Showing 6001 words to 9000 words out of 92177 words
Chapter 3 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
yari da sark'a na sannan na kalli mudubi, ni kaina nasan nayi kyau sosai, Munnu da Mimi suka saki baki suna kallona, nace" Meye wai!? Munnu tace." Anya baza ki cire kayan kuwa ba kinga yanda suka matse ki, ke gaki tubar kallah." Nace" lallai Munnu wallahi ko Umma yau baza ta hanani futa da kayan nan ba.Mimi tace" sai ki sanya hijabi idan muka je can ka cire,amma dai kin San gurin ya hada samari da 'yan mata duk budurwar da take da saurayi zata gayyace shi yazo gurin." Nace" Mimi ina ruwana wai don Allah Ku k'yaleni mana." Ganin raina ya b'aci ya sa suka k'yale ni. Umma na zaune s rumfa tana kule-kulen ta muka futo takalemu a tsanake tace "kunyi kyau tamkar wasu amare,amma ke Asma'u meye kika sanya hijabi."?
Nace" Umma dinkin ne ya matsani shine nace"idan na shiga cikin 'yan uwana mata sai in cire." Tace" haka yayi to Ku kula don Allah Ku tsare mutumcin Ku ana gama taro ku dawo gida kar Ku tsaya kad'e-kad'e da raye-raye." Muka ce insha Allahu."
Muna shirin futa daga gidan wayar Munnu tayi k'ara ts dauka a nutse tare da kashe muryar ta, kasa kunne nayi cike da mamaki jin tana ambatar sunan Shamsu. Ni da Mimi muka kalli juna. Ji mu kayi tana fadin"Eh ka shigo da motar yanzu zamu futo." Sukayi sallama, dukaninmu muka kalleta cike da mamaki nace"Munnu yaushe Shamsu ya dawo kuka kuma jone wa." Murmushi tayi tace" shekaran jiya ya dawo da k'arfin sa, Wallahi aurena zai yi domin aranar da ya dawo ma Baban shi yazo gurin Babanmu baku ga kayan da ya kawo mun ba, wannan hayaniyar da muke ciki ce ta hana ni fada muku."
Ni da Mimi muka Ce"Toum Allah ya sanya alkairi lallai alk'awarin Allah ya cika. " dariya Munnu tayi cike da farin ciki muka futa daga gidan. Samari na bakin titi suka bimu da kallo kamar wasu mayu.
Wata had'adadiyar mota na hango a fake gefan titi Shamsu na zaune a mazaunin dravar tare da wani Wanda ban gano fuskar shi na, suna sanye da wata masifaffaiyar shadda wagambari hade da hula damanga sunyi kyau har sun gaji. Ganin zuwan mu gurin yasa Shamsu futowa da sauri ya bude wa tauratowar shi motar yana fadin" Girman kujerar ki ne." Hararasa nayi tare da tab'e bakina nace"Haji Shamsu Ashe zaka dawo ai na dauka muma yaudarar tazo kanmu." Dariya yayi yace." Inaaa!! Baby Asma, Ai Munnubiya ta daban ce cikin mata, tab'e bakina nayi nace"Allah yasa da gaske kake."
Tunda na fara magana abokin Shamsu yake kallona ina kallonsa ta wutsiyar ido tsaki naja a fili na tsani kallo wallahi.
Munnu ta shiga ta zauna Mimi ta zauna nima nashiga sannan Shamsu ya koma gurin zaman shi hade da kunna motar muka tafi.
Shamsu sai janmu da hira yake yana fad'in"Ai duk naji labari lokacin da na tafi har daku ake cewa dama yaudarar Munnu nake yi humm yanzu Asma baby kina ganin zan aikata haka kuwa."
Nace"sosai ma kuwa Shamsu namiji ne fa kai hunm halin Ku sai Ku."Abokinshi ya juyo yana kallona tare da sakin murmushi yace." Baby Asma wasu mazan ne suka bata wasu amma abokina da gaske yake." Tab'e bakina nayi nace" muna da labarin fa duk 'yan Matan da ya yaudara sun kai goma. " Shamsu ya rike baki yana dariya tare da fadin" duk sharri ne wallahi, karya suke min." Mimi tace"Babu sharri nan gaskiya ce mu dai don Allah kar ka kara guduwa domin wancan karon sai da mukayi jiyyar ta" suka kwashe da dariya shi da abokinsa.
