Showing 6001 words to 9000 words out of 72572 words
macen da ta isa na zube saman guyiwowi na gaban ta , wai da sunnan hakuri , uncle har yanzu ba a yi ta ba " ya kai karshen ya mike wa tsaye ya fara takawa ya fice dining room din
Da kallo Rayan ya raka shi har sai da ya fice dining room din sannan ya bushe da dariya ya na fadin " za ka shigo hannu kai ma " da ga haka ya ci gaba da cin abincin shi har ya ma manta da maganar da su ka yi shi da junior
Bangaran Ash kuma kai tsaye stair ya Haye , wajen kamar dan balcony ne , an saka mishi wasu sofas farare kal kamar parlourn
Part bakwai ne a saman , na farko shi ne na Rayan , na biyu kuma na Ummi , sannan na Iqbal , sai na Vedad , da na Junior shi kuma Ash na shi ya na karshe kuma duk cikin part din na shi ya fi girma
Kai tsaye part din shi ya nufa , har ya wuce part din junior ya tsaya cak
Slowly ya juyo ya nufi door din , ya daura yatsar shi saman finger print , saboda duk kofofin da finger print su ke buduwa
Ya na daura wa kofar ta yi wata yar karamar kara sannan ta bude kan ta
A hankali ya shiga part din , parlourn ya na da dan girman , komai na cikin shi navy blue ne wajen ya tsaru gaskia
Ya na shigowa parlourn ya ga junior zaune saman doguwar sofa ya na rike da maltina a hannu daya hannun kuma ya na rike da taba
Karasowa cikin dakin Ash ya yi sannan ya zauna saman sofa geffen Junior ya zuba mishi wadanan sexy blue eyes din shi ba tare da ya ce komai ba
Juyowa Junior ya yi ya kali Ash ya ce " what are you doing here ?"
Shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba sai da ya dauki wajen good ten minutes kafin ya ce " what are you doing ?"
Dan murmushi Junior ya yi ya kai tabar shi a baki ya busa kafin ya ce " smoking " ya kai karshen ya na kai maltinar shi a baki ya sha kadan
Slowly Ash ya kai hannu ya karbi Tabar hannun junior ya daura saman table
Cike da nitsuwa ya ce " junior you are a soldier , na zata ka daina bushe bushen ga "
Dan karamin tsaki junior ya yi ya na kai maltinar shi a baki ya sha ya na kauda kai gefe
" please Ash let me , wlh ba na jin dadin zuciya ta ne , shi kadai ya ke rage min radadin da na ke ji "
Mikewa tsaye Ash ya yi ya na fadin " Junior , na san tun da mu ka taso ba wani sake maka fuska na ke yi ba , but don't forget ni dan uwan ka ne , duk wani abu da ke damun ka za ka iya fadamin , ba ka tsaya ka na cutar da kan ka ba " ya na gama fadar haka ya juya ya fara takawa cike da nitsuwa ya fice part din
Da kallo Junior ya raka shi har sai da ya fice sannan ya sa hannu ya ciro wata yar remote da ga cikin aljihun shi ya danna wani button , nan take door din ta koma ta rufe kan ta
Bangaran Ash kuma ya na fita ya koma kai tsaye part din shi , kai tsaye bedroom din shi ya wuce
Bedroom din ya na da girma sosai , ga shi ta hadu kamar ba a duniya ta ke ba , komai na cikin ta white colour ne har curtain din
Wata yar door ta glass ya nufa , ya na isa wajen ta bude kan ta ya shiga wani katafaren dressing room
Cikin dressing room din a geffen dama akwai wata door ita ma ta glass
Kai tsaye wajen door din ya nufa yanzu ma ya na tsayuwa gaban ta ta bude kan ta ya daga kafa slowly ya shiga
