Showing 36001 words to 39000 words out of 92177 words
Chapter 13 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*50*
Umma tace." Ameen suma ameen Hajiya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wata b'araka da taza faru a tsakaninsu zasu zauna lafiya tunda Allah yasa sun hada miji gasu kuma 'yan juna, komai zai zo da sauki. "
Granny tace." Masha Allahu to Allah ya tabbatar mana da alkairinsa, hira tsakanin Umma da granny ta mik'a sosai ba tare da sun gane ba, ni bar dakin cike da kunya, Sai ga Mimi ta biyo bayana kwanciya tayi kusa dani hade da lumshe idonta, murmushi nayi ina kallonta cikin tsokana nace." Mimi amaryar Amjadu Alherin Allah."
Bude idonta tayi tana kallonta fuskarta dauke da murmushi nace." Ko ba haka bane."? Girgiza kanta tayi tare da fadin." Ni amarya ke kuma Uwar gida ko."? Nace." A ina na zama Uwar gida ke amarya kuma ke Uwar gida. " mik'ewa zaune tayi ta rike hannuna tare da fadin "Yanzu kakarshi take fada cewar k'arfe biyar zai dawo ya dauke ta, wane irin Abu zamu tanadar masa."?
Nace." Mimi duk abunda kikayi NIYYA ki bashi domin ki faranta masa kuma kinyi dabara hakan zai k'ara jawo hankalinsa gare ki." Tace." Me zan bashi yanzu."? Dariya na sanya hade da fad'in "Idan baki da abunda zaki bashi in yazo to ki bashi labari mai dad'i da wannan sanyayyar muryar taki." Dariya tayi hade da bani hannu muka tafa, haka dai na dinga biye wa Mimi da duk abunda zata ce min akan Amjadu kuma bana bata shawarar banza.
K'arfe shida shaura kira ya shigo wayar tata lokacin tana band'aki tana wanka, Kin dauka nayi don na duba naga shine, motsin ta naji bakin rijiya nace"Mimi yi sauri kizo ana kiran waya. " aikuwa sai gata ta shigo da sauri hannunta na digar ruwa ta karb'i wayar daga hannuna. Kallo na bita dashi. Wata irin murya da ban Santa da ita ba naji tace." Hello." Daga bashi bangaran naji muryar shi sama-sama yace."Momyna kuna ina ina ta kiran waya kusan sau biyar babu wacce ta dauka a cikin Ku." Muryar ta a sanyaye tace." Ni ina wanka ne."
"Asma'u fah."! Yafad'a babu sauki a muryar shi,kallonta tayi sai kuma naji tace." Gatanan. " yace." Ok kina nufin kice min tana ganin kirana taki d'aukar wayar."? Mimi shiru tayi taki bashi amsa. Shurun da Mimi tayi shi ya tabbatar masa da abunda yake zargi. Tsaki! Yaja yace." Ok ki fad'awa granny gani Nazo ta futo mu tafi OK." Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayarsa. Jikinta a sanyaye take kallona nima ita nake kallo nace"Dole ki koyi hakuri fa, kuma kiyi hakuri da halin shi tunda aure zakuyi ." zama tayi kusa dani tare da fadin"Wai sai ki dinga cewa aure zamuyi eh aure zamuyi har dake a ciki ai,ko" mik'ewa nayi ina dariya nace." Har dani mana, ni ai farin cikin ki ne nawa kar ki damu dani." Futa nayi daga dakin ba tare da na saurari abunda zata ce ba."
Cikin sauri Mimi ta shirya ta futo tana ta zabga kamshi ina zaune kofar kicin ina gyara kayan miya na bita da kallo sakin fuskata nayi tare da fadin "Kinyi kyau sosai Mimi." Mirmushi tayi ta shiga Rumfar inda naji grnnay tana sallama da Umma, suka futo a tare Umma sai godiya take mata, sun kuyar da kaina nayi kasa na cigaba da aikina har tazo kusa dani ta tsaya da sakskkiyar fuska tace." To ke zan tafi naga sai wani b'uya kike yi ko tsorona kike ji tun kafin ki shigo kinga 'yar Uwar ki ta saki jikinta mun saba da ita."
