Showing 12001 words to 15000 words out of 92177 words
Chapter 5 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
miliyan yazo nan bamu aje ba bamu bawa wani ajiya ba, gaskiya ni bazan iya fada masa haka ba."
Umma tace "Zaman kishi tsakanin Asma'u da Mimi akwai kwara Mimi sanyi hali Asma'u wayo da rashin kunya gata itace k'arama bana son abunda zai tab'a zumumcin su." Aminu yace." Sai dai idan sune suka so haka amma in sun hade Kansu babu wata matsala. Umma tace" Shikkenan zanyi magana dasu." Ya Aminu ya mike ya futa jikinsa babu kuzari.
Mimi na daki a kwance ni kuma ina bakin rijiya ina wanki Umma ta kwala mana kira, aje sabulan hannuna nayi na amsa hade da cewa "Gani nan zuwa Umma.
Ina zama Mimi ta shigo salo-salo Umma tace." Kun San abunda yake faruwa kuwa."? Girgiza kaina nayi, tace" A cikin Ku Wa ya tab'a furtawa Kalmar so." Nace"Umma waye." ? Hararata tayi tace"Wanda kuka sani mana." Kaina sai ya daure kawai domin ban fuskanci abunda take nufi ba."
Tace"Ke ya baki KUDI hade da yi miki shopping ke kuma ya baki waya, shine nake tambayar wacece a cikin Ku ya taba cewa wance ina son ki,saboda yau ya bujoro mana da bukatar son ya aure Ku duk Ku biyun."
Das!das! Haka gababa ya dinga fad'uwa, baki na rawa nace"Umma ban...ban fahimce ki ba." Mimi ta kalla tare da fadin"Ke dai nasan kin fahimce ni ko."? Mimi ta gyad'a kanta tare da fadin"Na fahimce ki Umma a gaskiya ni dai Kalmar so bata tab'a hadani dashi ba sai da ko ita Asma'u. " harara na banka mata nace"Ki fad'i gaskiya dai ko kinyi maganar aure dashi amma ni meye shafe ni da har zai ce zai aure mu ni dake, babu wata kyakyawar alaka mybe ma duk abunda yayi min saboda kene, Umma ni kam babu abunda ya shiga tsakanina dashi Mimi yake so." Na fada raina a bace. "
Umma tace"Yanzu dai ya turo Aminu da sako saboda haka sai kuje Ku sasanta kanku."
[11/5, 7:40 AM] .: Tab'e bakina nayi na mike hade da barin gurin. Wankina na cigaba da yi ina tunanin al'amarin lallai ma, wai yana so ya aure mu ni da Mimi kiji sai kace Wanda aka ce masa mun rasa majin aure aiko sama da kasa zata hade bazan aure shi ba, Mimi taje ta aure shi, ni gani nake ma kamar da wata manufa ya shirya hakan
Ina kallon Mimi ta futo salo-salo ta shiga dakinmu kallo na bita dashi ina tab'e bakina nace"Kin had'u da aiki babba a rayuwar ki, Ya Aminu ne naga ya shigo cikin gidan da sauri hannunshi rike da wayar Mimi ya nufi dakinmu, babu wayar ya futo, da alama shi yake kiranta. Zuciyata naji babu dad'i naji ina son inji wace hira suke dashi, daurewa kawai nayi na cigaba da wankina, ina jiyo muryar Mimi k'asa-kasa tana magana...... Kwafa! Kawai nayi cikin zuciyata nace"wannan guy shigowar shi cikin al'amari mu ba k'aramin hatsari bane domin zai iya wargatsa mana zumuncin mu." Sai da na gama tsaf! Sannan na shiga dakinmu ina k'okarin cire kayan jikina Mimi ta kalleni baki na rawa tace." Asma'u kin San meye."? Kai tsaye nace"sai kin fada."
A hankali tace"Wai Amjadu ne zai zo bayan sallahr Isha'i zai kawo mana tsarabar mu." Ba tare da na kalleta ba nace"zai kawo miki tsaraba dai." Har da ke ai." Girgiza kai nayi nace" ni kam bana son komai nashi, ban sani ba ko sai kunyi aure sannan zan daina jin haushin sa." Tace"Waye ya fada miki zan aure shi." Cike da mamaki nake kallonta na kasa cewa komai ma, na cigaba da saka kayansma tace" bazan Iya hada miji dake ba Asma'u, gwara in hak'ura in bar miki shi." Muryar ta na rawa ta k'arashe maganar.
