Showing 18001 words to 21000 words out of 92177 words
Chapter 7 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
Cikin zuciyata nace"Dana dauko shi sai in jire rigar jikina nasan dole Aminu sai yayi magana
Ina k'araso wa ya bini da kallo
Simi simi Nazo na wuce cikin gidan ya biyo ni a baya yana zabga tsaki
Sakata ya zura sannan ya shiga
Umma na tsaye tsakar gida na shigo kallona tayi tace"Sai yanzu ya tafi. "?
Gyada kaina nayi jikina tabi da kallo cike da mamaki.
Da sauri nace" Wannan masiffafn karan ne ya hanani shigowa layin nan, shine ya bani babbar rigar shi na sanya.
Ya Aminu yace." Dole yayi miki haushi dama an hana ki sanya bakin hijabi kink'iji sai kinje wata rana ya cije ki.
Girgiza kai Umma tayi ta shige daki.
Nima dakin mu na wuce jiki babu k'wari
Mimi sarkin bacci har tayi bacci
Rigar na cire na zaune gefan gado ina sauke ajiyar zuciya
Tunanin rashin mutumcin da guy nan yayi min nake, hanyar da zanbi in rama nake nema
Wani shashe na zuciyata yake fada min kull kika ce zaki rama domin duk WANNAN abunda kuke dashi baki tab'a samun galaba a kansa ba,
Duk abunda yayi ado ne a garunshi ke Kuma zubewa mutumci ki rabu dashi kurrum
Rigar shi na dauka ina shashanawa lumshe idona nayi hade da kwanciya rigingine tsigar jikina ta fara mik'ewa abunda na Dade ban ji shi ba yau shi naji, muguwar sha'awar sa kawai nake, nipple d'ina suka fara k'aik'ayi kasa na ta soma motsi, rike rigar nayi da k'arfi ina cije bakina, matse jikina nake sosai tare da rungume rigar shi ji nake kamar shi na rungume a jikina. Karar waya naji Mimi na can tana bacci da sauri ns dauki wayar saboda lokacin ji nayi ina son in kara jin muryarsa ko zan samu sassauci
Kasa&kasa nayi sallama,
Bashi b'angaran ya fahimci muryat ta ce, Kai tsaye yace." Ina Momyna bata wayar zamuyi hira. " muryata a shake nace"Tayi bacci."
"Ok ke me ya hana ki yin baccin."? Ya fada Kai tsaye... Nace" Ban sani ba nima.
Sai da na fad'i haka kuma na fara Dana sani.
Shiru yayi na minti biyu yace." Ko dai Jarabar ki ce ra hanaki bacci don na lura da halin da kike ciki d'azu.Shiru nayi idanuna a lumshe, shine yake abun shi don ba jinsa nake sosai ba, ina can duniyar shauki jin muryarsa ji nake kamar yana kusa dani ga k'amshin sa a jikina motsi kawai nake ina lumshe idona wayar ma saura kad'an ta fad'i, yace." Ko bakya ji ne."? S hankali nace "Uhmum."!! Nashi bangar yaji tsigar jikinsa ta tashi yanayin yanda tayi maganar ya tada masa da sha'awa, lumshe idonsa yayi hade da gyara kwanciyar sa, yace." Shikkenan tunda kina so nayi hira dake, yanzu ki fada min wane shawara kika yanke a kan auranmu ki zab'i guda ni ko Saurayin ki."
Shiru nayi ban ce komai ba
A hankali naji ya ambaci Sunana *Asma'u* wani iri naji a jikina ya iya fad'ar sunana.
"Uhum."!! Abunda nace kenan.
Yace" Malama ki bude baki kiyi min magana ko in kashe wayata meye wani Uhumm.!? Nace "Me kace to? Nifa ban ji abunda kace ba."
Tsaki yaja yace." Baza ki ji ba dama fitinanniya kawai."
Kitt!! Ya kashe wayarsa
A hankali na aje wayar ina tab'e bakina ko banza na samu sassaucin abunda nake ji.
Mimi sahorama tana can tana bacci ko motsi ta kasa yi
Amjadu yana sane ya kashe wayar shima saboda yanda ya fara jin Jikinsa ya sauya joystick dinshi ta mike sosai wata irin sha'awa ta bujoro masa, yasan haka zai kwana cikin mawuyacin hali.
Haka suka kwana suna juye-juye sai dab da asubah bacci ya dauke su, cike da mafarkin jununsu.