Murmushi nayi nace." Ki gaida gida mun gode." 'Yar dariya tayi tare da fad'in"Na ga alama gudun angon naki kike yi 'yar uwarki tafi ki sonshi." Ni dai ban ce komai ba har suka fuce ita da Mimi da aunty Hauwa har soro Umma ta raka ta sannan ta dawo cikin gidan.
Yana zaune cikin mota ya hango zuwan su, Mimi yake kallo tun daga nesa taci Uwar kwalliya abun ya bashi mamaki sosai, yarinyar Da jiya I Yanzu take kwance magashiyan rai a hannun Allah, amma dubi kamar ba ita ba, abunda bai sani ba shine tunda Mimi taji labarin auransu zai yi wu dashi da ita ta watsake tamkar bata tab'a cuta ba, har suka k'araso gurinsa yana mamakin wannan abu .
Murmushi mai k'ayatar wa take sakar masa, Wanda Sam hankalinsa baya kanta yana can gurin Granny wacce take kokarin shiga mota sai mita take masa, yace." Idan zaman gidan ne bai ishe ki ba sai ki koma ai ban ce miki dole ba." Tana daga cikin motar take fadin"Wallahi karshen zamana a wancan gidan yazo domin baza ka aje ni ba sai kace mayya ni daya gida kullum kana gidin matan ka, nima gidan naka Zan dawo ." dariya yasa yana kokarin futowa daga motar yace." Sa ido ne zai kawo ki gidana bana Neman ki." Bude motar yayi ya futa yana jinta tana surutai ya shareta
Fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Mimi yace." Momyna jiki yayi kyau gashi har anyi min kwalliya mai kyau da burgewa." Mimi ta rufe fuskarta cike da kunya, yace." Kinyi kyau sosai zan so in ta kallon fuskar ki, sai dai Dole zan bar gurin nan saboda idon Jama'a ina fata babu wata matsala ko."? Cike da shauki Mimi tace." Babu wata matsala dama ji nayi zuciyata baza ta iya nutsuwa ba dole sai ta ganka." Murmushi yayi hade da Sosa kansa yace." Momyna kenan nagode sosai da wannan kaunar ina alfahari dake."
Mimi ta dinga jin dad'i a zuciyarta yau gata ga masoyinta Amjadu Sam bata so yayi mata sallama ba, taso suyi ta tsayuwa a gurin tana kallon kyakyawar fuskar shi.
Sai dai motar tayi nisa har ta daina ganinta sannan ta bar gurin cike da nishadi.
*****
Labarin auran *Amjadu Young millionaire* ya baza garin kano da ka bude redio zan can kenan Young millionaire zai yi aure a Sati biyu masu zuwa inda zai auri 'yan gida daya ya da k'anwa jama'ar gari na mamakin wannan Abu, masu bin kwakwkwafi kuwa sai da suka bunkito ko su waye 'yan matan da zai aura hade da bunkice 'yayan wane mai kud'in ne ko kuma mai mulki a jahar kano da sauran garuruwa.
Abun mamaki surutun jama'ar gari sai ya karu wannan gayawa wannan 'yan matan da *Amjadu Young millionaire* yake nema da aure 'yayan talakawa ne tilis d'aya ubanta ma ba'asan inda yake ba tun tana jaririya ya gudu ya barta ana zargin ma 'yar shege ce bayan yayi cikin ta ya gudu daga gari, ita kuma d'ayan ubanta ma'aikacin company ne na madara dake Sharada ya mutu bashi da ko kwabo bashi da famsho balle garatuti ya mutu bashi da gidan kansa,sai a company da yayi wa aiki ne suka bar mishi gidan da suka bashi a ro saboda iyalinsa, Duk ana zargin'yan matan da zai aura 'yayan mace ne." Duk cikin jarida ta gaskiya dokin k'arfe Amjadu ya karanta wannan labarin. Zufa ce kawai take keto masa ko ta Ina, wani irin kira ya kwalawa Rambo sai gashi ya shigo farlor da sauri. Jaridar ya mik'a masa muryar shi a sama yace."Kuna ina haka ta faru. "!! ? Rambo ya karb'i Jaridar yana dubawa hannunshi sai rawa yake yi, shima abunda ya gani ya tsorata shi, yasan makiyan sa ne suka shirya wannan Abu domin su tozarta shi, Yace." Sir ka kwantar da hankslinka wannan duk sharrin jama'a ne kar ka manta kana tare da mahassada ko su zasu aikata maka wannan Abu."
