Showing 54001 words to 57000 words out of 92177 words

Chapter 19 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

nasan komai, Wallahi i n da nasan haka zakuyi min da ban gayyace Ku brhday na ba, Maciya amana kawai."

Mimi ta mike tsaye da sauri tare da buge hannun Alina dake kokarin kai mata wani sabon marin, tace"Ba Isa kizo har cikin gidana kiyi min iskanci ba, wallahi yanzu zan sanya ayi miki fata-fata a gidan nan."!! Dariya Alina ta kwashe dashi ta daki! Kirjin Mimi tana watsa mata kallon raini tace"Nasan fa komai banza kawai kema da kike rawar Kai kin aure Sugar Boy a banza domin bake ya ke so. Ba ya fi son wancan mutsiya ciyar yarinyar mummuna Asma'u, to Wallahi duk sai nayi maganin maciya amana kawai."
Mimi ta fusata ta d'aga hannunta zata kai mata duka Alina ta goce da sauri ta sanya gwiwar hannunta cike da mugunta ta mangare Mimi ta fad'i kan kujera, takalman ta masu tsini ta cire ta fara dukan Mimi dasu abun. Mamaki, Mimi ta fara kokarin k'watar kanta tana kare fuskar ta, inda Alina ta sanya tsinin takalmin ta ta buga mata a goshi da mugun k'arfi sai jini ya soma zuba, da sauri ta futa daga parlor.Mimi ihu kawai take hade da dafa goshin ta dake zubar da jini duk ya b'ata mata fuska.

Alina kuwa a fusace ta figi motar ta ta fuce daga gidan.
Da kyar ta dauki wayar ya ta fara Neman numbar sa, kira kusan biyar bai dauka ba, gashi dai tana ringing aje wayar tayi tana kuka ta nufi firji k'ankara ta dauko ta Dora a goshinta inda yake zubar da jini gurin har ya kumbura yayi tsini

Alina kuwa tana tafiya cikin motar ta tana tunanin sharrin da zata kulawa Mimi gurin Amjadu. Wayar ta dauka ta fara kiran shi, sai da tayi ringing sau uku ba 'a dauka ba. Ana hudu ne ya d'auka,
Murya sa s tsaye yayi sallama domin ya gane numbar Alina ce.
Wani irin mahaukacin kuka ta fashe dashi, tana fadin "Na shiga uku na lalace!! Hubby naje gidanka sun taru sunyi min duka."
Kasa gane inda maganar ta ta dosa yayi yace." Ke wai meye ne, ina da uziri yanzu."
Alina tana gursken kuka tace." Asma'u da matarka Mimi ne sukayi min dukan mutuwa Yanzu na ina kan hanyar zuwa hospital."
Cike da mamaki yace." Me kika yi musu? Kuma me ya kaiki gidana." Cikin kuka kamar gaske tace"Kasan munyi skull tare dasu sai ince maka gurin zaman mu d'aya dasu, dake ban samu damar zuwa bukin ba, sun gayyace ni, shine naje nayi musu Allah ya sanya alkairi Asma'u tazo gidan ,shine suka taru suka dinga dukana."

Kashe wayar yayi saboda tsabar takaici, Alina ta fashe da dariya tana draving tace"Shegu 'yan iska ai tunda bani na aure shi ba, sai na hada muku sharri a gurin sa, wayar sa ta kara kira yana kallon kiran yak'i dauka.
Tunani yake wato bayan futowar shi daga gida Asma'u taje gidan shi, yasan duk abunda Alina ta fad'a Asma'u zata aikata sun mayar masa da gida sansanin yak'i baya ganin laifin kowa sai na Mimi gani yake Asma'u ce take murza akalar ta, sai abunda tace da ita sannan take yi,
Wayarsa ya dauka ranshi a b'ace! Sai yaga kiran Mimi kusan sau shida, lallai zancan kenan, bugu daya wayar tayi Mimi ta d'auka tana shashshekar kuka.
Wata irin tsawa ya buga mata tare Da fadin"Babu babban mai laifi sai ke Momy menene zaku Tara mata a gidana kuna fadace-fadace sai kace wasu yara, na lura sai abunda Asma'u tace kiyi kike yi ko."!!
Mimi ta tsananta kukan ta tana so ta fahimtar dashi amma Sam yak'i sauraranta masifa yake mata.
Daga k'arshe yace." Kafin in dawo ki sallami Asma'u domin baza ta zo gidana tana tada min da fitina ba."
Kashe wayar yayi bai bari tace Komai ba.

