Showing 33001 words to 36000 words out of 92177 words
Chapter 12 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
tada hankalinsa a kan hakan.
Da kyar Aminu ya futo daga d'akin sai yaji duk ya samu sauki ma domin halin da yaga Mimi a ciki ya tsora tashi babu shakka zai iya SADAUKAR da soyayyarsa a kanta domin ta rayu. Wannan shine sahihin so.da wannan tunanin ya futo.
Ya Tarar da tashin hankali a waje Inda Umma ta kasa nutsuwa ta tare wata narse tana share hawaye tana rokonta wai ta fada mata idan Mimi ta mutu shikkenan sai su hak'ura saboda d'azu da Dr ya futo Lokacin su Kawu Yunusa nan yake tambayar sa,lafiyar Aminu yace masa ya dawo dai-dai Ita Mimin ce bata dawo normal ba shine hankalin ta ya tashi .
Aminu yazo ya rike ta zuciyarsa nayi masa rad'ad'i da zugi ga wani irin jiri yana d'ibar muryarsa a shake yace." Kiyi hakuri Mimi lafiyar lau bata mutu ba, yanzu daga gurin ta nake." Umma ta rike hannunsa tana kallonsa cike da tausayi ta bude baki zata yi magana ya katse ta ta hanyar fadin "Umma na hak'ura da Mimi idan shine samun kwanciyar hankalinta na hak'ura ta auri Wanda take so. Umma ta rungume shi tana share hawayen ta tace." Aminu Allah yayi maka albarka Ubangiji Allah ya zab'a maka mafi alkairi a rayuwar ka, nagode da wannan karmanci da kayi min yarona ka fidda ni daga zargin mutane."
Rungume ta yayi tare da tausar zuciyar ta, Ni da aunt Hauwa muka kama ta muka zaunar da ita jikinta sai bari yake. A hankali Ya Aminu yace." Ni zan je gida in kwanta in huta jiri nake ji." Aunt Hauwa tace." Idan kana ganin babu matsala shikkenan. " gyada kansa yayi kawai ya bar gurin yanda yake tafiya zaka San ba shi da cikkakiyar Lafiya.
Tun lokacin da Ya Aminu ya fad'i cewar ya janye maganar auran sa da Mimi naji wani irin sanyi a zuciyata tayi wasai duk wani bacin rai da fargabar da nake ciki naji babu shi. Umma ma na lura ta sauya ta saki jikinta
Munanan zaune har sha biyu babu Wanda yake kokarin kwanciya ko gyangyadi muna sauraren futaw Dr wata narse ce ta futo daga d'akin da Mimi take Fuskata babu yabo babu fallasa tace." Wacece "Asma'u a cikin Ku."? Da sauri nace" Nice." Tace." Kizo maralafiyar nan da kuka kawo na Neman ki. Hamdala Umma tayi tare da fadin"Ta farfado kenan." ? Narse tace "Eh kusan awa biyu da farfadowar ta shine Yanzu tace." Wai a kira mata Asma'u." Umma tace." Maza jeki kiji kome ye ko kara kwantar mata da hankali." Da sauri na bi bayan nurse din.
Mimi na zaune ta jingina da jikin gado kanta a kasa tana wasa da hannunta kamar wata sokuwa ko kuma sabon shigar hauka duk ta sauya, cike da tausayin ta na zauna kusa da ita tare da fadin"Mimi gani menene."?
D'ago kanta tayi hawaye na bin kuncin ta, ta rike hannunwa tamau!! Bakinta na rawa tace." Habbity ya zanyi da rayuwa ta ne."!!!!? Ba kasaifai take kira na da wannan sunan ba, sai muna cikin damuwa da ni da ita.
Hannunta na rike sosai nace." Mimi ba dai *Amjadu* ba."? Shiru tayi min hawaye na zuba a idonta. Murmushi nayi me ciwo nace." Kamar kin aure shi kin gama an gama komai manya ma sun shiga maganar Ya Aminu kuma ya janye maganar auran ki, Yace ki auri Wanda kike so." Na k'arashe maganar fuskata dauke da murmushi na karfin hali.
