Showing 66001 words to 69000 words out of 92177 words
Chapter 23 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
anyi anyi dani kan na dawo gidan da zama har Mimi ta haihu naki ya Umma ma babu yanda bata yi dani ba, Amjad da kanshi ya turo Jahid gurina wai ya rarrashe ni naje na kula da Mimi fafar naki nace nima makaranta, lokacin mujahid har fushi yayi dani ya daina kirana a waya, kwana uku, nima shareshi nayi na cigaba da sabgata, da yaga Uwar bari ne yazo har inda nake ni kuma a lokacin na butsare masa sai ya dinga bani hakuri muka cigaba da sosyayar mu Cikin aminci da yardar juna.
****
Tun da watan azimi ya kama yake zurga-zurga har sai da ya tabbatar komai ya kammala ta fannin company shi sosai ake aiki tare da fidda kaya samfura iri-iri abun sai son barka sosai jama'a suke tsallakowa daga garuruwa suna zuwa d'aukar kaya.
Yaduka na mussaman ya sanya company ya shirya masa mai manyan zane ko wane kusan bandur dubu aka futa dashi gidanan yari(prison) bayan nan ya sanya aka futa da bandura na tampopi aka dinga shiga kauyi ka ana rabo, hatta da takalma sai da aka futa dasu aka rabawa mabukata.
Farkon wata kenan tsakiyar wata ma haka ne ya kasance, karshen wata ma haka.
Addu'a da fatan alkairi babu irin Wanda bai sha ba abakun mutanan gari
Yau saura kwana bakwai sallah.
Muna ta shirye-shiryen sallah. Lokacin Cikin Mimi ya futo sosai tunda yana matakin watanni shida tayi kiba sosai sa sosai kuma ta kwantar da hankalin ta.
TV muke kallo inda muke kallon tafsiri daga bakin Marigayi shak Isa Waziri Allah ya jikansa.
Kawai. Umma ta kunna redio murya wani shararan Dan jarida muka ji yana fadin"Salamu alaikum jama'ar jahar kano, labari da dumi-dumin sa, an yaka dai ta tashi yanzu-yanzu muka samu labari daga majiya me k'arfi shararar mutumin nan Wanda yayi suna a jahar kano, wato *Young millionaire Amjadu Abul Abbas mai nasara* wato mamallakin wannan shararan company me kawo muku nauin kayan sawa kama daga atamfoffi yadiga lesuka mayafai dogwayen riguna bulawus kayan yara hijab da sauran su, wannan company mun samu labari yanzu yanzu daga bakunan wadanda suke sari a cikinsa, cewa company ya hada baki da yahudawa nasara masu yak'i addinin musulunci masu adawa da fad'ar Annabi Allah wato Annabi Muhhamadu Slw a takaice dai an samu jikin takalman da company ya ke kerawa kasan takalmi an rubuta sunan Allah da manzon sa wato Allahu Muhammad, Jama'ar gari me zaku ce da wannan shirkar da wannan yaro da kuka amunce masa ya aikata.""
"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un shine abunda Umma take fad'a, take ta fashe da kuka tana gyda kanta take fad'in" Wannan zan sharri ne tswagaran sa na tabbatar yaron nan bazai aikata wannan danyan aikin ba."
Nima jikina wani irin shocking yake jin abunda Dan jaridar yaje fad'a, Cikin zuciya ta nace"Anya kuwa guy nan zai aikata Wannan Abu, duk da dai nasan Duk ak'idun shi na nasara ne kuma Duk yawanci abokan shi turawa ne, wata zuciyar tace min tabbas zasu iya rinyarsa dama ba wani tsoron Allah yake ba, tunda yana aikata zina." Kuka Umma take yi sosai da sosai Ya Aminu ya shigo gidan hannunshi rike da Leda me zane-zane da Lemo da a yaba a ciki.
Ganin Umma na kuka ya tabbatar labari ya same su
Umma tace"Kaji sharrin da jama'ar gari sukaiwa wannan yaron mijin Mimi ko."?
Ya Aminu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya yace." Duk naji Umma gashi can ko ina ana surutu zancan ya cika gari.
Matasa sun fara gazgatawa domin wani Dan kasuwa ya futo da takalma na company an duba an ga gaskiya al'amarin.
