Showing 15001 words to 18000 words out of 92177 words
Chapter 6 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
shak'o wuyana dake cikin hijabi, Murya k'asa-k'asa yace." Maimata irin zagin da kikayi min a waya jiya." Kifkifta idona kawai nake, ya k'ara shak'e min wuyana hade da d'aga kaina sama sosai, yace"Ko bakya ji ne."?
Da kyar na samu na kakaro magana nace"Sakar mun wuya kar ka kashe ni."
Kin saki yayi sai ma kara damk'e wuyan yayi, hannuna guda na sa ina kokarin b'anb'are hannunsa daga jikin wuyana, ko motsi ya kiyi, wuyana yayi bala'in sagewa, nace"Ka Sakar min wuyan....... Ka tsani Yayi ta hanyar fad'in" Ki maimata irin zagin da kikayi min jiya Zan sake ki."
Babu wasa a cikin maganar sa.
Hawaye na ziraro min nace"Wane irin zagi nayi maka, duk abunda na fada maka gaskiya na fada ciki babu sharri ko kashe ni zakayi sai dai ka kashe ni."
"Very good."!! Ya fad'a yana k'ara bank'are min wuyana sama, cike da mugunta, yace." Na lura da abunda kike so in yi miki ni kuma bazan yi ba, na daina hora ki da abun domin na lura yana miki dad'i shiyasa kike bukatar haduwar mu, Yanzu zanyi miki horo ne irin na gidan prison. " Kasa magana nayi saboda yadda naji mak'o gwarona ya bushe,
Hannu ya sanya ya cire hijab din jikina, na rintse idona saboda nasan babu rigar arziki a jikina wata vest ce mai kama jiki sosai kuma iya kacin ta cibiya ta, domin nayi shirin bacci Mimi ta tashe ni shine kawai na zura hijab din a kai.
Miskilin murmushi ya saki tare da cije lips d'insa yace" Surprise!" Wato dama kin tawo da shirin ki kenan ko."? Shiru nayi masa wasu zafafan hawaye na zubo min a Kumatuna.
Murmushi yayi had'e da shafa sajan shi yace."Wannan karon baza ki samu abunda kike so ba, domin na fara nisanta kaina dake, sai kije gurin wannan saurayin naki mai kama da alade,sai Yayi miki wasa dasu."
Shashshekar kukana ce ta fara futowa fili ina mugun Jin ciwon rashin mutumcin da yake min.
Muryarsa a kaurare! Yace." Wancan karon kin min lafi nace ki bani hakuri kink'i OK wannan karon ki bani hakuri ko kuma in dauki mata ki nag gaba a kanki."
Cikin shashashekar kuka nace"Babu hakurin da zan baka tunda banga laifin da nayi maka, ba, kuma bak'i mai kama da alade da kake magana a kansa gwara min shi sau dubu a kanka, Allah ne ya hallice shi a haka. "
Gyada kansa yayi tare da fad'in"Wannan ke yake damu, kiyi abunda na umarce ki kafin in Riga goma." Cikin daga murya ya fad'i maganar.
Jin nayi shiru ne yasa ya damk'i gashin kaina hade da ja da mugun k'arfi !! Ihu! Na kurma ina fad'in"Zan y......Fuzgar gashin Yayi da k'arfi yace." Oya! Ce ne *Amjadu* kayi hakuri sau goma sha biyu nake so ki fada."
Rintse idona nayi ina cije bakina na fara fad'ar *Amjadu kayi hakuri bazan k'ara ba.!"* sai fa na fad'i haka sau goma sha biyu kamar yanda ya umarce ni.
Babu sauk'i a muryarsa yace." Duk naga shirme da kika rafka naga irin rashin mutumcin da kika tsula a gurin party ku , to ki sani ma Sam! Bakiyi wani kyau ba, kullum kina kiran kanki da Me aji mace mai daraja to duk baki amsa wannan sunan ba, *Momyna* ita za'a kira da wannan sunan."
Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Momyna ita yafi dacewar na aura a tsakanin Ku, to kuma sai d'azu wanki Aminu yake rokona kan in hada in aure Ku gaba d'aya, cewar kin tayar da hankalin ki, ke ni kadai kike so, hake ko ba haka bane."? Kallonsa nayi cike da mamaki anya Ya Aminu zai fada masa haka.? Wata zuciyar tace" Tsaf Ya Aminu zai iya fada masa haka saboda daman ba shiri kuke dashi ba."