* WASHE GARI ๐ค๐ค๐ค๐ค๐ค
* NIGER ( ZINDER STATE )
* KAUYEN NAWACH KALร
Wata kyakyawar budurwa ce ta ke tafiya a tsakiyar wata gona , ta na sanye da wani kodaden hijab navy blue har kassa
Ba laifi yarinyar nan ta hadu , skin din ta Chocolate ne amma duk ya yi baki saboda dauda , ta na da dara daren idanun farare kal , kwayar cikin su kuma Ash colour ne amma bai ciza sosai ba , Idan ka gan shi da ga nesa za ka yi tunanin idanun duk farare ne babu kwaya a ciki , ta na dogayen eyelashes bakake kirin kamar ta saka mascara , eyebrow din ta su ma bakake ne a konce luff kamar ita ta zana su , ta na dogon hanci kamar pencil , da wani dan karamin bakin ta , lips din ta duk bakake ne a bushe kuma har sun dan tsatsage , a shekaru ba za ta wuce 14 years ba , amma Masha Allah ta na da shape gaskia dai'dai shekarun ta
Ta na tsaka da tafiyar ta ta ji an rufe mata idanu ta bayan ta
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta bude bakin ta a hankali cikin wata yar siririyar murya ta ce " Hawa , tun dazu fa na ke jiran ji Na dauka ba za ki zo ba "
Yar karamar dariya Hawa ta yi kafin ta sake mata idanu ta zagayo ta koma gaban ta ta tsaya
Ta na sanye cikin wata doguwar riga green colour , da hijab zuwa guyiwa fari amma duk ya tsufa
" hmmm , ki ce dai ki na son ki koma gida , dama ai saura sati biyu auren ki "
Ba ta gama rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar yarinyar nan ta saki kuka
Da Sauri Hawa ta ce " Hayat ! Wlh wassa na ke yi miki , na minene kuka "
Girgiza mata Hayat ta shiga yi cikin kukan na ta , ta ke fadin " a'a Hawa ba haka ba ne , wlh ba ni son auren Rabeh , ba ni son shi na tsane shi "
Dafa kafadar ta Hawa ta yi cikin sigar rarrashi ta ce mata " ki yi hakuri Hayat , inda na san yadda zan yi a fassa auren nan da na yi , wlh ba na son ganin ki cikin bakin ciki , kin fi kowa sanin duk cikin kauyen nan ke daya ce aminiya ta , kowa ya san Rabeh ba mutun kirki ba ne bare matar shi Kulu , ba ta da tausayi , na san da kin shiga gidan kashe ki kawai za ta yi , Adda ya san da hakan amma ya matsa zai aura miki shi kawai dan ya fi kowa shanu cikin kauyen nan "
Hannu Hayat ta sa ta fara goge hawayen ta
Sai da ta gama sannan ta dago kai ta kali Hawa ta yi mata murmushin karfin hali ta ce " sai dai ki yi hakuri Hawa amma ni na yanke shawarar zan bar kauyen nan , ba zan iya auren Rabeh ba gaskia , ko matar shi ba ta kashe ni ba , na san shi sai ya kashe ni "
Da sauri hawa ta katse ta da cewa " ke Hayat ki na jin abun da ki ke fada , ki bar kauyen nan ki tafi ina , kin san yadda rayuwar birni ta ke kuwa "
" Hawa ya ki ke so na yi , kin fi kowa sanin duk cikin kauyen nan kallon aljana su ke yi min saboda idanun ga na wa , babu wanda ke raba ta , ko shi Rabeh dan Allah ya yi mishi mugun son mata ne kawai ya ce zai aure ni Adda kuma ya ba shi ko sadaki na bai biya ba sai ka ce wadda ba ta da gata ba dan haka ko kallo ban ishe shi ba , Adda da kan shi ya bude baki ya ce ya ba shi sadaka kawai dan ya bar gani na kusa da shi " Hayat ta fada kuka na neman kubce mata