Umma tace." Karya ne sharri ne aka shirya masa ni na tabbatar.
Ya Aminu yace." Umma sai ta iya kasamcewar gaskiya ne Wallahi mutane da basa tsoron Allah, ni dama wannan uban kud'in sa suna tsorata ni, akan ya samu duniya babu abunda ba zai yi ba."
Nace"Wallahi Ya Aminu nima na gasgata saboda d'abi'un sa duk na turawa ne.
Gaskiya gomnati ta shiga maganar kuma kamata yayi a dauki mataki akan sa, domin Allah da manzon sa ba abun wasa bane."
Ya Aminu ya bude baki zai yi magana kawai mukaji ihu!!! Da hanayi ana gudu radadada!!! Da gudu nayi waje ya Aminu ya biyo ni a baya.
Gungun matasa majiya k'arfi ne suke tada k'ura ko wanne hannunsa rike da makami wasu jarkar fetur da kalamzir da tayoyi suna fadin "Billahillazi sai mun k'one company mu zai yaudara! Sai mun konashi mu kashe shi!! Mu kashe banza."!!!!!!!!!
D'uuuuuu suke wucewa sunfi su Dari ga magariba ta gabato ana shirye-shiryen shan ruwa
Umma ta tsorata mutuka fad'i take" Asma'u maza buga wa Mimi waya ta tawo gida innalillahi wa'ina ilahi raji'un. " Jikina na kyarma! Na koma cikin gida zuciya sai harbawa take yi mutukar wad'annan matasan sukayi arangama dashi to babu shakka sai sunga bayan sa, hannuna na rawa nake Neman numbar Mimi, kiran duniya taki shiga. K'afafuna na rawa na futo in na fadawa Umma halin da ake ciki.
Hannunshi rike da jarida yake zagaye parlor bashi, Rambo da doh Mimi da granny duk suna tsaye suna tararrabi da al'ajabin wannan Abu.wayoyinsa kuwa tuntuni ya sanya rambo ya kashe su, saboda a halin da yake ciki magana ma bazai iya yi ba. Shin wai me ya tsarewa mutane ne a duniya.?
Granny kuka take yi tana fadin"Wannan kaddara da masifa Allah ka ije mana ita, Ubangji kaga zuciyoyin mu bamu aiktaba Allah ka tona asirin masu San su ga bayanmu.
Granny ya rungume a jikinsa yana d'an dukan bayanta da hannunshi ya ma kasa cewa komai, idanunsa sunyi wani irin jajazur! Tsabar tashin hankalin da yake ciki.
Tv suka k'urawa ido inda suke ganin jama'ar gari kofar company sa sune turareniya da rigima da masu gadi kan lallai sai sun shifa ciki wasun su kuwa tuni sun soma k'ona tayoyi suna watsa fetur da kalanzir jikin company, ihu! Da hayaniya ya cika gurin, 'yan jarida sai dauka suke yi. Tuni wani tsagera daga cikinsu ya k'yatta ashana ya yi wani tsalle hade da jefa ashanar sama, kafin k'iftawa da bisimillah wuta ta kama fa!fa!fa! Jikin gatangun company har ta soma haurawa ciki, hucin wuta yasa jama'a darewa kowa na gudu domin ceton ransa, ciki kuwa har da masu gadi.
Tuni matasan suka samu damar shiga ciki kasancewar gurin ya hargitse kowa na ceton ransa.
Take 'yan jarida suka rufa musu baya domin dauko rahoto.
Lungu da sak'u ko ina sai da suka bi suka watsa fetur ko zafin wuta basa ji, da gudu ma'aikatan suka dinga futowa suna kama Katanga suna haurawa domin ceton rayukansu, ganin yanda wuta take ci ne ba!ba!ba! Yasa 'yan jaridar dasu matasan suka dinga gudu suna kama Katanga suna dura kasa, duk da haka wasu sun jikkata kuma sun k'one cikinsu sudai kawai burin su ya cika ganin sun rusa company.
