Showing 66001 words to 69000 words out of 72572 words

Chapter 23 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

342

daban , yanzu kuma abun da Iqbal ke fada mishi daban , tabass akwai wata a kassa , shi ya san akwai wani boyayen al'amari a cikin familyn shi wanda ba a fada mishi ba , amma Maya ita kuma da ga ina , ta ya za ka mance mutumin da ka ke so haka lokaci guda har ka manta a ina ku ka hadu tabass akwai wani abu a kassa

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Iqbal ya na fadin " Big bro tunanin mi ka ke haka ? "

slowly ya dawo cikin hayacin shi kafin ya ce mishi " zan iya ganin Pics din ta ? "

gyada mishi kai Iqbal ya yi kafin ya kai hannu cikin Aljihun trouser din shi ya fido wayar shi ya fara latsawa
sannan ya mikawa Ash wayar ya na fadin " ga ta nan "

hannu ash ya kai ya karbi wayar ya na kallon Screen din
slowly ya dago kai ya kali Iqbal kafin ya Meda kallon shi kan wayar , sannan ya mikawa Iqbal kayan shi

hannu ya kai ya karba sannan ya mike ya fice dakin
da kallo Ash ya bi shi har sai da ya fita sannan ya kai hannu cikin aljihun shi ya fido wayar shi ya fara latsawa

sai da ya dauki wajen good five minutes kafin ya kai wayar a kunne murya cen kassan makoshi ya yi sallama sannan ya ce " in sha Allah next week ina dawowa US , akwai wani abu da na ke son mu tatauna a kai " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran ya ajiye wayar saman table sannan ya mike ya nufi toilet ya shiga


▪MISALIN KARFE 12 NA DARE


▪HAYAT 💦



A hankali ta fara motsi ta na kokarin tashi
ta na bude idanun ta ta fara tari , ta na kai hannu ta na shafa wuyan ta
slowly ta mike zaune ta na karanto kalmar shahada , ta na bin dakin da kallo kamar bakon ta

sai da ta dauki good ten minutes a haka kafin ta sauko da kafafun kassa ta mike tsaye ta nufi kofar fita dakin ta fito parlour
kai tsaye part din ta fito ta na tafiya a hankali kamar wanda a ka zarewa lakar jiki

a haka har ta fito parlourn gidan , amma sai ta ga ba kowa tsaya wa ta yi ta na bin wajen da kallo ta na cewa " Aunty Ummi ? "
ta fada ta na karasowa cikin parlourn tsaya wa ta yi ta na bin wajen da kallo amma ba kowa ita sam ba ta san da dare ya yi ba saboda Hasken wajen

Slowly ta juyo za ta bar wajen kawai sai ji ta yi ta bugi kirjin mutun
da sauri ta yi baya ta na cewa " yi hakuri " ta kai karshen ta na dago kai ta kale shi

dum ta ji zuciyar ta ta buga da ci karo da wadanan Sexy blue eyes din na shi nan take duk abun da ya faru ya dawo mata a kai

har ta bude baki za ta saki kara ya yi sauri ya kai hannu ya toshe mata baki ya na kallon cikin idanun ta ya ce " idan ki ka kuskura ki ka yi min kara sai na kashe ki a wajen nan "

wasu wahalalun yawu ta hadiye dan ba karamin razana ta yi ba specially da ta tuno irin shakar da ya yi mata dazu da safe nan take tsoron shi ya shige ta

slowly ya zame hannun shi ya ce " wacece ke , su wa su ka aiko ki , me ya sa ki ka kashe matar nan ? "

a hankali ta fara girgiza mishi kai ta na cewa " ni ban san abun da ka ke cewa ba " ta fada dan da turanci ya ke mata magana

a dubu dari ya kai hannu ya damko wuyan ta ya ware idanun shi da kyau ya na kallon cikin nata ya ce " kar ki ce za ki raina min hankali , su wa su ka aiko ki na ce "

nan take idanun ta su ka kawo ruwa hawaye na zubo mata ta lumshe idanun ta dan ba za ta iya jure kallon cikin nashi ba

rage shakar da ya yi mata ya yi kafin ya ce " open your eyes "

slowly ta fara bude idanun ta , sai cikin nashi ko
Dum ya ji zuciyar shi ta buga , ba shiri ya saki wuyan ta ya ja da baya
slowly ya juya ya ba ta baya ya lumshe idanun shi cikin zuciyar shi ya na cewa " Alyasat ka kontar da hankalin ka , it's just a dream , dream it's not true , it can't be true Never "

ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bude idanun shi ba tare da ya juyo ba ya ce mata " Wacece ke , minene sunan ki ? "

murya na kerma ta ce mishi " suna na Shahd " ta kai karshen kamar za ta yi kuka

dan zaro idanu ya yi ya na maimaita sunan cikin zuciyar shi cen kuma sai ya ce mata
" matar da ki ka kashe wacece ita , minene hadin ki da ita ? "

a hankali ta saki kuka ta na cewa " ni ban kashe ta ba , sayar da ni ta so yi shi ne na gudu , don Allah kar ku kaini wajen yan sanda "

bai ce mata komai ba ya nufi stair ya haye ya koma part din shi

ta na ganin ya haye stair ta nufi corridor da gudu ta shige part din Ummi , ta koma bedroom din ta ta Haye gadon ta dunkule waje guda ta na kuka ta na fadin " ni wajen Inna ta zan koma , don Allah ku meda ni wajen inna ta " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta
a haka har barci ya dauke ta


▪ASH 🔥


kai tsaye part din shi ya koma ya na shiga bedroom din shi ya ga Vedad konce saman bed din shi ya yi daya daya ya na barci
bai ce mishi komai ba ya nufi toilet ya shiga ya yi wanka
jim kadan ya fito sanye da bathrobe ya shiga dressing room ya shirya cikin kayan barcin shi farare kal , ya nufi bed din shi ya Haye geffen Vedad ya konta ya kai hannu ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps ya kara gudun ac sannan ya lumshe idanun shi

ya na lumshe su ya jiyo Muryar Vedad ya na fadin " Big bro , ka ce mata ta baro min bedroom di na " ya kai karshen cikin shagwaba

slowly Ash ya juyo ya kale shi ya ce " My angel , kai da wa kuma ? "

a hankali Vedad ya bude idanun shi ya turo dan bakin nan nashi ya ce " ba da kai na ke ba , ni ka je ka ce mata ta baro min bedroom "

cikin rudu Ash ya ce mishi " wacece cikin bedroom din ka ? "

" Big bro ni ma ban san ta , kawai da na rufe ido na , sai ta yi ta tabo ni , ni ka je ka ce mata ta baro min bedroom ko kuma na kwana a nan "

" me ya sa kai ba ka taba ta , tashi ka je ka ce mata ta kyale ka , ko kuma ka kashe ta " ya na gama fadar haka ya juya ya na fuskantar ceiling ya lumshe idanun shi

kukan shagwaba Vedad ya fara yi mishi ya na fadin " big bro , ba ta jin magana ta , sai da na ce mata ta kyale ni amma ta ki dainawa , ita wai sai ta ga abun da ke cikin trouser di na "

ya na gama rufe bakin shi ya jiyo Muryar Iqbal ya Bushe da dariya
ashe tun lokacin da Vedad ya fara magana ya ke tsaye bakin kofar dakin ya na sauraron shi
sai da ya Kamala dariyar shi sannan ya shigo dakin ya na sanye da kayan barcin shi , shi ma farare kal kamar na Ash ya nufi bed din ya Haye

ya na kallon Vedad ya ce " Cutie pie , irin wannan mafarkin ka fara yi kennan ? "

hararrar shi Vedad ya yi ya na fadin " ni ba mafarki na yi ba , kuma mu je ka gan ta cikin bedroom di na , ka ce mata ta bar min bedroom "

dariya sosai Iqbal ya yi har da kontawa ya na dafe ciki
kukan shagwaba Vedad ya shiga yi mishi ya na fadin " ni ka daina min dariya ko na fadawa mummy "

tsagaita dariyar shi Iqbal ya yi kafin ya matso da kan shi ya kai bakin shi saitin kunnen Vedad ya rada mishi " ka na ji ko Next time idan ta dawo ka kyale ta , ta duba abun da ke cikin trouser din ka , da ga nan ba za ta sake dawowa ba "

noke mishi kafada Vedad ya yi ya na cewa " no ni ba zan kyale ta ba , sai dai mu je ka ce mata ta kyale ni , ko kuma na sa gun na harbe ta "

