Showing 78001 words to 81000 words out of 92177 words

Chapter 27 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete

Yanda Munnu take masifa sai ya bani dariya nace"Munnu ni da zaki bi ta tawa da mun hak'ura wallahi duk son ki da baby baki kaini ba, amma na hak'ura na bar masa kayan sa kamar yanda ya fad'a d'in, nasan duk daran dadewa baby zata neme mu." Munnu tace"Ai sai munje har gidan mun ganta wallahi hakkin mu, dole zan hurawa Babanmu waya muje tare." Shuru nayi mata ita kuma ta hau tura hoton baby a wayar ta.


******
Amjadu kuwa ranar da yaje amsa kiran da me girma governor yayi masa basu kwashe da dad'i ba, domin wasu zantukan banza yake masa wai yaga jama'ar gari suna zargin sa kan harda sa hannunsa kan afkuwar abunda ya faru, ya kama rantse-rantse yana fad'in kwata-kwata bai San zancan ba, don haka yayi hakuri kar ya kulle CE shi kuma a matsayin sa na shugaba insha Allah zai sanya a tsaurara bunkice domin gano wadanda suka aikata haka." Kallon shashasha Amjad din yake masa domin ya ma kasa cewa dashi komai kawai ya mike zai bar gurin, governor yadawo dashi, cikin sigar rarrashi yace." Sai magana ta biyu cewar nayi maka alk'awari insha Allah wannan kujerar tawa Kaine zaka maye gurbin ta, tunda na lura jama'ar gari na sonka zamu had'a baki dakai muyi murdiya ga Wanda yaji zab'e zaka tsaya takara a jam'iyya ta, sai milki ya dawo hannuna." Amjad yaji kamar ta kwakwkwad'a masa Mari lallai shaye-shayen da yake yi ya soma tab'a masa kwakwalwa da har yake tunanin dashi zaiyi wannan aiki.
Kallon banza Amjad yayi masa yace." Idan ina sha'awar mulki kai! Baka isa ka sanya ni nayi ba, lokacin da zaka ji ni a duk jam'iyyar da nake so zakayi mamaki so wannan Ba damuwar ka bace tawa ce, maganar zaka tsaurara binkice kan mutanan da suka shirya wannan sharri gami da yin izgili ga Allah da manzon sa, wannan bai dame ni ba, saboda ni nasan ko su waye kar ka bawa kanka wahala kuma zan dauki mataki a Kansu."!! Tebur din gaban shi ya buga da k'arfi! Ya mike tsaye hade da fad'in"Na barka lafiya." Futa yayi cikin yanayin tafiyar shi, ta gwarazan maza.
Governor ya bishi da kallon mamaki! Wato duk inda yake tsammanin yaron ya wuce nan, lallai su Alhaji Hashimu mai citta sun shirya masa sakiyar da babu ruwa ya tabbata da babu wannan maganar a kasa, zai iya Jan ra'ayin yaron ya karb'i takarar governor kano a jam'iyyar su, domin ya tabbatar Da babu abunda zai hanashi ya lashe zab'e saboda kaunar da jama'ar gari suke masa, shi kuma tanan sai yayi amfani da damar shi, shiru yayi yana tunanin mutukar ya sauka daga kan mulki kashin sa ya bushe zai tabbata bashi da tsunsu bashi da tarko.

