Showing 84001 words to 87000 words out of 92177 words
Chapter 29 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
yake sauka d'akinta na shiga na kwabe kayan jikina pant fa breziyya ta duk sun jiki jagab suma sai da na sanya sabbi, sannan na dawo rumfar Umma na shafa Robb din duk jikina, can k"uryan dakin ta na shige na k'udindina jikina ina jin shigar zazzab'i. Sama sama naji muryar Umma tana fadin "Yarinyar nan zazzab'i ya kamata ga k'irjinta yana harbawa duk da cewa dare bai yi ba sosai ki kira Mujahid a waya yazo ya kawo mata magani duk ke kika jawo mata." Futowa nayi jikina lullub'e da zanin gadon Umma saboda sanyi da nake ji nace"Umma har dani za'a kawo wa magani domin nima zazzab'i har ya rufe ni wallahi." Umma tace." Ai kema kin San kanki ganganci ne kawai." Handbag dina dake yashe a gefe INA dauka ina kokarin fito da wayar naji duk abunda ke ciki ya jike har wayar, na dauko ina gogewa abunka da babban Abu ina kunnawa ta kama, numbar Mujahid na fara kira... Ya dauka a nutse muka gaisa na fada masa halin da ake ciki. Take yace gashinan zuwa. Kashe wayar nayi na mike har zan shiga daki na dawo ina lekan fuskar baby dake bacci a bayan Umma kanta na taba da hannuna naji zafi rad'au! Gefan Umma na zauna zuciyata duk babu dad'i Jahid kawai nake jira ya zo. Cikin daran Mujahid ya kawo mana magunguna ya fada min yanda zan bata, Cikin ikon Allah da na bata maganin zazzab'in tsakanin 15mintus zuwa 20minuts zazzab'in ya sauka sai dai majinar da take zuba har yanzu. Maganin na kwanta baby kam a gurin Umma ta kwana domin tunda na sha maganin bacci me nauyi ya dauke ni, Ko da safe wayar Jahid ce ta tashe ni, yana tambayar jikin Baby dalili shima Amjad tun asubah ya kira shi a waya shi ya dauka ma ko har ya samu labarin abunda ya faru yake fad'a masa a jikin da sauki Amjadu ya shiga mamaki sosai ya kira wayar Jahid din ne a matsayin sa na mskusanci ga Asma'u ya sanya ta ta maida baby gida kafin ya dawo domin shi yayi alk'awarin bazai kara kirararn ta a waya ba kawai yaji yana masa wata magana. Bai nuna bai sani ba sai yayi shiru kawai yana sauraron Jahid, shi kuma ya cigaba da cewa "Hakane da ma idan ruwan sama ya daki k'ananun yara zasuyi ta fuskantar wannan matsala kafin jikinsu yayi k'wari gobe insha Allahu nake so na auna ta sosai saboda ina gudun nimonia ganin yanda take Jan numfashi da kyar."!