A d'age na kalleshi ina ya mutse fuskata nace"Sai dai Mimi don da ita kuka fi dacewa amma ni ko maza sun k'are bana jin zan aure ka gwara in k'are rayuwata a haka."
Miskilin murmushi yayi bai ce komai ba ya sake ni, hijabina na dauka ina kokarin sanyawa naga ya tada motar nace"Ina zaka kaini."? Ko kallo ban ishe shi ba, ya figi motar da gudu.!
Da sauri na sanya hannu guda na rike sitiyarin motar murya ta na rawa nace"Ka mayar dani gida don girman Allah." Ko kallona bai yi ba, ya cigaba da fafura gudu, kuka sosai na sanya tsoro ya shige ni ganin fuskarsa murtuk!! Nace"Wai me nayi maka ne kake kokarin wulakantani ? Ita Mimi meya sa baka yi mata abunda kake min. " Shiru babu Amsa, yanzu tsoron gida nake da tsoron dukan da Yaya Aminu zai yi min.
Hannunsa na rike tamau! Ina rokanshi motar ta fara gargada! A fusace! Ya fuzge hannuna had'e da yarfa min mari." Cike da mamaki na dafe kuncina ina kallonsa... Da Jan ido ya kalle ni tare da fad'in"Ki shiga hankalin ki."
Shiru nayi tsoro yana shigata.
Gudu yake sosai kan kwalta, naga mun wuce Jambulo wajan gidan shi ya mik'e titin BUK bakina na rawa nace"Kayi hakuri." Hankalinsa na kan driving ki kallona bai yi ba.
Rimin Gata muka shiga sosai, yayi parking dai-dai wani k'aton gidan mai
Haske ko ina jama'a na ta shiga da motocin su Suna shan mai.
Da sauri naga wani mai aikacin ya nufo mu jikinsa sanye da Uniporm orange da tambarin sunan mai gidan mai yana k'araso wa na ga jikinsa rigarsa an sanya *A&A Amjadu Mai nasara feturolium* nace Ashe har gidan mai ne dashi, cikin turanci naji suna maganar Sam ban fuskanci komai ba na dai ga mutumin ya juya ya tafi da sauri!
Minti biyar sai ga mutumin shida wani, sai da suka k'araso sannan naso na gane wanene. Gaba na ne ya fad'i ganin Abokin Shamsu wato Abba gana, yayi tsuru-tsuru,
Bude kofar motar Yayi hade da umar tarsa ya shiga
Abba gana ya shiga motar ba tare da gaddama ba. Shi kuma ma'aikacin ya koma gurin akinshi
Juyo wa yayi yana kallonsa, muryarsa babu wasa yace." Malam meye sunan ka? Kuma meye ya kawo ka wannan jahar."?
Abba yace." Sunana Abba Gana ni mutumin mai duguri ne, yau sati na biyu a jahar kano, Nazo Neman kudi."
Gyada kansa yayi murya a cunkushe yace." Kasan wannan yarinyar."?
Naji gabana ya buga damm!!!
Shiru Abbah yayi, tsawa ya buga masa tare da fadin" Answer me." Baki na rawa Abba yace." Banga fuskarta ba Yallab'ai."
Cikin wata irin kyara da hantara yace." Ki juya masa fuskar ki ya kalle ki."!!!!
Da sauri na juya muka hada ido da Abbah Wanda tun ranar party mu bamu sake had'uwa dashi ba.
Da sauri Abba yace." Na Santa sosai Yallab'ai. "
"Good."!
Yafad'a yana jin jina kansa. Bakina na rawa nace" A ina ka sanni da har kake cewa kayi min farin San.....ban k'arasa ba, ya gwab'e min bakina da gwiwar hannusa. Dafe bakina nayi ina kallonsa hawaye na zubo min.
Kallona yake shima fuskar sa babu sauk'i.
Minfi minti biyu a haka sannan ya juya da kaurarriyar murya yace." Abba kana son ta ko."?
Abba yace." K'warai kuwa Yallab'ai. "
Gyada kansa yayi yace."Zaka aure ta ni zan tsaya maka a kan komai zan baka gida akin yi da duk abun bukata."