Munnu sai mintsina take wai in daina surutan da nake yi ina jinta na kiyin shiru.
****
Lokacin da muka Isa guri ya soma cika sosai aka kawata gurin gurin malamai daban da iyayen yara wajan dalibai daban, muma wajan mu daban wajan manyan baki daban .. Masu hotona da vedio baza su kirgu ba, saboda ko wacce da nata,muma mun dauki namu can muka tadda shi, MA kad'a sun fi su biyar suna gefe suna jiyar taro ya watse a fara shagali. Ko wane class da gruop d'insu da kuma irin kalar ankon su, ko wacce tana wace wannan.
Mai girma principal ya bude taro da addu'a tare da yi mana nasiha sannan yayi wa 'yan matan da aka kusa bikinsu a cikinmu addu'ar zaman lafiya Wanda basu da mazaje Allah ya kawo musu, hakanan Wanda suke shirin cigaba da karatu Allah ya bada sa'a.
Haka Malamai suka dinga mik'ewa suna jawabi tare da addu'a, taro ya tashi guri ya hautsine kowa da ta wagar mutanan shi, da kawayen shi sai d'aukar hoto ake hade da vidio,
Ina gefe tare da jama'a ta domin wasu ma ranar na fara ganinsu duk ya wancin su maza ne, tuni na cire hijabina ina yawo yanda na gadama 'yan ajimu sai jana suke dole sai munyi hoto duk inda na sanya kafa abokin Shamsu nan yake sauke tasa ya zame min jele, haka na dinga shiga cikin abokan da samarin 'yan ajinmu muna hoto wasu nayi da waya wasu nayi da Camera man. Abun mamaki ni kadai jama'a suke ja lallai sai sunyi hoto dani, haka Alina ma duk gabar da muke da ita sai da tazo ta jani cikin a bokanta maza da mata mukayi hoto wasu daga cikinsu na fiddo wayoyinsa nayi min.
Mimi ce tazo ta jawo ni da k'arfi tana fadin" meye haka kike yi don Allah ki daina ratsa maza kina shiga tsakiyar su baki San suba
Fuzge hannu nayi INA fadin "Kinga Mimi yau rana daya ce daga ita babu wata ki k'yaleni." Mimi ya rabu dani ta koma gurin Munnu da sauraynta
Duk ankon da mukayi sai da muka sanya su Shadda ce karshen sawa. Waiiiii!!! Fitina! Lokacin Dana futo cikin shadar idanun jama'a kamar ya cinye ni, ni kaina sai bayan na futo a haka Nazo ina da na sani dinkin fitat ne iya cibiya Sam rigar bata da hannu gashi ta matse ni, siket din yayi d'an, kwankwaso na kamar zasu yi magana da kyar nake cire k'afa ta saboda yanda ya matse ni.
Tuni suka yo kaina suna ihu!!! Wani Dj ya saki wak'arnan ta *Hamusu brekar wato shimfidar fuska* Filin na nufa sauran k'awayenmu suka rufa min baya, rawa sosai na dinga *wakokin gwanja kamar ni na rera su* mussaman wak'ar shi ta *d'akin bak'uwa dudu bak'ar ashana* ai ina bala'in son wak'ar nan na zage ina rawa tare da sauran 'yan ajinmu Mimi ma da Munnu sun shigo filin ana yi da su.
Alina ce tazo ta ja hannuna wai inzo muyi sallama da abokanta, muka nufi bakin get, kamar walkiya naga gilmawar motar guy nan ta futa daga gurin. Abunda yasa na gane sunan shi dake bayan motar kuma na shiga cikin kusan sau biyu. Mamaki ne ya kama ni, mutumin da baya gari me ya kawo shi gurin nan.
Sama-sama mukayi sallama dasu na koma ciki ina tab'e bakina.
******
System d'in shi a kan cin yar shi yana dubawa Anthony na gefan shi yana waya cikin yaran na chana.