Mik'ewa yayi yana kai wa da kawo wa a farlor yace." Kaje ka tsaurara bunkice ka gano gaskiyar abun shin abunda na karanta jikin jaridar nan hakane Mimi Bata da uba shegiya ce kamar yanda suka fad'a shin hakane wannan gida dasu ke ciki na company ne kaje ka tsaurara bunkice ka gano wane company mahaifin Asma'u yayi a aiki a sharada."
Rambo yace." Insha Allahu Sir ka kwantar da hankalinka duk sharrine domin da d'aga maka hankali kuma a tozarta ka a don duniya. " Wayar shi tayi kara Rambo ya mik'o masa da sauri, kunnenshi ya kara wayar a dake yace." Salamu alaikum. " Kawu Yunsu Ya amsa cike da tashin hankali yace." Yaro mai halin manya na bugo ne in kwantar maka da hankali kan abunda jama'ar gari da kafafan yad'a labarai suke shela a kai, ina so in tabbatar maka da cewar mu 'yar mu Asma'u tsarkakkiya ce da Ubanta kuma muna da nasaba me kyau duk fadin koki da cikarta babu Wanda bai san mahaifinmu Malam Sulaiman mai ishiriniya ba, idan kana so kattabar da haka ka sanya ayi maka bunkice."" Muryar shi a sama yace." Babu bunkice da zan sanya ayi min akan Asma'u na yadda da ita Dari bisa Dari, kokwantona yanzu akan Mimi yake shin da gaske ne mahaifin ta ya gudu ya barta ko kuwa."?
Kawu Yunusa yace." Hakane tun bayan haihuwar ta ya gud ..... Katse shi kafin ya karasa yace." Tabbata kenan abunda nake zargi." Kawu Yunusa har yayi niyyar cewa gaskiya ne sai kuma ya fasa tunowa da yayi da maganar Asma'u inda take fadin bata har indai Mimi bata aure shi ba itama baza ta aure shi ba, yayi saurin cewa." Yarinyar 'yar sunna ce sai dai ubanta ya hofintar da ita ne shine mahaifiyar Asma'u ta dauke ta ta raine ta.
Amjadu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin"Yau saura kwana nawa d'aurin aure."? Kawu yace." Kwana shida ne." Shiru na minti biyu sannan yace." Yau muna laraba ko."? Kawu yace.'k'warai kuwa" Yace. "Idan Allah ya kaimu jibi d'aurin aure insha Allahu Ku zauna cikin shiri daga yanzu a fara shiri duk wani Abu da ake bukata kayi min magana kar ka samu damuwa.
Kawu yaji wani irin sanyin dad'i ya shiga ransa yace."Insha Allahu komai za a yi kamar yanda kake so Allah ya kara arziki da wadata." Amjad yace." Ameen suma Ameen ina so in zauna da Waliyin ita Mimi domin akwai wasu muhiman tambayoyi da zanyi mishi." Kawu yace." Ai babu damuwa yana aiki ne a babbar makarantar ta PCE nan kofar famfo." Gyada kansa yayi yace." Insha Allah zan same shi a ofis din." Nan suka yi sallama da juna.
Wanka ya shiga a gurguje ya kimtsa jikinsa ya futo sai zabga kamshi yake kamar ko da yaushe , fuskar sa a daure ya futa, abun mamaki da daure kai can ya hango 'yan jarida suna rigima da masu gadi gurin wai lallai sai sun shigo Estate din."