Abba ya dinga godiya tsakanin sa da Allah, yace." Kana iya tafiya"Abba ya fara kokarin bude motar sai kuma ya daka ta tare da juyo wa Cikin sauri yace." Yallab'ai nagode k'warai da wannan karamcin naka, hak'ika idan ana samun mutane irin Ku to da talakwa sunji dadin su, amma ka yafe min hak'ika yanzu na kara tabbatar da cewar Asma'u matar manya CE, nagode da karamcin ka, Asma'u da kai ta dace Yallab'ai. "
Wani kallo Amjadu ya watsa masa yace." Bayan kun gama wasan soyayyar da ita zaka ce dani ta dace. Tab'e bakinsa yayi yana girgiza kansa yace." Ni nafi k'arfin socond hand, kawai idan baka so in bawa wani."
Abbah yayi shiru yana tunani daga bisani yace." To Yallab'ai duk yanda kayi dai-dai ne."
'Yar dariya yayi yace." Yanzu kayi magana guy kaje kawai ka fara shiri."
Simi-simi Abbah ya bar gurin yana mamakin meye manufar sa kan haka, yarinyar da yayi-yayi ta bashi numbar waya tak'i yau ita za a bashi, shi ba Yaro bane yana kallon tsantsar so hade da kishi a idon sa, addu'a yake Allah yasa kar ya auna shi garinsu dama jarabar fad'an da ake ne yasa ya biyo Shamsu tunda dukanin su iyayen su sun mutu.
Kunna motar yayi muka fara tafiya. Da gefan ido ya kalleni tare da fad'in"Ko kiyi min shiru ko kuma in sauke ki anan."
Cikin kuka nace"Allah kad'ai na mik'a masa kuka na akan ka, ka zame min bala'i ka shiga rayuwa ta, me na tsare maka a duniyar nan, da kake kokarin tozar ta ni." Cikin zafin zuciya yace." Kika tozarta kanki dai! Ni gata nake so nayi miki saboda na lura da yanda bagalar ki take, kar ki dauko abun kunya domin baki da juriya, nace zan rufa miki asiri in aure ki kin ce bakya so, tom naje gurin sauranyin naki da Kuka gama rungume-rumgume dashi zan taimake Ku, shine kike min kuka harda hada ni da Allah, me kike so ayi miki."?
Murya ta a shak'e nace"Idan na dauko abun kunya meye damuwar ka? Na farko dai dani da kai bamu had'a dangartakar komai ba, babu wata alak'a a tsakanimu,saboda haka baka da damuwa da wannan....ka tse ni yayi ta hanyar fadin"Sai kace ba musulumi ba, wato kina so Allah ya kama ni kenan ? Idan kika je kika dauko zunubi dole ya shafe ni tunda Allah ya nuna min ko wacece ke, kuma kina maganar dan gantaka a tsakanimu idan yanzu babu ita tom nan da kwanaki kad'an zata samu, bana so duniya ta dinga kallon ki a matsayin k'anwar matata wacce ta dauko abun kunya......Ihu!!!! Na kurma da k'arfin gaske ina zuciya ta kamar zata tsage, dukan shi na kama yi kamar wata sabuwar mahaukaciya ina Kuka ina fadin "Allah ya Isa na."!!!! Motar ya tsayar da sauri ganin tana kokarin sauka daga kan titi.
Bakina ya matse da k'arfi!!! Muka fara kallon kallo dashi, babu alamun sassauci a fuskarsa yace." Duk abunda na fada gaskiya ne, ga zahiri ne nan na gani, saboda na saba tab'a jikin ki in muka had'u shine kika sanyo k'aramar riga don in gani inyi sha'awa, tab'e bakinsa yayi ya cigaba da cewa"Ko tsirara zakiyi a yanzu bazan sha'awar komai naki ba, saboda kin gama rabawa gayu a titi yanzu sunan ki sorry."!! Ya k'arashe maganar sa hade da Sakar min bakina da ya matse yana shegen murmushin sa da ya saba.
Fad'ar tsananin b'acin ran da nake ciki a lokacin b'ata wa ne,raina yayi min bak'ik'ikirin ta inda naji duk a fadin duniyar nan bani da babban makiyi sama da guy nan, tunda nake a rayuta ba a tab'ai min tozarcin irin na yau ba, lallai na yarda ko wane namiji akwai sharrin shi don shi wannan guy ma na rasa a ina zan aje shi, duk inda kake zaton sa ya wuce nan........