****
Tsaf ya fito cikin shiri, granny da Iyami na zaune a parlor suna hira, ya k'araso tsakiyar parlorn hannu ya mik'a ya dauki baby dake jikin granny a kwance sai wuntsin-wuntsil take, sama ya d'aga ta kamar yanda ya saba yi mata yana kyalkyala dariya itama na b'angale baki, yafi minti goma yana wasa da yarinyar sannan ya zauna da ita a jikinsa yana fad'in"Baby zanyi missing dinki fa....Granny don Allah Ku shirya mu tafi tare kinji. " cikin shagwaba yayi maganar, granny tace"Kasan Allah babu inda zamu bika kai dai kaje kurrum Allah ya bada sa'a idan ka dawo ma ina so muje muga 'yan uwa Chadi. " yace." Sai dai idan kin yarda mu tafi tare bayan nagama Abunda ya kaini sai mu wuce Chadi din ko ya kika ce." Girgiza Kai tayi tana fad'in"Oh-oh!! Kaje dai ka dawo idan kuma kak'i kaini ai da k'afafuna sai in tafi ka dawo ka tadda bama nan." Yace." Ki Bari zamu je granny nasan halin don girman Allah kar ki d'aukar min Baby kuje wani guri." Tsakaninsa da Allah yake maganar. Granny tace"Ikon Allah!! Yanzu ni kakewa gargad'i kan 'yar ka K'ato! Lallai baka da ta ido!! Dariya yayi ya mike yana fad'in"Granny soyayyar sweetheart dina ta cika min zuciya ta shiyasa idona yake rufewa. " romot din dake kusa da ita ta dauka ta jefe shi dashi, tace"Marakunya kawai, ni kam bana maka fatan samun matsala da duk matar da zaka aura nasan kam Aysha zaka iya sakin ta." Babu wasa a fuskar shi yace." Granny duk wacce zata zauna min da sweet heart lafiya ina maraba da ita, zaman lafiyar mu da ita ta so baby Aysha." Granny da Iyami suka girgiza kai cikin mamaki

Iyami ya mik'awa baby din ya kalli agogon dake daure a hannunsa, Cikin nutsuwa yace." Ni zan tafi sai munyi waya ko
"? Granny tace" Allah ya kiyaye hanya muna maka fatan alkairi,Iyami ma fatan alkairi take masa ya fuce daga parlor da sauri,baby ta bishi da kallo tana d'aga hannunwan ta, yarinyar sun saba sosai da baban ta.
Yana futa su Rambo suka rufa masa baya, kai tsaye airport suka kaishi sai da suka ga tashin jirgin su sannan suka bar gurin. Hade da yi masa fatan dawo wa lafiya.


