Showing 87001 words to 90000 words out of 92177 words
Chapter 30 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
hakincin sa, yace"Granny nifa bana ganin laifin kowa sai naki ke da kika dauke ta kika basu." Cike da jin haushi yayi maganar. Granny tace"To ka dawo ko zaka fara iyayin naka to me kake nufi iyayenta sunzo su dauke ta sai in hanasu ni kam ban iya wannan k'ek'e da k'ek'en ba irin naka." Baice komai ba ya sanye leb'anshi na k'asa bakin ta, kamar yanda yake mata tana jin jira, aikuwa ta kama tsotsa yarinyar bata manta ba. Kallon ta yake yana jin wani irin tausayin ta cikin zuciyarsa duk sanda zai kalleta sai ya tuna masa da Wife dinshi Mimi ko da yaje Saudia duk Rabin addu'ar shi tata ce. Baby Aysha ta fara lumshe ido kalaman bacco still leb'anshi take tsotsa kad'an kad'an har bacci ya rinjayeta ta saki. Ajiyar zuciya ya sauke ya rungume ta tsam a jikinsa tare da fad'in"Iyami ta gyara mata gurin kwanciya tayi bacci."! Granny ta bude baki zata kwalawa Iyami kira kamar yanda ta saba. Da sauri ya d'aga mata hannu yana yamutse fuska da ido ya nuna mata baby wai kar ta tashe ta. Tsaki granny yaja ta mike daga gurin. Da kanta taje ta gyara mata gurin kwanciya ta dawo zata karb'i ta kamar kurma haka ya zama Mik'ewa yayi ba tare da ya bata babyn ba ya nufi bedroom d'insa da Yarinyar granny tayi sakaro da baki, tana fad'in"On ni naga iyayi da feleke a ka dawo din zaka fara nuna mana iyakarmu ni da Iyami komai mukayi bamu iya ba hummm! Allah ya sawak'e maka." Ni da Munnu ne zaune a Uwar dakin aunty Hauwa ta sanya muku tsuguna cikin wani dogon bokitin na k'arfe inda ta sanya wata k'aramar tukunyar k'asa da garwashin wuta had'e da wani mugun turare da wasu saiwowi masu wani irin kamshi, kullemu tayi a dakin har da Dan mukkuli, tsaki babu irin wannan banyi ba, a ganina ni budurwa CE ba bazawara ba, mai zasa aunty Hauwa ta dinga azabtar damu da turaran matsi kawai garin Neman gira a rasa ido, tunda akace saura kwana goma sha hudu d'aurin auranmu aunty hauwa ta sanya mu a gaba, domin har munnu ma da take surukar ta tace ita bata dauke ta a matsayin suruka ba, k'anwar tace duk abunda zata min zata yi mata, kuma bayan haka Si Dan uwanta take gyarawa Munnu tun tana jin kunya ta daina ji domin yau kwananmu uku a gidan aunt Hauwa tana yi mana izaya iri-iri, magani kullum ta dama da nono mai Dan iskan bauri da wani irin k'amshi kai hawa ka taje sai mun shanye tasa, wallahi ina daga tsigar jikina na Mik'ewa saboda yanayin dandanon sa a bakina babu dad'i bauri yaji zak'i d'aci duka, ranar dai da taba ni zubarwa nayi Munnu kuwa saboda kunya sai ta shanye tasa ta aje kofin ni kuwa kullum rigima muke da ita kan hakan. Yanzu ma Mik'ewa nayi da sauri jin wani Abu na zuba daga k'asa na, zani na nasaki na mai da pant dina. Munnu tace"Ya kika tashi ne." Cikin b'acin rai nace"Munnu ke in zaki zauna zauna ki cigaba da azabtar da kanki kina budurwa ace wani Dole sai kin matse mtssss to wace irin katsewa kuma ake buk'ata. " munnu tace "Don Allah ki koma ki zauna Wallahi tunda kikaga ta dage akanmu hakan yana da amfani." Tsaki naja nace"Sai kiyi ke ni dai na gaji." Kofa na nufa ina bugawa hade da kiran sunan aunt hauwa nace"kizo ki bude min zan shiga band'aki. " bude min tayi taba fadin kiyi sauri ki fito kar maganin ya sane so nske ya bi jikin Ku sosai." Hararata nayi ganin ta juya baya zumb'ura baki nayi na shiga band'akin ta dake parlor. Ina tsungawa naga ni bu mai yauki na dilala daga gabana, dama tun da aunt ta sanyamu a gaba nake jin wani azabbaban feelings na taso min. Ruwan zafi cikin wata butar.k'arfe na dauka na daureye gurin sosai sannan na fito raina duk babu dad'i
*30/11/2019*
*BABAN YARO*
*MALLAKAR BINTA UMAR
*69*
Shirye-shirye ta kowa wane fanni ya kammala Ya Aminu ya had'a lefe na gani na fad'a sosai Umma da aunt hauwa sukayi kokari a kansa, yanzu nawa lefan ake jira sai a fara Rabin goro kullum muna tare da Jahid a waya muna shirya tsarin buki da yanda zai kasance.