*6/November/2019*
[11/7, 11:04 AM] BintuUmarAbbale: [11/6, 10:37 PM] .: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*
*43*
Wani irin gudu yake da motar kan kwalta, tsoro duk ya kama ni burina kawai in ganni a gida, tun lokacin da yace nayi shiru na rufe bakina domin ina jin tsoron kar ya tsoro da wata futunar. Dai-dai tal'udu yayi parking din motar hade da futa kallonsa nayi ina cikin motar naga ya dauko glass cikin aljihunsa ya sanya a fuskar sa, tsallaka titi yayi ya nufi had'addan gurin abincin nan wato *Mai takobi* ina nan zaune mintuna goma na hango shi,
Saurin kauda kaina nayi cikin zuciya nake fadin"Mutum har mutum amma babu kyawun hali
Hannunsa rike da ledoji ya shigo motar kujerar baya ya aje ya kunna motar muka tafi
Bacci ne ya fara daukata kamar daga sama naji muryar shi yana fadin
"Kar ki sake kiyi min bacci a mota"
Zumbur na bude idona
Da suka fara yin ja.Kauda kansa yayi yana ya mutse fuska.
Nima ban sake kallonshi ba,
Har yanzu fuskata a hade take tamau! Nayi alk'awarin har in sauka daga motar bazan kara kula shi ba duk abunda yayi min na barshi da Allah.
Wayar shi ce tayi kara a lamun ana kira, a hankali ya sanya hannunsa ya dauki wayar da take kusa dani.
Ji nayi tsigar jikina ta mike jin hannunshi na tab'a gefan cinya ta.
Addu'a ns fara yi a zuciyata ta neman rinjaye.
Cikin wani irin voice naji yana fadin"Hibbah!! Wai sau nawa zan fad'a miki ki rabu dani ."! Ban ji abunda tace ba, sai naji ya ja tsaki yana fad'in"Ki jik'a ki sha kayan ki, kwanan nan zanyi aure in huta da bala'in Ku, ko wace 'yar iska ita dai a cita."
Kallonsa nayi a fakaice ina mamakinsa cikin zuciyata nace"Zaka aikata abunda yafi haka.
Ina jin budurwar tashi tana kaskantar da kanta hade da yi masa magiya, takaici ya she ni, cikin zuciyata nake fadin"Mata yanzu sun koma bin maza har da magiya akan ya so ta wallahi abunda bazan taba iya wa ba kenan.
Tsaki ya ja ya kashe mata waya
Draving dinshi ya cigaba da hannu daya daya hannun kuma da wayar a hannunsa yana dubawa.
K'arfe goma shaura na dare,
Aje wayar yayi gefe na, saurin matsawa nayi jin hannunshi ya tab'a ni
Haka muka isa unguwar mu, masu sana'oin dake kan layinmu duk sun fara tashi unguwar tsitt!! Gashi duhu dumd'um muna Matsalar wutar NEPA.
Parking yayi hade da juyo wa yana kallona.
Dauke kaina nayi da sauri!
Yace."Kina iya tafiya." Hannu nasa ina kokarin bude kofar
Taki bud'ewa, hannunshi ya d'ora kan nawa cikin wani irin salo ya shafa sannan ya bude min kofar
Jikina a sanyaye na futa daga motar ina wurga ido domin akwai ni da bala'in tsoro ga unguwar mu da karnukan tsiya gari yayi tsitt ga duhu. Leda guda ya mik'o min cikin ledojin nan yace."_Karb'i ki kaiwa my Wifi bayan haka kice ta kunna wayar ta ina son muyi hira."
Share shi nayi ina kokarin tsallaka titi.
Sunana naji ya ambata *Asma'u* kin ji yuwa nayi na wuce da sauri!
Wani kare ne yayo kaina da gudu, yana haushi.
Ihu!! Na sanya na dawo da baya ina haki!
Dariya yayi ya bude motar ya futo
Karan ya kara haushi da k'arfi!
A hankali yace." Wannan bakin hijab din na jikin ki shiyasa yake miki haushi.
Cikin tsoro na kalle shi, nasan bala'in karan nan bashi da sabo.
Yace." Ni zan tafi ki San yanda kika yi kika wuce gida,ko kuma ki kira saurayin ki.
