Showing 81001 words to 84000 words out of 92177 words

Chapter 28 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

gaskiya naji haushin wannan Abu." Mu dai hakuri muke bata, sannan muka gaisa da Iyami dake kallon tana dariyar durmarmu d Granny tace"Iyami Kawu musu abunci." Duk da ina jin yunwa sai da nace "Granny a koshe muke Wallahi." Hararata tayi tace"Wato kinanan da halin ki na cutar kai ko? Dubi bakin Ku a bushe kice min a koshe kuke ai nasan daga makaranta kuka dawo." Shiru nayi kawai domin nasan dukanin abunda zan fada Granny ba yarda zata yi ba. Munnu tace"Ina baby Aysha ne? Domin munzo aba mu aronta." Granny tace"Yanzu kuwa tayi bacci wallahi ai kun fi k'arfin abaku Aron ta idan ma kyauta kuka je a baku za'a baku ita kyauta." Munnu tace"Granny da gaske nake wallahi zamuje da ita ta kwana biyu sai mu dawo da ita." Granny tace "Nima ai da gaske nake." Iyami ce ta shigo da k'aton tire cike da nau'ikan abunci da abunsha ta aje kan dogun tebur din da yake gabanmu. Granny tace "Iyami maza hada kayan baby Iyayenta zasu je da ita su ta kwana biyu." Iyami tace"To Hajiya amma fa zamu sha kewa da yawa." Granny tace"Zamu huta da rigima dai kinga zamuyi bacci harda munshari musamman ke." Dariya muka yi harda Iyami ta nufi wani daki da sauri tana fad'in "Baby Aysha rigima kenan. Sosai muka saki jiki muka ci muka koshi mana hira da granny Cikin barkwanci ni kam Allah-Allah nake a fito da baby Aysha na ganta. Aikuwa sai ga Iyami ta fito da ita a kafadar ta daya hannun NATA kuma k'aramin akwatu ne. Ni da Munnu rige-rige karb'ar ta mukayi Allah ya bani sa'a ina karb'ar ta na manna mata kiss a kumatu ina dariya ganin yanda take motsa bakinta tana tsotsar hannunta, da alama yunwa take ji. Granny tace" oh! Oh oh!! Wai meye amfanin abunda kuke yi ne, kuyi ta tsotsar kumatun yarinya shima haka wancan sakaran yake yi, mata har bakinta tsotsa yake." Ni da Munnu muka dariya nace"Ni kam sumbatar kumatun ta kawai nayi granny gaskiya Iyami ta iya raino naji dadin ganin baby Aysha haa duna granny kamar ba bakwai ni ba."