********
Umma da Wuri ta futa Unguwa don abun kari ma mu muka Dora ni da Mimi
Kowa sabgar gabansa yake yanzu dukanmu mun rage sakewa da jununmu.
Tare muka karya da muna hira sama-sama Mimi ta kalli gurin kwanciyata taga rigar Amjadu.
Tace"Asma'u waccan kamar.... Kafin ta karasa nace"Eh rigarsa ce ya bani na kare jikina da ita jiya dare yayi kafin in shigo gida ga shegen karanan yayi ta yi mun haushi. "
Fuskarta ta sauya tare da dauke kanta tace"Har nayi bacci ina sauraron shigowar ki."
Ina sane nace "E Wallahi unguwa na raka shi.
Kallonta tayi fuskarta a hade ta tab'e bakinta.. Nace." Jiya kina bacci ya kira wayar ki."
"Meya sa baki tashe ni ba."?
Nace" Shine yace"A k'yale ki ki huta, shine mukayi hira sai kusan k'arfe daya na dare na kwanta.
Wani irin kishi ya bujoro wa Mimi mik'ewa tayi taje ta kwanta kan katifar ta
Kallon ta nayi cike da Mamaki nace"Mimi kishi kike dani ko."?Cikin wayancewa tace"Wane irin kishi zanyi dake Asma'u. "?
Nace" Gashinan daga magana kin je kin kwanta ko abincin ma kin kasa ci."
Murmushi tayi tace"Ji nayi bakina babu dad'i tunda naji kin ambaci Amjad gabana yake fad'uwa.wani irin nauyi k'irjina yake min."
Nace."Mimi ya zama Dole fa ki ragewa kanki damuwa soyayyar da kike nunawa. Mutumin nan fa akwai matsala domin zata ita kai ki ta baro kuma duk sanda ya fahimci son da kike masa wulakanta ki zai yi, Sam! Ba'ayi wa Namiji haka."
Lumshe ido tayi tace"Asma'u wani irin nauyi nake ji cikin zuciyata da ina iya hak'ura da guy nan da na hak'ura na bar miki shi Wallahi saboda na fahimci kamar yafi sonki dani."
Nace"Ki barmin shi ko in bar miki shi, Amjadu Mijin ki ne ki kwantar da hankalin ki." Shuru tayi ba ta sake cewa komai ba.
Minti goma tsakani wayarta tayi kara dauka tayi tana lumshe ido na na tabbatar da cewar shine ya kira ta, mik'ewa nayi na fuce daga dakin domin bana son inji hirar da zasuyi ballantana i n shiga damuwa.
Sai bayan Sallah la'asar Umma ta dawo gidan, jikinta duk babu k'wari tace" Asmau Zuba min ruwa inyi Alwala a hanya la'asar tayi min."
Da sauri na zuba mata na mik'a mata ina nazarin ta, har ta shige band'aki
Dakinmu na shiga jikina a sanyaye a zuciyata nace Akwai matsala gaskiya tunda naga Umma ta shigo gidan nan jikinta babu k'wari.
Kusan Rabin awa da shigowar ta ta kwala mana kira. Ni da Mimi muka amsa a nutse muka Isa Rumfar, tana zaune da carbi a hannunta tace"Duk Ku zauna muyi magana."
Zama mukayi ko wacce da Abunda take saka wa.
Carbin ta aje ta kallemu tare da fadin "Babban al'amari ne yake tunkaro mu dani da Ku, ina so kuyi min adalci kuyiwa kanku a adalci bana son zumuncin Ku ya lalace saboda duk inda akace kishi to sai anyi shi ko ciki daya kuka futo
Yanzu daga gidan Yunusa nake Wannan yaron da yake Neman Ku da aure tun safe ya turo magabatan sa, da kud'in aure harda sadaki yace." Nan da wata guda yake so, ayi komai a gama. Kawu Yunusa ya amsa musu hade da karb'ar dukiyar auran, kafin in futo daga gidan Aminu yaje da maganar shi ta cewar yana son auran ki." Tafad'a tana nuna Mimi da hannu, a cewar sa tun kina yarinya yake sonki ya ki fada ne kawai saboda yana ganin baza ki fi k'arfin sa ba, sai Kuma gashi lokaci guda wanki hula na Neman ya kaishi dare.
