uban kyau jikinta sai shek'i yake,murmushi kawai take yi ga lallan ta ya futo radau abunka da farar fata.

Bayan mun idar da sallahr La'asar ne, muka tafi can yakasai gurin dinki kayamu kala uku duk iri daya dinki iri daya komai iri daya muka karbo a dai-dai muka shiga muka dawo gida sai murna nake Mimi ta saki ranta, Muna Isa gida muka tadda Munnu tazo dakinmu muka shige muka cigaba da tsara yadda zamu gudanar da walima domin lokaci yazo a kurace gobe daurin aure jibi kuma walima kuma a ranar za'a kai Mimi.

*****

K'arfe biyar da kwata na ranar alahamis yana zaune a harabar gidan shi jikinsa sanye da kayan motsa jiki Rambo ya shigo cikin gida a mota ya gyara parking ya futo hannunsa rike da ledoji manya manya masu dauke da tambari na sunan company nin sa, karasowa yayi kusa da shi tare da fadin"Sir barka da yamma." Dago kanshi yayi yana kallonsa kana ya amsa, Rambo yace." Komai ya kammala kamar yanda ka Umarta naje har gidansu na kai kayan. " Fuskarsa babu wasa yace." Alhmdullahi ina bunkice da na sanya kayi min." Rbow yace." Mahaifin yarinyar dai kamar yanda aka fad'a talaka ne sosai Dan duk 'yan uwansa sun fi shi rufin asiri yana aikine karkashin company madara ta cowbell bayan rasuwar sa, haka naji daga bakin abokan sana'ar shi ya rasu sanadiyar hatsari a titin sharada mota ta take shi."

A hankali yace." Wane company yake wa aiki a lokacin."? Rambo yace." Cowbell ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login