Tana dariya tace"Yanzu zata nuna muka halin nata na k'uya Iyami kadai ta sani saboda ita take bata abunci ni kaina wani lokacin sai taga dama take yarda dani." Aikuwa sai ta fara tab'e baki tana so tasa kuka, rungume ta nayi ina rarrashin ta, granny kuwa sai dariya take mana, Iyami ta shigo da fidar ta da sauri ta sanya mata a baki ta kama tana tsotsa sosai, Dan kanta ta cire bakinta sannan ta fara daga hannu wai zataje gurin Iyami aikuwa Munnu tace"Baki isa ba kuwa kin bar hannunta da sauri ta karb'a ta a hannuna ta dauki towel dinta ta goya ta a bayan ta, mik'ewa nayi da sauri Iyami ta mik'o min duk abunda zamu bukata nata, nace "Granny zamu tafi gida." Tace"To Ku gaida min Ummanku da kyau kuce ta kyauta." Nace insha Allah kuwa. "Har waje Iyami ta rako mu tana d'agawa baby hannu ita kuwa sai dariya take bangala mata tana daga bayan Munnu." Ganin rana ta kwalle nace dama zanga su Rambo da sun kaimu gida. Wata zuciyar tace min lallai Asma'u kina da samun shiga. Ni kaina dariya nayiwa kaina. A dai-dai sahu muka shiga nace"Munnu muje gida yau Umma taga baby inyaso sai ki tafi da ita ko."? Munnu tace "Shikkenan muje.""' Wasa nake ma baby daga bayan Munnu ita kuma sai bangale min baki take, nace"Laa Munnu kinga har ta soma hakori wallahi. " Munnu tace"Da gaske ne." Nace sakkota ki gani.' Aikuwa ta fara kokarin saukota tana dubawa, Kuka ta fara yi da alama tafi son goyon nace"Munnu mai da ita bayan baki ji yanda nake jin zafin Ku kanta Cikin raina ba." Kokarin mai da ita take, naji kira ya shigo waya ta, hankalina na can gurin rarrashinta ban duba waye me kiran ba na d'aga wayar hade da sallama.
Kukan Sweet heart dinshi ne yayi masa sallama, ranshi ya kara b'aci a fusace! Yace." Wai ke wace irin mayya ce ne? Meye alak'ar ki da baby da zakiji har gida ki dauke ta, OK naji kamar alamu kuna cikin abun hawa ne ana min gwajab-gwajab da yarinya tana kuka na rashin sabo. Maza ki mai da ita inda kika daukota tun wuri."! Hannuna ne yake rawa bakina na motsi na rasa abunda zan ce masa, Munnu dake kusa dani duk taji abunda yake cewa, hannu ta mik'a min wai in bata wayar , domin in fidda kaina a gurin shi nayi saurin bata wayar ta karb'a a nutse tace"Yallab'ai barka da rana." Jin muryar da bata Asma'u ba ya amsa da " Barka dai wacece ke."? Munnu ta tsorata jin muryar sa a kausashe!! Tace." Munnubiya ce, dama umm! Dama.... Babanmu ne yace muzo humm nazo in d'aukar masa baby Aysha yana so ya ganta.......... Sam bai gane Abunda take nufi domin shi har ga Allah ya mance da Kawun Mimi wato babban su Munnu, yace." Ke! Bana son shashanci dallah!Ku mai da min da yarinya wato wayar ta baki domin Ku shirya karya ni sa'anku ne."!? Cikin tsawa ya fad'i maganar! Nan Munnu ta kara daburcewa tace"Da gaske ne kayi hakuri Wallahi an turo ni daga gidan profesor Muktar Gyaranya ne ni 'yar shi CE" sai da ta fadin sunan Profesor Muktar sannan ya tuna da Mutumin , kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba .Munnu ta kalleni tana dafe k'irji tace"Bala'i wannan guy anyi masifafe irin sune suke rigima da matayen su akan 'yaya gaskiya yana do son "yaya tab!!!!!!!

Girgiza kaina nayi ina tunanin abunda zanyi na huce takaicin abunda guy nan yake min aka 'yar Mimi wai ni yake kira da mayya lallai duniya. Ji nayi wasu hawaye na kokarin zubo min. Cikin zuciya ta nace zaka cigaba da kirana da wannan sunan indai akan baby ne. Nafi maye ma maita!
Umma taji dadin ganin baby sosai ta karbe ta ta rungume ta sosai a jikinta tana kallon Munnu tace"Ki bar min ita ta kwana a gurina gobe sai ki zo ki dauke ta ki kaita can gidan NAKU." Munnu tace"To Shikkenan, haka tayi mana sallama cike da jin kunyar Umma.

****
Amjad Kuwa bayan futar Su Asma'u ne ya kira wayar granny domin ya ji gwalatun babyn shi dama baya minti ashirin bai kira waya ba, kawai granny tace masa wai su Asma'u sun zu sun tafi da ita, a lokacin ji yayi kamar ya bar Abunda yake yi ya dira najeria ya yaga yarinyar saboda rashin zuciyarta har granny ma sai da ta fuskanci b'acin ransa dama ta saba indai akan baby ne rufe ido yake yayi kamar bai San mutum ba shiyasa Iyami take takatsatsan dashi, kashe wayarta tayi ta k'yale shi shine fa ya kira Asma'u a waya ya sauke mata rashin mutumci, ya Riga ya saba da baby kullum kafin yayi bacci sai sunyi hira Sam bai ji dadin wannan Abu ba, Dan dai kawai yana ganin mutumcin Mutumin ne.