Mimi rasa abunda yake mata dad'i tayi goshinta ya suntume yayi tsini ga zugi yana yi mata, ta lailaiya shi, duk da haka babu sauki, kwamciya tayi kar kujera tana kuka tare da tunanin maganganun Amjadu da inda suka dosa, wanene Ya sako Asma'u cikin case din gidan sa, da zai kama fad'ar bakaken maganganu Sam ya maki tsayawa ya saurari maganar ta.

Wayar ta ta d'auka ta nemo numbar Asma'u lokacin ina kwance kam katifa sai juyi naje yi yanzu har na saba da kwanciya ni kadai a daki, k'atuwar waya tace a hannuna wacce Mujahid ya kawo min ita shekaran jiya, yanzu ka chat muke dashi sai dariya nake ni daya.guy ya iya zuba kalaman soyayya ina so ayi ta nuna min so, ina tsaka da bashi amsa kiran Mimi ya shigo cikin wayata
Da sauri na daga wayar murya ta a sake nace"Mimi yane."? Kuka ta fashe dashi! Nayi saurin mik'ewa zaune tare da fadin "Menene."? Tace." Asma'u Alina yazo har gida tayi cin mutumcin har da su duka da mari baki ga yanda ta fasa min goshi ba." Kai tsaye nace"Zata ai kata abunda yafi haka, tunda naji labarin cewar haukane kawai bata yi ba, da ta samu labarin d'aurin Ku.
Yanzu ke wane mataki kika dauka."?
Cikin kuka Mimi tace"Asma'u kin San dai halin Alina da sharri da kitifi shi kan shi Amjadu ta hada ni dashi, baki ga yanda ya bugu min waya ba yana cimin mutumci har dake a ciki."

Shiru nayi ina mamakin maganar ta yo ni me ya kawo ni cikin sabgar su, idan ba Neman fitina ba, meye alakata dasu ina gefe guda.
Nace "Mimi kar ki kara Bari wata 'yar iska tazo har cikin gidan ki ta doke ki kuma duk sabda Alina ta kara zuwa gidan ki kira ni a waya, Wallahi sai taci kutumar ubanta."
Mimi tace"Shikkenan ni kaina nayi kokarin k'watar kaina ta samu rinjaye a kaina. " tsaki naja cike Da takaicin ta da jin haushin ta nace"Banza kema babu abunda zaki iya sai aukin kuka idan zaki d'age ki kwatarwa kanki 'yanci ki zage ki kwata."
Ina gama magana ta kashe wayar cike da jin haushin Mimi domin duk shashancin ta ne, mace tazo Har cikin gidan ka ta doke ka, lallai Alina tayi kaurin suna.


Ko da ya dawo gidan ma fad'a sosai ya dinga sirfawa Mimi har ta dinga mamakin dama haka yake da fad'a kuka take tana bashi hakuri, bedroom d'insa ya shige cike da b'acin rai.!
Wanka yayi ya futo daure da towel me girma zama yayi gefen bed ya dauki lopto dinshi yana dubawa.
Mimi tayi sallama simi-simi ta shigo dakin. Ba tare da ya d'ago kansa ba ya amsa mata sallamar, hankalinsa nakan loptop dinshi.
Zama tayi kusa dashi jikinta a sanyaye!
Da gefan ido ya kalleta yaga goshinta s kumbure d'ago kansa yayi yana kara kallon gurin, shi Sam bai lura da gurin ba
A ya mutse yace." Kin ce Alina karya take muku ga shaida nanan a goshin ki alamun kun daki juna da ita."
Shiru Mimi tayi saboda ita yanzu bata son a kara maganar.
Tsaki yaja abunsa ya cigaba da duba loptp dinda
Mintin goma sha biyar ya aje ta gefan bed din, ya kamo Mimi tare da rungume ta a jikinsa.
Goshin ta ya kama ya sanya karfinsa sosai ya hau mulmulawa, kuka take sosai, sai da ya tabbatar gurin ya koma sannan ya sake ta, tare da fadin"Idan har kin San Asma'u zata dinga zuwa gidana tana hada min husuma da tashin hankali tom kice mata inji ni bama Neman ta tayi zaman ta inda take, ina laifin Alina don tazo taya ki murna. Kawai sai Ku hauta da duka sai kace marasa hankali, nasan sharrin duk ba na kowa bane sai na Asma'u."