" ba sai an kai ga haka ba , kai dai ka kyale ta ta duba za ta ga abun da ya fi karfin ta "

" da gaske ? " Vedad ya fada ya kallon Iqbal ta wutsiyar ido

gyada mishi kai Iqbal ya yi ya na sakin wani makirin murmushi

a hankali Vedad ya mike zaune , Ya kai hannu a hankali ya riko wandon barcin Ash ya yi sama da shi ya leka

dan karamin tsaki Vedad ya saki kafin ya saki trouser din Ash ya juyo ya kali Iqbal da ke faman Zaro idanu ya ce " yo ai ni ban ga abun da ya fi karfi na ba " ya fada dan ya ga Ash ya na sanye da Short kassan wandon shi

Iqbal bai ce mishi komai ba ya sauko da kafafun shi kassa , ya fara takawa a hankali kamar barawo ya nufi hanyar fita bedroom din

sarai Ash ke lure da shi , sai da ya bari ya kai bakin kofar dakin sannan ya diro da kafafun shi kassa a dubu dari ya damko shi ta baya ya daga sama ya tila shi saman bed geffen Vedad

wata yar karamar kara ya saki kamar zai yi kuka ya ce " wayooo mummy ya karaya min baya "

da sauri Ash ya ce mishi " yi min shiru ko kuma na harbe ka " ya na gama fadar haka ya koma inda ya taso ya konta ya lumshe idanun shi ya aza hannun shi guda saman forehead din shi

dariya sosai Vedad ya ke ya na kallon Iqbal da ke faman murkuso saman bed din ya marairaice fuska kamar zai yi kuka

ya na tsaka da dariyar shi Ash ya kai hannu ya damko bayan wuyan shi ya na fadin " kai kuma me ka ajiye cikin trouser di na ? "

shagwabe fuska ya yi ya ce " Iqbal ne ya ce min na duba zan ga abun da ya fi karfi na "

da sauri Iqbal ya ce " Wlh big bro ban ce ba ya duba , Vedad sharri za ka min "

Vedad na shirin magana Ash ya ce musu " ku yi min shiru , zan yi maganin ku , ku tabbatar na tarda ku a dakin horo gobe " ya na gama fadar haka ya janye hannun shi da ga bayan wuyan Vedad ya Meda saman cikin shi ya lumshe idanun shi

dan karamin gunguni Iqbal ya shiga yi murya kassa kassa ya ce ma Vedad " bari mu koma part din mu za ka ga aiki na "

murguna mishi baki Vedad ya yi kafin ya juya ya rungume Ash kamar ya samu wani Teddy ya lumshe idanun shi , ba jimawa barci ya yi gaba da shi haka zalika Iqbal
Ash kuma dama ba barci ya ke ba , kawai dai ya lumshe idanun shi
ko cen dama ba wani barci ya ke ba , dalilin da ya sa ma ya ke yi wa kan shi Allurar barci dan sai ya yi kwana uku idon shi biyu kuma babu gajiya dan kamar robot ya ke
tun lokacin da Aylan ke a raye da ya fara ba shi training din Soja ya koya mishi wannan rashin kwanan , dan sai ya saka shi cikin daki ya ce sai ya yi kwana biyu a ciki kuma kar ya sake ya rufe idanun shi da sunnan zai yi kwana da haka har ya saba
bayan ya shiga millitary camp kuma nauyin barcin shi ya bace , dan ko nunfashi sama sama ka yi geffen shi in ya na barci sai ya farka , wani lokaci idanu bude ya ke barci
duk cikin training din da ya samu ne , Ash fa soja ne mai zaman kan shi dan karyar mutum ya ce zai gwada mishi training din soja duk girman kato in Ash ya buge shi sai ya kai ga kassa
a headquater din su da ya shigo waje kowa ke shan jinin jikin shi , ko wata magana za a yi mishi sai dai a fadawa Junior sannan ya je ya fada mishi , sam ba ya sakin musu fuska , kullum ta na a tsuke ya saka bakaken glass , dan wadanan sexy blue eyes din nashi kadai sun isa tsoratar da mutum ,
tun bayan rasuwar Aylan ya daina sakin fuska , ko murmushi yanzu tsawan shekara 15 har yanzu bai sake yin shi ba har ya ma manta yadda a ke yin shi
dama dama in ya na gida ya na sakin musu fuska ya yi wassa da Vedad amma kuma in ya bata mishi sai Nihal da Rayan sun kwace shi dan dakin horo ya ke tafiya da shi sai ya kwana a ciki babu ruwa babu abinci
ga shi kuma ba ya daukar raini , ko Rayan da kan shi ya yi wa Ash maganar rainin hankali sai Nihal ta shiga tsakanin su dan ba ya kyale shi , da ya tashi dauko Zuciyar Aylan sai da ya wuce shi
ga kuma training din kwararen soja da ya samu zuciyar shi duk ta bushe ba dan ya na ganin girman Nihal a matsayin ta na mahaifiyar shi ba na san da ko ita ba zai kyale ta ba


▪MISALIN KARFE 5 NA SAFE


misalin karfe biyar na safe bayan sun Kamala sallar asubahi , Nihal ta shirya za ta mayar da Hayat kauyen su tare da Vedad da Iqbal , tafiyar ta su ta wayo ce dan su tserewa Ash , Ummi kuma ta ce ita ba za ta je ba za ta jira su a gida

cikin mota guda Nihal da Hayat su ka shiga , Vedad da Iqbal kuma su ka shiga mota guda , sai motocin guards din su a haka su ka baro gidan su ka kama hanyar Niger
Hayat baki ya ki rufuwa yau za ta koma gida kamar ta yi furkakai ta ga kan ta cikin gidan su
Nihal kuwa ba da Niyyar baro Hayat za ta je , tabass da ita za ta dawo



▪NIGER ( KAUYEN NAWACH KALE )


▪ MISALIN KARFE 2 NA YAMMA


zaune Barira ta ke cikin harabar gidan su , ta yi zugum waje guda duk ta rame har wani duhu ta yi , yanzu wajen sati guda kenan ba Hayat ba me kama da ita , har mutanan kauyen sun daina cigiyar ta

ta na a haka Inna ta fito da ga cikin Dakin ta , ta karaso wajen tabarmar da Barira ke zaune ta zauna ita ma cikin sanyin murya ta ce " Barira , wai har yanzu ba za ki daina damuwar kan ki ba "

wani dogon nunfashi Barira ta ja kafin ta ce " Inna ya ki ke so na yi , kin fi kowa sanin Hayat ita kadai na mallaka , ba zan iya rayuwa babu ita ba , ni yanzu babban abun da ke damu na shi ne halin da ta ke ciki , ta na cikin koshin lafya , ta na hannun mutane na gari ko kuwa , inna don Allah ku kawo min Hayat di ta " ta kai karshen ta na fashewa da kuka

ba karamar karayawa Inna zuciya ta yi ba da kukan nan nata , tun da ta auri malam ba ta taba samun haihuwa ba , car Allah ya yi wa kanwar shi rasuwa su ka kamo Barira ta dawo wajen su da zama tun ta na da shekara bakwai , har ta yi aure ta haifi Hayat dole ta ji ba dadi saboda ita kadai ce yarinyar ta , ita kadai ce jika a cikin gidan idan wani abu ya same ta tabass ba za su ji dadi ba

cikin sanyin murya Inna ta ce ma Barira " Don Allah ki kontar da hankalin in sha Allah ba abun da zai same ta "

da sauri Barira ta katse ta da cewa " to inna ina ta ke , in har ba abun da ya same ta me ya sa ba ta dawo gida ba ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login