Hannuna dake damk'e da nata ta matsaye sosai tana gyda kanta,bata CE min komai ba, minti biyu tsakani nace." Kuma d'azu yazo duba ki lokacin kina bacci ya dad'e ma tare da dr duk wasu hidima shine yayi, nima na amunce ya aure mu tare ki kwantar da hankalin ki."
Cikin nauyin baki tace"Nagode Habibty 'yar uwata ta kaina hak'ika kin cika 'yar halak Nagode Asma'u na rasa wata irin zuciya ce dani narasa wace iri ce ni, ki yafe min zuciya ta tafi karfina bazan iya sarrafa ta ba."
Murmushi nayi hade da rike hannunta nace "Ba laifin ki bane Mimi sharrin so ne kawai kowa ma haka tana iya faruwa dashi, kuma kinsan kowa da irin zuciyarsa wani yana da dauriya wani kuma bashi da ita, hakanan wani yana iya sarrafa zuciyar sa, wani kuma zuciyarsa tafi k'arfi sa, kamar ke kenan, hummm!! Yanzu dai magana ta wuce insha Allahu baki da miji sai Amjadu zakiyi rayuwa inuwa guda dashi."
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin wani irin murmushi Wanda dashi gwara kuka tace." Asma'u na Dade da sanin cewar *Jad* baya sona nice nake haukana a kanshi, ke yake so inda ke kuma baya gaban ki!! Ki bani shawarar Ya za'ayi na jawo hankalin sa kaina. "
Murmushi nayi ina mamakin Mimi da so ya rufewa ido ashe har suna ta sanya masa wai *Jad* humm!! Sunan kuwa yayi min dad'i. Domin in kara kwantar mata da hankali nace" Mimi ke kike abunki kar ki damu ni nasan da an d'aura aure zai so ki kamar ya mutu zai so ki fiye da yanda Ya Aminu yake son ki, Mimi kina da kyau kina da kira mai d'aukar hankali gaki fara alkyabar mata, babu namjin da zai kauda kansa daga kanki ki kwantar da hankalin ke dai."
Murmushi tayi hade da sunkuyar da kanta har yanzu hannuna guda na rike da nata.nace "Kinga wayar ki ma a hannuna Bari in kira miki shi Ku gaisa ko."?
Bata ce min komai ba, na fara kiran numbar shi, bugu daya ya dauka muryar shi da alamun bacci yace."
*HUSNAH."!* Sai da naji wani irin yarrrr! A jikina jin yanda ya ambaci sunana da ba kowa ne yake kira na dashi ba, ga muryar tayi low sosai kamar me mura. Ajiyar zuciya na sauke babu yabo babu fallasa nace"Ga Mimi za kuyi magana. "
Shiru naji yayi nace ."Hello." Gyaran muryar shi na ji yace." Owk bata wayar." Mimi na mik'awa wayar da murmushi a fuskata, hannunta na rawa ta karb'i wayar tayi sallama da dusashashiyar muryar ta.
Ina jinsa yana amsa mata a sake, yace." Ya jikin naki Momyna."? Tace." Jiki da sauki." Yace." Alhmdullahi ki kwantar da hankalin ki kinji ko duk abunda kike tunanin bazai yi wu ba to zai yi yuwu da izinin Allah idan Allah ya kaddara ke din matata ce Sai ki ga munyi aure, ki daina tashin hankalin ki, Tare da yardar 'yar Uwar ki ni na amunce zan aure Ku a tare ina fatan alkairi a kan haka, daga k'arshe nake ce wa dake ki godewa 'yar Uwar ki, domin tabbas ta sadaukar da nata farin cikin a kanki da samun fi gaban ki hade da lafiyar ki. Momyna hak'ika kin sa'ar 'yar uwa me kyawun zuciya."
Ya karasa maganar tasa cikin nutsuwa.