Kawu Yunusa yace magana ta wuce tunda har ya bari aka karb'i kud'in auran ki. Sai dai yayi hakuri kawai. Yanzu halin da ake ciki yana babban asibiti na Malam Aminu domin fad'uwa yayi a gurin har na tawo bai dawo dai-dai ba."
Umma ta k'arashe maganar ta zuciyar ta babu dad'i.
Nace"Umma me yasa Ya Aminu bai yi magana da wuri ba har sai da ya bari aka karb'i kud'in auran ta, to ai itama Mimin. Zata shiga wani hali
Kuma jiya mun gama magana da Amjadu cewar ya janye aurena saboda rashin dacewar haka, Mimi zai aura kuma daga baya azo ana kace nace."
Umma tayi shiru fuskarta cike da alhini.
A hankali Mimi tace." Umma ki kwantar da hankalin ki, Indai akan sona Yaya Aminu ya suma har ta kaishi ga kwanciya a asibiti insha Allahu ni zan share miki hawaye
Dama nike son Amjadu bashi ba Asma'u yake so tuntuni zuciyata takasa yardar min da haka, Umma zan auri Ya Aminu ki kwantar da hankalin ki."
Umma ta share hawayen ta, tace"A'a Mimi bazan miki dole ba bayan an kawo kud'in auran ki saboda son kaina ince ban yarda ba ga Wanda nake so ki aura duniya sai ta zage ni mutanan gari su dinga fadin"Don bani na haife ki ba shiyasa nake miki bakin cikin shiga cikin daula bayan haka kuma zuciyar ki tana son Amjadu idan nayi haka ban miki adalci ba, dole Aminu shine zai janye kudurinsa."
Kuka Mimi ta sanya hade da rungume Umma tana fadin "Wallahi Umma da gaske nake babu abunda zaki nema a duniyar nan ban yi miki ba, mutukar ina dashi, Na hak'ura da Amjadu zan auri Ya Aminu."
Cikin kuka ta k'arashe maganar.
Rungume ta Umma tayi tana kuka, nima naji k'walla ta cika min ido nace"Umma yaushe zamu je asubitin ."? Je ki d'aura abunci da sauri ana idar da sallahr magariba sai muje."
Mik'ewa nayi na nufi kicin.
*7/November/2019*
[11/8, 11:36 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
Mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
44
A gurguje na kammala dafa abunci shinkafa da faduka nayi wacce taji allayyahu da albasa, Bayan mun idar da sallahr magariba ne muna shirye-shiryen tafiya sai muka ji sallama Umma ta futo da sauri Yaya Aminu ne da Musa da Kawu Yunusa suka shigo, Umma tace"Kaddai an sallame shi."
Kawu Musa yace." Gashinan kina gani dama nace Zai farfad'o Suma yayi."
Ya Aminu ya zauna kan tabarma hade da dafe kansa.
Nida Mimi muka futo muka tsaitsaya
Dariya nake wa Ya Aminu ganin yadda ya fyad'e lokaci guda.
Sallama Kawu Yunusa yayi suka tafi ni da Musa kuwa babu Wanda ya kula kowa.
Umma tace"Maza je ki kawo masa abunci."
Kicin na nufa da saurina.
Mimi ta zauna gefansa tana yi masa ya jiki.
Abunci na kawo na aje gabanshi
Naje na dauko ruwa pure watar babu sanyi,yace." Kije ki siyo min me sanyi."
Umma ta mik'o min ashirin tare da fadin"Ki siyo guda hudu.
Hijab din Umma na zura na futa daga gidan da sauri
Ya Aminu bai ci abincin sosai ba ya aje cokalin ya mike ya bar gurin.
Duk muka bishi da kallo. Umma tace"Cuta ta samu manya ." murmushi nayi kawai
Mimi kuwa tashi tayi simi-simi ta shige dakinmu
Nida Umma bamuyi hirar arziki ba muka tashi
Ina shiga dakinmu na tadda Mimi ta juya baya tana Kuka harda shashsheka.
Cikin mamaki nace"Mimi kuka kike yi."?
Banza tayi min
Da sauri naje na birkitota sai naga idonta yayi mugun ja sai ajiyar zuciya take.
Zama nayi kusa da ita hade da rike hannunta nace"Mimi nasan kin amsawa Umma ne domin ki kwantar mata da hankali.
Nasan bakya son Ya Aminu Amjadu kike so Mimi me zai sa baza kiyi wa kanki gata ba zaki jefa kanki cikin mummunan hali. Kinsan bakya son Ya Aminu me yasa kika amsawa Umma."