Sai ta bani tausayi mutuka nace"Mimi zaki iya hakuri da ruhin ki Ashe? Zuciyar ki tana mutukar kaunar mutumin nan, idan kikayi haka to zaki jefa kanki a halaka, wallahi in har don ni zakiyi haka, to bari kiji wallahi zan iya sadauakar miki da komai na rayuwata domin ki samu farin ciki, ballanta d'a namiji ki kwantar da hankalin ki, ni ba bakuwar zafi bace, Sam Amjadu baya gabana, a yanzu na bar miki shi zan cigaba da yi miki fatan alkairi har karshen rayuwar ki."
Kuka tq fashe dashi hade da rungume ni sosai take kuka nima sai na tsinci kaina da share hawaye tace"Asma'u kin San Allah sai dai in mutu da sonshi mutukar kika ce baza ki aure shi nima na hak'ura gwara soyayyar shi ta zama ajalina."
Yanda take fad'ar maganar tana shashshekar kuka hade da wani irin Abu yasa hankalina yayi mugun tashi Mimi kuka take wiwi tana dukan k'irjinta hade da fadin"Me yasa zuciyata zakiyi min haka.? Meyasa kullum kike azabtar dani akan son mutumin nan, Asmau da nasan inda zanje in jefar da zuciya ta da najefar na huta da masifa" tana wani irin kuka ta k'arashe maganar.
Hankali a tashe nace"Mimi meye haka? Mai yayi zafi? Kina so ki kashe kanki ne? Kike dukan kirjinki." Cikin kuka tace" Asma'u gwara in mutu akan i n rayu a duniyar nan, kwata-kwata zuciyata ba tayi min adalci ba, Asma'u na san ke Amjadu yake so amma saboda sharrin zuciya kullum sai take fada min karya ne, ni yake so, kinga kuwa wannan zuciyar bata da amfani a gare ni, Tunda tana kokarin sanya min abunda bazan samu ba." Cike da tausayin ta nace" Mimi yaya zaki ce baza ki samu ba, kinga na farko dai mutumin nan ya fad'i kirkin ki da kyawun halin ki kyawun zuciyar ki, ko wannan ma amsa ce ta ki gane cewar yana sonki, ki saka a ranki baki da Miji sai Amjadu insha Allahu zan iya bakin kokarina gurin ganin tabbatuwar auran Ku." Hawaye ne kawai yake zubo mata na sanya gefan zanina INA share mata, da kyar na samu tayi shiru dadin da naji ma Umma ba taji ba yara sun cika gidan suna siyyaya.
*********
K'arfe shida dai-dai ya futo cikin kyakyawan shiri yau, shigar manyan kaya yayi wata lafiyayyir galila ce a jikinshi skyblue dinkin babbar Riga da 'yar ciki taji lafiyayyan sirfani na masu hannu da shuni yau mutumin Ku ya sanya hula inda ta kara futo masa da ainihin kyawun sa hade da kwarjinsa, hannunsa daure da agogo shi mai tsada sai zabbuna na azirfa guda uku a ya tsunsa masu wani irin ado hade da stons kana ganinsu kasan zasu ja kudi, takalmi me gidan ya tsa ne a k'afafun shi kamfanin Gucci Dan Asali yayi kyau har ya gaji inda kasan wani ango, *Ni ko nace ba dole ba za'a tafi neman aure* fuskarsa babu yabo babu fallasa ya futa, bodyguard d'insa suka mike da sauri, hannu kawai ya daga musu ya karb'i key hannun Doh-doh da kanshi ya futo da motar daga inda take mai gadi ya bude masa gate ya futa daga gidan suna daga masa hannu Kai tsaye gidan granny ya nufa, bai shiga gidan ba sai da ya gabatar da sallahr magariba a massalacin dake manne da gidan sannan ya shiga.