Ba Mimi ba ni kaina kalaman sa sun yi min dadi kuma naji dadin yabon da yayi min abunda bai tab'a faruwa ba ni dashi, bai tab'a fad'ar alkairina ba sai yau.
Murmushi naga tana yi kunne na kasa sosai ko zan ji abunda yake fada mata Wanda yake sata sakin wannan kayataccan murmushi, babu abunda nake ji daga b'angaran sa saboda ya k'ara yin kasa da muryar sa sosai, ita kanta Mimi sai ta kasa kunne sosai sannan zata ji abunda yake fad'a.
Ji nayi zuciyata nayi min wani irin zafi nayi saurin kauda kaina tare da ambatar innalillahi cikin zuciyata domin ji nayi take wani kunci ya ziyarce ta, zuciyar tawa sai take raya min kamar da akwai wani munafurci a ciki don me yasa zai dinga magana a waya kamar munafuki wannan bayi bane ni a ganina. Maganar da Mimi tayi ce ta dawo dani hayyacina , wayar take mik'o min tare da fadin"Yace." A baki wayar ku yi sallama."
D'aga murya nayi domin yaji nace"Mimi kashe wayar nan don Allah bacci nake ji, tunda dai kun gaisa dashi shikkenan dama haka nake so in sanya zuciyar ki farin ciki, kashe wayar mu kwanta Wallahi nayi bala'in gajiya."
Ga mamaki na sai naga Mimi ta kashe wayar kamar yanda na umarce ta ta aje wayar gefan kamar ba ita ta saki fuska sosai tana yi min hira. Mamakin ta kawai nake, nace ta kashe waya ta kashe babu kara bare tayi min magiya kan in karb'i wayar kamar yanda ya bukata, lokotan baya idan taga ina mishi wulakanci haushi take ji amma banda yanzu. Kwanciya nayi gefan ta ina lumshe idona sama-sama naji muryar narse na shigo tana tashina, na bude idona Wanda suke cike da bacci ina kokarin mik'ewa zaune.
Mimi tace" Ki k'yaleta mu kwana tare domin ko a gidama a tare muke kwana." Nurse ta futa bata kara magana, sama-sama muke yin hira da Mimi bacci yaci karfina ban San sanda ya kwashe ni ba.
Shida shaura na Safiya na tashi lokacin har masu bada magani sun shigo dakin sun bawa Mimi wacce take zaune dungurgur taki yin bacci saboda tsabar farin ciki, mik'ewa nayi ina hamma idona cike da bacci nace." Mimi shine baki tashe ni ba ko? Kinga na rasa sallah asubah."
Murmushi tayi tare da fadin "Asma'u naga a gajiye kike gashi kince bacci kike ji shiyasa na kyaleki kiyi hakuri." K'wafa nayi kawai na sauka daga gado toilet din dake cikin dakin na shiga.
K'arfe takwas dai-dai likita ya shigo ya gama aune-aunen sa kan Mimi kuma yaji dad'i da ya duba yaga yanda ta kwantar da hankalin ta, nan ya rubuta sallama hade da kara tausar Mimi sosai kan ta kiyaye ta daina saka damuwa a ranta. Nima kuma yace." Mu dinga sanya ido ankata sosai muna guje b'acin ranta.
9:00 am mun futo daga asibiti da bamu shigo da kaya komai ba amma zamu futa dasu niki-niki a hannu muna futa harabar asibitin wata shirgegiyar motar *Siyana* mai dauke da tambarin *A&A mai nasara* sabuwa dal! Ta shigo gurin, Dravar shi ne ya futo da sauri muka hada ido dashi. Saurin kauda kaina nayi daga kansa
Ya k'araso gurimu hade da zubewa gaban Umma yana gaishe ta ta amsa a sake, Ummansu Munnu ma ta amsa ita da aunty Hauwa, sai ya mike hankalinsa na kaina yace." Ranki ya Dade oga ne yace in zo in kaiku gida."