******
*"Hahahahahaha"* wata mahaukaciyar dariya na juyo a ofis din me girma governor, da sauri na lek'a ta k'afar mukuli, na gansu sun fi su goma zaune Cikin kujeru tsakiyar su kwalebe ne da cup reras kan wani makeken teble. Mai citta ya dauki abunda yake cikin cup din gaban sa ya kurba tare da ajewa fuskarsa cike da annuri da farin ciki, naji yana fadin"Shegen kaya! Wa yaga masa barno gabas take! Ai sai ya daina motsi a duniyar nan sannan zamu saurara masa."!! Dariya suka shek'e da ita "Hahhahahahahaha."!!!!
*****
Har aka sha ruwa yana tsaye a tsakiyar parlor babu yanda granny bata yi dashi ba kan yazo ya karya yak'i kamar ma kurma ya zama Wanda baya ji ba ya gani, kawai ya zubawa guri guda ido .Su Kansu Rambo da doh-doh sun tausayawa masa.
Mimi na kuka tazo ta rungume shi tana rarrashin sa, da sauri ya juyo jin tsinin cikin ta yana zungirin shi a bayan sa.
Tsungunawa yayi ya kasa kunnesa cikin NATA yana lumshe ido.
Kamar wani zautacce ya d'aga rigar ta yana shafa cikin nata, a hankali yace." My boy ina cikin damuwa!!!! Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Kalmar da ya kamata ya fad'eta tun farko fara abun bai fada ba sai yanzu Allah ya bashi iko.
Mimi kuka granny kuka an rasa me rarrashin wani a cikin su.
Wata irin hayagaga! Da hayaniya! Suka ji ta cika gidan.
Zumbur! Ya mike yana niyyar futa
Rambo da doh-doh suka dakatar dashi da sauri suka futa.
Gungun! Jama'ar gari suka hango suna kokawa da masu gadi dole sai sun shigo Estate din......... Rambo ya koma ciki da sauri yana fadin "Sir babu lafiy!... Kafin ya rufe bakin sa saga Mujahid da Khalid sun shigo da sauri. Mujahid yace." Meye abun yi ne? Idan fa suka shugo gurin nan zasu yi barna domin dukanin su 'yan daba ne da 'yan Sara suka."!!! Amjad yace." Ni suke nema baku ba, zan futa su kashe ni kan abunda ban aikata ba."
Da sauri yayi nufin futa. Mimi tq buga wani irin ihu!!! Da gudu tayo kansa tana fad'in"Kar ka futa su kashe ka."!!!!!!!!! Hannunta ta mik'a tana son rik'o shi santsin tayal ya kayar sa ita ta fad'i a kan cikin ta hade da sakin wata razananniyar k'ara!
Hankalin su duk ya koma kanta suna salati,
Hakan ya bashi damar fucewa da sauri! Ba tare da ya juyu yaga me yake faruwa ba.
*23/11/2019*
[11/24, 12:07 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*61*
Wani irin nishi! Mimi take yi idanunta na lumshewa yayin da bakin ta yake motsawa tana so tayi magana amma babu hali hannunta biyu tasa ta damk'e cikinta dashi da kyar ta fad'i"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Sharaf! Ta zube a jikin granny.
Rungume ta tayi ta fashe da kuka hade da d'ago kanta tana Neman Amjad, wayam babu Shi a gurin, da sauri ta kalli Mujahid murya a sark'e tace" Ya futa shima zasu kashe shi."!
Dukaninsu hankalin su ya dawo jikin su, take suka fara rige-rigen futa, suna salati.
Granny kuwa rungume Mimi tayi tana kuka duk basirar ta ta toshe a lokacin.
Yana futa ya hangosu sun samu nasarar shigowa, ciki dake akwai tazara mai mugun tsayi kafin su gurin shi, sai suka yanko da gudu suna ihu!
K'ik'am ya tsaya had'e da hard'e hannunsa a kirjin sa yana jiran k'arasowar su.
Mujahid Khalid da Su Rambo sun tsorata mutuka suka fara Jan rigar shi.
Fuzgewa yayi a zuciya! Yace. " Ku jira Ku ga abunda zai faru, wallahi duk Wanda yazo gurin nan to sai dai Uwarshi ta haifi wani."
Ja da baya suka yi cike da tsoro! Fito yayi sai ga DOG dinshi ya shek'o a guje! Yana wani irin haushi!!! Magana yayi masa da ido. Aikuwa sai ya buga wani uban tsalle ya tunkari su yana wani danbanzan zufa ya cafki k'afar daya daga cikinsu sai da ya huda ta tukkuna ya sake shi. Kafin kace kwabo ya fad'i a gurin yana nishi ga jini ya fara zuba.
