Showing 12001 words to 15000 words out of 72572 words

Chapter 5 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

327

hana ku yin bet ba "
Dum Vedad da Iqbal su ka ji zuciyoyin su sun yi muguwar faduwa , har wasu fitsari Iqbal ya ji sun taho mishi

Ash kuma tsaye ya ke bayan su ya rike hannayan shi a baya , ya na sanye da Trouser Black colour da T-shirt white colour , ya daure wannan darck black curly hair din na shi a baya sai tashin kamshi ya ke yi kamar wanda ya yi wankan turare

Wasu yawu Iqbal ya hadiye har hawaye su ka zubo mishi ya san yau tashi ta karre laifi biyu rana guda ya san yau sai ya yi jinya word room

Wata razananiyar tsawa ce Ash ya daka musu , ba su Vedad ba har shi junior sai da ya sha jinin jikin shi ya na zaro idanu
" Marshal kai min su dakin horo ina zuwa " ya fada ya na juyawa ya nufi part din Nihal
Da kallo su ka raka shi sai da ya shiga sannan Iqbal ya saki wani marayen kuka kamar karamin yaro ya na fadin " wayooo na shiga uku ni Iqbal , Vedad Allah ya isa tsakani na da kai , yanzu za ka janyo min "

Bai gama rufe bakin shi ba junior ya mike tsaye ya fara takawa ya nufi door din fita parlourn ya na fadin " zauna nan ka na kuka ya tardo ku , wlh sai na lahira ya fi ku jin dadi "
Ai bai gama rufe bakin shi ba su ka tashi da gudu su ka bi bayan shi su ka fice parlourn

Bangaran Ash kuma , a hankali ya shiga part din Nihal ya na sallama cen kassa kassa
Kai tsaye bedroom din ta ya wuce , ya na shiga ya isko ta zauna kassa ta jingina a jikin gadon ta kamar wata yarinya ta na kuka ga pics din Aylan duk zube a gaban ta

Bai ce mata komai ba ya karaso gaban ta , ya duka duk ya kwashe pics din nan ya bude box din bedside drawer ya saka su a ciki sannan ya koma geffen Nihal ya zauna a kassa shi ma ya na kallon gaban shi bai ce mata komai ba

A hankali ta fara rage sautin kukan ta , ta na sa hannu ta goge hawayen ta , ta gyara zaman ta , ta yi irin zaman cin tuwo
Sannu sannu har ta daina kukan baki daya Ash bai ce mata komai ba , ko kifta idanu bai yi ba

Sai da su ka share wajen 30 minutes a haka ba wanda ya ce ma wani ufan
A hankali Ash ya bude baki ba tare da ya juyo ba ya ce " mummy , na gaji da ganin ki cikin wannan halin , duk fa abun da ki ke yi ina sane da shi , impossible ne a ce rana guda ta wuce ba ki yi kuka ba ko da cikin dare ne , wani lokaci cikin barcin ki , ki ke yin kukan , Why mummy ? A ganin ki in ya san halin da ki ke ciki zai ji dadi ? Mummy you know , you are my power , you are my weakness and you are my happiness , duk lokacin da na gan ki cikin farin ciki ko ban nuna ba , cikin zuciya ta ina farin ciki , please mummy ki daina cutar da kan ki haka , ke kadai ki ka rage min a duniya don Allah kar ki jawa kan illar da za ta raba ni da ke "

Wani cool murmushi Nihal ta saki ta na daura hannun ta saman kan shi , a hankali ta dan sunkuyo da kan shi ta mana mishi kiss a goshi ta na fadin " shikenan my little , duk yadda ka so haka za a yi amma ina da sharadi "

Slowly ya juyo da kan shi ya daga mata gera allamun miye sharadin ?
Kara fadada murmushin ta ta yi kafin ta ce " ina son ka yi aure ka ga in ina ganin jikoki na zan rage wannan yawwan damuwar "
" ba banza ba Daddy ke cewa ki na yi mishi wayo " Ash ya fada ya kokarin mikewa