Take ya fahimci inda maganar take wato ruwan sama ne ya doki sweet heart dinsh, babu walwala a tare dashi yace." Jahid idan na fahimci maganar ka kana so kace min ruwan sama ya tab'a lafiyar baby Aysha hakane ko.'? Jahid yace." Eh mana ai na dauka ka sani kaima maganar zakai min." A kaurare yace." Inso in ce dakai ka sanya Asma'u ta mai damin yarinya gida sai naji wannan mummun labarin daga bakinka Asma'u taje ta dauko min yarinya ba tare da yadda ta ba shine dalilin kiran da nayi maka, gaskiyar magana Mujahid Dan dai Kaine ina ganin girman ka a idona amma da sai na dauki mataki kan Asma'u tunda abunda ta shirya min kenan kan wane dalili zata futa da k'aramar yarinya ruwa ya dake ta, kaga irin sakacin da nake fada maka ko, ita bata rike kanta ba taya ya zata iya rike wani."!! Ya k'arashe maganar tasa a zafafe! Jahid yace." Gaskiya bata kyauta ba gani bata gayamin haka ba, amma kayi hakuri don Allah komai ka gani tsautsayi ne amma tabbas bata kyauta ba. " Cike da takaici yace." Yau kwana biyu rabona da in ji sweetheart nayi kewayar jiya babu yanda banyi da yarinyar nan ba ta bani ita muyi hira ta kashe min waya, ni da yarinya ta." Jahid yayi murmushi tare da fadin"Sai kace Wanda zakayi hira da babban mutum ka kwantar da hankalin ka zaka dawo ka yadda sweetheart dinka cikin koshin lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke yace." Insha Allah karshen watanan zan dawo zan je Umara insha Allah." Jahid yace." Alhmdullahi kayi mana addu'ar zaman lafiya ni da Asma'u da samun zuria mai kyau kasan karshen wayan aka sanya lokacin d'aurin auranmu." Amjad yaji wani irin fad'uwar gaba ta rikito masa zan can yazo masa a baza ta! Yace." Jahid yaushe aka sanya rana babu labari."! Jahid yac."Wallahi my friend abun yazo a bazata kuma a kurararn lokaci Dan har yanzu hankalina ba a kwance yake ba dalili Momyna bata kaunar auramu da Asma'u, shine nake cikin wani hali shaf na manta ban fada maka ba." Cikin dakiya da kokarin danne damuwa yace." Na tayaka murna Aboki amma INA baka sha'wara cewa ka bi umarnin iyaye domun Neman albarkar su, ina ganin tunda Momy tace bata so kayi hakuri mana ka bari."! Jahid yace." Wallahi nayi kokarin hakan na kasa INA yiwa Asma'u wani irin so Wanda nakasa gane irin shi ka tayani da addu'ar Neman zabin Allah." Girgiza kansa yayi yana jin wani daci Cikin zuciyar sa yace." Insha Allah zan sanya ka a addu'a. " Jahud yace." Nagode my Aboki. " Amjad yayi murmushi tare da fadin. " ka kula min da baby please kuma ka sanya ta ta Mai da ta gurin granny yau INA son muyi hira da ita please. " Jahid dariya kawai yake masa sukayi Sallama. "
***
Babu laifi Zazzab'i ya sauka daga kaina sai baby ce take fama sosai Jahid da yazo kafin ya tafi gurin aiki ya fada min duk yanda sukayi da Amjad din na dinga mamakin rashin kawaici irin nashi nace"Insha Allah Jahid ko baka fada bs yau din nan zan mai da masa yarinyar gida nagaji da wannan gorin wallahi,." Jahid yace." Baki fahimce shi bane shima yana da tasa manufar shiyasa ." nace "Jahid Dan dai abokin ka ne kake kareshi dariya yayi min tare da fad'in"Ya jikin baby dim nace DW sauki kam hancin ta ya daina yoyo sai dai zazzab'i"Yace shima zai sauka Insha Allah." Godiya nayi masa shi kuma ya tafi tare da jaddada min in mai da baby gida nace insha Allahu." Ko da na fadawa Umma abunda mahaifin. Baby yace a kanta sai tace aikuwa baza a maida ita gida tana cikin wannan yanayin ba, Sam baza a fita da ita ko ina ba kasamcewar akwai sanyi a gari har yanzu kuma da akwai sauran hadari, shuru kawai nayi ina jiran Abunda zai biyo baya.
****
Duk abunda yake yi k'arfin hali yake tunda yaji labarin d'aurin auran Jahid da Asma'u ya nemi nutsuwar sa ya rasa hak'ika al'amarin yazo masa a bazata! Kullum ta Allah kokarin sa ya yakice yarinyar daga rayuwar sa, abun ya fassakara duk abunda yake mata yana sane yake mata domin ya kuntata matane suyi fad'an da zai ji tafi ta a ranshi gaba daya amma dake yarinyar taurin rai ne da ita taki yadda suyi fada da ita sha fa yanzu gani yake babu yadda za'ayi ya auri Mimi daga baya kuma ya aure Asma'u a da dai yayi niyyar ya hadasu ya aura dalilin son da yakewa Asma'u, sai bayan ya auri Mimi ne ta koya masa sonta kyawawan haleyen ta suna burge shi, a wannan zamanin dai samun mace kamar Mimi sai an tona... Yini yayi yana tunanin Abu d'aya. K'arfe goma na dare dai-dai ya jira granny dake shirin kwanciya, ta dauka suka gaisa Yace. " Granny bani baby Aysha ko tayi bacci ki tashe ta kinji."" Cike da mamaki tace." Wai kai baka da lokacin kiran waya ne sai dare."? Yace." Time din nake da sukuni ki bani sweetheart please."Ya wani marairaice murya. Tsaki yaja tace." Wace baby kuma wacce take gidan kakaninta." Tashi yayi da sauri yace." Me kika CE Granny. "!? Cewa nayi baby na gidan kakanin ta, yo ko tans gurina kana tunanin zan tashe ta daga bacci saboda shirmen ka." Kashe wayar sa yayi ba tare da ya tsaya ya gama sauraron Abunda granny take fada ba.