Sak'o ne ya shigo yana dubawa yaga rambow ne, pictures ya fara gani kusan guda Dari suna shigowa, da sauri ya bude yana dubawa, ji yayi zaman gurin ya gagare shi a sabili da abunda ya gani cikin loptop din shi, babu shiri ya mik'e da sauri ya shige wani had'addan bedroom hade da sanyawa kofar key ya zauna gefen bed hannu na rawa yake duba hotonan wani irin gum! Yana tsatstsafo masa a saman goshi
*3/NOVEMBER/2019*
[11/4, 11:56 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*
*39*
Yarinyar yake gani cikin maza ko ta ina, ga sassan jikinta a bud'e ko duk motsin da zata yi kana ganin saman breast dinta ga sunan a waje hankalinsa bai k'ara Tashi ba sai inda yaga ta shiga filin rawa tana juyi ana mata watsin kudi, wani uban ihu!! Ya kurma hade da jefar da loptop din ta fad'i kasa ta gangara can bakin kofa, mike wa yayi a zafafe! Ya kai wa bango duka da hannunshi!! "Ni wannan yarinyar zata tozar ta. ? Da k'arfi ya fad'i maganar, kaiwa yake yana kawo wa a dakin, a fusace! Yaje ya dauki wayar sa, yana lalubar Mimi, bugun duniya yayi tak'i shiga, jefar da wayar yayi ta fad'i kasa, dafe kansa yayi dake mugun sara masa, fuskar guy nan kawai yake hangowa Wanda yake nanikar yarinyar duk inda ta sanya gaba shine ya fi kowa zak'ewa, shifa idan ba idonshi ne yayi mishi gizo ba sai yace kamar yaga ya rungume ta, wani irin ihu ya kurma!!! Hade da sanya hannunsa biyun yana dukan katifar dake kam bed din sai kace wani mahaukaci, da sauri Anthony ya shigo domin yaji ihu!! Cin karo yayi da lopot bakin kofa a kife, cike da mamaki ya sunkuya ya dauko ta yana gyarawa, k'araso wa nan ma yaga wayar sa a jefe.. Ajiye loptp din yayi kusa dashi ya dauki wayar yana dubawa dake mai hade da batir ce kunna wayar yayi ta kama abunka da abu matsada nan take ta kama.
Zama yayi kusa dashi cikin harshen turanci yake tambayar sa." Dago kamshi Yayi yana kallonsa da idanunsa Wanda suka kad'a sukayi mugun ja!! Hannu ya mik'a masa alamun ya bashi wayar, da sauri Anthony ya mik'a masa wayar, Numbar Mimi ya kara kira is switch up, cikin sauri ya nemo numbar Rambo, bugun farko ya dauka, bai saurari maganar da yake masa ba, yace." A ina guy nan yake? I wiil kill you!!!." Rambo ya tsorata jin muryar Oban gidan shi, na wani irin rawa!! Yace. " Sir ban gan..........kafin ya karasa maganar ya katse shi cikin wata irin razananniyar tsawa yace." Rambo!! Ni kake fad'awa baka gane ba, Dan ubanka me ka turo min Yanzu."!!! Rambo yace." Sorry sir Wallahi ban San dai a ina yake ba, a tare dai suka zo gurin cikin mota.... Yace." Kafin safiya ka bunkito min a wani guri ya ke shi Dan gidan uban waye, sai na kashe shi."!!!!! Rambo yace." An gama sir insha Allah... Katse wayar yayi yana wani irin haki!
Shiko Anthony ya dauka irin mutanan sa Wanda suka sanyo shi a gaba wato abokan a dawar sa, sai ya dafa kafad'ar sa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Gyad'a kansa kurrum yake yana tunanin irin hukuncin da zai dauka kan yarinyar da shi kanshi guy...wani irin rad'ad'i da zugi zuciyarsa take masa in da yake jin kamar ya Dora hannu aka yayi ta kurma ihu ko ya samu sassauci,, cikin maza don rashin nutsuwa ko wane namiji yazo ya jata kamar tinkiya ta bishi tana murguda masa mazaunai hade da gantsaro masa nonuwa duk Rabin nonuwan ta a waje da ta d'aga hannu hammata a waje
*Ya ilahi!!* abunda ya fada kenan da mugun k'arfi, Anthony ya mike da sauri gami da bude kofar dakin ya futa.