Da sauri hawa ta sa hannu ta janyo ta jikin ta ta rungume ta na dan bubuga bayan ta sigar rarrashi
Sai da ta yi kukan mai isar ta sannan ta yi shiru ta na sauke ajiyar zuciya sannan ta dago a hankali da ga jikin Hawa ta na dan karamin murmushi
Murmushi ita ma Hawa ta yi mata ta na kai hannayan duka biyu saman face din ta , ta goge mata hawayen ta na fadin " Shikenan yanzu ya isa haka , wuce mu koma gida , ni fa yunwa na ke ji "
Yar karamar dariya Hayat ta yi kafin ta kai hannu ta dunguri kan Hawa ta na fadin " sannu sarkin ci , wuce mu tafi ni ma yunwar na ke ji "
Riko Hannun ta Hawa ta yi kafin ta juya ta fara takawa ta na janye da hannun Hayat su ka bar gonar
Sai da su ka dan yi nisa da tafiyar su sannan Hawa ta saki hannun ta , su na tafe su na hirar su har sai da su ka fara hango gidaje
Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar wani mutun da ga bayan su ya na fadin " ke Hayat "
Cak Hayat da Hawa su ka tsaya da ga tafiyar su , nan take Hayat ta ji zuciyar ta buga da karfi har sai da ta hadiye wasu yawu
Ta na haka ta sake jiyo wannan muryar ya na fadin " ba da ke na ke magana ba ? "
Slowly Hayat ta juyo kai a sunkuye murya na kerma ta ce " ina kwana ? "
Wani dan dattijo ne tsaye a gaban ta sam ba shi da kyan gani , a shekaru zai kai 37 haka ya na rike da wata sanda irin ta korar shanu
Kare mata kallo da kyau ya yi da ga sama har kassa kafin ya kali hawa ya wurga mata wata muguwar hararra
Dum ta ji gaban ta ya fadi har sai da ta dan zaro idanu , da sauri ta ce ma Hayat " Hayat ni zan tafi gida sai an jima " ta na gama fadar haka ta juya da sauri ta bar wajen
Ta na barin wajen wannan mutun ya dawo da kallon shi kan Hayat ya ce " ba ni son na kara ganin ki tare da yarinyar nan kin ji na fada miki ? "
A hankali ta gyada mishi kai ba tare da ta dago ta kale shi ba
" shikenan wuce gida mazza kar ki tsaya ko ina "
Bai gama rufe bakin shi ba ta juya da gudu ta bar wajen
Shi kuma tsayawa ya yi ya raka ta da kallo har sai da ta fara kurewa ganin shi sannan ya juya ya yi tafiyar shi
Ba ta daina gudun ta ba har sai da ta karaso bakin kofar wani gida na jar lakar ko kofa ba shi da wani zane ne a ka sa a ka yi mishi kariya , kun san dai yadda yanayin gidajen kauye su ke ba sai mun bata lokaci a kai ba
Bakin ta dauke da sallama ta shigo cikin gidan ta na tafiya simi simi kamar barauniya
Har ta karaso bakin kofar wani daki ta jiyo Muryar wata mata da ga bayan ta ta na fadin " to malama da ga ina ki ke ? "
Slowly Hayat ta juyo ta kali matar ta saki wani cool murmushi ta ce " Inna na je wajen Hawa ne "
Matar sam ba ta yi kama da Hayat ba , asali ma Hayat ta fi ta haske da kyau gaskia
Ta na sanye cikin wasu kayan na atanfa riga daban zane daban dan kwalin ta kuma kalar zanen ta rike da kugu da hannayan ta biyu
Kare wa Hayat kallo ta yi da kyau kafin ta ce " Rabeh ya zo neman ki "
Da sauri Hayat ta ce " eh mun hadu saman hanya , har ya ce na gaishe ki "
Dan karamin murmushi inna ta yi kafin ta sauke hannayan ta ta juya ta na fadin " je ki dauki abincin ki , tun bai yi sanyi ba "