Hannuna ta rike tamau! Naji jikinta sai karkarwa yake
Tace." Asma'u na rasa yanda zanyi da zuciyata nayi-nayi incere son Amjadu abun yaci tura ji nake kamar zan mutu Mimi zuciyata tana azabtar dani kan abunda bazan samu ba, don girman Allah ki taya ni da addu'a zuciya tabar cutar dani, soyayyar da nakewa Amjadu Allah ya cire min ta gaba daya ta koma kan Ya Aminu."
Kuka nasa saboda tausayin ta tabbas so bala'i ne hannunta NA rike dake yin wani irin karkarwa nace"Mimi zan sanya ki a adduata in sha Allahu, kinga na farko ke kika cuci kanki d'azu da Umma tayi miki maganar Aminu sai ki nuna rashin amincewar ki, tom kinga daga baya baza kije mata da wata magana ba.
Zan cigaba da taya ki addu'a Ubangiji Allah ya yaye miki ya zab'a miki mafi alkairi."
Sosai take kuka ina rarrashinta
Sai kuma naji ta fara wani irin tari!! Na mike da sauri na dauko mata ruwa
D'ago ta nayi na fara bata,
Tana shan ruwan tana tari da idonta yayi jazur
Cire ledar ruwan nayi na bugun bayan ta.
Tare da yi mata sannu.
Dana ga tarin yak'i sauk'i futa nayi da sauri na dauko gishiri a kicin na zo na Dan gwala mata a baki.
Tafi minti goma tanayi sannan ya lafa.
Sai haki! Take.
Ruwan na mike mata ta karba ta sha kadan.
Nace "ki kwanta kiyi bacci zakiji sassauci.
Kwanciya tayi tana lumshe idonta
Sai dana ga bacci ya dauke ta sannan nima na kwanta ina sak'e-sak'e Cikin zuciyata.
Bacci ya soma fuzgata naji kiran waya
*haetbeat* tsaki naja na dauki wayar na kashe gaba d'ayan ta domin shi nake mutukar jin haushi a ganina duk shine ya jawo mana wannan masifar.
Tun farko da bai nunawa Mimi yana sonta ba, ina ganin duk haka baza ta faru ba.
Da tune-tune bacci b'arawo ya kwashe ni.
******
B'angaran Amjadu kuwa, tun bayan da Wakilansa suka zo suka Sanar masa da cewar An bashi guda cikin 'yan Matan da yake so ya aura sai gaban shi ya fad'i ya tunini ko Mimi ce, shine dalilin da yasa ya tambaye su kud'in wacce a ka karb'a a cikinsu nan Kawunsa yace." *Asma'u* yaji dadin haka don haka kafin su tafi sai da yayi musu kyauta ta mussaman.
Shirye-shiryen bude company ya kammala yau saura kwana biyu gari ya dauka kafufin yad'a labarai in ka bude zancan kenan *Ranar Juma'a Biyu ga watan bakwai za'a bude shaharrarn company nan wato AmjaduAbulAbbas materials* za'ayi bononza a ranar abun dubu daya Dari biya abun dubu goma dubi biyar. Mutanan gari sun kunzige kudinsu suna jiran ranar domin su je su kwaso garab'asa.
***
Washe gari muka tashi da jiki a sanyaye Mimi ta rame lokaci guda, shi ko Ya Aminu dama tunda Kawu Yunusa ya Sanar dashi cewar an fasa karb'ar kud'in Mimi ya watsake ko da ya tashi da safe tamkar Wanda bai yi ciwo ba, yanzu Mimi CE abun tausayi so ya tasa ta a gaba.
Da kyar na rarrashe ta ta Karya kummalo
Umma ta tsaya bakin kofar mu tana fadin "Menene wai naji kuna takkadama."?
Zuciyata tace kawai ki fadawa Umma ko menene ko Allah zai sanya ta fahimta."
Kaina a kasa nace"Umma ina ganin wa....Shiru nayi na kasa magana.
Umma tace." Meye kika yi shiru."?
Bakina na rawa nace"Umma don Allah Ya Aminu ya janye kudirin sa a kan Mimi akwai cutar wa a ciki, ya kamata Mimi a bata zabin zuciyarta Ya Aminu Namiji ne shi zai iya jure komai kinga Mimi ko yarinya ce mai karanci shekaru gata kuma mace."