Wayar Asma'u yake kira, busy yau ma tana waya da wani, zuciyar sa kamar tayi bundiga ya jefar da wayar kan bed d'in ya dafe kanshi da duk hannunwan shi biyu.
*29/11/2019*
*BABBAN YARO*
*MALLAKAR_BINTA UMAR*
*68*
Yafi Rabin a wa a Zaune a gurin sannan ya mike Cikin mutuwar jiki ya shiga toilet alwala ya dauro ya fito yana hada hanya, dadduma ya shimfid'a ya fara sallahr nafila cike da Neman zabin Allah domin shu kanshi al'amarin sa tsoro yake bashi. Komai ya da gule masa lokaci guda, bayan yayi idar ya jima yana rokon Allah ya kawo masa dauki a rayuwar sa, yaji wani sanyi cikin zuciyar sa, kwanciya yayi kan daddumar bacci ya dauke shi mai nauyin gaske.
Ni kam bayan mun gama waya da Jahid tunani na fad'a mai tsayi zahiri dai gashi mahaifiyar shi ta nuna bata kaunata karara ko yanzu sai da ya kara fad'a min irin artabun da suke bugawa da ita kan Dole ya janye maganar saboda ta samu labarin kai kud'in da akayi a family lokacin da taje gidan buki suka dinga yi mata Allah ya sanya alkairi, sai abun yayi ta bata mamaki sai daga baya ta fahimta, shine tasa akai kiran sa, ta kare masa tanadi har tana ikirarin zata tsine masa in har bai janye maganar ba, duk yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta na lura Jahid idonshi ya rufe a kaina baya tsoron Abunda zai je ya dawo, dole in Sanar da Umma halin da ake ciki, yanzu jikina ya fara sanyi da al'amarin hak'ika ina son Jahid tsakani da Allah kuma bazan so ya fad'a cikin halaka ba, tunani na gwara ya hak'ura kawai domin ya samu albarka iyaye da wannan tunane-tunanen nayi bacci kwata-kwata na manta da Wani Amjad da damuwar shi. Da safe duk na warware wa Umma abunda yake faruwa tace"Asma'u dama ni tuntuni sai DW nace ki hak'ura da yaron nan tunda uwarsa bata so kika k'i, kuma kin san halin Kawun Ku ba kirki ne dashi Yanzu in wata magana ta sake faruwa zasu har gida su ci mun mutunci ne ki jawo tashin hankali ya kare a kaina da ban ji ba ban gani ba." Shiru nayi wasu zafafan hawaye na zubo min duk ja rasa wane tunani ma zanyi.. Karar waya ta naji a dakinmu da sauri naje na dauko ina duba baby dake bacci cikin kwanciyar hankali, INA dubawa naga jahid din ne ya kira sallama nayi ya amsa murya babu dad'i ya Dora da fadin"Asma'u duk abunda kike ki aje don Allah ki mai da wa da mutumin nan yarinyar shi, wallahi yai shi ya tashe ni daga bacci dama ga shi da kyar na samu ya dauke ina fama da damuwa."