****
Kwata kwata na mance da rashin mutumcin da guy yayi min, hidimar baby kawai nake yi yini Abu daya. Don har gidan aunt Hauwa mukaje da ita wai lallai sai na bar mata ita naje bazan iya ba. Ko sallama banyi mata ba na futo daga gidan.


Misalin goma na dare na gama lallab'ata tayi bacci na bude data muna hira da Mujahid, kira ya shigo wayata, ina dubawa naga numbar k'asar waje ne sai nayi mamakin waye zai kirani da wannan numbar ne. Cikin sanyin murya nayi sallama, nashi b'angaran yaji wani irin fad'uwar gaba jin muryar ta da alamun bacci ta kashe masa jiki, gyaran murya yayi yana kokarin dai-dai ta nutsuwar shi, yace." Ki duba na miki magana ta whstsap ki bani amsa yanzu."! D'iff! Ya kashe wayar mik'ewa zaune nayi da sauri ina kara duba numbar, tabbas shine domin numbar irin ta d'azu ce da ya kira lokacin muna a dai-dai sahu. Messages na fara dubawa Aikuwa na ga nashi can k'asa, ni ban ma San sanda ya shigo ba, girgiza kaina nayi kawai na bude ina dubawa.

_Ki turo min numbar wannan k'awar taki ina so muyi hira da Sweetheart_

Abunda ya rubuta kenan. Na karanta ya Kai sau goma da gayya na kashe data ta ganin yana online nasan ni yake jira. Cikin rashin sa'a kuma Jahid ya kirani a waya ganin na rufe data yace." Ko bace zakiyi ne naga kin rufe data gashi ni kuma ban gaji Da jin muryar ki ba." Nace"Nima haka my Jahid muyi hira mai dad'i aikuwa muka dinga hiraramu ta soyayya

Amjad nashi b'angaran yana sauraron yaga ta turo masa da numbar Munnu kawai sai yaga ta rufe data kuma gashi ta ga sakon bashi,ranshi a b'ace " ya fara kiran wayar ta a karo na biyu . wayar taki tafiya sai ace masa busy ya kira ya kai sau goma busy jifar da wayar yayi kan bed din da yake kwance yana Jan wani mutsiyacin tsaki tare da mamaki dawa take yin waya tsawon wannan lokacin..........................







*28/11/2019*
[11/29, 9:22 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*67*






Mun fi rabin awa muna hira da Jahid a waya sannan yayi min sallama tare da fad'in"My Wife insha Allah, kiyi bacci mai dad'i kuma kiyi mafarkin kina gidana da yardar Allah." Cike da kulawa nace"Insha Allah Jahid zan kwana mana addu'a ni da kai." Sosai yaji dadin kalamai na cike da farin ciki ya kashe wayar......Mik'ewa nayi nima na futa domin wani irin futsari ne ya kulle min Mara, tsakar gidan shuru Umma ta juma da yin bacci, ina dawo wa na tadda baby ta farka tana cilla k'afafu daukar ta nayi da sauri don kar tayi min kuka, ruwa na fara bata sha ina kokarin bata madarar ta naga ta zura k'aramin ya tsanta a baki tana tsotsa bacci ya dauke ta, ajiyar zuciya na sauke na gyara mata kwanciya na kwanta kusa da ita, bacci ya soma fizgata naji shigowar kira waya ta na manta ban kashe ba, idona a lumshe na dauki wayar ina dubawa tsaki naja kamar in kashe wayar sai kuma wata zuciyar tace dauki kiji me zai miki." "Hello." Abunda na fada kenan kamar me ciwon baki,, sama-sama naji shi yana fadin"Ke ni kika rainawa hankali na miki magana kin share ni, kuma na kira wayar ki kina waya Lokaci mai tsayi! Nace "Ki turo min numbar Munnubiya ko." Kamar wani Ubana haka yake min magana da masifa! Cikin sigar kuntatawa nace"Ni fa duk ka dame da wani surutun ka, bani da numbar Munnu ko ina da ita ma bazan bayar ba, ba dai a kan 'yar kake min wannan hayaniyar ba Tom sha kurumin ka baby Aysha na gurina yanzu ma ta farka daga bacci na bata ruwa tasha, ka cigaba da kirana mayya a kanta wallahi dad'i nake ji, maganar da wa nake waya bai dame ka ba, mutum na son yayi bacci an dame shi."!! Kashe wayar nayi gaba ki d'ayan ta, wani irin sanyi naji cikin zuciyata na mayar masa da Martani Nasan yau da kyar in zai iya bacci.