Momyn Mujahid ce take kai kawo a parlor ta takasa tsaye ta kasa zaune wato Mujahid ya yaudare ta ya rufe ta sun hada baki da ubanshi ya bujerawa bukatar ta, lallai ne ka haifi da a cikin ka ya wulakanta ka lallai zata nuna masa iyakarsa, yanzu ta sakko daga sama dalili shi mijin NATA ya kira ta tazo taga kayan lefa kuma saboda sun raina mata hankali wai itace zata nemi masu kaiwa don haka baram!_baram suka rabu da mijin nata ta sauko a fusace jiran zuwan Jahid din take domin tayi masa magana ta k'arshe kan auran.
Tunda ya shigo yaga tana kai kawo hankalinsa ya tashi yasan dole duk abunda yake b'oye wa ta sani, ko k'araso wa bata bari yayi ba ta karasa gurinsa a zafafe ta zabga masa mari Tana huci! Kamar zakanya tace"Ni zaka yaudara Jahid wato kun hada haki da ubanka kun rufe ni saboda baka dauke ni a bakin komai ba ko? Jahid yayi shiru hade da yin kasa da kansa. Ta cigaba da cewa "Wallahi in har nice na haifeka baza ka auri yarinyar da ta zageni ba, idan kuma kayi ganganinci auranta to babu shakka a ranar zaka sake ta ko kuma in d'aga maka nono don tsine maka zanyi wallahi tallahi kaji domin bazan yi kaffara ba."!!! Ta k'arashe maganar tata a zafafe! Ya wani irin huci!
Jahid ya shiga cikin wani irin mugun yanayi a lokacin gumi ya dinga tsiyayar a jikinsa duk yanda yaso ya fahimtar da mahaifiyar sa al'amarin ta kasa fahimta. Wasu mazan sukan fuskanci matsala daga gurin matayen su a sanda zasu kara aure, shi daga gurin mahaifiyar shi ya fuskanci matsala. Mik'ewa yayi baya ko kallon gabansa, ya fita daga parlor. Wani irin kallo ta bishi dashi ta ta tabka wani irin tsaki, ta zauna kan kujera tana fadin" da in hada jini da talaka gwara duk abunda zai faru ya faru.
Jahid kuwa kai tsaye b'angaran Amjad ya nufa a lokacin hankalin sa a tashe! Granny na ganinsa cikin wannan halin ta tabbatar babu lafiya, zama yayi kan kujera hade da dafe kansa, granny Tace "Tabbas komai yayi tsanani maganin sa Allah, Mujahudu akwai damuwa a tattare da kai. Ya d'ago kansa yana kallonta, kawai sai taga hawaye a fuskar sa yana zubah, cikin mamaki tace" kafadamun damuwar ka Insha Allah zan taya ka da addu'a. " Cikin karkarwar jiki ya warware mata dukanin abunda yake faruwa. Granny ta jima tana mamakin al'amarin daga bisani tace"Tabbas Hajiya Sa'a ta tabka babban kuskure, waye ya fada mata ana jayayya da al'amarin aure duk yanda bakason hada zuri'a da mutum idan Allah ya kaddara faruwan haka babu makawa sai ya faru idan tana tsananta kamar Yanzu Allah sai ya dauke ta ayi babu ita, tashi muje gurin ta." Jahid ya mike da sauri ita kuma dauki hijab dinta ta zura, suna fita motar Amjad na shigowa gidan, yana kwance a bayan mota ya hango Jahid din da granny sun nufi motar sa, duk da cewa Jahud ya fahimce shine bai tsaya ba, da gudu ya fafari motar sumar bar gidan.. Shi kuma Amjad sai dinga tunanin ko wanine babu lafiya cikin iyalin Jahid din, ya dauki granny domin taje ta dubasu. Sam bai kawo komai cikin ranshi ba, ya shiga gida yanayin tozali da sweetheart dinshi ya manta da koma.
