Showing 60001 words to 63000 words out of 92177 words
Chapter 21 - Babban Yaro Book 2 Hausa Novel Complete
shigo min da wancan banzan gida, ko an fada miki kowa ma irin ki ne."!
Murya ta na rawa nace"Kullum baka da zance sai gida-gida dai gida-gida wai meye a cikin gidan ne? Da har kake ihu! Ina ce duk gida sunan shi gida mutukar za'a shiga a kwanta a cikinsa, sannan za'ayi kashi da futsari a cikinsa, ko da ko gidan bunu ne Wanda aka yi da karare sunan shi, gida kuma bashi da maraba da Wannan da kake magana a kan sa."!
Mari! Ya kai mata a fusace! Yace." Ni kike kokarin fad'awa magana Cikin gidana, na fad'a gidana idan kinyi zuciya kar ki kara zuwa balantana kiyi min shirme dama rashin zuciya ne, tuntuni na fad'a miki bana son ganin k'afar ki a gidana ko. Ba haka ba."!? Ya fada cikin sigar rashin mutumci.
Cikin mugun takaicin sa nace"Tabbas gida gidan ka ne, kuma dole inzo gidan nan,tunda 'yar uwata na cikin sa, da bata cikin gidan kai kanka kasan babu abunda zai had'a ni da kai."
Tsaki yaja ya nuna ni da Dan ya tsaya "Wallahi wannan ne na farko da k'arshe a gurin ki ko da wasa kar ki kara shigo min da wani banza cikin gidana."
Cikin sigar kuntatawa nace"Mutum da kake magana akan shi ni yafi min daraja a kan ka, so ina mutukar jin ciwo idan ka zage shi."
A kufule yace." Owk don Allah kiyi gangancin sake shigo min dashi gida, Wallahi ke dashi sai na daure Ku! Duk iskancin da zakiyi kije kiyi shi a waje ya fi miki sauk'i ba sai kin kawo min gardi gida ba."!! Wani irin kallo nayi masa sai naga duk ya wani burkuce sai hura hanci yake!
Nasan na kular dashi
Nace"Allah sarki My Jahid hummm yanda ka dauke shi shi ba haka yake ba, a tunani na kai zaka yi shaidar shi, tunda ka rigani sanin sa, wallahi tunda nake dashi ko gyalena bai tab'a rikewa ba, balle har ta ja shi ga tab'a jikina."!
A hasale! Yace." Me kike nufi."?
Shiru nayi mishi ina kokarin barin gurin.
Jawo ni yayi da sauri ya matse jikin bango, muka fara kallon juna ni dashi. Murya ta na rawa nace"Kasan da wannan abun da kake aikata wa haramun ne ko? Idan da Kayi min iskanci son ranka yanzu ka tab'a ni ka tab'a haram! Kana auran 'yar uwata."
Sam! Baya cikin hayyacin sa, idonsa na can wuyan ta idan yake bin lafiyayyar fatar wuyan ta da gashi ya kwanta a gurin, lumshe idon sa yayi ya bude su a gurin, jiki na kyarma ya cusa fuskar shi tsakin gurin yana sakin wata shegiyar ajiyar zuciya, k'ugunta ya rungume da hannu d'aya Jikinshi na wani irin kyarma, sosai yake murza gemun shi a wuyan ta had'e da kuncin ta.
Wani irin masifaffan yanayi na shiga mai wahalar fassarawa gabobina suka yi wani irin laushi! Yayin da na fara Jin k'asa na ya fara tsiko.
Kamar yanda ya saba min duk lokacin da ya kusance ni, lumshe idona nayi, kokarin tuno addu'ar Neman tsari nake na kasa, gashi duk ya bi ya matse ni jikin bango tare da sake min k'arfin shi, zubewa nayi a gurin ina nishi!
Ya bini hade da Dora hab'arshi kafad'a ta, idanunsa sunyi wani irin ja, duk sun kankance fuskar shi, yake gogo mun a gefan fuska ta, tsigar jikina na mik'ewa, a hankali naji muryar shi na fad'i"Kin cuci ni.!!! Cikin zafin nama na mike ya maida ni da sauri, a hard'e yace." Babu inda zaki je sai kin bani sweet lips dinki na tsotsa, shine hukuncin ki."!!!!! Kallon Mara hankali nayi masa, da kyar! Nace"Kaji tsoron Allah a duk inda kake." Hannunsa ya Dora kan lips dina yana d'an girgiza kai yace." Ke tsoron sa kike ji? Me zai sanya ki saka wad'annan kayan a gidana."? Yafad'a yana kallon jikina, da k'irjina da suka futo Samar Riga.