Cikin zuciyata nace shi kuma ko wa ya fada masa anyi sallama oho! Shiru nayi masa, aunt hauwa naji tana fadin"Aikuwa mungode dama yanzu muke tunanin a dai-dai ta nawa zamuyi damu da kayan mu." Na muka nufi motar kowa na fadin albarka cin bakinsa.
Duk yawan mu damu da kayanmu motar sai da ta dauke mu, hat guri Yayi saura doh-doh yaja motar muka tafi gida, Mimi ta sake sosai ina jinsu suna hira da Munnu ban tanka musu ba.
Goma shaura muka Isa gida Har ya danyi kura saboda rashin mutane a gidan kwana biyu kawai, ni da Aunt Hauwa muka fara aiki Ummi da Mimi kuwa na rumfa daga inda muke muna jin yanda Umma take rarrashin Mimi da kalamai Masu dad'i da kwantar da hankali.
******
Yau Kwana ki biyar kenan da bud'e sabon company me zaman kansa a jahar kano company *A&A mainasara* ya amsa sunansa sosai ya samu daukaka domin an fara gudanar da harkoki yanda ya kamata kullum a cike yake da baki daga garuruwa daban-daban sun shigo d'aukar kaya.
Hakanan Sauran company sa na waje suma komai ya kammala harkoki ake sosai da sosai Allah ya shiga al'amarin.
Sanye yake da wani yadi mai masifaffan kyau da tsada ni kam sai ince ma a jikinsa na tab'a ganinsa milk coulor ne mai sharashara anyi masa dinki boda yayi amfani da singlet black kana ganin shatin ta, bai sanya hula ba taje lafiyayyar sumar sa yayi wace take bakkirin sai shek'i take, ya gyara sajan sa kamar ko da yaushe ya feshe jikinsa da turaran shi na ko da yaushe, takalmi mai gidan ya tsa ya sanya a fararen k'afafun shi, blck ne sunyi masa kyau ba kad'an ba, hannunsa daure da agogon shi, na zallar fata fad'ar kudin shi ma b'ata wa ne, komai na Amjadu colour ne domin bai fiye amfani da Abu gama gari ba.
A nutse ya futo hannunshi rike da wayoyin shi, kana kallonsa zaka fuskanci akwai damuwa a tattare dashi Dan dai jarumin namiji ne me b'oye damuwar sa. Harabar gidan ya futa, Doh-doh da Rambow suna tsaye kamar dogarai suna ganinshi ya futo Rambo ya nufi inda yake shi kuma doh-doh ya fara kokarin futo da mota.
Wayoyinsa ya karb'a yana yi masa barka fa futowa a dakile ya amsa masa ya wuce shi kuma ya bi bayan sa, motar ya bude masa ya shiga ya zauna shi kuma ya zaga ya gurin zaman shi, motar ta futa daga gidan.
Sai da sukayi nisa sosai Doh-doh yace." Oga ina muka nufa."? Zaman shi ya gyara tare da Dan ya mutse fuskarsa yace." Muje gidan granny ko." Doh-doh yace." Angama sir."
Wayarsa guda ya karb'a gurin Rambo ya fara laluben numbar jiya yaji mugun haushi abunda tayi masa ta sanya Mimi ta kashe masa wayar wato bata buk'atar tayi magana dashi abunda yarinyar take ya soma b'ata masa rai, Sam bai saba ganin wannan shariyar ba a gurin 'yan matan da suke son shi, amma yana ganin dole zai rage zak'ewa a kanta ko zata gane muhumamcin sa.
Cikin ikon Allah da ya kira wayar itace ta dauka muryarsa shi a cunkushe ya amsa mata sallama minti biyu tsakani yace." Kina jina ko."?
"Umm." Abunda tace kenan. Yace." Munyi waya da dector d'azu an baku sallama shine na turo Doh-doh ya dauke ku a mota babu wata matsala ko."?
"Ummm."! Nace. Haushin yanda take masa yaji Umm da Umm sai kace wata kurma, k'aramin tsaki yaja yace." Yanzu zanje in dauko granny zata zo ta duba Momyna."