Kamilar Dattijuwa na zaune kan dadduma da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallahr ne, zama yayi a kujera Yana jiran ta kammala, minti goma a tsakani ta shafa addu'ar ta, ta kalle shi bayan ta aje carbi tace"Babban mutum." Kallonta yayi cike da mamaki! Tace"Yau dole in kira ka da wannan suna
Wannan kwalliyar ta burge ni sosai don har na fara kishin ka tun kafin kaje inda zaka je." Dariya ya sanya tare da fad'in"Ai kuwa sai da kiyi domin babu abunda zai hanani tafiya Neman aure, auran ma na mata biyu kece ta ukun. Kafin in cika so ta hudun.
Hararsa tayi tare da fadin"Mace biyu ai bata kama ce ka ba kaji da guda daya, ta Isa." Yace." Ba kin ce zaki shiga kauyika ki samo min maganin k'arfi ba."? Zama ta gyara tana kallonsa tace"K'warai kuwa yau a can muka yini nida Iyami ga wani sassak'e can na karb'o maka Wanda za'a dafa shi da jar kanwa ya zama shine ruwan shanka, insha Allahu mai maganin yace zaka koma kamar zaki gurin k'arfi."
Dariya ya kyalkyale da ita Sam! Ya manta da b'acin ran da yake ciki yace." Toum kinga sai in fara Neman aurena da hujja." Mik'ewa tayi tsakanin ta da Allah take fad'in"Ai mutukar zaka diman ci shan maganin matar ka baza tayi takaici ba." Cikin dariya yace." To kawo min na fara sha yanzu ya bi jikina nasan dai already kin had'a min." Tace"Yanzu kuwa a i mikewar da nayi zan dauko maka ne, NASA Iyami ta k'ukkula maka shi a farar Leda kullum ka dinga shan d'aya." Yace" maza ki kawo min uwargina." Bedroom dinta ta nufa, tana tafiya tana kara tisa maganar.
Shi kuwa bayan shigewar ta dariya ya kama yana mamaki wai shi Granny zata bawa maganin k'arfi hummm! Yana zaune ta futo dashi cikin Leda viva sabuwa dal, dauru kusan ashirin ya karb'a yana dubawa, dauri daya ya dauko yana sansanawa, cikin haushi da takaici tace"Meye haka kuma zaka haramtashi fa." Cikin dariya yace." In na haramanta ma ai ni nawa ne kuma ni zan sha." Tace" To fasa dauri daya kasha a gabana." Aikuwa ya fasa hade da zukewa yace." Idan cikina yayi ciwo kece kin yadda." Tace"Na yarda wannan maganin bazai saka ciwon ciki ba sai dai ma ya gyara ka." Yace." Naji to zauna muyi magana dake."
Granny ta zauna kusa dashi.
Yace." Neman aure zanje fa."
Granny tace." Alhamdullahi yau Allah ya kawo ni wannan lokacin. "
Gyad'a kansa yayi yace." Mata biyu zan aura ya kika gani. "
Shiru tayi tana nazari daga bisani tace"Ai Matsalar Ka ce abun ji." Murmushi yayi yace." Kar kiji komai duk zan iya dasu.
B'ata fuska tayi tace"to naji amma dai ta biyun Hafsa ce ko."?
Yace."Wacece Hafsa kuma."? Tsaki taja tace"Kamanta kenan kana so ka hadani da Innar ka kenan? Dama suna cewa sai abunda nace dakai kake yi baka zumunci dasu dukiyarka baka Mora musu sai dai su ji a gari."
Shiru yayi kawai domin shi kanshi ya San baya kyautawa Sam baya ziyartar dangin mahaifiyar sa, sun gani da korafin sun hak'ura dole yanzu ya gyara ko don kada duniya ta zage shi, Granny ya kalla yace." Yanzu yaya kike so ayi. "? Zama ta gyara tare da fadin" Kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar na da kirki kuma tana sonka." Ya mutsa fuskar sa yayi wannan bukatar ta granny baza ta yi wu ba, yace." Kiyi hakuri Granny bana so ayi Abu daga baya azo ana da an sani kin fi kowa sanin halina bana rufa-rufa yarinyar bata yi min ba, zan dai yi kokari gurin ganin naje mun gaisa dasu kuma zanyi musu alkairi sosai."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin "Shikkenan to Ubangiji Allah yayi maka zab'i na alkairi "
"Ameen yace yana kallon agogon dake daure a hannunsa.