****
Gurin Jahid naji cewar yayi tafiya sai ban nuna komai ba, ko da wasa ban fada masa abunda ya faru tsakanina dashi ba, haka muke tafiya dashi cike da kauna da kulawa kullum kuwa idan ya shiga gaida granny sai ya dauko min picture din baby ya turo min, mu yini muna kallonta ni da Umma.
Allah mai iko tsakanin Ya Aminu da Munnu soyayya ce mai k'arfi ta kullu shiyasa ma Munnu ta rage zuwa gidanmu a cewar ta wai kunyar Umma take ji,magar auran su ta kankama inda Baban su Munnu da Kawu Yunusa suka tsaida magana insha Allah wata uku za'a d'aura auransu tunda Ya Aminu ya yarda ta cigaba da makaranta a gidan shi, Kawu Yunusa da kansa yazo gidanmu ya karewa Umma zagi har dani sai da ya had'a ya dinga zaginmu da cin mutumci iri-iri wai tunda na ki auran Amjadu to in fito da miji a hada da Aminu ya fuskanci wannan yaron da yake Neman aurena Mujahid yaudara ta zaiyi tunda gashinan kullum sai yace zai turo magabatan sa a tsaida magana sai yak'i saboda haka inyi maza in futo da miji ko kuma Wallahi ya d'aura min aure da Musa tunda dama tuntuni shine ya fara cewa yana sona." Ranar kuka ns yini ina yi ina samun chaji a waya ta ns kira Jahid din tare da fashe masa da kuka duk na kwashe Abunda yake faruwa na fada masa. Shima babu shiri ya je ya Sanar da mahaifin sa halin da ake ciki. Take Alhaji Auwalu yace." Zai tura akai kud'in aure da sadaki. To ko da Jahid ya samu mahaifiyar sa da maganar tsalle tayi ta dire tace wallahi Sam! Bata yadda yaje ya auro 'yar talakawa ba, domin baza ta tab'a had'a jinita da talakawa masu dattin hula ba, tsaf! Ta sanya akaje akayi mata bunkican su waye su Asma'u kai har gidan su sai Da tasa aka binkito mata. Aikuwa ita da Aminiyar ta suka shirya cikin shiga ta alfarma suka tafi gidan, Baban abunda ya tayar mata da hankali yanda taga wani k'aramin gida kamar akurki wai nan gidan Mujahid dinta zaije ya nemi aure salon ya zubar mata da mutumci da kima a fusace! Suka shiga gidan Momy Mujahid din ns karkada key dinta motar ta cikin izgili
Ina sunkuye bakin rijiya ina dauraye hijabai na, Umma kuma na cikin rumfa tana d'aurin sukari hira baby Aysha muke yi da ita kawai naji wani mugun kamshi ya bak'unci hancina sawun tafiya naji na kalli kofar shigowa da sauri, wasu hamshakan mata ne suka shigo cikin ya tsine fuska sukayi sallama, na d'ago Cikin nutsuwa nake amsa musu, Hajiya Fatima ta kalleni ya a mutse tace"Da'alama kece "Asma'u ko."? Babu walwala a tare dani nace" Nice." Kallon banza tayi min ta wani ya mutse fuskar ta had'e da tofar da miyau! "She is ugly girl!!." Ta fad'a tana kallon Momyn Jahid dake bin tsakar Gidanmu da kallo kamar Wanda take Neman wani Abu.... Wani irin tsinkewar zuciya naji lokacin da tafad'i min wannan Kalmar kallo nake binsu dashi cikin mamaki!! Momy Jahid ta kalleni a wulakance tace"Ke! Ina uwarki kwad'ayyaya gurun ta nazo ni." Umms ta futo tana fad'in "Asma'u ke da waye ne."? Cikin takaici da jin haushi nace "Umma wad'annan sakarkarun matan ne suka shigo mana gida babu sallama ko wacce tana fama ra karnin bleecing sune har suke kiran wani da mummuna."! Momy Jahid ta kawo min wani bahagon mari tare da fadin" Ke don ubanki kin San kuwa ni wacece a gari nan. "? Kaucewa nayi da sauri ina fadin " Sanin ko ke wacece bai dame ni ba nasan dai ke macace mara tarbiyya mace mai izgil...... Kafin in karasa Umma ta gwab'e min bakina tare da fad'in"Asma'u baki da hankali ko."? Nace. " Umma kin..... Tsawa tw buga min tare da fadin",wallahi in bakiyi shiru ba ranki zai b'aci a gurina."!!Momy Mujahid tace "Ki k'yaleta ta zageni da kyau! Nagode Allah da ya nuna min halin ki tun kafin Dana ya aure ki dama jama'ar gari na fadin haka a kanki,to bari kuji gargadi na daku da babban murya tun wuri Ku janye jikin Ku domin har indai nice mahaifiyar Mujahid wallahi bazai aure ki ba bazan hada jini da talakawa fakirai irin Ku ba, mutsiyata kawai."

Mamaki ne ya lullub'e ni jin Ashe da da mahaifiyar Jahid nake magana naji tsoro da kunya sosai amma lokaci guda naji wata irin muguwar tsanar matar domin a rayuwata na tsani masu kudi marasa kaunar talaka ya rab'e su. Cikin daki na shige cike da takaici a fili nace "Wallahi kinci darajar Mujahid ne kawai." Ashe taji duk da k'asa kasa nayi maganar aikuwa naji tana fad'in"Da kin sani kin dake ni kamar yanda kikayi NIYYA marakunyar yarinya kawai. " Umma kuwa hakuri kawai take basu Hajiya Fatima ta daka mata wata irin tsawa "Dallah rufe mana baki."? Umma ta rike hab'a cike da mamaki! Hajiya Fatima ta cigaba Da cewa" DUk laifin naki ne ai hausawa suka ce ido na mudu ba yasan k'ima, in banda abunki ina mu INA Ku kwadayi ne ya rud'e ku kuma kinyi a banza domin dai d'anmu bazai auri yarinyar Ku ba." Umma taji zafin maganar da Hajiya Fatima ta fad'a to dake kowa na da nashi hankalin, sai ta share kawai tace "Shi aure nufi ne daga Allah idan Mujahid shine mijin Asma'u babu mahalukin da ya isa ya hana, idan kuma bashi bane Allah ne masa ni don haka Ku kwantar da hankalin Ku."