Da sauri ta riko hannun shi ta medo shi ya zauna ta na yar dariya ta kai hannu ta ja hancin shi ta ce " shi dai ya ke min wayo , yanzu maganar auren ka ? "
" soon " ya fada a takaice
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta ce " wlh ka fitar da matar aure idan mu ka je Nigeria ko kuma na yi maka irin yadda papi din ku ya yi mana , kawai sai jin na yi ya aura min Daddyn ku " ta kai karshen ta na sakin hannun shi

Mikewa tsaye ya yi ya yi taku biyu gaba sannan ya tsaya ya dan juyo da kan shi ya ce " mummy duk duniyar nan babu matar da ta kai na bude baki na ce ina son ta bayan ke , zancen aure kuma gwara ki bar shi dan ba zan taba yi ba " ya na gama fadar hakan ya sa kai ya fice

Da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta yi yar karamar dariya ta ce " yaro man kaza, ba ka san wuta ba sai ka taka , ni na ke da iko da kai ba kai je da iko da ni ba , Allah ya kai mu Nigeria wlh da matar ka za ka dawo ko ka ki , ko ka so zamu gani " ta na gama fadar haka ta sake bushewa da wata shegiyar dariya irin ta mugun ta


โ–ชASH ๐Ÿ”ฅ


Bayan ya baro part din Nihal kai tsaye part din shi ya koma , allamun ya manta da Su Vedad
Bayan ya shiga bedroom din shi a parlourn ya zauna saman sofa three seaters ya fido wayar shi da ga cikin aljihu ya fara latsawa
Bai fi five minutes ba da zama ya , Felix ya shigo parlourn ya na dauke da wasu bucket biyu na ruwa wanda a kila za su kai 30 liter na ruwa

Gaban shi Felix ya ajiye bucket din nan sannan ya sara mishi ya fice dakin , dai'dai lokacin da Junior ka shigo dakin Vedad da Iqbal na biye da bayan shi
Cikin dakin Junior ya karaso ya zauna saman sofa geffen Ash ya ce ma su Vedad su karaso ciki
Wasu yawu su ka hadiye kafin su ka karaso gaban shi su yi kneel down

Ba tare da ya dago kan shi ba Ash ya ce musu su shanye ruwan da ke cikin bucket din nan
Ba karamin zaro idanu Vedad da Iqbal su ka yi ba su na kallon bucket din gaban Ash , ai ko cikin kwana guda ba su iya shanye ruwan nan
" idan har ku ka bari na sake maimaita abun da na ce " Ash ya fada ba tare da ya dago kan shi ba

Nan take kuka ya kubce wa Vedad kamar baby har da shagwaba ya na fadin " Big bro don Allah ka yi hakuri wlh ba zan sake ba , duk Iqbal ne shi ya ce mu yi bet din ai , ni ban da kudi wlh " ya kai karshen ya na kara sautin kukan shi

Ya na gama rufe baki shi ma Iqbal ya shiga yin kuka ya na fadin " I'm sorry big bro ba zan sake ba "

Slowly Ash ya dago kai ya zuba musu wadanan sexy blue eyes din na shi , sai kuka su ke yi , Vedad har da majina ya na hadiyar zuciya
Shi kuma junior sai kumshe dariya ya ke , ya samu mugun ta
( munafiki ko shi ne a ka ce ya shanye fiye da liter goma ta ruwa lokaci guda ba zai iya ba , har da yi musu dariya ๐Ÿ˜‘๐Ÿ˜‘๐Ÿ˜‘๐Ÿ˜‘ )

Ajiye wayar shi gefe ya yi kafin ya mika wa Vedad hannu a kan ya zo
Da sauri Vedad ya matso gaban shi , ya na ci gaba da kukan shi
Hannu Ash ya kai ya kamo kunnen shi ya murde ya na fadin " nan gaba ko game za ku yi kar ku daura bet , na san ba yau ba ku ka fara , to yau shi ne na karshe in na sake kama ku da irin wannan laifin " ya na gama fadar haka ya saki kunnen Vedad , sannan ya kali Junior

Gyada mishi kai Junior ya yi kafin ya mike ya nufi table din da ke kassan makekiyar Tv plasma din parlourn ya dauko kwallin handkerchief ya dawo ya zauna saman sofar ya mikawa Ash