"Sosai granny take fahimtar da Momy amma ta gagara ganewa da k'arshe ma so tayi tai mata rashin kunya inda take fadin" Kinga Hajiya d'anki ko nawa da zaki dame ni lallai sai na yarda, shin kin Sam irin rashin mutumcin da yarinyar tayi min kuwa, tsinanniyar yarinya mummuna 'yar gidan malam shehu irin wannan har ta kalle mu ni da aminyata tace muna warin dauka da bleecing a i wallahi Jahid ya sake ya auri yarinyar nan sai na tsinke masa."
Granny tace"Ki daiyi hakuri Asma'u yarinyar arziki ce Wallahi akasi aka samu kuma hada zuria dasu akwai albarka Hajiya baki San ko akwai rabo tsakininsu ba, sai ki mutu saboda wannan abunda kikayi ubangji baya so." Jin abunda granny tace ne yasa Many zuburowa! Tace"kaji ni da tsohuwar najadu tsohuwar kawai! To wallahi sai dai idan kece zaki mutu,au!! Fatan mutuwa kike mun, aikin banza to wallahi ba yanzu zan mutu ba." Jahid ya Dora hannunsa aka cikin tsantsar tashin hankali da nadamar dauko granny inda yasan wannan cin mutumcin za'ayi mata da bai dauko ta ba, ya zama dole duk son da yake wa Asma'u ya hak'ura da ita, domin yana hango mugun rikici a gaba idan ya aure ta Hausawa suka ce idan so cuta ne hakuri magani ne, nan ya mike ya futa daga parlor a karo na biyu, granny ta mike cike da taikacin da b'acin rai tace"Duk yanda naso nussashe dake kin kasa ganewa har kina Neman kiyiwa danki baki, ni zagin da kikayi min bai dame ni ba, tunda kin kwatanta hali irin na Asma'u da kike cewa bata da tarbiyya Shikkenan na barki lafiya." Momy yaja tsaki da k'arfi tana fadin "Allah ya rakataki gona, nace Umma ta gaida Ayshaaaaas."! Granny ko juyowa batayi ba cike da takaici da damuwa ta samu Mujahid tsaye a gurin yana kiranta, mota ya bude mata ta shiga da sauri suka bar gidan. A hanyarsu ne granny take rarrashin sa da kalamai masu sanyi kana tace " Tunda mahaifiyar ka ta nuna bata so tom shawarar da zan baka ka hak'ura ka kwantar da hankalin guri guda rashin Asma'u ba zai hanaka rayuwa ba insha Allah zaka cigaba da rayuwa Cikin amincin Allah da yardar sa, idan Aure kake so ka sake samun mace wacce zucuyarka ta kwanta maka sai is aura mutukar ta amunce din, wannan shine shawara kayi wa uwarka biyayya." Amjad yace." Granny ban taba nadama akan al'amarin auran nan ba sai yau, da Momy ta ci miki mutumci kawai domin kina so ki fahimtar da ita, insha Allahu na hak'ura da Asmau amma INA Neman wata alfarma agurun ki." Tace" kafad'a komeye insha Allah mutukar INA da iko dashi zanyi maka." Yace." Inaso al'amarin auran nan ya koma kan Amjad ba tare da sani ba inaso ne ranar d'aurin aure yaji bazata !."