Cikin dauriya Mimi tace"Wai Alina ce tace maka har da Asma'u? To wallahi karya take tsabar sharrinta ne, tun ranar da Asma'u tazo gidanan bata kara zuwa ba." Yace." Dole ki kare ta dama saboda kar ta tsigale ki, ni dai na fada miki ki kiyaye." Cikin kwantar da Kai tace shikkenan Insha Allah haka baza ta kara faruwa ba."
Kwanciya yayi kan bed din yana lumshe idonsa, ita kuma ta tashi jiki babu k'wari ta nufi toilet wanka tayi ta futo salau-salau ta bude wardrobe kayan baccin ta ta dauko ta sanya Riga da wando ne amma irin masu santsin nan, a hankali ta nufo bed din, ta kwanta gefan sa.
Gogan Ku kuwa k'amshin turaran ta ya dame shi, abunka da mayen turare nan take ya jawo ta a zafafe ya hau ya mutsa ta, yanzu Mimi ta saba da jarabar shi, haka ta hak'ura yana ta murza mata nonowa yana wasa da joystick dinshi a gurin. Mimi Sam bata iya komai ba, ta dinga kauda kanta kenan wai ita kunya shi kuma ya dinga buga mata tsaki da harara ya na nuna mata inda zata tab'a masa, idan taki sao ya dau hannunta ya d'ora a gurin.da kyar take kamawa take masa wasa, inda yake sakin wani irin nishi na dad'i
Haka suke rayuwar sai tayi wuta sannan zai yi sex da ita amma yana samu ya kawo sai daya yake rabuwa da ita.


*******

Tsaf ya futo cikin shiri yana sanye da wasu suit blue and white wanda suka yi masa kyau sosai komai na jikin shi kalar blue da white ne, sai kamshi yake Mimi na binsa a baya idanunta duk sun kode da kuka, wai tafiya chana zai yi dagan ya wuce Ingila kuma yak'i Sanar mata da ranar da zai dawo, shine ta damu.

Hannunta ya rike sosai yace." Momy kiyi hakuri kinji ko, ki kwantar da hankalin ki, granny zata zo ta taya ki zama har in dawo babu matsala cikin tafiya dama nasa ba lokaci zuwa lokaci." Mimi ta fashe da kuka hade da rungume shi, da kyar ya cire ta daga jikinsa ya futa daga parlor cikin sauri bodyguard d'insa suka rufa masa baya.

Zubewa tayi tsakiyar parlor tana wani irin kuka ta ina zata fara rayuwa a cikin gidanan ita d'aya ko sati biyu bata cika ba an tafi wata uwa duniya an bar ta, kuka take sosai.

Mimi tafi a wa gudu a gurin tana kuka daga bisani ta mike jikinta babu k'wari ta shiga bedroom dinta wayar ta ta dauka ta kira Asma'u.