Wani tsagera ne ya kawo sharb'eb'iyar wuk'ar zai dab'a masa, da sauri yayi sufa ya datsa masa hak'oran sa a fuskar sa, dai-dai hancin sa, ya yago Innalillahi sai ga rabin hancin sa da naman kumatun sa a bakin DOG din. Kwanciya yayi a gurin yana ihu! Shi kuwa Amjad nad'e hannun Riga yayi ya tunkare su, yana wani zare idonsa!
Tsoro ne ya shige su dukanin su ganin yanda dog din yake barna har ya jikkata mutum biyar gasu nan a kwance a gurun.
Take suka fara guduwa domin ceton ransu.
Amjad ya buga musu wata irin tsawa! Tare da fad'in"Ku tsaya mana ku kashe ni kamar yanda kuke bukata."!!! Ko juyo wa basu yi ba, gudu kawai suke su Isa bakin gate.
Daga murya yayi sosai Wanda sai da gurin ya amsa yana magana da masu gadi cewar maza su rufe gate din nan, kar su bar kowa ya futa."
Aikuwa suka mike da kuzari suka ja gate din da k'arfi suka datse
A nutse yake tafiya hannunshi goye a bayan shi, fuskar sa a murtuke ya k'araso gurin su: One by one yake kallonsu tsawon five minutes, murmushi yayi mai ciwo yayi gyaran murya gami da gyad'a kansa har sau biyu murya sama! Yace." Kun shigo da shirin aika ni barzahu ko."? Shiru su kayi suna muzurai! Gefe guda kuma ga *Tegar* na wani irin haushi!!!!! Shiru suka yi........ Ya cigaba da cewa"Zaku kashe ni kan abunda kuke zargina dashi, Wanda ni nasan ban aikata ba hakane ko ba haka bane."?
Sunkuyar da Kansu suka yi cikin mutuwar jiki. Girgiza kansa yayi cikin takaici da tsabar bakin ciki yace." Gani ga ban Ku Ku kashe ni, ni Ku kashe banza kamar yanda kuke fad'a. "! Tsit! Suka yi.
Yace." Duk Ku aje makaman hannun Ku."
Aikuwa suka aje da sauri!
Yace." Kuna so Ku kashe ni Wanda baku San in kuka aikata haka ba, to babu shakka hukuma zata dauki mataki akan Ku, tunda ba ita ta sanya Ku ba,hakane ko ba haka ba."
Duk suka ce "Hakane."! Yace." Duk abunda kuke zargina dashi ban aikata ba, sharri ne kawai, akai mun. "
Shiru suka yi ya cigaba da cewa"Kuma Ku zuba ido zaku ga irin hukunci da za'a dauka a kaina, tunda dai kun k'one company na kunji dad'i shikkenan, amma babu shakka sai na binciko Wanda aka had'a baki dasu aka kullamin wannan k'azafin." Duk sai suka ji jikin su ya mutu, take suka zube suna bashi hakuri.
Murmushi yayi yace." Ba wai na fad'a muku Wannan maganar ba ne domin Ku yarda da ita, A'a duk wani hukunci da zaku yanke kaina Ku yanke Ku kashe ni ku kashe banza."!
Ya fada da wani murmushi a fuskar sa, na tsantsar takaici.
Hakuri kawai suke bashi cikinsu kuwa har da masu kuka saboda tausayin sa. Yace." Mutukar nakama mutanan da aka hada baki dasu cikin ma'aikatana tom ni da kaina zan hukunata su da kaina in yaso nima a kashe ni saboda kishin Allah da manzon sa." Ya nagama maganar shi ya juya bayan ya bada umarnin a bude musu k'ofa su futa.
*Tega* ya bishi a baya Yana shinshina m asa jiki: Wani irin salati Granny take yi,lokaci kank'ani jikinta ya kama rawa ganin wani irin jini yana malalowa k'asa daga jikin Mimi.
Kuka ta fashe dashi tana salati ta janye Mimi daga jikinta
Ta mike Da sauri ta nufi kofar futa.
Karo suka buga dashi ya shigo.