Muryata na rawa nace"Motar ai zata shiga lugun don Allah in shiga ka kai ni
Girgiza kansa yayi hade da bude murfin motar ya shiga.
Shahada nayi na kara yunk'urin tsallaka titin a karo na biyu
Cikin fusata karan yayo kaina.
Da sauri na koma baya kamar wata zarrariya na dunga dukan motar ina fadin bude min don Allah.
Sauke glass din motar yayi yace." Meye wai! Kiyi tafiyar ki ki k'yale ni." Hawaye suka zubo min nace." Nasan wancan karan bashi da mutumci kuma bashi da sabo Wallahi zai iya cizo na, kwanaki da ya ciji wani sai mutuwa yayi don dafi ya zuba masa "
Cikin k'osawa yace."Tom yanzu ya kike so ayi."?
"Ka taimake ni, wani in ya ganni anan ba zai min kyakyawar fahimta ba."
Wani kallo ya watsa min tare da fadin"Au ke kina jira jama'ar gari suyi miki kyakyawar fahimta. "
Shiru nayi
Yace." Ki cire wannan a ran ki."
Kunna motar yayi zai tafi, da sauri na bude na shiga ciki
Kallona yake cike da mamaki yace." Meye haka? Kin damu in kawo gida na kawo ki, kin hanani tafiya."
Karyar da kaina nayi cike da tausayin kaina nace"Ka taimake ni." Hannunshi na kama na rike gam!! B'ata fuska yayi tare da fadin "Wane irin taimako zan miki. Kai tsaye! Nace" Ka raka ni gida wallahi karan can bazai Bari in wuce ba."
Tausayi ta bashi amma bai nuna ba yace."gaskiya bazan iya shiga lokon can ba, kawai kiyi tafiyar ki,ko kuma ki cire hijab din jikin ki ki yar.
Nasan saboda hijan din ya Hana ki wuce wa, da zaki gane ma kawai ki daina sanyawa domin mugun muni yake saki."
Wani irin. Kallon nayi masa nace"In cire hijab dina fa kace."
Gyada kansa yayi tare da kanne min ido daya yace." Meye a ciki to bayan babu kowa a unguwar idan ma da mutane ai abun ba sabo bane a gurin su, tunda duk kin raba musu.
Naji ciwon maganar sa, amma dake taimakon sa nake nema ban tanka masa nayi Shiru hake da sunkuyar da kaina har yanzu hannunsa na rike da nawa gam!!! Murya k'asa-k'asa yace." Sakar min hannu." Sakin sa nayi ya fara kokarin cire babbar rigar jikinsa,
Mik'o min Yayi yace. " cire hijab din ki sanya wannan."
Cike da mamaki nake kallonshi
Yace." Kin ce in taimake ki kuma kin tsaya kina kallona.
A hankali na karb'i rigar kamshi turaran shi sai tashi yake
Yace. " Cire hijab din ki lullub'e jikin ki."
Nace"Matsalar Idan naje da rigar gida."
Katse ni yayi da sauri yana fadin" wannan kuma damuwar ki CE, kina bata min lokaci."
Da sauri na cire hijab din na fara kokarin kare jikina da babbar rigar tashi
Ina kallonsa yana min wane mayen kallo hankalin shi duk yana k'irjina, ni kuma sai kare wa nake.
Hannunsa ya sanya Wai zai gyara min.
Cikin dubara naji ya shafo nonuwana, Ni dashi ban San Wanda ya fi shiga d'imuwa ba.
Rigar ya tattato a hannunsa dai-dai k'irjina ya kama hannuna hade da Dora gurin, murya a harhade yace." Ki rike nan da kyau."
Shiru nayi ban amsa ba.
Ya bude motar ya futa
Futowa nayi jikina babu k'wari
Tsalla titin mukayi a nutse sai naga karan ya koma gefe ya zauna ya daina haushin.
Sai da muka shiga layin mu sosai sannan ya juya ba tare da yace min komai ba.
Nace"Rigar ka fa."
Yana tafiya yace." Ki jefar da ita ana.
Shiru nayi ina kallonshi har ya tsallaka titin ya shiga motar sa hade da barin gur Rigar na rike sosai ina sakin ajiyar zuciya, cikin sauri na tsallake kwatar dake kusa dani na nufi gida, daga nesa na hango Aminu tsaye a waje hankalina ya tashi nan na tuna hijab dina Dana barshi a motarsa