Mota ya nufa zuciyarsa nayi masa suya wato yanzu za a sanya shi a bakin duniya kenan Saboda ana zargin zai auri Shegiya mata uba, shi yarinyar da suke maganar ta ba su San ba sonta yake ba, kaddara ce kawai auran su, da ita zasu sashi a duniya duk Wanda yayi masa tunon asiri nan bai kyauta masa ba.
Ganin shi ya futo yasa suka dinga kokawar shiga cike da b'acin rai yace." Doh doh kayi kamar zaka bi takan 'yan iska da mota." Aikuwa Doh_ doh ya fafuri motar da guda! Lokaci guda suka watse amma duk da haka wasu daga cikinsu sai da suka dinga d'aukar motar tashi hoto masu vedio ma nayi kamar bala'i suka bi motar da gudu suna fadin"Yallab'ai me zaka ce a game da jita-jitar da jama'ar gari suke a kanka wai zaka auri shegiya Mara Uba shin hakane ko karya ne, Yallab'ai muna so mu ji ta bakin ka."
Ko kallonsu bai yi ballanta su saka ran zai amsa musu motar ta b'acewa ganinsu. Sai da sukayi nisa sosai sannan yace." Doh ka kaini makarantar FCE Yanzu." Doh yace." OK Sir. motar na shiga makarantar samari da 'yan mata suka yi mata Caa! Da ido kasamcewar duk inda motar shi take an Santa saboda tambarin da yake bayanta. Doh.. Yayi parking inda aka tana da kana ya futo da sauri ya bude masa kofar motar.
A hankali yace." Ka shiga ciki makarantar ka bunkita min ofis din Muktar Inuwa Gyaranya." Shine ai nihin sunan Kawun Mimi wato Baban su Munnu kenan. Nan da nan doh-doh ya tafi cika umarnin da aka bashi
*****
Muna cikin tsananin tashin hankali da rud'u tun lokacin da Umma taji labarin abunda jama'ar gari suke fada a kan Mimi take kuka ta tana fadin"Yarinyar sinna ake shigantawa ni Mariya Innalillahi kuka take sosai tun muna daurewa har muma muka fara taya ta, Ya Aminu ya shigo gidan shima ranshi a bace domin yaga sai Wani irin kallo jama'ar gari suke masa sai kace Wanda yayi sata ko maita Mimi ya kalle ranshi a mutukar bace yace." Kukan karya kike yi Mimi, ko kin dauka auran Wanda ya shahara a duniya wasa ne? Kin dauka in kin auri Young millionaire zaki samu irin kwanciyar hankalin da kike so, to bari kiji auran irin su Sai kayi ta fuskantar kalubale kinga ishara yanzu da Uwar ki da ubanki jama'ar gari suna kiran ki da shegiya, tom me zakice game da wannan zargin da suke miki, ku sani ga 'yan jarida can a waje suna kokarin shigowa cikin gidan nan nine na hana su na rufe kofar gidan da sakata. "
Mimi kukan ta ya tsananta ta inda ta fara karkarwa tari ya sark'e ta har tana kokarin kifawa k'irjinta ta rike tam da hannu biyu sai tari take ga hawaye na zuba daga idonta. Hankali a tashe nayi kanta ina kuka wurjajan ina ji kamar in tashi in gaggaura Aminu mari, murya ta a sama nace." Ya Aminu ka k'yaleta mana baka ga tari ya sark'e ta ba."!!!! Ko kallona baiyi ba ya futa daga rumfar a fusace,!! Ni da Umma muka rike ta sosai muna dukan bayan ta duk mun gigice.!
Wata irin zufa ce take keto wa Baban su Munnu bayan ya gama sauran maganar da Amjadu yaje masa da ita, to son ya San meye dalilin da yasa Uban Mimi ya gudu ya barta ko zancan da jama'ar gari suke yi gaskiya ne.". Hankali a tashe Baban su Munnu ya fara magana kamar haka.
