Showing 72001 words to 75000 words out of 92177 words

Chapter 25 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

hak'ura.

Umma da Granny ne suke jiyyar ta sai Ummansu Munnu dake zuwa kullum tana kawo musu abunci bayan an sha ruwa, duk da cewa Amjadu yana iya bakin kokari su akan su, komai sai ya sanya an kawo musu na ci da bukatar rayuwa.

Ni ma ina zuwa amma ba kullum ba, watarana idan muka taso daga makaranta ni da Munnu sai mu wuce aikuwa Mimi tayi ta murna, ranar yini muke ni da Munnu muna sanya ta motsa jikin ta, kamar yanda Jahid ya fada.

Yau sati na guda da barin asibiti Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu a asibitin kuma yau sallahr saura kwana bakwai sati daya kenan. Ranar juma'a ne na tashi da wani irin mutuwar jiki. Naji bana son zuwa skull din, cikin sauri na shirya jikina na bar gidan, kai tsaye asibitin nasarawa na nufa, duk sunyi mamakin ganina lokacin makaranta nace musu yau baza ni ba, muna tsaka da hira Mimi ta mike ta shiga toilet din dake cikin dakin. Minti biyu naji ta kwalamin kira, da sauri na bude band'akin na shiga ina fadin"Menen..... Kafin in karasa naga jini jazur nabin kasan gurin gata a tsugune ta rike kan famfo na toliet din tana cije bakinta cikin azaba ta rike Cikin nata tana ynukurin tashi tsaye amma ta kasa
[11/25, 7:38 AM] BintuUmarAbbale: Hannun ta na rike ina kokarin mikar da ita tsaye abun ya gagara, babban abunda ya bani tsoro da ita shine yanda naga jini na zuba da sauri na fita na kira Umma ta shigo taga halin da ake ciki, itama hankalin ta ya tashi tace"Maza ki karawo Jahid din zubar jini na da matsala futa nayi da sauri kafafuna na rawa, Granny tana tambaya ta menene? Ko juyowa banyi ba, Ina kokarin shiga ofis din ne shi kuma yana kokarin futowa muka buga karo dashi, dauke kaina nayi daga kanshi ina kokarin shigewa, tunda ya ganta a d'amauce ya tabbatar akwai matsala da sauri ya fada dakin da Mimi take, dama zuwan shi kenan asibiti ya tsaya ofis din Jahid domin su gaisa, yana shiga yaga granny tsaye kofar toilet tana fadin"Kama ta Ku futo a hankali, kai amma dai jinin yayi yawa likita yazo ya duba ta." Granny yake kokarin bugewa yana kutsa kai ban dakin inda Umma take kokarin mikar da Mimi ta kasa ko da d'aga k'afarta guda d'aya, da sauri ya mik'awa granny wayoyin shi ya tartare hannun rigar shi, ba tare da damuwar komai ba ya d'auki Mimi hankalin sa duk a tashe ya futo da ita jikinsa duk jini hakanan itama doguwar rigar dake jikinta sharkaf take da jini. Hannunta ta mik'a ta kamo wuyansa tana lumshe ido dishi-dishi take gani. Ya kwantar da ita da sauri ya futa daga dakin, Jahid da Asma'u ya ci karo dasu, sai yayi saurin koma wa dakin, shi kuwa Jahid ganin jikin Amjad din da jini ya tabbatar masa da akwai matsala, aikuwa suna shiga dakin suka tadda Mimi tana wani irin buge-buge kan bed din tana wani cije bakin ta ga idanunta sunyi sama sun k'afe fari tas!! Da su. Innalillahi wa'ina ilahi raji'un " Shine Abunda Jahid ya fad'a ya futa daga dakin da saurin tsiya, mu kuwa rifuwa mukayi kanta Umma addu'a kawai take tofa mata, ni kam baki na ya kulle a lokacin kallon ta nake kurrum tana buge-buge na rasa wane taimako zanyi mata, a takaice ma da naji ina Neman fad'uwa sai na zube a gurin ina fad'in "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un." Amjad hannunta yake kokarin rikewa abun ya faskara domin yau duk k'arfin sa Mimi yafi shi, kokarin fadowa take daga bed din yayi saurin tare ta ta fad'i jikin shi, har ila yau ba daina cije-cije da take ba.

Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Mimi domin ceto rayuwar ta suma sun tsorata da al'amarin kuma yayi musu bazata lallai ubangji Shahidi ne kuma shine yasan gaibu kana taka Allah na tashi, duk iya bunkicen su a kan Mimi bai nuna musu wata alamar na cewa zata yi jijjiga ba, amma dake Allah Allah ne ya saukar da hukuncin sa kan baiwar shi, a war su biyu a kanta suna kokarin shawo kan Matsalar da tsayar da jinin da yake zuba Abu ya fassakara, Wanda a wannan lokacin Mimi ta amsa kiran Ubangji dukanin su sun tsorata mutuka duk da suke likitoci suna ganin irin wannan tashin hankali amma al'amarin Mimi ya girgiza su, Dr Faruk ya lura cikin na na motsi take suka shirya yi mata CS domin a Ciro abunda yake Cikin tunda da ran shi.
Jahid daure wa yake akeyin aikin dashi, zuciyar sa nacan tunanin ya za'ayi ya Sanar da Amjadu wannan mummunan labarin. Cikin hukuncin Allah suka samu nasarar ciro baby girl 'yar wattani bakwai ba sati d'aya, yarinyar 'yar mitsitsya da ita, tana cikin koshin lafiya take suka sanya ta Cikin kwalabar su, da aka tana da domin irin su, suka kimtsa gawar Mimi , cike da alhini da tausayi suka futo
Da Amjad suka yi karo tsaye a kofar dakin dasu ke, Jahid yaji gaban shi na fad'uwa, hannunsa yaja suka shiga ofis din sa.
Amajad yace." Jikina na bani bazan ji alkairi ba daga gare ka, kawai ka fad'a min menene? Domin fuskar ka ta nuna alamun damuwa." Babu wani kwane-kwane da b'oye-b'oye domin dole ya Sanar dashi hakkin shi, yace." Allah yayi wa Mimi rasuw..... Kafin ya karasa ya d'aga masa hannu da saurin! Yace." Kar ka k'arasa min naji."!!!!!!! Jahid ya mike daga inda yake ya zauna kusa dashi da kalamai masu taushi yace." Ubangji shine ya hallice ta a sanda yaso babu tsammani kuma a karb'i abunsa a sanda yaso kar ka manta dani da kai duk zamu je inda Mimi taje komai daran dad'ewa mutuwa riga CE, aya ce ga dukanin wani musulmi Mimi tayi sha hada ta mutu ta farkin haihuwa addu'a zaka yi mata."!!
Hannun Jahid ya rike tamau! Leb'anshi na rawa haka zalika jikin shi na wani irin tsuma yace." Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!!!!!!!! Jahid ya dinga dukan kafad'un shi alamun rarrashin yana tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, d'ago idonsa yayi Wanda suka zama kamar Jan gauta bakin shi na rawa yace." Muje a shirya min gawar Momyna ayi mata suttura."!!
Jahid ya mike tare da shi suka futa kai tsaye dakin dasu ke aje gawarwaki suka nufa, tuni an daure Mimi guri guda tana kwance sambal kan wani siririn gado an lullub'e ta da wani farin zani, fuskar ta ya bude, yaga tayi kyau sai murmushi take kamar yayi mata magana ta amsa, zubewa yayi jikin gado yana sakin wani irin kuka. Tare da fad'in"Momyna Allah ya jikan ki, halin ki nagari ya biki, Momyna na hafe miki insha Allahu kece Uwar gida na a aljannar Fiddausi."!

Jahid na tsaye yana kallon shi cike da tausayi da alhini, mik'ewa yayi hade da sanya tafukan hannayen shi ya shafe fuskar shi, ya kalli Jahid din a dake yace." Muje." Jahid ya bishi a baya suka futa.
Ko da ya shigo dakin da muke bai yadda ya had'a ido da kowa ba yace." Zamu je gida yanzu Jahid ya bamu sallama."
Granny da Umma ba yara bane balle maganar sa ta shige su Granny tace"Kai k'ato bana son kumbiya-kumbiya kawai ka fad'a ma kome yi mu 'yan Adam ne zamu dauki kaddara rufewar bata da amfani, shin ya jikin Aishatu ne."? Yana kokarin futa yace." Allah ya amshi ta." Wani irin ihu! Na kurma had'e da bin bayan sa a guje, ina kokarin taddashi tafiyar mu ba d'aya bace ina kuka nake fad'in"Karya kake mugu azzalimi sai dai idan Kaine ka kashe mana ita, idan hakan ta kasance sai na dauki fansa."!!!!!!! Ko juyowa bai ba, ya shiga wani daki, kokarin binsa nake wasu nurses suka rirrike ni suna bani hakuri, wani k'arfi ne ya zo min a lokacin na fuzge daga jikin su sai kace wata mai iskokai na afka dakin a guje! Abunda na gani ya sani jin wani irin jiri tuni na fad'i a gurin ina kallonsu dishi-dishi inda suke kokarin Dora mimi kan wani gado Duk an dad'adaure mata k'afafunta da hannaye ta babu Wanda yabi ta kaina harshi kanshi Jahid din suka tura Mimi dake kwance kan Wani k'arfe suka futa.
Silalewa nayi na fad'i a gurin ba tare dana San a wace duniyar nake ciki ba.
Tuni Umma da Granny sun futa sun tsaitsaya aka futo da gawar Mimi tare da sanya ta a motar asibiti Umma sai share hawaye take yi, suka shiga, dravar yaja motar, lokacin kowa ya manta dani sai Jahid din da ya dawo ta kaina shine duk yayi min taimakon su na likitoci na dawo hayyacina kuka sosai nake yi had'e da dukan shi kamar mahaukaci nake cewa an hada baki dashi an kashe min Mimi, ganin kamar bata cikin hankalin ta ya sanya yayi mata allura take bacci me nauyi yayi gaba da ni.

Wasu nurses ya sanya suka shigar masa da ita mota, ya bar asibitin cikin halin damuwa da tashin hankali, Kamar gawa a ka shiga dani cikin gidan Amjadu inda ya cika da Jama'a maza da mata lokacin tuni an shirya gawar Mimi an futo da ita, saboda haka Jahid kawai ya tsaya nan aka sallace shi da ita, shine a gefe Amjad din a gafe suka dauki makarar dukanin su zuciyoyin su babu dad'i amma dai komai ubangji ya saukar kan bawan shi ne dai-dai.







*25/11/2019*
[11/26, 9:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*63*




Mutuwar Mimi ta girgiza zuk'atan Al'umma bamu kad'ai ba hatta da masu gadin gidan sai da suka ji a mutuwar a jikin su, Jama'a kuwa daga ko ina b'arkowa suke yi ta'aziyya wasu kuma gulma ce take kawo su, domin 'yan jarida sun ruga sun gama wa tsawa duniya cewa mutuwar mayar Young millionaire tana da nasaba ne da harin da jama'ar gari suka kai masa, wa 'yanda basu San yayi aure ba suka dinga mamaki shine suke zuwa zaman makoki, mai girma governor Sarkin kano duk dasu akai sadakar uku, su mai citta ma duk dasu babu tsoron Allah ko na kwabo a tare dasu, a fili sun nunawa Amjadu kara a zuciyarsu kuwa murna suke yi sosai, shi kuwa governor abun ne ya soma bashi tsoro ganin yanda yazo zaman sa na k'arshe jama'ar gari na raka shi da dutsina suna fadin "Ba mayi."!!! Kuma tunda ga mutuwar Mimi jama'a suka fara gane cewa harda sa hannun governor akan sharrin da akai wa Amjdin, ranar a tsorace ya bar kofar gidan Amjad ganin yanda matasa suke jifansa kamar ba governor ba, sai da jami'an tsaro suka fara sakin harbi sannan kowa yq shifa taitayin sa, Umma kuwa jin irin zantukan da jama'ar gari suke yi kan mutuwar Mimi yasa tace" Suyi hakuri kar su bata wa Mimi gawa kawai Allah ya amshi abunsa lokacin da yaso.

*****
Yau kwanan Mimi bakwai a karkashin k'asa, na fige na tsigale sai Umma tayi da gaske nake cin abinci kullum ina zaune zukud'inm! Ko kuma in tafi dakin ta in kwanta kam bed dinta hade da rungume wani k'aramin hoton mu, dake cikin frem a kan drowr gefan gado ta aje shi, kuka nake yi sosai, Umma granny dashi kanshi Uban gayya naga duk sun saki jikinsu har hira suke yi suci abunci hankali kwance kuma suyi dariya, ni kadai ce nake cikin halin damuwa da bakin cikin rashin Mimi, tsakanina dashi kallone domun tunda Mimi ta mutum magana ta fatar baki bata hada mu dashi yau kwanakinmu bakwai kenan a cikin gidan shi, ya sake sosai yayi wanka ya shirya harda fesa turare sai abun yayi ta bani mamaki ina zargin sa, dama ya fi son Mimi ta mutu ya cigaba da tsula tsiyarsa take wata irin tsanar sa ta cika min zuciya ta.

Jahid kullum yana kirana a waya sai dai Sam bana sakewa dashi domin gani nake yi kamar bakin su da daya da Amjad din, matar shi Hafsa me kirki da ita duk a gama zaman makokin INA lura da ita da yanda take satar kallona a fakaice.

Babu kuzari a jikina na futo daga dakin Mimi hannuna rike da k'aramin hoton mu, kusa da Umma na zaune a hankali nace"Umma zaman me muke yi a gidan nan? Wallahi nagaji gani nake kamar Mimi zata dawo gwara mu tafi." Umma tace"Eh dama yau kam zamu tafi tunda an share makoki, muna jira maigidan ya futo ne zamu je duba baby insha Allah daga asibitin sai mu wuce gida." Granny tace"Habadai Ku kuwa ai sai kace Wanda ake kora kwabari kuyi sati biyu mana in baza Ku bari ayi ar'bain ba, har yanzu fa ana zuwa gaisuwa." Umma tace"Tafiyar tamu ta dole CE Hajiya ni kaina a takure nake a gidanan wallahi, kiyi hakuri duk Wanda zai mun gaisuwa ya same ni a gida." Granny tace"To Allah dai ya gafartawa wannan yarinya.
Tsaf ya futo Cikin dogayen kaya,na lura tunda akayi mutuwar nan bai sanya k'ananun kaya ba, k'amshin sa ne ya cika parlor ya tsaya bakin kofar shi yana gyara links dinshi, saurin kauda kaina nayi daga kanshi ina jan tsaki kasa-kasa wallahi wani mugun haushin sa nake ji. Umma tace"Ka futo kenan."? A hankali yace." Eh Umma Ku tashi muje yanzu, amma naji kuna wata magana ko." ? Umma tace"Eh kam yau zamu tafi gida." Yace." Umma kuyi hakuri ayi sadakar ar'abain mana." Umma tace"Bazai yiwu ba, INA da uziri Asma'u kuma makaranta zamana a gidanan bashi zai dawo da Mimi ba." Yace." Hakane Umma shikkenan Allah yasa ka da alkairi. " mik'e wa Nayi da sauri na bar gurin, hijab dina na dauko dama tunda nazo kayan Mimi nake amfani dasu, Umma ko granny ce ta dauko mata wasu sabbin atampopi super take sanya wa yanzu daya daga cikinsu a jikin ta, Granny ta mike tana fadin "Baza Ku barni a baya ba, muje inga 'yar yarinya cikin kwalba."


Aikuwa ko da sukaje Asibitin fafur likitoci suka hana su shiga ganin baby Aisha yarinyar da Ubanta yayi mata huduba da sunan mahaifiyar ta, shi kam ai dactors din sun San shi farin sani dolen su suke kyaleshi ya shiga yaga babynshi kullum baya iya bacci sai yaje ya ganta haka kazalika kullum kara kaunar yarinyar yake Cikin zuciyar sa, yarinyar kamar su daya da uwarta sai dai ta kwaso hasken fatar shi, fara ce sosai, Amjad kam yafi Mimi haske nesa ba kusa ba, Alhmdullahi tana samun kulawa sosai daga gurin dactors ta fara k'wari da girma jikinta ya fara murjewa tana rayuwa cikin kwalba cikin hukunci ubangji.
Babu yanda muka iya haka muka hakura amma naji babu dad'i a zuciya ta domin naso inga baby nan wallahi ga yanda naji ubanta na fadin kamar si daya da Mimi, Jahid nayi ta kira a waya yak'i dauka saboda yasan zancan dokar asibitin CE, yana ganin kan Asma'u ba zai sanya ya karya ba.
Amjad har gida ya kaimu Cikin motarsa, zuciya babu dad'i na futo daga motar ba tare da na jira su Umma da aunt Hauwa ba, barin su nayi tare dashi suna sallama, Ya Aminu ne kawai a gidan dama yasan da dawowar mu tunda aunt Hauwa tayi masa waya tsaf muka tadda gidan, rumfa na zube kan leda na fara kuka.
Suka shigo suka same ni a haka aunt tace"Wannan wane irin shirme ne." ? Cikin kuka nace"Aunt don baki San yanda nake ji bane a zuciya wallahi Ashe duk gujewa mutuwa da muke yi akan Mimi tana jika aunt Mimi tasha wahala a rayuwar ta wallahi" aunt tace"Sai hakuri dukanin mai rai mamaci ne addu'a kawai zamu yi mata."
Ya Aminu ya shigo dakin yana fadin"Wannan kukan da kike yi kina kara mata azaba ne idan ta fado miki a rai kiyi mata addu'a. " shiru kawai nayi musu.

Ko da na koma makaranta ba wani sake ba, kullum muna tare da Munnu muna zancan Mimi da halayen ta na hakuri da ban dariyar ta da saurin kukan ta wani lokacin idan na tuno hae sai na share hawaye sai kawai inyi mata addu'a samun rahamar Allah.

Kullum kuwa sai na damu Umma da zancan babyn Mimi nace ta nemi alfarma gurin Amjad ta dauko ta ta raine ta kamar yanda ta raini Mimi, Umma tace wannan kuma nice zanyi hidima tunda nice mamanta a yanzu, nan na dauki a niyar fad'awa Mujahid kudirina kan Baby Aisha, yarinyar da ta zama cikkakiyar mutum domin yanzu tayi k'wari sosai ta cika wataninta na haihuwa, Jahid yace." Zai fad'awa mahaifin ta ko zai amunce, dama ya karb'i babyn sa, yau kwana uku kenan, jin abunda Jahid din yace sai ya d'aga min hankali Ashe har sun bashi baby babu labari mu gamu a zaune kullum muna kwadayin ganinta, to yanzu da ya karb'a wa ya kaiwa? Ni kadai nake tambayar kaina, ina dawowa daga makaranta na fad'awa Umma halin da ake ciki, tace "Aikuwa bai kyauta mana ba, muma ai muna da hakki a kanta, gashi kwana biyu ya daina kiran Aminu a waya balle kusan halin da ake ciki." Nace"Umma to yanzu wa zai kaiwa babyn ma." Umma tace "Kakarshi mana." Shiru na minti biyu nace "Umma kakarshi bata da k'wari don Allah ki amunce a dauko ta." Umma tace"Ai dama bani naki amincewa mutukar zai bamu muna so hakkin sa ne." Nace "Nayiwa Jahid magana zai nemi alfarma a gurin shi." """"

Rayuwa kenan duniya babu tabbas yau kwanan Mimi Hamsin da bakwai a karkashin kasa komai yayi farko yana da k'arshe Amjad ya sake ya barwa Allah komai ya tabbatar dukanin Abunda ya same shi daga Allah ne.
A halin yanzu ya maida hankalin sa ne gurin k'ara bunk'asa harkokinsa na waje, a cewar sa mu'amula da turawa yanzu ya fara saboda wasun su sun fi muslumin mu amana da tausayi, tunda gashi da Dan uwanshi musulmi aka hada baki dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login