Aikuwa sakato yayi da waya a hannu yana kallon abun kamar almara baby Aysha na hannun Asma'u wato duk kauce kaucen sa yarinyar nan sai da taje ta dauko mata sweetheart, yasan halin Asma'u farin sani bata munafurci yasan da gaske take, shifa yanzu babu wacce yake jin haushi sai granny domin yana ganin itace ta bada fuskar a dauko masa 'yar sa, da kyar bacci ya dauke shi yana tunanin maganganun da Asma'u ta dankara masa. Abunda yafi tsaya masa a ransa shine tunanin da wa take waya, yasan dai idan da 'yar uwarta mace take waya baza su kai kusan a wa guda ba, wata zuciyar tace masa ko Mujahid ne? Take ya yardar wa zuciyar sa shi din ne....... Cike da tunani. Ta da mafarkin sweetheart d'insa yayi bacci. Ko da safe ma da ya tashi babu kuzari a jikinsa har abokansa suka gane, nan yace musu baya jin dad'i ne kawai, yini yayi a kwance yana kewar gwalantun baby kuma yayi alk'awarin bazai k'ara kiranta a waya ba balle ta kara fada masa magana shifa Yanzu neman hanyar da zai yi nesa da ita yake saboda alak'arsu da Mujahid.

Da safe da kyar baby Aysha ta yarda da Umma lokacin da zan tafi skull ma sai Goya ta Umma tayi ta shige da ita daki don kar taga futata ko gilmawa ta ta gani zata fara zillo idan kuwa ban dauketa ba sai ta sanya kuka.

Koda muka had'u da Munnu a skull cewa tayi wai kunyar Umma take ji baza ta iya zuwa ta dauki baby ba, sai nace ta bari zan kawo ta insha Allahu. Bayan sallahr la'asar na fito tsaf dani baby na bayan Umma a goye ta sauko ta, ina kokarin sab'ata a kafad'a Umma tace"Ki Goya ta akwai sanyi- sanyi hadarin nan ya zama sanyi, towel din na karba na Goya ta sosai na saki hijab kana nayi wa Umma sallama, gidan su Munnu na nufa kai tsaye.