Fuskar sa ya Dora a gurin yana murzawa.!
Wata shegiyar a jiyar zuciya na saki, tare da fashewa da kuka, nace" Ka Ubangji kayi min maganin ka" : Cikin wata irin shashsheka yace." Nima Allah yayi min maganin ki."!
Kauda kaina nake yi yana kara kusanto da fuskar sa, bakina. Bana son in bude bakin inyi magana hakan zai bashi damar yin abunda yayi niyya shiyasa na ki budewa, cikin shakakkiyar murya yace." Harshen ki kawai zan tsotsa in k'yale ki, ni shi kadai nake muradi." A zuciya ta nace ban tab'a ganin tantari irin guy nan ba
Hawaye ne ya cigaba da zubowa a idona hakuri nake bashi da ido ko da wasa naki bude bakina kar ya samu dama. "
Miskilin murmushi yayi yace." OK tunda kin ki bude min sweet month din bari in tsotsi sweets nipple din ki, da alama shi kike so in tab'a miki." Hannunsa ya sanya yana kokarin bank'are min k'irji.ihu! Na kurma!
Granny da Mimi suka nufo kicin din da sauri. Surutun granny yaji tun kafin su k'araso kicin din ya sa ya mike da sauri! Kofar da zata sada ka da store ya bude da sauri ya mai da kofar ya rufe.
Mik'ewa nayi da sauri sai haki nake yi. Rigata na gyara da sauri! Na dauki wuk'ar da ta fad'i kasa. Suka shigo kicin din.
Granny tace"Menene kike yin ihu!? Ina kuka nace"Granny yanke wa nayi."
Mimi ta k'araso gurin tana duba hannuna kuka ta sanya tace"Muje ki zauna na fasa cin miyar."
Nace"Mimi me zaki ci ki bari in k'arasa miki domin yau Zan tafi." Granny tace" A'a kije ki huta kinji yau dai daya."
Rike hannuna tayi muka futa daga kicin din gabana na fad'uwa.
Yana dai na jin motsin su ya futo yana Jan tsaki. Parlor ya shiga lokacin duk suna dakin Mimi. Kai tsaye dakin shi ya nufa, dole ya sake yin wanka, domin jikinsa duk ya b'aci ga wata irin kullewa da mararsa take masa, ba bu tantama dole ya nemi me biya masa buk'ata.
Kuka Mimi take min kar in tafi ita a ganin ta nice garkuwar ta a gidan nace"Mimi ciwo da lafiya duk na Allah ne ki kwantar da hankalin ki insha Allahu zaki samu lafiya."
Granny ta sanya bakin ta tace"Kiyi hakuri ki zauna mata tunda tana son zaman ki kuma tana walwala zaki samu lada gurin Allah, kinji ko, ubangiji Allah yayi miki albarka.'
Karamcin matar ya sanya na hak'ura amma ni kaina nasan zama a gidan hadari ne ina ganin mutumin nan zai iya fad'o min tsakar dare. Dole in dawo kwana da granny.
Sai daf da sallahr magrib ya futo daga dakin shi, lokacin muna zaune a parlor muna kallo ko ince suna kallo domin ni Sam bana Cikin hankalina.
Yana sanye da jallabiya ash coulor hannunshi rike da carbi me maddanai, yayi shirin zuwa masjid, Granny ta kalle shi tare da fadin"Au! Kana cikin gidan Ashe."? Babu walwala yace." Eh zan je massalaci."kallonsa nayi cike da wani irin tsanar sa, kullum yana nunawa duniya shi na Allah ne amma bayan fage yana aikata sab'o Allah ya shirye shi idan me shiryuwa ne.
Futa yayi ba tare da ya kalle mu ba, granny tace." Yau me zamu ci ne me mana girki ta yanke a hannu."
Mimi tace"Rambo yayi mana take away kawai.
"Ke kika San wani take away ni kam ban San shi ba, gashi me gidan ki ya dawo bai ci abunci ba kuma naga baki damu ba, ya kamata ki shiga kicin din in zaki iya kiyi masa girki ko."