Hannunsa ta rike takasa cewa dashi komai sai dai nuna masa gurin da Mimi take kwance take.
Da sauri ya kalli gurin, jini duk ya kwaranya kan tayal din gurin. Wani irin ihu! Ya kurma! Ya saki granny da gudu ya k'arasa gurin Mimi ya dauke ta kamar zautacce yake kiran sunan ta"Momy na."!!!!!!! Ina Mimi bata San wace duniyar take ciki ba, da gudu ya futa daga Palo, mota ya nufa da gudu su Rambo dake tsaye suka bishi, Mujahid ya bude motar da sauri ya shiga mazaunin dravar, jiki na rawa Rambo ya bude masa mota ya shiga rungume da Mimi a jikinsa jini duk ya b'ata shi har ila yau bai daina zuba ba.!!
Da gudu Jahid ya figi motar masu gadi suka bude gate din tun kafin motar ta karaso. Wani irin gudu Jahid yake yi kamar zasu tashi sama, Allah yasa titi akwai saukin motoci kasancewar kowa na gida an sha ruwa an gaji wasu kuma na massalaci suna sallahr tarawi.
Rungume da Mimi yake yana tofa mata duk addu'ar da tazo bakin sa, wasu zafaffan hawaye ne su ka fara zuba a kuncin sa Amjad jarumi ne da kafin kaga kukan sa a duniya sai ka manta ko da iyayansa suka mutu bai yi wani kuka ba, yanzu tsananin tausayin Mimi da irin azabar da take sha akan soyayyar sa yasa shi zubar da hawaye masu zafi, matseta yayi sosai a jikinsa yana tuno maganar ta ta d'azu lokacin da zai futa *"Kar ka futa su kashe ka."!!!!* Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Abunda ya fada a fili kenan hawaye na zubo mishi wato shi irin tashi kaddarar kenan.
Tun kafin su karasa hospital din Jahid ya kira waya cewar su futo da gado ga emergency nan, aikuwa suna shiga ciki da sauri wasu mata ma'aikata suka turo gado na d'aukar marasa lafiya, ya bude motar da sauri ya zagayo ya budewa Amjad din dake ruk'unk'ume da Mimi dake cikin halin rai da rayuwa.
Futowa yayi ko kallonsu bai yi balle ya saurari abunda suke CE masa, Mimi na rungume a jikinsa ya wuce su. Dr Jahid ya bishi a baya, suna nurses din suka rufa musu baya da sauri.
Likitoci kusan biyar kan Mimi ciki kuwa har da Jahid din sun dukufa domin ceto rayuwar ta.
Yana zaune a reception ya hade fuskarsa da tafukan hannayen sa, kwata-kwata baya so ya bude idonsa ganin irin kallon da jama'ar gurin suke masa, wato yanzu ya zama abun kallo kenan? Tsoron sa d'aya kada Allah ya kawo 'yan jarida gurin, yasan sai sun fed'e biri har hutsiyar ta.
Aikuwa Ko minti talatin bai yi da zama a gurin ba suka shiga su uku. Daya daga gidan redio daya daga gidan television daya kuma daga gidan jaridar Gaskiya dokin k'arfe
Kewaye shi sukayi suna gyara kayan aikin su, ya d'ago kanshi Yana kallon su da idanunsa wanda sukayi wani irin ja!! Babu fargaba a tare dasu tunda a kan aikin su suke .
Daya daga Cikin su yace." Ranka ya dad'e me zaka ce game da zargin da mutane suke maka."? Shiru yayi musu yana binsu da kallo
D'ayan yace." Kuma muna son karin baya ni daga bakin ka, shin zargin da ake maka cewar ka had'a baki da yahudawa domin Ku tuzarta Allah da manzon shin hakane."?
Amjadu yaji wani k'aton bakin ciki ya tokare masa a mak'ogwaro shiru yayi bai ce musu komai ba, kallonsu kawai yake kamar zautacce.! D'ayan da bai yi magana ba shine yace." Ranka ya dade jama'ar gari sun ci alwashin sai sun kashe ka kan abunda ka aikata sai sun k'one gidan ka sai sun k'one company ka, sai sun kona ka, yanzu dai sun samu nasarar k'one company ka kurmus! Ta inda babu wani Abu da zaka Mora a cikinsa, abun mamaki da daure kai kuma