Granny tace'' hak'ika ka cika Aboki na gari Mujahid kuma idan kayi haka babu shakka ka kyauta min, domin ni kaina ina tunanin matar da zai je ya auro wacce zata kula da baby Aysha tsakani da Allah,Dole sai ita Asma'u da take a matsayin Uwa a gare ta, mungode mutuka da alkairi ka." Jahud yace." Granny Amjad yafi k'arfin komai a gurina wallahi." Tace"Yanzu abun damuwar shine ita Asma'u kana ganin ba'a shiga hakkinta ba."? Murmushi yayi yace." Nasan inda zanyi da ita itama baza tasan abunda yake faruwa ba har a d'aura aure zanje cigaba da zuwa gurun ta babu abunda zan FASA, gefe guda kuma zan je na nemi Kawun ta mu kashe magana." Granny tace"Kayi nufin alkairi Allah yayi maka jagora Kai kuma ubangiji Allah ya sanja maka mafi alkairi. " murmushi yayi ya cigaba da driving har ya sauke ta gida ya wuce ofis din mahaifinsa domin ya Sanar dashi abunda ya yanke, to shima bai Wani jayyaya ba tunda dai Shi Jahid din yace ya hak'ura to shi meye bashi sai fatan alkairi yayi yace inda Allah zamu cigaba da shirye-shiryen d'aurin aure kamar yanda muka tsara, Cike da kwaran gwiwa Jahid ya nufi gurin Kawu Yunusa, duk abunda yaje faruwa ya Sanar dashi a bazata Kawu yaji al'amarin dad'i kamar ya kashe shi sai ya dinga shiwa Jahid albarka kamar me."take ya shaidawa 'yan uwansa suka soma shiri amma ya gargadesu da cewar bayaso maganar ta futa har Asma'u taji. Suka ja bakinsu suka yi shiru.
Duk wasu shirye-shiryen Jahid ya kammala su dai-dai da kayan da zasu sanya ranar d'aurin aure suna hannunsa hakanan kayan lefe na kece raini da ya yahadawa Asmay an kai kwanaki uku da suka wuce, shi ta b'angaran sa komai ya dai-dai ta. A zahiri ya nunawa Momy nsa ya janye maganar shiyasa ta saki ranta, kuma Mijin ta bai kara tayar mata da maganar ba sai ta yadda da maganar.
Saura kwanaki uku d'aurin aure aunt hauwa ta bude mans wuta kullum cikin durkar magani kullum INA kwana da ciwon ciki da wata muguwar Sha'awa Mara fasali sai in sanja pant sau uku a rana, maganar gyaran jiki ba'a cewa komai aunt Hauwa na da abokai iri-iri wata kawarta ce ta tsaya a kanmu ni da Munnu ta hado mana kayan gyara jiki kullum sai munyi dake aunt Hauwa ta iya hadawa sosai take samu a daki muna murje jikinmu bayan mun kama wani irin turare ne mai k'amshin tsiya shima zata sanya mun mulke sako da loko na jikinsu dashi sai munyi a wa daya tukkuna zamu wanke jikinmu tuni wani sihirtaccan kamshi ya kama fatar jikin mu, duk inda muka zauna sai kamshi ni kaina bala'in son k'amshin jikina, kullum muna tare da Jahid a waya, duk wasu k'awayenmu na nesa da na kusa mun gayyace d'aurin auramu, Alina sai wani shishshige min take Sam ban Wani saki jiki da ita ba duk sabgar buki da ita akeyi taki yin zuciya.
*Ranar d'aurin aure*
Amjad Jahid Khalid Ma'aruf suka futo cikin shiga iri daya shadda CE fara tas dinki babbar Riga da 'yar ciki fad'ar tsadar shaddar bata lokaci ne, takalman su iri daya hulunsu irin daya agogonsu iri daya komai iri daya sukayi amfani dashi kamar yanda suka yi ranar d'aurin auran Amjad da Mimi mota suka shiga guda Khalid ne take draving har suka isa gurin d'aurin auran dake cike makil da jama'a take wani maroki ya saki wata shegiyar gangarsa ya fara wasa Amjad da fadin"Ango Na Asma'u sarauniyar mata gwarozo a cikin maza! Sai Amjadu! Hak'ika Wannan yarinya tayi dace da miji na nunawa sa'a fari mai farar aniya yaro mai halin manya gugan k'arfe sha kwarafniya gaba salamin baya salamun.!!!!!!!!! Jama'ar dake gurin suka dinga mamaki yaya ga ango kuma maroka na wasa abokin ango wai meye yake faruwa ne."! Shi kuwa Amjad Sam! Bai Kawo komai cikin ransa ba, kawai dai yafi tunanin ko don yanayin sunansu daya sa Jahid din yasa marok'an suka kasa ganewa wanene angon a cikinsu.