Hannu ya sa ya zaro handkerchief biyu sannan ya shiga gogewa Vedad hawayen shi , sai da ya goge mishi sannan ya ce ya tashi ya je ya sha fruits din shi ,
Ai ko da sauri Vedad ya tashi ya fice parlourn
Ya na fita Ash ya mike ya nufi bedroom din shi ya na ce ma Iqbal ya biyo shi
Ba musu Iqbal ya tashi ya bi bayan shi a hankali kamar wanda a ka yi wa dole
( ko da ya ke dolen ce a ka yi mishi ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ )

Bayan sun shiga bedroom din , zama Ash ya yi bakin gadon shi , shi kuma Iqbal ya yi tsaye gaban shi ya sunkuyar da kai sai jan majina ya ke yi
" dauko min waya ta " Ash ya fada mishi ya na kai hannu ya dauki laptop din shi da ke saman bedside drawer , shi kuma Iqbal ya juya ya koma parlourn babu kowa junior ya yi tafiyar shi , dauko wayar Ash da ya bari saman sofa ya sannan ya koma bedroom din ya ajiye ta saman bedside drawer ya koma gaban Ash ya yi tsaye






TAURIN ZUCIYA ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’

( RETURN )


( ROMANTIC LOVE STORY )๐Ÿ’‹๐Ÿ”ฅ



โค๐Ÿ‘‘ MALLAKIN MEERAH ๐Ÿ‘‘โค



ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒโค๏ธ



BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM



PAGE 4 โค๐Ÿฅ‚



TAแƒฆRIN ZแƒฆCIYA ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’




( RETแƒฆRN )









(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐Ÿ’‹๐Ÿ”ฅ







โค๐Ÿ‘‘ ๊ช‘๊ช–๊ชถ๊ชถ๊ช–ฦ™แป‰แญข ๊ช–๊ช‘๊ซ€๊ซ€๊ชน๊ช–๊ซ ๊ช–๊ช‰แฆ”๊ชฎ๊ช—๊ชถ๊ช–๊ช—๊ซ€ ๐Ÿ‘‘โค

๐—”.๐—ž.๐—” ๐€๐๐ˆ๐’๐‡โฅ ๐Ÿ•Š๐Ÿ’ž


Wattpad : @bennybite







Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )








FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐Ÿ‘๐Ÿ’•






ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ๏ธ







DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i








๐—ง๐—”๐—ฃ ๐—ง๐—›๐—œ๐—ฆ ๐—Ÿ๐—œ๐—ž๐—˜ ๐—ง๐—ข ๐—๐—ข๐—œ๐—ก ๐— ๐—ฌ ๐—ฃ๐—ข๐—ฆ๐—ง๐—œ๐—ก๐—š ๐—ฅ๐—ข๐—ข๐— 

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054













_________________โœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆ__________________











[ ๐Ÿ…ฟ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ…ถ๐Ÿ…ดฬฅ 4 โค๐Ÿ”ฅ ]






dauko wayar Ash da ya bari saman sofa ya yi sannan ya koma bedroom din ya ajiye ta saman bedside drawer ya koma gaban Ash ya yi tsaye , ya sunkuyar da kai

Cikin nitsuwa Ash ya dago kai ya kali Iqbal sannan ya ce " na san dalilin da ya sa ka yi bet din nan , next time in ka na bukatar kudi ka taho ka fada min , sannan wannan kukan da ka ke yi kamar Vedad ka daina shi , ba girman ka ba ne , idan mu ka dawo da ga Nigeria za ka fara karbar horon soja "

Gyada kan shi Iqbal ya yi bai ce komai ba , har ga Allah ba ya son zama soja amma tun da Ash ya ce zai fara ba shi horon soja babu wanda ya isa ya hana shi

Ya na haka ya ji wayar shi da ke ciki trouser din shi ta yi ruri
Shi ya ma manta da Ash na gaban shi kawai ya kai hannu ya ciro wayar da ga cikin aljihun shi ya na duba text din da ya shigo , nan ya ga One hundred Millions of Dollars da Ash ya turo mishi cikin account din shi