Mik'ewa yayi yace." Insha Allahu komai ya dai-dai ta zamu je ki ga kawayen naki ko kuma in ce kishiyoyin naki." Tace",Allah ya kaimu yanzu ma ace dasu ina gaishe su."
Har ya futa ta bishi a bays hannuta rike da ledar magani tace." Ka manta kuma." Shiru yayi yana nazari,hannu ya mik'a ya karb'a sukayi sallama ta koma gida
Mota ya bude ya zura ledar maganin kusa dashi ya zauna sosai hade da kunna motar mai gadi ne ya mik'e da sauri ya bude masa Gate ya futa daga gidan.
Kai tsaye,....... Gidansu Asma'u ya nufa.
*5/November/2019*
[11/6, 5:13 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*
*42*
Yana tafe cikin mota yana sauraron wak'ar Joy mutumin shi, gyada kansa yake da alamun Yana jin dadin wak'ar, sai da ya kusa shiga unguwar tasu ne ya kira Mimi a waya, lokacin muna zaune a tsakar gida bayan mun gama cin abunci muna ta fama da wasu shegun cinna ku da suka addabe mu, dama duk lokacin damuna haka suke futowa a gidan ta cikin ramuka suyi ta cizon mu. Wani ne ya cije ni a hannuna ina ta faman sosawa hade da haska gurin da toch din wayar Mimi neman sa nake in kashe, kira naga ya shigo wayar *Heartbeat* abunda na gani kenan, siririn tsaki naja hade da mik'a mata wayar ta karba hade da tashi daga gurin, Umma ta bita da kallo tana girgiza kanta. Minti uku sai ga ta ta futo da wayar a hannu tana sink'e kai Umma tace "Waye ya kira ki harda barin gurin."?
A hankali tace" Amajad ne, yazo Umma." Sakin fuska tayi tace" To masha Allahu, alamu sun nuna ke yake so, tunda gashi ya kira ki a waya yazo zance maza je ki shirya Ubangiji Allah ya sanya alkairi." Umma ta k'arashe maganar cike da murna da farin ciki.
Mimi ko kunya ta shiga dakinmu da sauri, sai abun ya bani mamaki ganin d'azu take kuka tana cewa ta hak'ura dashi ta barmin amma dubi yanda take rawar kafa saboda zuwan sa. Ni dai shiru nayi kawai, har ta futo Cikin shiri sai zabga kamshi take. Tace"Umma sai na dawo." Umma tace." Ki gaishe shi da kyau kuma ki iya ladabi da biyyaya." Tace"To tana k'okarin futa sai farin ciki take.
Hira muke da Umma sama-sama nake jin ta domin a lokacin bana cikin hayyacina wani irin lami bakina yayi sai kace mace mai yaron ciki haka nake jin wata irin kasala da sagewar gwiwa jiki babu k'wari na shige dakinmu hade da fadawa kan katifa ruf da ciki rumtse idona nayi sam zuciya ta babu dad'i ni kadai nasan abunda yake damuna.
Parking yayi bakin hanya hade da kunna Fitilar wayar sa, unguwar duhu dumd'um!! Sai hasken masu ababen siyarwa dake kan hanya, masu charge masu wanki da guga, masu provision da sauran su, yaji dadin haka domin baya son ya futo har jama'a suka gane shi, wayar Mimi ya kira hade da fada mata gashinan ya iso. Lokacin tana kan hanya. Inda ya Saba parking ta nufa cikin yanayin tafiyar ta tsallaka titi tayi ta isa kusa da motar hade da d'an kwankwasa wa, a hankali ya bude motar tare da haske fuskar ta da wayar hannunshi, sakin Fuska yayi yace." Momy na tafi ta kowa." Mimi tayi wani fari da ido. Yace." Shigo ciki mana." Cike da kunya ta shiga motar ya mai da murfin ya rufe. Kashe ta yake da kallonsa na goggun 'yan duniya, sunkuyar da kanta take tana fadin"Sonka zai iya kashe ni." Cikin zuciyar ta tayi maganar
Yace." Bamu gaisa ba Momyna kunyar ki na bani mamaki tana d'aya daga cikin abunda yasa naji kin kwanta min a raina"
Mimi tayi murmushi yace." Ok ni ne yafi kamata na gaishe ki tunda nine danki. Kinga kuwa dole in nemi albarka." 'Yar dariya tayi sai kace sokuwa, tace"Ina wuni"?