*****
Ummansu Munnu tayi farin ciki sosai ta karb'i baby ta goya ta tam a bayan ta har sai da tayi bacci ta tashi sannan ta sakko da ita, tace " Ya kamata a gwada bata abunci fa." Dariya nayi nace"Ta isa cin abunci yanzu."? Tace"Bari ki gani." Wake ta Mirza ta sanya mata a baki Aikuwa baby ta lamushe ni da Munnu muka dinga dariya, Ummansu Munnu tace"Yaran yanzu da wayon su ake haifar su, gashi dai daga laluba mata wake ta lamushe, haka Ummansu Munnu tayi mata kusan sau biyar sannan ta k'yaleta ta bata ruwa, kuma Allah ya taimaka bata yi kuka ba, sai bayan magariba Babansu Munnu ya dawo gida, ya dauki baby Aysha yayi mata addu'a hade da sanya mata albarka yayi mata addu'a sosai da sosai kana ya sanya k'aramin yaron shi yaje kanti yayi mata siyayya sosai kalolin biscuits iri-iri Ummansu Munnu tayi ta dariya tana fad'in "Irin wannan siyayar akai wa kishiyata alhalin gani a zaune ba'a min ba, dadin abun dai cin abunci ma ni na koya mata." Baban su Munnu yace." Da kin sani Baki koya mata ba ai." Mudai dariya kurrum muke musu, hira muke da Munnu sosai wacce ta dauke min hankalina sai da Ummansu Munnu ta leko dakin tana fad'in "Asma'u ko anan zaki kwana ne ga hadari nan yana had'owa." Agogo na kallah da sauri naga tara shaura da sauri na mike INA fad'in "A'a wallahi Yanzu zan tafi." Baby na dauke wacce ta Dade da yin bacci na Goya ta da sauri na zura hijab na fito wani bakin hadari na gani a gabas Nace"Munnu Allah ya kiyaye ni da dukan ruwa." Tace "ameen dai amma ni shawara ta ki bari sai gobe kawai kya tafi." Ko kallonta banyi ba nayi hanyar futa ina sallama da Ummansu dake Uwar daki.
Ina futowa titi aka fara wata irin iska mai k'arfi abubuwan hawa sai gudu suke akan titi duk yawanci motocin gida ne da kyar na samu a d'an sahu Wanda ya rage mutum d'aya a ciki na shiga aikuwa kamar almara ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,ni da nake gefe ruwa ya fara duka na, kafin kice me na jike jagab, ta karewa nayi ina tsoran kar ruwa ya taba baby sai ta fara motsi tana k'ananun kuka, gaba na ya fad'i jijjigata nake yi INA so tayi shiru yarinya kamar wacce ake zugawa ga feshin ruwa sai dukan fuskata yake, kamar zanyi kuka nace "Don Allah kayi sauri babyna na Kuka."! Mai dai-dai ta yace." Hajiya ai ina ganin parking ma zanyi saboda ban San iya inda ruwan zai tsaya ba, domin karfinsa yayi yawa sai ya tsagaita sai mu tafi." Kafin ince komai ya tsayar da 'Dan sahunsa, nace"Na shiga uku ni Asma'u nayi da na sani tawowa da na hak'ura na zauna na kwana gidansu Munnu zai fi min, tausayin baby nake ji jin yadda take sakin ajiyar zuciya tana baya sai kyarmar sanyi jikinta yake yi, ni da ita duk mun jike matan dake a dai dai ta na kalla naga sai hirarasu suke yi babu abunda ya dame su, su kadai ne single babu wacce take da yaro Karami balle tayi fargaba. Sai da aka dauki 30minutes ana ruwa mai k'arfi sannan ya tsagaita sai wata irin iskar sanyi ta soma kadawa, a lokacin naji Baby ya fara atishawa sakkota nayi ina duba jikinta, naga jagab duk da dabarun da nayi mata sai da ta Nike hatta da gashin kanta, kuka take so tayi ta kasa sai sakin atishawa take, hawaye na fara sharewa kana na rungume ta tsam! A jikina Ina fadin"Duk nice na jawo miki babyna."!

Jagab! Muka shiga gida muna d'igar ruwa Umma na gani cikin ruwa ta dinga min fada "Shin baza ki bari gobe idan Allah ya kaimu kya dawo ba, ko kuwa gidan su Munnu din bak'on ki ne.? Ko tausayin k'aramar yarinya bakya ji sai kinje kin kwaso mata mura da da tari ko." Fada sosai Umma take min, ni kam hankalina na gurin baby wacce take ta motsi majina har ta fara zurara a hancin ta, kayan jikinta na cire mata da sauri na sanya mata Pampers na sanya mata kayan sanyi masu kauri kudindine ta nayi. Umma tace"Bani itanan mu gani." Mik'a mata ita nayi, ina tsaye da jikakkun kaya ban damu da In cire su ba, duk da nima hakan take kamar baby kwata kwata bana son dukan ruwan sama Shikkenan zazzab'i da mura zai kama ni. Robb Umma ta dinga Mirza mata k'irjinta da bayan kunnen ta, da tafin kafarta sannan ta Goya ta.
Futa nayi jikina duk babu kwari, har yanzu da ragowar ruwa kadan kadan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login