Mimi tace"Granny baki San halinsa ba, wallahi zai iya cewa baya ci." Shiru tayi minti biyu tace"Nasan halinsa farin sani, amma bari inyi sallah ni da kaina zan shiga kicin din."
Kafin Isha'i granny ta kammala girki tsaf inda ta shirya jalop din macaroni da dankalin turawa hade da kayan Lambu da bushashen kifi
Kamshi ne kawai yake tashi.
Mik'ewa nayi ina taya shirya daining din tsaf ya shigo hankalinsa a kanmu ganin granny a tsaye a gurin ya k'araso da sauri yana fatan ita CE tayi abunci
Matsawa nayi daga gurin da sauri, ni yanzu tsoro yake bani.
Mimi ce ta hada masa abunci ta zauna kusa dashi
Yana ci suna hira sama-sama, ni da granny muna parlor a zaune. Mujahid yayi sallama ya shigo kamar yanda ya saba, babu iso babu komai yana ganin duk an zama d'aya.
*21/11/2019*
[11/22, 9:48 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*59*
Da murna granny ta tare shi tana fad'in"D'an halak yanzu nake zancan ka, a zuciya ta Ashe kana tafe."
Mujahid ya k'araso tsakiyar parlor fuskar sa a sake yake fadin" Ina shigo wa naga alamun mutumin ya dawo shiyasa ko gida ban shiga ba na shigo." Granny tace" Aikuwa ka kyauta. "
Daining din ya nufa yana fadin"Kai baka ce mun kana kan hanya ba, muje dauka ka."
Amjadu fuskarsa ya ya mutse Sam! Yak'i sakar wa Mujahid din yace." Akan me zan kashe maka aiki."
Jahid ya sanya dariya yana kallon Mimi yace." Kai kake ganin haka amma kafi k'arfin komai a gurina."
Shuru yayi masa ya cigaba da cin abuncin sa.
Mimi tayi saurin mik'ewa domin kar ya fuskanci komai tace"Dr zauna ina hada maka abunci."
Zama yayi kamar yanda ta umarce shi.
Yace." Madam lallai yau lafiya ta samu, har da shiga kicin."?
Mimi na hada masa abunci tace"Aikin granny ne."
Girgiza kansa yayi yana fadin " lallai yau zanci abunci me gamsarwa domin girki tsaffi daban yake da 'yara."
Granny ta sa Dariya domin duk tana jin hirar su tana parlor a zaune.
Ni kuwa tun shigowar sa na mike da sauri na bar gurin,
Saboda tun kafin ya zauna naga kallon wulakancin da Amjad din yake masa
Simi-simi ta Mimi ta hada masa abincin ta bar gurin.
Domin itama ta lura da kallon rainin da Amjad din yake masa Sam bata so ayi abun kunya.
Mujahid bude ciki yayi yaci abunci sosai suna hira sama-sama, Wanda shi Jahid din ne yafi magana Amjad sai ya ga dama yake amsa masa.
Tsaf suka kammala ko wanne ya goge bakin shi da tissue, Mujahid ya kalle shi, cikin nutsuwa yace." K'warai naji dadin dawowar ka wallahi."
Gyara fuskarsa yayi yace." Alhamdullahi, nima naji dadin dawowa Cikin nagode K'warai da kulawa Allah ya kara zumunci."
Jahid yace." Kar ka damu Aboki duk yiwa kai ne, nima ban sani ba ko akwai ranar da zaka yi min nan gaba."
Murmushi Amjad yayi halin Jahid yana burge shi guy akwai saukin kai Sam! Bai dauki duniya komai ba.
Mujahid yace." Cikin madam wata uku ne, amma hakikanin gaskiya tana cikin hadari tare da yaron dake cikin ta, domin NASA anyi mata scanning kuma Abu guda yake nuna min.
Twins ne daya cikin mahaifa daya bayan mahaifa, to amma kasan ba yadda Allah baya tsara al'amarin shi."" Wani irin shocking jikinsa yayi lokacin da yaji abunda Jahid yake cewa, da sauri yace"Please ka fada min in fahimta Dr akwai k'wayaye na cikin Mimi sai me kuma kace."?