Shiru Umma tayi tana nazarin magana ta.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace"Kin yi gaskiya Asma'u ni ma zuciyata batayi na'am da haka ba, saboda ina gudun zagin jama'ar gari tunda duk sun San komai Da Aminu da ke da Mimi duk daya kuke a gurina babu Wanda zan ce nafi so, amma kina ji da bakin ki tace ta amunce da Aminu kuma ko jiya Kawun Ku ya maimata min maganar babu gudu babu ja da baya tunda sunyi magana da mahaifin ta a waya yace ya bashi wuka da nama, Babansu Munnu ma har dashi cikin maganar kin ga bani da ta cewa."
Nace "Umma kina da ta cewa mana don Allah ki sanya Ya Aminu ya janye magana.....kafin in karasa naji saukar Mari a kuncina Ya Aminu ne tsaye a kaina yana wani irin huci! Yace." Kina so naci ubanki Asma'u, wato kina zu ga Umma kina zuga Mimi kan su bujirewa Bukatata ko me? Ni kinsan halin da Zan shiga idan na rasa ta, ko kinsan irin son da nake mata, mutukar ina Raye a duniyar nan bani da mata sai Mimi, dake da ita kuje kuyi abunda zakuyi akin gama ya Riga ya gama."
Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace!
Umma barin gurin tayi ni da Mimi mukayi shuru muna sak'e-sak'e
A hankali naji tace"Asma'u don Allah kar ki kara wata magana kan al'amarin nan, kinji tunda dai kince zaki taya ni addu'a tom na gode miki.".
Murya na rawa take maganar
Nima naji zuciyata ta karye nace"Mimi sai dai idan gani nayi am d'aura muku aure da Aminu shine zan daina magana domin nasan ki nayi a banza ne, bakin alkami ya bushe, amma magana kan al'amarin yanzu na fara."
Shiru tayi tans kallona.
Mik'ewa nayi na futa daga dakin zuciya nayi min zafi!
*RANA BATA KARYA*
Manyan attajirai da manya manyan 'yan boko 'yan siyasa masu mak'ami daban-daban Sarkin Kano sarkin Zazzau Sarki Katsina Jama'ar gari tsakunsu da kwarkatar su, sun hallara a wannan guri.
Hayaniya ce ta tsananta tare Da jiniya wannan ya tabbatar min da cewa me girma governor ne ya iso bani kadai ba, duk wani Wanda yasan da akwai dabi tsakanin *Amjadu* da me girma *Governor* sai da yayi mamaki, tuni jama'ar gari suka fara ihu!! Suna fadin abunda ransu yake so ga me girma governor.
Ko kunya babu me girma governor ya futo daga mota tare da jamarsa ya dinga ratsa jama'a Yana daga musu hannu hade da washe musu baki wai shi lallai ga governor tsagerun matasa masu goyon bayan Amjadu suka sanya ihu!! Da dariya suna fadin abun da yayi musu kan governor din, wasu na fadin"Ba mayi!!!! Sai da 'yan sanda suka tsawa tar sannan hayaniyar ta lafafa, can gurin da aka tanadar wa manyan baki governor ya nufa, police na biye dashi a baya domin sun tsorata da irin ihun da jama'ar gari sukeyi,
Sai da suka ga ya zauna sannan suka koma gefe suka tsaya da bundigun su a hannu.
Can na hango Mai citta shida abokanan shi, sai zare ido suke.
Limamin babban massalacin jama'a na garin kano ne ya tashi ya bude taro da addu'a yayi karatun alkur'ani me girma sannan daya baya daya manya baki suka fara jawabi kowa yana yaba kwazo da jajircewa irin ta Amajdu
'Yan jarida a gurin baza su kirgu ba, domin wasu jamar gari na gida kowa na gaban TV Wanda bashi dashi kuma kunne shi mak'ale da waya ko redio yana saurara.
Lokacin da Amjadu ya futo zai yi Jawabi Ihu!! Jama'ar gari suka sanya tare da fadin"Sai kayi fari me farar aniya ka iya ka huta *AmjaduAbulAbas* muna biye da kai insha Allahu *2004* taka ce sai ka zama shugabanmu." Ihu! Kawai suke, sun hana aji bayanin da yake, da kyar jami'an tsaro suka shawo Kansu suka yi shiru.
*Amjadu* yayi jawabi me gamsarwa jawabin da ya ratsa