Nima cikin damuwa nace"Jahid ka kwantar da hankalin ka dama yau nayi niyyar mai da ita saboda Umma tace a k'yaleta ne yasa saboda sanyi jiya amma insha Allahu yau zan mai da ita Nima na huta da jaraba." Kashe wayar nayi a fusace! Ban saurari maganar shi ba. Hakan ce ta kasance bayan sallahr la'asar Munnu tazo gidanmu nan muka tafi domin mai Da baby kamar yanda nayiwa Jahid din alk'awari munnu tq kalleni cikin damuwa tace"Asma'u fyskar ki ta nuna alamun damuwa tabbas da Abunda yake damun ki."! Girgiza kaina nayi nace"Tabbas Munnu abokin kuka shi ake gayawa mutuwa nan na kwashe duk abunda yake faruwa na fada mata har irin rashin kunyar da nayi Monye Jahid din sai da na fad'a mata. Munnu ta dinga mamaki daga bisani tace"Wallahi wasu masu kud'in haka d'abi'ar su take Sam basa son talaka kiri-kiri ta zo har gida ta ci muku mutumci saboda zubar da girma yanzu kuma idan mukayi aura kuka Tara zuria tace me? Da aure da mutuwa duk na Allah ne mutane ne basa ganewa wallahi." Nace"Ke wace shawara kike gani." Tace"Kawai ki cigaba da nan zabin Allah idan da Rabin auran Ku za'ayi dashi amma ko da wasa kar ki nuna masa kin karaya domun kinga shima yana daurewa gashi saboda ke ya bujerewa mahaifiyar sa." Da wannan zancan muka isa. Babu walwala a tare damu muka shiga, Iyami da Granny na zaune a parlor kamar ko da yaushe ta amsa mana sallama a sake Iyami kuwada saurin ta ta k'araso gurin mu tana fadin "Oyoyo baby kokarin daukar ta take yi nayi saurin kwantota ta dauke ta tana cilla ta sama, yarinyar ta gane ta sai ta fara yi mata dariya. Zama mukayi a nutse muka gaisa da granny dake tambayar mu Umma nace" Tanan k'alau tace ma a gaishe ki da kyau kafin tazo." Granny tace"Ina amsawa nima...Iyami kawo musu abunci." Tafad'a tana kallon Iyami dake wasa da baby Granny ta karb'i baby ta nufi kicin, cikin zuciya ta nace yau kam baza muci abincin gidannan ba wallahi Mik'ewa nayi Munnu ta mike granny ta bimu da kallo tana fad'in"Za'a kawo muku abunci kun mik'e." Nace"A koshe muke Wallahi." Cikin nazari tace" kamar akwai abunda yake samun Ku kun shigo babu walwala kinji sakewa Lamar yanda kuka saba, yake kawai nayi nace"granny kenan babu komai wallahi mu dai mun tafi sai mun sake zagayo wa." Hanyar futa muka nufa Abun kamaer almara babyta fashe da kuka tana d'ago hannun ta! Granny tace"To maza Ku dawo Ku tafi da ita gashinan tana kukan rabuwa da Ku
" gaba nayi cikin zuciyata nace yarinyar nan ko kukan me zata yi bai same ni ba wallah" Munnu CE ta koma da baya ni kuwa tuni na fuce da sauri, ina jiyo kukan ta har waje, ko da Munnu taje kin yarda tayi da ita sai kuka take yi Granny tace"Asma'u take nema ba ke ba. iyami ta kwalawa kira tana fadin "Bazan iya da wannan rigimar ba zo ki dauke ta yarinya k'arama da gane mutane." Iyami ta shigo da sauri ta dauke ta tana rarrashin ta, Munnu tace "Asma'u baby ta gane ki sosai wallahi har nayi sha" awar Dadyn ta ya Baki tunda kuna kusa in Allah yayi nufin auran ki da Mujahid." Murmushin takaici nayi nace"Munnu kenan, nasan ko mutuwa zanyi bazai bani ba, kar ki so kiji yanda nake jin zafi a zuciyata jin kukan da take yi." Munnu tace"Allah ya kyauta masa amma gaskiya na lura guy nan ya sanja hali da ba haka yake ba." "Hummm! Munnu kenan dole yayi abunda yake so tunda gonar sa a ka shiga kuma yana ganin ya wuce komai na rayuwa shiyasa." Munnu tace"Wallahi maganar ki gaskiya ce Allah ya kyauta." Nace "Ni Abunda yake damuna Abu daya ne aurana da Jahid wallahi yanzu abun tsoro yake bani ina jin tsoron abunda zanje in Tarar."! Insha Allahu alkairi zaki yadda ke dai ki cigaba da yin addu'a.'a" nace "Nagode Munnu." Da Wannan hirarar muka isa gida.