Bai san lokacin da ya saki wani kyawatencen murmushi mai sauti ya nufi Ash da gudu ya rungume shi ya na fadin " Thanks a lot my big bro "
" okay sake ni yanzu "
Da sauri Iqbal ya sake shi ya na fadin " Sorry sorry "
Kallon shi da kyau Ash ya yi kafin ya kai hannun shi ya yi mishi dan karamin mari ya na fadin " nan gaba ka fara tabbatar ka na da kudi kafin ka yi mata alkawarin fita shan ice cream , duba cikin dayar bedside drawer akwai Cash ka dauki wanda zai isar ka "

Kara fadada murmushin shi Iqbal ya yi da sauri ya tashi ya nufi dayar bedside drawer ya zauna bakin gadon ya bude box na farko , cike ya ke makil da dollars bandir bandir a jere tsab , ko ni sai da na hadiye yawu

Cike da zalama Iqbal ya kai hannu ya fara debar kudin nan , akkila sai da ya dauki wajen bandir goma kafin ya rufe box din ya taso ya dawo gaban Ash ya dan sunkuyar da kai ya manna mishi kiss a kumatu ya na fadin " na gode big bro "
" in ka wuce karfe 8...... "
Da sauri Iqbal ya katse shi da cewa " karfe 6 ina cikin gidan nan ba za mu jima ba " da ga haka ya sa kai ya fice part din baki daya ya koma part din shi

Da kallo Ash ya raka shi sai da ya fita , har ga Allah ya na mutuwar son ganin yan uwan shi cikin farin ciki , duk lokacin da ya gan su cikin farin ciki ji ya ke ba ya da bukatar wata mace a kusa da shi in har zai ci gaba da ganin su a haka
Ko yanzu kawai dan ya ba su tsoro ne ya ce su shanye ruwan nan , amma shi da kan shi ya san ba za su iya ba , amma ba ya son su na yin bet , ya san kuma ba wanda ke kawo shawarar nan , sai Iqbal , dan shi Vedad wani sha tara ne , duk Nihal ta tsangarta shi , in ya na son kudi kai tsaye ya ke tambayar shi ba ya jin tsoro , Iqbal nai de ko ya na son kudi sai dai ya je wajen Nihal ko Ummi dan ya san ba za su tambaye shi ba me zai yi da kudin , Ash kuma sai ya yi mishi tambaya fiye da goma ,

Iqbal na fita ya dauki laptop din shi ya ci gaba da aikin shi
Shi kuma Iqbal ya na baro part din shi kai tsaye ya koma , ya na shiga ya wuce toilet ya yi wanka , ya fito ya shirya cikin trouser white colour da t-shirt navy blue , ya daura wata jacket White color , kafafun shi kuma cikin wasu sneakers Navy blue ma su mugun kyau sai tashin kamshi ya ke , ya yi kyau over , a haka ya sa kafa ya baro cikin gidan , ya nufi parking space ya shiga wata dankareriar mota Fara kal , har wani kyali ta ke yi na daukar ido sannan ya bar gidan da mugun gudu

Ya dauki wajen Good ten minutes ya na driving kafin ya iso bakin wani makeken Building na apartments , Building din ya na da girma sosai a killa zai kai hawa 100

Ya na isowa Bakin kofar shiga Building din ya yi parking din motar ya dauki wayar shi ya rubuta text sannan ya meda ta ya ajiye ya hada kan shi da steering motar

Bai fi five minutes wata Kyakyawar budurwa ta fito da ga cikin building din ta karaso wajen motar ta nufi bangaran mai zaman banza ta bude ta shiga , ta na sallama kassa kassa
Yarinyar kyakyawa ce ba laifi a shekaru za ta kai 20 years haka , amma da ga gani ba cikakiyar baturiya ba ce , fara kal da ita amma duk da farin ta Iqbal ya fi ta dan Haske , ta na sanye cikin wata Gown white colour har kassa mai mugun kyau ta sha ruwan stone , ta yi Rowling veil din ta navy blue a kai , ta yi simple make up , abun dai Masha Allah

Ya na jin ta rufo kofar motar ya dago kan shi slowly ya juyo ya kale ta
Wani kyawatencen murmushi ta saki ta na daga mishi gera guda
Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login