Ganin Amjad din ya gigice lokaci guda yasa Jahid din yace." Tabbas hakane amma gurin kwanciyar kowa daban. Ma'ana kowa na da mahaifar shi, kuma d'aya yana zaune a wajen da ba'a so."
Wata irin zufa ce ta ke to masa.
Take ya ci wata irin fad'uwar gaba ta rikito masa.
Baki na rawa yace." Jahid meye abun yi yanzu, Ina son baby's dina duka."
Cikin damuwa Jahid din yace." Ka kwantar da hankalin ka, insha Allahu komai zai zo da sauki, aiki kawai za'a yi mata mugani tunda cikin bai yi k'wari ba, sai a cire shi akwai a huta."
Jim! Yayi yana tunani yace." Dr babu yadda za'ayi dole sai abunda ka fada."
Jahid yace." K'warai kuwa shi ne zamu samu Madam insha Allah Amma tabbas idan cikin jikinta ya kai wata biyar tabbas tana cikin hadari ita da baby."
Kamar zai yi kuka yace." OK amma babu abunda zai samu d'ayan ko." ? Murmushi Jahid yayi yace." Babu insha Allah mu fatan nasara muke yi."
Amjad duk ya rud'e Allah da ya hallice shi yana da mutukar son yara mussaman Twins shiyasa yanzu duk ya damu, wani irin tausayin Mimi da kaunar ta suka dura a zuciyarsa. Ya manta ma da haushin Mujahid din da yake ji.
Nan suka zauna suna tattauna maganar, cike da tausayi da al'ajabi.
A nutse na futo ina Jan jakar kayana.
Duk suka bini da kallo har shi uban gayyar.
Granny tace"ke 'yar nan ina ce ba mun kashe magana ba, ya kuma na ganki da jakar kaya a hannu."
Tsayuwa nayi bakin kofa babu yabo babu fallasa nace"Granny kiyi hakuri Don Allah, Umma babu lafiya zanje in kama mata aiki. Dama saboda mijinta baya gari ya sanya na zo, to tunda ya dawo zan tafi."
Mimi ta k'araso gurina da sauri ta rike jakar kayan, tana fadin "Me ye haka Habbity."?
Tab'e bakina nayi nace" Abunda kika gani sakar min don Allah in tafi gida haka."
Rau-rau idonta yayi tace." Please Asma'u wallahi in ina ganin ki cikin gidanan nafi walwala ina jin dad'i don Allah kar ki tafi."
Mujahid ne ya k'araso kusa damu ya Dan bata fuskar sa tare da kallona cikin tuhuma yace." Ya muka yi dake."?
Marairaice fuska ta nayi cikin sigir shagwaba da han hankali nace."My Jahid please Umma bata ji dad'i ba, zazzab'in nan da ake fama dashi, Yanzu ina shiga daki Ya Aminu ya kira ni a waya Dole ce ta sanya ni tafiya please. "
Jakar kayana ya rike yana kallonta kurr! Nasan sigar da nayi magana dashi ne yaja hankalinsa.
Murmushi nayi masa nace"Kayi hakuri kullum ai muna tare a waya ko."?
Daga kansa yayi kamar wani yaro Karami.
Amjadu yana zaune a daining duk yana ganin abunda yake faruwa haushi duk ya k'umshi ganin yanda Mimi take rarrashin Asma'u tana bata hakuri amma tayi buris da ita.
Da kuzari a jikinsa ya mike gami da Isa inda suke tsaye, Mimi yazo ya kama ya rungume yana rarrashin, shifa yanzu duk wani Abu da zai b'ata mata rai bai so, sosai yake rarrashin ta.
Tace"Hobby kace da ita kar ta tafi."
Kallona yayi da Jan ido ko bata fada masa ba yasan abunda zai sanya ta bar gidan
Yace."wai ke dole sai da ita zaki iya rayuwa ne? Uhumm! Kinyi aure kina da 'yan kin fita daraja ta ko wane fanni kike zubar da hawaye ki a banza ki daina wannan kuka kina ganin lafiya bata is he ki ba."
Jahid ne yayi masa wani irin kallo yace." Kalaman ka sunyi tsauri malam, itama Asma'u ta kusa shiga wannan sahu."!! Yanda Jahid ya fad'i maganar ne ya tabbatar masa da cewar ransa ya b'aci
Dariya yayi kad'an Dan ya kara tun zura musu zuciya yace." Ai ba karya bane sai ka bari idan ta hau wannan matakin kayi magana."