Minti biyu ya dawo hannusa rike da wata bak'alar kwalba wani Abu mai kyali a saman ta, bude wa yayi da sauri ya mik'a masa, cikin harshen turanci yake fadin "karb'i ka sha wannan zaka ji sassauci a zuciyar ka." Giya ce Anthony yake mik'a masa a zuciyarsa yace." Asma'u bata Isa ta sashi ya fara shan giyaba ko da zuciyarsa zata yi bundiga sai da ya mutu da bakin cikin ta. Kauda kansa yayi yak'i karb'a, Anthony ya aje kwalbar giyar da sauri ya Ciro kwalin sigari hade da leghtar ya kunna guda ya mik'a masa, aikuwa da sauri ya karb'a ya fara bata huta, duk guda zuk'a biyu yake mata ya shanye, tas!! Ya shanye kwali guda Anthony ya mike da sauri ya futa domin dauka masa wata, shi zufa kawai yake lokaci guda yaji wani irin sanyi-sanyi a jikinshi alamun zazzab'i ya kama shi. Kwanciya yayi rigingine kan bed din yana sak'e-sak'e cikin zuciyarsa
*********
Kwata-kwataKwata-kwata ma ni mantawa nayi da naga Rambo cikin jama'a na koma muka cigaba da sabgar mu, har lokacin da taro ya watse.
Ana kiran sallahr Magariba muka shiga gida, nida Mimi Yaya Aminu da Umma na tsaye da alama magana suke, kafin in an kara naji duka ko ta ina!! Ihu! Na kurma ina fadin "Yaya Aminu me nayi maka kake dukana." Fad'i yake "Asma'u gwara in kashe kan inga abun kunyar da kike k'okarin jawo mana banje gurin party Ku ba, amma ina da labarin dukanin abunda ya faru so kike ki futa zakka a jikinmu Asma'u Ashe 'yar iska ce ke ban sani ba,."!!! Ya k'arashe maganar cikin tsananin b'acin rai!
Umma naga tayi shigewar ta daki ranta a bace babu abunda tace kan irin dukan da yake min, kuka na fashe dashi INA fadin" wallahi Allah ba zai barka ba sai ya saka mi... Wani irin mari ya galla min tare da fadin" a gidan uwarki sai ya hau dukana da kafafunsa ina karewa tare da fashe wa da kuka.
Mimi na tsaye tana kallonmu daman abunda take guda kenan shiyasa tun farko ta hanani, ganin yanda yaya Aminu yake dukana ne yasa Mimi shahada taje ta rungume ni sosai itama tana kuka tana tayani bashi hakuri, amma saboda rashin imani na Aminu ko kallonmu baiyi ba ya dinga duka yana fadin "Ai dama bakinku daya, wato ke mai tausayi ko? Asma'u zata Kai ki ta baro.!!! Sai da yayi mana lilis sannan ya kyalemu.
Da Jan jiki muka shiga dakinmu ko wacce tana shararar hawaye Mimi tace" Tun farko abunda na hango kenan, amma da yake kedin me taurin kan tsiyace kika ji, kika dinga shiga cikin maza saboda rashin kamun kai, wallahi Kiyi wa kanki fad.... Katse ta nayi a fusace.! Nace"Mimi kiyi min shiru ki k'yaleni inji da guda d'aya mana.""" Itama a fusace! Tace"bazan k'yale ki ba Wallahi ai dama gaskiya ce bakya so sai kije kiyi tayi." Mik'ewa tayi ranta a bace ta fara cire kayan jikinta.
Ni ko zama nayi ina duba jikina inda Ya Aminu ya FASA min wani gurin ma har fatar ta kwailaye gefan bakina ya fashe hannu na NASA na shafo jinin , a fili nace " Allah ya Isa Wallahi bazan tab'a YAFE wa, duk abunda nayi ai ba akaina farau ba, ballanta na ma banyi komai ba tunda dai ba kamani a kayi gidan karuwai ba ina zina ko ina cacah,tsabar mugunta da rashin tsoron Allah yayi mutum yawo aikin banza da wofi"!! Da k'arfi na karasa maganar domin ya Aminu yaji na dauka yana gidan, Umma ce ta d'aga labulen dakin tace" Yayi miki kyau! Asma'u wuyan ki ya Isa yanka kiyi ba dai-dai ba kice baza'ayi miki fada ba, lallai kin cika, kuma kin kai munzali Yanzu kin kara tabbatar min da cewar aure kike so bari gobe tayi da kaina zai wanke kafafuna naje gidan Kawun Ku Yunusa muyi magana gwara in aurar dake tun kafin ki jawo min abun kunya."
Da sauri na mike na Isa gurin hade da rike mata kakafu ina kuka tare da bata hakuri ina fadin"Umma wai me akace muku nayi a gurun party nan ne, Umma ki lura dani wallahi bazan tab'a zubar da mutumci na ba da kima ta ta 'ya mace, Umma ki yafe min kina kallon yanda Ya Aminu yake duka na kamar zai kashe ni." Umma ta fuzge k'afafunta ta futa daga dakin ba tare da tace komai ba
Bakin kofar na zauna ina kuka Mimi tazo ta tsaya a kaina tare da fadin "Bani waya ta,aikin kawai kin karar min da chaji a banza da hotunan ki, kin San ba wuta ake kawo wa ba"Wani irin kallo nayi mata ina gyad'a kai cike da takaici nace" Ki duba wayar ki cikin jakata gata can a tsakar gida. " tsallake ni tayi ta futa, daga dakin.
Chaji taje ta kai domin bai zama lallai su kawo mana wuta ba,
Ranar ko abuncin dare hanci ba, haka na kwana da cikina tsabar bakin ciki ya hanani bacci sai juyi nake.
*****
Kamar yanda ta kwana tana juyi to shima haka ya kwana yana murk'ususu zuciyarsa Sam! Babu dad'i ga uban zazzab'i da ya kwana dashi, ko da asubah ma a daddafe yayi sallah Yana jira gari ya waye musu a can , time din ko wace k'asa daban yake
K'arfe Biyar na asubah mun tashi Ya Aminu ne ya tsaya a kanmu har sai da yaga ko wacce ta mike tsaye sannan ya nufi massalaci, motsin Umma Naji a tsakar gida tana alwala da sauri na koma na zauna, domin bana son na futa mu had'u. Mimi ta futa ta barni,, ko minti biyu ba ayi ba kira ya shigo wayar Mimi, daga inda nake in hangowa *Heart beat* sunan da nagi kenan, cikin zafin zuciya na dauki wayar na kashe! A fili nace"Aikin banza da wofi asubar fari za'a damu mutane. " wani kiran ne ya kara shigowa na kashe da sauri,, A'a wani kiran ya kara shigowa na kashe, sai da ya kira sau bakwai ina kashewa, yana kiran na takwas din ne kawai na kashe wayar gaba d'aya.
Nashi b'angaran sakato yayi da wayar a hannu lokacin da ya kira suka fad'a masa cewar an kashe wayar ma gaba d'aya, tunani ya shiga yi anya Mimi zata kashe masa waya kuwa? Why!!! Me yake faruwa ne.? Jefar da wayar yayi kan bed ya yunk'ura ya tashi zaune kwalin sigari ya dauko ya bata wuta ya fara fesawa cikinsa hayak'i da sanyi safiyar na, da sauri kuma ya dauko wayar tare da nemo numbar rambow bugu guda tayi ya dauka baki na rawa yace."good morning sir." Bai amsa ba yace." Meye labari ina fatan ka yi aikin da na sanya ka."? Rambow yace." Yes sir Ashe ma ba d'an gari bane yazo bak'unta ne dan barno ne wato mai duguri." Da babbar murya yace."kaje Sanar dashi cewar inji ya bar garin nan kafin in k'araso idan ba haka ba sai da uwarsa ta haifi wani Wallahi. "!!!! Rambo ya tsorata jin furucin oban gidan nasa, ta yaya zai