"Hak'ika Aishatu yar halak ce mahaifin ta Dan uwana ne cikin mu daya, mu 'yan kano ne gaba da baya yan Asalin unguwar Gyaranya dake k'aramar hukumar Dala, tun bayan rasuwar Matar shi wato Aisha mahaifiyar Mimi kenan ya ji zaman garin ya ishe shi bayan sadakar ar'abain ya tafi Neman kudi a cewar sa, yau shekara goma sha shida kenan, ban sanya shi a idona ba sai dai labarin sa yana zuwar mana sa'i da lokaci kuma kullum yar shi tana ranshi yana yi mata ake akai akai, Mariya yar mahaifiyar ta Itace ta dauke ta shayar da ita nonota lokacin tana goyon 'yar ta Asma'u sai ta had'a ta shayar dasu tare babu abunda zamu ce da Mariya domin ta cika jajurtacciyar macace. Wannan shine ainihin abunda yake faruwa." Kawu ya k'arashe maganar sa yana goge zufa.!!
Shima Nashi b'angaran wani irin faragaba da fad'uwar gaba ne ya riske shi lokacin da ya gama jin abunda Babansu munnu yake fada, hannunshi na rawa ya Ciro hankici daga aljuhunsa ya fara tsane gumin dake saman goshinsa, minti goma babu Wanda yayi magana a cikinsu, da kyar ya bude baki yace." Kana so ka fada mun cewar *Asma'u da Mimi* sun sha nono d'aya kenan."? Kawun su Munnu ya gyada kansa tare da fadin"k'warai kuwa."
Amjad ya sauke gwaron numffashi yace." Aurena da Mimi ya haramta idan Asma'u zan aura idan kuma Mimi zan aura aurena da Asma'u ya haramta.!!!!!!! Babansu Munnu ya tsinci kansa da shiga rud'u da fargaba Sam!! Ya manta da wannan k'aulin *Innalillahi wa innailahi raji'un*
*K'ak'a k'ara k'ak'a tsara*
*13/November/2019*
[11/14, 7:52 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*51*
Cikin yanayin damuwa Babansu Munnu yace." Wannan abu akwai rikita-rikita a cikinsa akwai daure kai, tunda ake wannan sabgar ban tab'a tunanin wannan alak'ar ba, Babbar magana ce wannan, tsarin na addini islama babu aure a tsakanin mutum biyu sai dai ka dauki daya ka bar d'aya, sun Riga sun tsotsi nono d'aya mutukar ba d'aya ce ta mutu a cikinsu ba, to baka da damar auran 'yar uwarta har abada, amma kasan ko wane ijma'in malamai da nasu k'aulin, Allah ne dai masani."
Babansu Munnu ya kare maganar sa cike da tararrabi yanzu idan Amjadu ya zab'i Asma'u ya bar Mimi wand irin hali zata shiga? Watak'ila ma karshen rayuwar ta yazo."
Amjadu jikinsa yayi wani irin sanyi tunda yake bai tab'a shiga rud'u da fargaba ba irin na yau, ko mutuwar iyayen sa bai shiga wannan halin ba duk da cewar mutuwar ta girgiza shi sosai wannan yasan dole ce ko wa sai ya d'and'ane ta.
Kusan mintuna goma babu Wanda yayi magana a tsakaninsu dukaninsu suna tunanin ya za'ayi su warware Matsalar, Mik'ewa yayi hade da mik'awa Baban su Munnu hannu sukayi sallama, ba tare da yace masa komai ba ya futa daga ofis din.
Yana shiga mota ya fara kiran wayar Kawu Yunusa buga daya ya dauka hade da yin sallama kamar zai masa sujjada, saboda kwantar da murya. Yace."Aure tsakanina da Mimi ya haramta saboda sun sha nono d'aya da Asma'u tun farko Asma'u ce zab'i na saboda haka na janye Neman auran Mimi ina rokon Allah ya fe min kuskurana, ita kuma Allah ya bata miji nagari."
Kawu Yunusa ya share gumin fuskarsa shima sai yanzu ya tuna da wannan alak'ar mamaki yake sosai me ya hana su tuno da haka sai da magana tayi nisa, idan hakane Ashe Aminu duk abunda yake akan yarinyr babu aure a tsakanin su."
"Kawu Yunusa yayi gyaran murya