Sama-sama nace"Sai tazo." Kafin na an kara ya kashe wayar a fusace.! Tab'e bakina nayi nace "Kai ka sani kuma.
Umma na fad'awa zuwan kakar shi ta tashi ya fara shiri aunt Hauwa na shirin tafiya gida Umma ta hana ta wai ta tsaya su tab'i bak'uwa sosai a ka gyara gidan duk a ka kauda kayayyakin sana'ar Umma dasu ke rumfar tamu kamar su kalazinr galan din mai robibin magi da su d'aurikan busassan kayan miya rumfar tayi tas da ita Umma ta shimfid'a tabarma ta zauna jiran zuwan su.
Wani irin kamshi ne ya bugi hancin mu kafin muji muryar dattijiwar matar cike da nutsuwa da kamala tayi sallama.
Umma ta amsa mata tare da fadin"Sannu da zuwa maraba lale shigo ciki Hajiya."
Granny ta shiga ta zauna kan tabarma fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, suka gaisa da Umma cikin mutumci, aunt Hauwa ta gaishe ta hade da dauko mata Lemo mai sanyi hade da ruwan roba Wanda aka siyo mata shi mussaman, Granny ta bude ruwan tasha tayi hamdala, sannan ta kalli Umma cikin barkwanci tace. " Nazo duba kishiyoyina ne, kafin a Kai min su mu fafata da juna."
Dariya Umma tayi tace." Aikuwa dai, dole suyi miki ladabi domin shi kanshi uban gayyar da bazar ki yake taka rawa ba a raba hanta da jini kuma da tsohuwar Zuma ake magani."
Dariya Granny ta sanya tace." Ai ya juya min baya kwana biyu baya ta tawa kullum bashi da zance sai na kishiyoyina kin ga kuwa dole inyi kishinsu." Umma tace"In ya gama d'akinsa ai dolen sa ya dawo gurin ki." Dariya suka yi a tare aunt Hauwa ta mike tare da fadin "Bari a kira miki su Ku gaisa wai kunyar ki suke ji."
Granny tace." Wane irin kunya? Suna jin dai tsoron su hada ido dani tun kafin su shiga humm zasu aure min miji ai dole su b'oye je ki kira wo mun su." Aunt Hauwa ta futa tana Dariya tare da mamakin halin grnay kamar sun saba mata Mai fuska da fara'a gaskiya tana da kirki.
Tun lokacin da naji sallamar matar gabana yake fad'uwa har yanzu narasa ko ta menene aunt ta shigo tare da fadin "Sai kuzo Ku gaisa da ita ko." Mimi tayi s'aurin mikewa tana gyara hijab dinta ko jira na bata yi ba tabi bayan aunt Hauwa cike da mamaki nake bin ta da kallo ina mugun mamakin azarb'ab'inta da rashin kawaici lallai Allah mai mutane sai ga mutum yana Abu shi a ganinsa ba komai bane.
Muryar Umma naji tana k'wala min kira na amsa da sauri na dauki zurmemam hijabi na sanya na futa da sauri Mimi na zaune kusa da ita sai faman sunkuyar da kanta take tana murmushi nayi sallama granny ta daga kanta tana kallon Asma'u fuskar ka a sake tace" Zo nan kema ki zauna mu fahimci juna daku domin bana don Ku kwace min mijina."
Babu yabo babu fallasa naje na zauna kusa Da ita kaina a kasa na gaishe ta, ta shafa kaina tana fadin"Sannu Asma'u d'iyar arziki Allah yayi muku albarka gaba ki d'ayan Ku, Allah ya baku hakuri. Zama da juna kuyi ta hakuri da Mijinku domin wani irin mutum ne shi muskili kuyi hakuri da dabiun shi, gaku 'yan gida daya nasan baza a samu wata Matsalar ba ta fannin kishi tunda 'yan uwan junane Ku, Ku rike junanku da amana kunji ko Allah yayi muku albarka."
*12/November/2019*
[11/13, 7:59 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK