Showing 30001 words to 33000 words out of 72572 words
ya saki wata razananiyar kara ya nufe su da gudu ya riko Ash ya na fadin " Big bro calm down please you are going to kill him "
ina sam Ash ba ya jin shi yau ya kai makura dama ya gaji da iskancin da junior ke yi wa Rayan bayan idon su , ga tabar da ya ke sha a matsayin shi na Soja
Hannu daya Ash ya sa ya ture Vedad cen gefe ya fadi kassa har sai da ya saki kara , ya nufi Junior ya damko bayan keyar shi ya nufi Stair ya Tila shi dai'dai Iqbal ya fito da ga cikin part din shi dama karar da Vedad ya yi ce ta fido shi
ya na ganin Ash ya tila Junior ta stair ya nufe shi da sauri ya riko hannun shi ya na fadin " ya isa haka Big bro please za ka kashe shi "
a cen kassa kuma Junior na ida sauko stair Ummi da ke zaune a parlourn ta taso da sauri ta nufe shi , ta zube gaban shi ta talabo kan shi , sannan ta daga kai ta kali stair din , Ash na tsaye ya kurawa Junior idanu babu ko kiftawa , duk jijiyoyin jikin shi sun fito baro baro , idanun shi sun koma jazir har tsuma ya ke , ga Iqbal rike da hannun shi ya na rokon shi su tafi
A hankali Ummi ta girgiza mishi kai allamun ya isa
da sauri ya juya ya bar wajen ya nufi part din shi
Iqbal na shirin bin bayan shi Ummi ta ce mishi " Iqbal kyale shi , zo taimaka wa junior ya koma bedroom din shi , na duba shi "
gyada mata kai Iqbal ya yi kafin ya sauko stair din da sauri ya karaso geffen junior , su ka kama shi da Ummi su ka tada shi tsaye sannan su ka nufi stair su ka fara takawa da kyair su ka iso part din shi
kai tsaye bedroom su ka wuce da shi , su ka kontar da shi saman bed , sannan Iqbal ya juya da sauri ya fice Part din
ya na fita ita kuma ta bude box din bedside drawer ta fido A box ta fara duba Junior da ga nan ta yi mishi allurar barci sannan ta fito bedroom din ta fice part din
bangaran Ash kuma har zai shiga part din shi idanun shi su ka sauka kan Vedad , ya yi irin zaman bokaye ya sunkuyar da kai ya na kuka kassa kassa kamar baby
a hankali Ash ya lumshe idanun shi ya sake bude su a kan Vedad kafin ya mika mishi hannu
ba tare da ya dago kan shi ba ya daura hannun shi saman na Ash sannan ya mike tsaye su ka shiga cikin part din , kai tsaye bedroom su ka wuce ya zaunar da Vedad saman bed din shi , sannan shi ma ya zauna gefe ya na fadin " If you cry , I ........ "
bai kai karshen maganar shi Vedad ya saki kuka kamar karamin yaro ya na fadin " let me , ni ba na son ganin ka , kar ka sake yi min magana , dubi yadda ka tura ni sai da na ji ciwo , ni na bata da kai " ya kai karshen ya na mikewa tsaye zai bar wajen Iqbal ya shigo bedroom din babu ko sallama
da sauri ya taro Vedad ya rungume shi , Shi kuma Vedad sai kuka ya ke da duk karfin shi kamar baby
dan karamin tsaki Ash ya yi kafin ya mike tsaye ya nufi toilet dan shi a yanzu ba ya cikin yanayin da zai rarrashin Vedad
ya na shiga toilet din Iqbal ya ja Vedad su ka bar gidan kai tsaye su ka fice part din , maimakon ya meda shi bedroom din shi sai ya sauko stair da shi su nufi part din Nihal dan ya san bayan Ash ba wanda ke iya rarrashin Vedad sai Nihal
ko knocking bai yi ba ya tura kofar ya shiga ya na fadin " mummy ! mummy ! "
bai kai ga kiran na ukun ba , Nihal ta fito da ga cikin bedroom din ta , Vedad na ganin ta ya rabu da Iqbal ya nufe ta da gudu ya fada jikin ta ya na fadin " mummy , Big bro is wicked , duka na ya yi "
a hankali Nihal ta dago kai ta kali Iqbal irin kallon nan na karin bayani
kamar ko ya sani sai ya ce mata " Big bro ne su ka yi fada da Marshal , shi ne ya yi kokarin tare Big bro sai ya ture shi ya fadi kassa "
janyo Vedad ta yi su ka zauna saman sofa sannan ta sa hannu ta fara goge mishi hawayen shi ta na fadin " My angel please stop crying , ka san ba na son ganin ka cikin wannan halin "
noke mata kafada ya yi ba tare da ya ce komai ba
dan karamin murmushi Nihal ta yi kafin ta ce " Shikenan If you stop crying zan je na yi maka Pancakes "
a hankali ya fara rage sautin kukan shi ya na turo dan bakin nan na shi ya ce mata " Da gaske ? "
" da gaske My baby " ta fada ta na ci gaba da goge hawayen shi
mikewa tsaye ya yi ya riko hannun ya na fadin " to tashi mu tafi , ni yanzu na ke so "
mikewa tsaye ita ma ta yi ta na fadin " sai ka daina kuka sannan "
da sauri ya hannayan duka biyu ya goge hawayen shi ya na fadin " na daina shikenan , mu tafi yanzu "
" ba ka yi min murmushi ba "
dan karamin murmushi ya yi ya na shagwabe fuska ya ce " uhm uhm mummy mu tafi don Allah "
murmushi mai dan sauti Nihal ta yi kafin ta riko hannun shi ta na fadin su tafi , su ka fice parlourn Iqbal na biye da bayan su
bayan sun fita kai tsaye Kitchen su ka wuce , nan su ka tardo duk Chefs din su da ke shirya musu abincin
su na ganin Nihal duk su ka shiga sara mata su ka koma gefe su ka tsaya
Vedad kuma kabar ba shi ne ba me kuka yanzu , sai ya nufi babban cikin su duka ya na fadin " Chefs ku tafi duk na sallame ku mummy na za ta yi min Pancakes yau "
a hankali chef ya dago kai ya kali Nihal
gyada mishi kai ta yi ta na fadin " Za ku iya tafiya idan mun gama sai ku dawo "
a tare duk su ka sara mata sannan su ka nufi dayar hanyar fita kitchen din
har ya kai bakin kofar ya jiyo Muryar Nihal ta na fadin " Chef ko za ka iya fidomin kayan ban san inda su ke ba "
" yes madam " ya fada cikin girmamawa kafin ya dawo cikin kitchen din
ya nufi wasu closet ya fido mata Flour , Milk , Vanilla , bakin powder , Sugar , chocolate , maple syrop , sannan ya nufi fridge ya fido mata eggs ya kawo komai saman yar Desk din tsakiya ya ajiye , sannan ya koma ya dauko basket din fruits ya ajiye , da Bowl da whisk sannan ya nufi wani closet ya ciro stewpan ya daura saman gas cooker
da ga haka ya koma gefe ya na fadin " Ku na bukatar wani abu madam "
" no shikenan , za ka iya tafiya nan da one hour sai ku dawo " Ta fada ta na nufar desk din da kayan ke sama
jinjina mata kai ya yi kafin ya juya ya fice shi ma
TAแฆRIN ZแฆCIYA ๐๐บ๐
( RETแฆRN )
(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐๐ฅ
โค๐ ๊ช๊ช๊ชถ๊ชถ๊ชฦแปแญข แฉ๊ชนแปแญขแจถ๊ซเฐเฐ ๊ช๊ซ๊ซ๊ชน๊ช๊ซ ๐โค
๐๐
Wattpad : @bennybite
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐๐
ุงููููููู
ูู ุตูููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุตููููููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูุ ุงููููููู
ูู ุจูุงุฑููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุจูุงุฑูููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏู๏ธ
๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ
๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
๐๐๐๐๐๐
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
๐ง๐๐ฃ ๐ง๐๐๐ฆ ๐๐๐๐ ๐ง๐ข ๐๐ข๐๐ก ๐ ๐ฌ ๐ฃ๐ข๐ฆ๐ง๐๐ก๐ ๐ฅ๐ข๐ข๐
๐๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
_________________โฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆ__________________
PAGE ............7 ..........โค๐ฅ
bayan chef ya fita Nihal ta kali Iqbal ta ce " To kai malam da ka biyo mu sai ka dauki wuka ka fara yanke Fruits "
ta na gama rufe bakin ta Vedad ya daura da cewa " yawwa mummy , ni kuma zan kale ku idan kin gama na taba na ji in ya yi " ya kai karshen ya na Hayewa saman desk din
hannu Iqbal ya kai ya dunguri kan shi kafin ya nufi wajen da su ke ajiye knife ya dauko sannan ya dawo ya fara yankar fruits
Nihal kuwa ta dauki bowl ta zuba flour , bakin powder , vanilla flavour ta juya
sannan ta dauki wani bowl ta fasa eggs din a ciki , ta zuba two spoon ta Sugar ta juya sannan ta zuba milk din a ciki ta juya su ka shiga cikin juna , sannan ta Zube mixture din cikin ta flour ta juya da kyau
sannan ta nufi gas cooker ta kunna sannan dauki wannan mixture din da ta hada ta koma gaban gas cooker ta ajiye ta fara zubawa cikin pan din
kamar da ga sama ta ji an rungumota ta baya sai da ta dan firgita
a hankali ya kontar da kan shi saman shoulder din ta ya na fadin " mummy dayawa fa za ki yi , sai na kai wa big bro "
" sannu malam , ba yanzun nan ka ida cewa ba shi da kirki , kuma shi ne za ka kai mishi Pancakes din ka " Nihal ta fada ta na ci gaba da kula da Pancakes din da ke cikin pan din
" ba shi da kirki amma ai ni ina da shi ya sa zan kai mishi , mummy kin san favorite dish na big bro , ni fa ban taba jin ya ce ya na son cin wani abu ba , ko wanda a ka ba shi ba ya cinye shi dika "
" No gaskiya ban sani ba , bai taba fada min "
" To na Daddy fa , Tun da kin ce su na kama , kenan Favorite dish din su ma zai zo daya "
wani cool murmushi Nihal ta saki kafin ta ce " Ba zan iya fada maka favorite dish din shi ba , amma na san Daddyn ka ya kware wajen iya girki , ko ni ya fi iya wa "
da sauri Iqbal da ke bayan su ya ce " mummy ni fa ban taba ganin Daddy ya na girki ba "
" ni kadai ya san da wannan , amma ai kun sha cin abincin da ya girka da kan shi , ko First time din da Vedad ya ci Pancakes shi ya yi su , your father was an excellent chef , Har yanzu ni dai ban ga wanda ya iya girki kamar shi ba " ta kai karshen ta na sakin wani cool murmushi , maganar ta tuno mata First time da ta ci grikin shi , har yanzu ba ta mance taste din Kazar amarcin su da ya girka mata da kan shi
( ko mu ba mu mance ranar nan ba ko ya ? ๐คฃ๐คฃ๐คฃ๐คฃ๐คฃ๐ค๐ค๐ค )
ta yi nisa cikin tunanin ta ta jiyo Muryar Vedad ya na fadin " mummy zai kone "
a razane ta dawo cikin hayacin ta , ta cire Pancakes din da ga cikin pan din ta juye shi cikin wani plate
sannan ta zuba wani ta na fadin " Don Allah kun cika ni da surutu , dubi car wannan ta kusa konewa "
yar karamar dariya Iqbal da Vedad su ka yi a tare sannan Iqbal ya ajiye knife din hannun shi ya karaso a hankali ya kontar da kan shi saman dayan shoulder din Nihal cikin sanyin murya ya ce " mummy fadi gaskia mu ne mu ka dauke miki hankali ko dai tunanin Daddy ki ka shiga yi "
murmushin geffen fuska ta yi ta na fadin " and so what ? ku ne ku ka hana ni yin tunanin shi cikin konciyar hankali mana "
" mummy kenan ki na tunanin Daddy ? " Vedad ya fada
" Sosai ma , Specially inda ya ke ce min ina yi mishi wayo " Nihal ta fada ta na yar karamar dariya
" Ai Daddy gaskiya ya fada mummy ki na yi mishi waฦดo " Vedad da Iqbal su ka fada a tare
" oh haka nan ya ke fada muku ko "
" Ehhhhhh " Vedad da Iqbal su ka fada a tare da dan karfi , dan ba kariya ta yi ba kullum sai Aylan ya ce musu ta na yi mishi wayo
murmushi mai dan sauti Nihal ta yi ba tare da ce komai ba
a haka ta ci gaba da aikin ta , Vedad da Iqbal su na konce saman shoulder din ta , har sai da su ta gama ta dauki plate din Pancakes din su ka koma wajen desk din tsakiya inda Iqbal ya ajiye fruits din da ya yanke , sannan ta ce kowa ya shirya na shi plate ita kuma ta ficewar ta
a tare Iqbal da Vedad ko wane ya shirya plate din shi , sannan su ka bar kitchen din , shi Iqbal ya tsaya a parlour
Vedad kuma ya Haye stair ya tafi part din Ash
da sallama a bakin shi , ya shigo parlourn ya na rike da tray din da ya daura plate din Pancakes din a sama
Ash kuma ya na zaune saman Sofa Three seaters , ya na sanye da wasu pajama farare kal ma su bala'in laushi , ya daure wanan curly hair din shi a baya sai tashin kamshi ya ke
gaban shi Vedad ya karaso ya na ta sakin murmushi ya zauna kassan carpet ya ajiye tray din gaban shi ya na fadin " sauko mu ci , mummy ta gyara mana da kan ta " ya kai karshen ya na daukar Fork
shiru Ash ya yi bai ce komai ba , kawai ya zuba mishi wadanan sexy blue eyes din na shi
jin yadda ya yi shiru bai sauko ba ya sa Vedad dago kai a hankali ya kali Ash ya shagwabe fuska ya ce " ba za ka ci ba "
girgiza mishi kai Ash ya yi slowly ya bude bakin shi murya cen kassan makoshi ya ce " no fara ina zuwa "
da to Vedad ya amsa mishi kafin ya fara cin Pancakes din shi ya na murmushi kamar wani karamin yaro gwanin burgewa
shi dai Ash haka ya tsaya ya zuba mishi wadanan sexy blue eyes din na shi , ya rasa dalilin da ya sa ya ke ji da Vedad sama da Iqbal , kamar gudan jinin shi haka Vedad ya ke wajen shi , ko dazu mistake ne a ka samu ya na cikin fushi ya ture shi ba dan haka ba , ko hannu mutun ya daura saman Vedad da sunnan cutar wa sai ya ga bayan shi
ya yi nisa cikin tunanin shi kawai ya ga Vedad ya dago kai ya kale shi , bai ce mishi komai ba ya sakin mishi wani cool murmushi ya na fadin " big bro ni fa zan cinye duฦa " ya kai karshen cikin shagwaba
" Okay cinye abun ka " Ash ya fada dan ya san dama da wuya ya raga mishi , Vedad ya na mugun son Pancakes ba zai iya yin kwana daya ba bai ci ba
bai gama rufe bakin shi ba ya jiyo Muryar Iqbal ya na fadin " noooo , kar ka cinye raga min " ya kai karshen ya na karasowa cikin parlourn ya na rike da fork a hannun shi
da sauri Vedad ya dauki plate din ya mike ya koma geffen Ash ya zauna ya na fadin " ba zan bayar ba , ai ni mummy ta gyara wa "
marairaice fuska Iqbal ya yi ya na fadin " please my Cutie pie , wlh bai ishe ni ba "
" ni dai ba zan bayar ba " ya kai karshen ya na kauda kai gefe
a hankali Ash ya ce mishi " My angel ba shi mana "
dan karamin gunguni Vedad ya yi kafin ya sauko kassa ya na fadin " zo ka ci , amma dan big bro ne ya ce na ba ka "
dan karamin murmushi Iqbal ya yi kafin ya matso da face din shi ya kai dan bakin shi ya mannawa Vedad kiss a kumatu
wani cool murmushi Vedad ya saki kafin ya sunkuyar da kan shi su ka ci gaba da cin Pancakes din a tare , Ash na saman sofa ya na kallon su gwanin burgewa
( ina ma Aylan na raye ya ga Triplets din shi cikin wannan farin cikin ๐ญ๐ญ๐ญ๐๐ )