Ina d'aukar wayar naji ta fashe da kuka, tsaki naja da k'arfi nace"Wallahi Mimi Matsalar ki ta fara isata da me zanji ne? Da karatun ko da Matsalar ki, kullum sai ki kira ni kina min kuka, ke baza ki iya gyara Matsalar ki da mijin ki ba."?
Da shashsheka tace"Asma'u yayi tafiya ya barni kuma yak'i fada min yaushe zai dawo." Tsaki naja a karo na biyu nace"To sai me."? Kiyi zaman ki mana." Tace"Yace ma kakar shi zata zo ts taya ni za ma." Nace"To kin huta ai amma don Allah ki daina Wannan kukan da kike yi bashi da amfani."
Mimi tace"Habibty Wallahi kwana biyu bana jin dadin jikina kullum bana iya cin abunci ga jiri da tashin zuciya ina ji." Nace" kinji asibiti ko kin San dai kina da maleria." Tace." Banje wallahi, amma don Allah gobe kizo muje ki rakani." Nace" Allah ya kaimu, yanzu kakar tashi tazo ko kuwa."?
"Tana kan hanya." Nace "Shikkenan Allah ya sawake don Allah ki kwantar da hankalin ki." To tace mun na kashe wayar.
Munnu ta kalle ni tare da fadin "Bata da Lafiya ne." Nace"Wai zazzab'i take ji da jiri. "
Munnu tasa dariya tare da fadin"Shikkenan Mimi ta hau network sai fatan sauka Lafiya. "
Take naji wani muguwar fad'uwar gaba, na kalli Munnu cikin mamaki nace"Ciki."? Munnu na dariya tace"Eh mana wallahi ko kaffara bazan yi ba Mimi ciki gare ta, kinsan ranar d'aurin auran ta tayi wank ma tsarki kin manta har su Maryam suka dinga tsokanar ta, tana shiga zatayi gamo aikuwa gashinan. "
Rasa miyau nayi a bakina ya bushe Kama's gashi babu wani tes ko na kwabo jikina yayi sanyi sosai Wahidun k'ahar Allah mai barwa da hanawa..........








*19/11/2019*
[11/20, 10:07 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*57*




Munnu ce kawai take surutun ta i ta kad'ai ni kam ina can duniyar tunani lamarin ubangiji wai Mimi har tayi ciki zata haihu, Allah babu yanda baya tsara almarin shi. Yanzu Sai dai kawai mu taya ta addu'ar sauka Lafiya, yau sama-sama nake a makarantar, domin na kasa sakewa da abun ya fado min zan ji fad'uwar gaba, ya zama Dole na cire son shi a cikin zuciya tunda yanzu nasan yayi min nisa na har a bada.


******
Ina koma wa gida Umma take min zancan Miki ta kirata a waya wai bata da lafiya bayan haka kuma Mijinta yayi tafiya tace kije ki taya zama."

A tausashe nace"Umma nima munyi waya da ita d'azu ta fad'a min, amma ni dai bata ce min naje in taya ta zama ba, tace kakarshi zata zo ta taya ta zama. Amma dai munyi maganar zan rakata hospital taga dactor. "

Umma tace"To tunda kakar shi zata zo sai kiyi zaman ki, ai na dauka ita kadai zata zauna a gidan."
Girgiza kaina nayi. Mik'ewa nayi na shiga kicin domin wata irin yunwa nake ji.


Washe gari da wuri na shirya Dan ma Allah yasa bamu da lecture a ranan da ko sai dai Mimi ta hak'ura Umma nayi wa sallama na tafi tana fadin 'ki gaishe min ita da jiki. Umma ba yarinya bace ta fahimci Mimi ta samu ciki. Sosai take murna da farin ciki.


A dai-dai ta sahu na samu har gidan Mimi na biya shi kudinsa sannan na tsallaka Titi na Isa jikin gate din inda nake hango masu gadi a zaune, fuskata ba b'oyayya bace a gurin su, nan d'aya daga ciki ya tawo da sauri ya bude min na shiga ciki ba tare da na kalle shi ba na wuce part din Mimi cikin nutsuwa.


Suna zaune ita da granny a parlor suna hira nayi sallama na shiga, Mimi ta amsa tare,da mik'ewa da sauri ta tare ni, kallon fuskar ta nayi sosai naga ta rame amma tayi haske sosai.

Zama nayi kan kujera ina gaida Granny ta amsa fuskarta a sake, take fadin"ai gwara kuje likita ya dubata tun d'azu take amai gashi bata ci komai ba Mimi na kalla dake ya mutse fuska nace"Ina gani ba sai munje asibiti ko in kira Mujahid ya duba ki, ko ya kika gani."