Cikin sangarta yace." Umum!! Nine zan fara gaishe ki." Mimi taji kamar tana yawo kan gaji mare don shauki gaskiya guy nan ya iya love.
Yace." Ya jin dadin ki Monyna hope komai lafiya Lou."
"Alhmdullahi wallahi."
Tafad'a fuskarta dauke da murmushi
"Ina *Asma'u?*
ya tambaye ta kai tsaye!!! Wata irin fad'uwar gaba taji jin ya baci sunan Asma'u.
Bakinta na rawa tace" Tana gida."
"Owk d'azu mun Dade da yayan Ku a waya ina fatan duk kunji sak'ona ni Amajadu zan aure ku dake da 'yar uwarki Asma'u."
Gyada kanta tayi tace"Ya fada ma Umma."
"Masha Allah." Ya fada da murmushi a fuskar sa, shiru na minti biyu sannan yayi gyaran murya tare da fadin" Shikkenan kije gida sai munyi waya, sai ki kira min *Asma'u* itama muyi zance kamar yanda mukayi dake."
Jiki babu k'wari Mimi ta bude mota ta futa, ya bita da kallo had'e da fadin "Kar ki manta fa ki kashe wayar ki, kafin in kwanta ina son jin muryar ki." Mimi taji wani sanyi ya tsirga mata a zuciyarta murmushi ta saki tare da fadin"Insha Allah."
Hannu ya d'aga mata ta tsallaka titi kana ta shiga layin su.
Umma na zaune a inda take tace"Har ya tafi."? Mimi tace"A'a Asma'u yace." A kira masa." Umma tayi shiru cike da mamaki tace." Asma'u Kuma. " daga Kai Mimi tayi.
Ina kwance a dakin ina jinsu sama-sama, domin bacci ya soma hawa kaina.
Ina jin sanda Umma take fadin "Sai kije ki kira ta tana daki."
Mimi ta shigo dakin hade da tsayawa a kaina tana kiran sunana.
Banza nayi mata.
Tace" nasan dai kina ji don yanzu ba lokacin baccin ki bane, kije Amjadu yana kiran ki."
Mik'ewa zaune nayi nace"Uwar me zanyi masa."
Tace"Idan kinje sai kiji."
Yanda ta fad'i maganar na gane taji zafin zagin da nayi.
Tsaki nayi na koma na kwanta.
Tace.don Allah ki tashi kije babu kyau wulakanci."
Ina daga kwance nace"Kin San Allah Mimi babu inda zanje domin ban ga tsiyar da zan masa ba.
Futa tayi daga dakin.
Can naji Umma na kwala min kira.
Mik'ewa nayi da sauri na futo tsakar gidan INA amsawa
Fuskarta a hade tace "kije kiran da ake miki ko ranki ya b'aci."
Shiru nayi raina a bace
Cikin tsawa tace." Ko bakya ji ne."
Nace" Tom Umma" dakin mu na koma na zurmo hijabina na sallah na futo silafas na zura a kafata na futa.
Tsayuwa nayi a waje ina tunanin ko in lab'e a wani gurin ne. ?
Wata zuciyar tace" kije ki kare masa rashin mutumci tunda yazo unguwar Ku.
Aikuwa tafiya nayi inda nasan zan ganshi
Can na hango motar shi kasancewar ya kunna futular motar.
Ina zuwa gurin na buga motar da k'arfi. Budewa yayi hade da haske fuskata da hasken wayar shi, kalon-kalon muka fara ni dashi. Gani nayi ya kauda kansa yana dariya
Haushi da takaici suka kama ni, sai kace mahaukaciya ya tasa ni a gaba yana dariya. Cike da takaici naja tsaki hade da juyawa da niyyar tafiya, ji nayi an fuzgo min hijabi da k'arfi na fada cikin motar.
Jikinshi ya kwanto kaina ya rufe motar hade da sanya mata security, kallonshi nake a tsorace! Naga fuskarsa a mutukar murtuke Yayi bala'in shan kunu irin Wanda bai tab'a yin irinsa ba,
Ya hasko fuskata sosai da wayar shi, Yana kallona tare da ya mutse fuskar sa.
Kauda kaina nake ganin yadda ya dallare min ido.
Hannunsa guda ya sanya ya