Kawu Yunusa sai kaiwa yake yana kawo wa ya sha babbar rigar shi, kana ganinsa kasan yana Cikin farin ciki, Liman yayi addu'a kamar yanda addini ya tanada Alhaji Isa mahifin Jahid ya mik'a sadaki Asma'u dubu Dari cif kana Liman ya fatiha tare da shafawa duk Wanda ke kusa da Liman a lokacin ya shaida Amjad da Asma'u Aka d'aura aure ba da Mujahid ba kamar yanda suka gani a rubuce a invitation, tofa wani maroki sake kusa da Liman ya kururuce! Fad'i yake." Allah ya tabbatar da Alkairi yau an d'aura Auran Amjad da Asma'u kan sadaki dubu Dari cif ladan ba ajalan ba, tabbas wani kaya sai amale muna rik'on Allah ya sanya alkairi badi iwar haka mu dawo suna." Take guri ya rikice jama'a da dama da su kasan Amjadu din suka rufu a kansa suna yi masa Allah ya sanya alkairi duk ya rikice a lokacin domin al'amarin ya gigita shi kuma yazo masa bazata! Wato abunda Jahid zai masa kenan, yawan jama'ar dake kansa yasa ya nemi su Mujahid din ya rasa, haka dai ya dinga gaisawa da jama'a babu yabo babu fallasa a tare dashi, shi tunani. Yake meye munufar Jahid din akan haka. Kafin kace kwabo 'yan jarida sun rufu a kanshi kowa naso yaji ta bakinsa da kyar ta sub'uce dafa hannunsu ba tare da tace musu komai ba...............
Kawai Yunsu da saurn yayyan babanmu suka shigo gidanmu lokacin INA gidan aunt Hauwa mai kunshi nayi mana Dana tunda na tashi nake jin fad'uwar gaba, Kuma ina kallon wani irin kallo da aunt Hauwa take min sai ta gyad'a kanta, Mamakin ko kallon me take min oho, ita aunt hauwa tasan da faruwar abun domin Ya Aminu ya sani shima Kawu Yunusa ne ya fada masa yace masa kuma yayi shiru da bakinsa shine shi kuma ya Sanar da aunt Hauwa din, to dukaninsu sunyi murna da farin ciki sun San Baby Aysha baza tayi maraicin uwa ba. UMMA ta shimfid'a musu ta barma suka zazzauna bayan gaishe-gaishe Kawu Yace." Ga sadakin 'yar kinan Asma'u an d'aura aure." Umma tace"Alhamdullahi Allah ne abun godiya ina yi mata fatan alkairi da samun zaman Lafiya gidan minjinta." Kawu Yunusa yw zakud'a tare da bata fuska yace." Ba da Wanda kike tunani aka d'aura mata aure ba, yarinyar mu Mun d'aura mata aure ne da yaro Dan kirki Wato Amjadu bisa fa yardar shi wancan yaron wato Mujahid mun b'oye muku faruwar al'amarin ne saboda kar Ku kawo mana nakasu a kai saboda haka shi Mujahid din yaga cancantar ya barwa Amjad din Asma'u saboda wasu dalili NASA,saura Wannan karon ma ki zugata ra bujirewa Umarnin mu."!! Yana gama maganar sa ya Mike yana wani baza babbar Riga, take sauran ma suka mike suka futa daga gidan. Suka bar Umma da kudi a hannu tana mamakin Wannan al'amari.
*31/11/2019*
*BABBAN YARO*
*MALLAKAR BINTA UMAR
*70*
Wannan al'amari ya d'agawa Umma hankali sosai ta inda ta fara tunani. Artabun da zata sha da Asma'u saboda tasan halin taurin kanta da kafiyar ta, Amma itama taji dadin wannan Abu ko babu komai baby Aysha ta samu uwa baza tayi maraici ba. Tanan zaune har jama'a suka fara cika gidan sai ta saki fuskarta ta dinga karb'ar baki. Har lokacin da 'yan d'aurin aure suka shigo Aminu ya shigo gidan da gayyar abokan shi sai fama