Momy Jahid ta Ciro d'aurarrun kudi cikin jakar ta dauri uku ta watsa ma Umma a jiki cikin izgili tace"Ki tofar da bakin miyau na bakin ki domun kinyi sab'o Wallahi Mujahid bazai auri yarki ba mutukar ina Raye. "!!! A fusace taja hannun Hjy Fatima suka futa daga gidan.
Umma ta shigo inda nake tana fad'in" Ikon Allah Ashe haka wasu masu kud'in suke? Ashe mahaifiyar Mujahid bata da kirki shikam yaron kirki dashi lallai albasa bata tayi halin ruwa ba." Nace Umma ki k'yaleta badai Jahid ne bata so na aura tom ni. Kuma sai na aure shi sai inga ya zata yi."!

Umma tac"A'a ni bana yi miki sha'awar auran shi tunda uwarsa bata so ko anyi anyi auran ma to ba dad'i zakiji ba, kowa ya shaida cewar matar shi mutuniyar kirki ce kingani ke babu Matsalar kishiya tunda ta amunce ko ka bata amunce mijinta ya aure ki ba tom Allah da manzon sa, sun hallasta amma gaskiya matar nan ta bani tsoro." Nace"Umma ki kwantar da hankalin ki, kamar yanda kika fad'a cewa aure nufi ne na ubangiji to ni ina nan kan bakana Wallahi babu gudu babu ja da baya sai dai in Jahid din ne yace ya janye maganar aure na tom sai in hak'ura. " Umma tace "To Allah ya zab'a abunda yafi alkairi dai." Amin nace zuciyata duk babu dad'i.


Kuka sosai Momyn tasa take da kyar ya shawo kanta tayi shiru yace." Ki fada min ko menene Mommy" Tace"Wai ni yau ka kajawo wa zagi a gurin wadanda basu isa ba, Mujahid yau matar da kake Neman auranta ta zage ni ta kirani karuwa wai mai bleecing sai ta kara fashewa da kuka sosai har da dafe kanta." Jahid ya sunkuyar da kansa cike da mamaki anya kuwa Asma'u zata iya zagin Momyn sa kamar yanda ta fad'a to wai ma shin a ina suka had'u da juna ne.?








*27/11/2019*
[11/28, 7:55 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*





*66*



Mujahid ya cigaba da rarrashin Momyn sa har sai da tayi shiru tukkuna ya kalleta a nutsu yace."Momy wai ina kika ga Asma'u da har tayi miki rashin kunya nifa abun nan ya bani mamaki."! Cikin fusata Momy tace"Naga kamar kana shakka ne Jahid har kana titsiyeni ka tambaye ni, to gidansu nasa aka kaini domin in gargade ta ta fita harkar ka domin naga mayu ne kana zaune da matar ka ta kirki ka je ka kwasowa kanka kaska shine fa ta yi mana wankin babban bargo nida Hajiya Fatima." Mujahid yayi kasa da dansa cikin mamaki jin wai momy gidansu Asma'u taje to in hakane Ashe itace ta jawowa kanta raina yasan halin Momyn sa da zubda girma mybe taje tayi wulakancin da ta saba ne. Tace "Saboda haka in dai nice mahaifiyar ka ban yarda k auri yarinyar ba, shida shiru yayi mata har sanda ta kare fad'an ta yayi mata sallama ya tafi gida. To ko da yaje gida ma matarshi kasa gane kansa tayi dama 'yan kwanakin nan haka yake mata duk ya sauya kwayenta nace mata dama idan namiji zai kara aure canza hali yake, ita dai tunda ta hada masa abunci sai ta shige d'akinta domin ta lura kamar zamanta a kusa dashu baya so. Jahid kuwa ba wani ci abunci da yawa ba, ta kwanta duguwar kujera yana tunanin ala'amri lokacin yi wayar su nayi ya kirata. Lokacin ina zaune ina yin game a wayata naga kiransa dama na tsammaci haka, Muka gaisa kamar yanda muka saba kana ya d'ora da maganar shi kamar haka" Asma'u wai da gaske Momyna tazo gidanmu."? Nace"Babu wai Mujahid Momynka tazo gidanmu. " shiru yayi na minti biyu yace."Ki fada mun gaskiyar Abunda ya faru." Nace"Jahid Momyn ka tazo tayi mana cin mutumci sosai takai har sai da na mayar mata da martani a rashin sani sai daga baya da ta fad'i cewar itace Momynka sannan naji kunya don Allah kayi hakuri nasan duk zata fada maka abunda ya faru tsakaminmu amma ni abunda nayi mata a rashin sanine." Jahid yaji ya kara kaunar Asma'u yana ganin ba zai iya janye kudirinsa akanta ba zai lallaba Momysa ta hak'ura ta barshi ya aure ta A halin yanzu ita kurrum yake gani yaji sanyi Asma'u tw zame masa wani b'angare na jikinshi, take ya manta da b'acin ran Momyna suka cigaba da hira shi da Asma'u Cikin shaukin so Sam! Ya manta ma cewar a cikin gidan shi yake kuma a patlor Maman Salim zata iya jinshi, Aikuwa tana daki tana tik'ar kukan takaici a zuciyarta tana ji ta tsani Asma'u tunda ta shiga tsakanin ta da mijinta da suka Gina rayuwar su cikin aminci da yardar juna.