Ni kam nan tsaya jin karshen maganar sa ba na futa da sauri domin idan na tsaya zuciya ta tana iya mutuwa saboda yadda nake jin bakin cikin bak'aken maganganun da yake tafka min
Bayan ta Mujahid ya bi da sauri ba tare da yayi musu sallama ba, wani irin tsaki Amjadu din yaja ya ja hannun Mimi dake kokarin mayar da hawayen ta suka koma parlor
Granny tace." Ai yarinyar ma tayi kokari wallahi kam bana ganin laifin ta, ka shigo gida kamar wani mala'ika sai muzurai kake dole taji zaman gidan ya gundure ta."
Ba tan ka mata ba ya ja hannun Mimi suka shige dakin shi shi da ita zuciyoyonsu duk babu dad'i
Shi kanshi bai so tafiyar yarinyar ba a wannan lokacin Zata d'ebewa Mimi kewa sosai.
Mujahid ne ya kaini har gida muka yi sallama dashi cikin so da kauna alk'awari yayi min zai zo a sati nan, sai sa motar shi ta bar gurin na ja jakar kayana na wuce gida
Umma na zaune a tsakar gida tana d'aurin kayan miya duk da dare ne amma yara sai shigowa siyan kalanzur suke yi, nayi sallama na gidan.
Cike da mamaki take kallona tace"Kece da daddaran nan." ? Zama nayi kusa da ita INA fadin"Wallahi kuwa Umma ya dawo me gidan dama nagani da zama ." tace"Dama ba kyaso a tursasaki."
'Yar dariya nayi tace"Ya jikin Mimi INA fata da sauki kuma tana cin abunci."
Jim! Nayi ina tunanin maganar Da Jahid yayi min a mota game da Mimi ni tsoron fadawa Umma nake yi saboda nasan halinta Yanzu zata tada hankalin ta.
Kallona tayi tace" Kinyi shuru."?
"Umma jikinta da sauki Alhamdulilahi amma Jahid yace." Dole ayi mata aiki fa."!
Cikin fad'uwar gaba Umma ta aje farar ledar dake hannunta, tana kallona .
Nace"Wallahi haka yace domin hakan shine mafuta.
Take naga hawaye yana kokarin zubawa a idonta, muryar ta na rawa tace"Banji dadin wannan labarin ba Asma'u, nifa idan naji ance za'a yiwa mace me ciki aiki sai naga kamar mutuwa zata yi
Nace"Umma ki daina wannan tunanin insha Allahu Mimi zata sauka Lafiya ."
Shiru tay min tana goge hawaye. A fakaice.
Zuciya ta naji ta karya nima na meke da sauri jin hawaye yana kokarin zubo min mutukar nayi kuka a gaban Umma to itama kukan zata yi.
Dakinmu na shiga na tube kayan jikina yunwa nake ji sosai domin ban samu damar cin abunci da granny ta girka ba saboda fargaba.
Da d'aurin k'irji na futo nace"Umma Allah yasa da akwai ruwan zaki a Fula's Wanka zanyi." Ba tare da ta kalle ni ba tace"Da akwai cikin babban Fula's din nan."
Kicin na nufa da sauri na hada ruwan zafi a bokiti dauka nayi na shiga band'aki.
*******
Tsanin azabar da Mimi ta sha a wannan daran ya d'agawa Amjadu hankali domin kuwa a zaune suka kwana Mimi rungume a jikinsa, kamar ranta zai futa rik'on shi kawai take ya YAFE mata. Saboda tausayin ta bai San sanda ya fara zurarar da hawaye ba, rungume ta yayi tsam!! A jikinsa yana tofa mata addu'oi. Sai daf da asubahi bacci ya dauke ta, shi kuwa dungurgur ya kwana a zaune yana kallonta sai da yaji kiran sallahr sannan ya mike toilet ya shiga yayi Wanka ya futo tsaf shirin massalaci yayi yazo ya tsaya kanta, bacci yaga tanayi sosai, cike da tausayi yake kallon fuskarta inda idonuwan ta suka zurma cuki
[11/22, 8:02 AM] BintuUmarAbbale: Ko da ya dawo daga massalaci Mimi bata tashi ba, bai tashe taba sai ya zauna kusa da ita hade da rik'o hannunta ya