*******
Amjad zaune a harami ya d'aga hannunwan sa sama sai kwararo addu'a yake, yana zubar da hawaye ni kaina ya mugun bani tausayi, ya kai Rabin awa cikin wannan halin kana ya shafa addu'ar ya mike a nutse ya dauki daddumar sa da glass d'insa dake aje a gefe ya nufi mazaunin sa, ko da ya isa ba zauna ba toilet ya nufa cikin kuzari yati wanka ya fito fes dashi kasamcewar ana zafi bai shafa mai ba, sai ya shafe jikinsa da turare ya sanya wasu ubansu parkinsan ash coulor hade da wata hula mai kamar net fara tasa da ita, takalmi mai gidan yatsa yayi amfani dashi ya d'aura tsaddan a gogon shi, kana ya manna farin tabarau din shi a fuskarshi, sai ya kara wani uban kyau, kasancewar ya Tara kasumba bai yi aski ba, sai abin ya bada sha'awa Amjadu ya saje da larabawan saudia domun duk kwakwar mutum bazai tab'a cewa ba balarabe bane ga yanayin fatarsa lufluf domin har tafi ta wani balaraben goge wa fuskarsa babu walwala a dauki wayoyin shi hade da wata k'aramar haka irin ta matafiya, kulle dakin yayi da key ya sauka k'asa. Amjad ya nufin koma wa gida Cikin iyalinsa bayan yaje dakin Allah yayi addu'a ga iyayen sa dashi kansa da sauran alumar musulmi.
Yana jirgi ya kira su Rambo ya Sanar musu gashinan kan hanya take suka wuce airport domin tarar sa, Granny ya kira a waya ya fada mata, tace"Amma kayi mana bazata! Mai kake so a girka ma." ? Murmushi yayi yace." Granny kuyi min Dambu da zogale." Dariya tasa tana fadin "Kasamu k'ato Allah ya kawo ka Lafiya." Kashe wayar tayi tana kiran Iyami. Tace" maza a shirya dambu mai kyau ga k'ato nan kam hanya." Iyami tace"Wallahi baby ce take kuka har yanzu taki hak'ura kawai tana wasa sai ta fashe da kuka." Dariya granny tasa tace"Tana tuno uwarta ne, jeki dauko min ita kije kiyi aikin ki." Da sauri Iyami ta dauko baby dake kuka har da majina. Granny ta mik'a hannu tana son ta karbe ta ta make kafad'a wai baza ta zo ba, dariya tayi tana fadin"Kaga ja'ira dole kuwa komai kukan ki kiyi shiru Ubanki na kan hanya. Tace iyami aje ta kije kiyi aikin ki." Iyami ta ajeta a kasan gurin ta nufi kicin da sauri. Lokacin baby ta tsandare da kuka, babu shiri granny ta dauke ta ta Goya Tana zagaye parlor da ita, Tunda ya doso kofar parlor yake jin kukan sweetheart dinshi yaji ranshi ya sosu da sauri ya shiga ciki hade da sallama k'asa_kasa granny ta amsa tana masa barka da zuwa, mamaki yake yi ganin baby a bayan granny a goye amma taba kuka, wayoyinsa ya zube kan teble din gaban shi ya fara kokarin daukar babyn da Granny take kokarin kwance ta, yace." Wai mai akayi mata ne take kuka tun kafin na shigo nake jiyo ihun ta." Granny tace"Sheganta ka ce kawai wallahi tun da taje gurun uwarta tayi kwana biyu Shikkenan ta dawo mana da rigima Don da kyar ma ta yarda da iyami, nu kuwa sai nayi da gaske nake daukar ta." Ya gane inda maganar Granny ta dosa, zama yayi cikin kujera yana goge mata fuska da