****
Mujahid ya nunawa Momynsa kamar ya janye maganar auran sa da Asma'u a b'oye kuwa sun hada baki da mahaifin sa, har anje gidan su Asma'u ankai kud'in aure da sadaki lokaci kurrum ake jira kuma kullum suna tare domin shakuwar su ta yanzu tafi ta da waya kullum babu dare babu rana haka suke yi.

****
Watan Amjadu Biyu a chana komai ya kammala nan ya wuce Ingila domin can ma akwai bukatar yaje din domin duba company shi da ganin irin cigaban da aka samu. A shkekarar kullum suna tare da granny a waya maganar guda ce Babu Aysha tayi kaza kaza wani lokacin sai dai granny ta kashe wayar ta kyaleshi ko kuma ta kara wayar bakin baby Aysha tayi ta gwalantu shi kuma yana kyalkyala dariya sai Granny ts karb'i wayar sannan zai ce da ita wai tana fad'a masa ne tayi missing d'insa sosai. Granny tsabar haushi sai ta kashe wayar tana fadin'Kai da ita kuka San wannan."

****
Muna a dai-dai sahu nida Munnu tace"Ke Wallahi yau sai munje gidan Young millionaire mun dauko baby Aysha ta kwana biyu a hannun mu tunda kince ai mahaifin nata bayanan ko."?Nace " Bayan nan yayi tafiya lallai Munnu ke 'yar rigima ce ni kam babu ruwana Wallahi. " Munnu tace"Ki sa wasa ki gani, mai a dai-dai muje Jambulo." Aikuwa Mai a dai-dai ta ya Karya kwana , nace "Munnu sai dai in ki shiga ke ni kam bazan shiga ba." Tace"Wallahi sai mun shiga tare "Dariya NASA Nace " Zakiyi kaffara kuwa. Muna isa Munnu ta biyashi kudinsa muka tsaya bakin gate din, take masu gadi suka bude mu din ba bakin bane a gidan, Jan hannuna take wai dole sai na shiga ganin kar abun ya zama da zargi yasa na bi bayanta gabana na fad'uwa ni yanzu Sam bana kaunar abunda zai hada ni da guy nan tunda yace s k'yale masa 'yar sa to sai a k'yaleta domin a zauna lafiya.

Granny da Iyami na zaune a parlor suna kallon shirin dadin kowa tashar Arewa24 muka yi sallama. Granny ta amsa tana fad'in "Lale maraba da manya baki lallai yau Baby Aysha na da baki domin dai nasan domin ita kuka zo gidanan." Murmushi nayi na zauna Cikin kujera a nutse muka gaisa sosai tace"Shikkenan saboda babu Aisha sai Ku yanke zumunci damu har Umman taku ma ai wallahi bata kyauta ba." Hakuri na dinga bata INA fad'in"Bana samun lokacin zuwa ne saboda makaranta. Granny tace" Yau watan baby Hudu a duniya ace kuna a matsayin iyayenta babu Wanda yazo duba ta ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login