Shuru tayi daga bisani tace"Bari in yi masa waya jiya na fad'a masa zamu je asibiti dake yace." Babu matsala amma yanzu nasan babu abunda zai ce tunda yasan Mujahid din. " Shiru nayi ina kallonta na dauki wayarta tana kiran sa, ina ji sai da tayi ringing sai biyu ana ukun ya d'aga muryar da da alamun bacci da gajiya naji yana fad'in"My wife kin tashi Lafiya ."? Mimi tace." Lafiya Lou Alhmdullahi nayi ta kiran wayar ka, tun d'azu baka dauka ba."
A hankali yace." Bacci nake Momy nayi aiki na gaji."
Mimi tace." Dama Asma'u ce tace ko Dector Mujahid za muyi wa magana tunda likita ne ba sai munje asibiti ba."

Tunda Mimi ta fara magana naji kamar in tashi in fuzge wayar daga hannunta in kwad'a mata mari, Mimi wata irin sukuwa ce da bata da wayo.

Nashi b'angaran kuwa Mik'ewa yayi zumbur ya wani hade fuskar sa tam! Yace." Bani Asma'u muyi magana da ita."

Wayar ta mik'o mun da sauri na bi hannunta da kallo, Idanun kakar shi ya sanya na karb'i wayar raina a b'ace.!


A hasale yace." Ke kar ki kuskura ki gayyato min wani gardi cikin gidana, wai da sunan yazo duba wife dina, saboda rashin hankali irin naki. Wallahi sai na b'ata miki rai, mutukar kika shigo min da saurayin ki gida, ki kaita Asibiti a duba ta ko nawa ne a kashe amma ban yarda da wannan iskan cin ba."!!

Shuru nayi INA saura shi yanda yake wani magana a zafafe nace k'ila da yana kusa duka na zai yi.

"Kinji ko baki ji ba."! Yafad'a cikin tsawa! Raina ya b'aci sosai amma ganin granny dake zaune idanunta a kaina yasa nace " Naji." Tsaki yaja ya kashe wayar sa.


Mimi ta karb'i wayar jikinta a salube domin da ita da granny din duk sunji irin tsawar da yake buga min.

Granny tace"Rabu dashi don Allah kinji Ina ce shi Mujahid din abokinsa ne kuma makocin sa, ne don zai taimaki iyalinsa sai ya hana kan wane dalili."?

Tace 'kira shi a wayar yazo ya duba ta Allah yasa bai futa aiki ba." Nace"A'a tunda yace kar ayi to a barshi granny kibar maganar Mimi ta tashi kawai muje a sibiti kamar yanda ya fad'a."


K'wafa tayi tace"Sai kuje Allah ya tsare nasan dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki Allah ya raba Lafiya sai kun dawo."
Ta fadi maganar tana gyara zaman ta cikin kujera.


Abun mamaki muna futa sai ga motar Mujahid ya futo, tsaf cikin shirin futa aiki.
Da sauri ya tsayar da motar kusa damu, fuskarsa a sake ya leko da kansa yana yi min wani irin kallo na so yace." Me yasa baki fada min zaki zo ba."?


Murmushi nayi kurrum, dauke kansa yayi ya kalli Mimi tare da fad'in"Madam yane da'alama babu Lafiya domin ga alamu nan na gani."


Nace"Aikuwa asibiti zamu je." Murmushi yayi yace." Shine baki Sanar da ni, ba, Ku shigo muje." Nace"A'a kaje kurrum." Fuskarsa ya b'ata yana kallona yace." Bana son gaddama Asma'u don Allah Ku shigo mu tafi."


Mimi da tsayuwa gurin ta gagare ta saboda jiri ta bude motar da sauri ta shiga, kallon ta. Nayi ina girgiza kaina, saboda kar ya fuskanci wani Abu yasa na bude motar na shiga na zauna kusa da ita yaja motar muka tafi

Rambo da doh da suke tsaye suna kallon duk abunda yake faruwa suka koma gurin zaman su, dama sun taso ne saboda su cika umarnin ogan su.


Rambo ya dauki wayarsa ya fara Neman numbar ogan shi. Bugu guda ya dauka, inda yake akwai hayaniyar mutane yasa yace da Rambo ya kashe wayar zai kira shi anjima Rambo ya kashe wayar kamar yanda ya fad'a, doh yace." Tunda ka kira zaka yi masa bayani ya kawo uziri shikkenan nasan ko kayi masa baya ni daga baya zai gamsu, Rambo yace." Ni tsoron fad'an mutumin nake ji, akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login