Da to Hayat ta amsa mata kafin ta nufi wani dan dakin wanda ina kyautata zaton kitchen ne
Inna kuma ta nufi hararrar gidan kassan wata yar inuwa ta shanya tabarma ta zauna
Dai'dai lokacin da Hayat ta fito da ga cikin kitchen din rike da wata yar kwalla ta abincin ta wani cup na ruwa ta nufi wajen da inna ke zaune ta zauna saman tabbarmar ita ma ta ajiye kwallar sa cup din hannun ta gaban ta
Sannan ta bude kwallar , dumamen tuwan dawa ne da miyar kuka a ciki
Hannu Hayat ta kai ta fara cin abincin ta cikin konciyar hankali
Ta na tsaka da cin abincin ta inna ta ce ma ta " ya kamata ki daina yawwan fitar nan da ki ke yi , kin ga auren ki da Rabeh saura sati biyu "
Slowly Hayat ta dago kai ta kali inna ta marairaice fuska ta ce " inna don Allah ki ma Adda magana wlh ba na son auren nan , kowa ya san cikin kauyen nan , Matar shi kulu ba ta da kirki "
Cikin nitsuwa inna ta katse ta da cewa " Shahd dole ki yi hakuri , ko ni ba na son auren nan amma ba yadda zan yi , Addan ki ya rufe ido a kan maganar nan , ko jiya sai da mu ka samu sabani da shi a kan maganar nan "
" yanzu inna ......... "
Da sauri inna ta katse ta da cewa " Hayat ya isa haka ki ci abincin ki tun bai yi sanyi ba "
Shiru Hayat ta yi ta juya ta ci gaba da cin abincin ta idanun ta na kawo ruwa , har sai da ta Kamala ta sha ruwa sannan ta dauki kayan ta meda su kitchen sannan ta fito ta nufi dakin da ta yi niyar shiga da farko
Ita dai inna da ido kawai ta ke bin ta har sai da ta shiga cikin dakin
TAแฆRIN ZแฆCIYA ๐๐บ๐
( RETแฆRN )
(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐๐ฅ
โค๐ ๊ช๊ช๊ชถ๊ชถ๊ชฦแปแญข ๊ช๊ช๊ซ๊ซ๊ชน๊ช๊ซ ๊ช๊ชแฆ๊ชฎ๊ช๊ชถ๊ช๊ช๊ซ ๐โค
๐.๐.๐ ๐๐๐๐๐โฅ ๐๐
Wattpad : @bennybite
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐๐
ุงููููููู
ูู ุตูููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุตููููููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูุ ุงููููููู
ูู ุจูุงุฑููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุจูุงุฑูููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏู๏ธ
๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ
๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
๐๐๐๐๐๐
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
๐ง๐๐ฃ ๐ง๐๐๐ฆ ๐๐๐๐ ๐ง๐ข ๐๐ข๐๐ก ๐ ๐ฌ ๐ฃ๐ข๐ฆ๐ง๐๐ก๐ ๐ฅ๐ข๐ข๐
๐๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054
_________________โฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆ__________________
[ ๐
ฟ๐
ฐ๐
ถ๐
ดฬฅ 3 โค๐ฅ ]
โช US ( WASHINGTON DC )
Misalin karfe 10 na safe Nihal ta na zaune cikin parlourn gidan ta na kallon Tv
Ta na haka kawai sai ganin wata yar karamar yarinya ta shigo parlourn da gudu ta na fadin " Mamie , Mamie , Mamie " ta kai karshen ta na fadawa jikin Nihal
Yarinyar fara ce tas kamar baturiya amma kallo daya za ka yi mata ka san jinin haoussawa ce , a shekaru ba za ta wuce 4 years ba , ta na sanye cikin wata gown pink colour mai mugun kyau
Wani kyakyawan murmushi Nihal ta yi kafin ta dauki yarinyar ta daura ta saman cinyar ta ta na fadin " Haleen di na , shi ne ba ki fada min za ki zo ba "
Yar siririyar dariya ta yi da Muryar nan ta ta irin ta yara
Ta na shirin magana Ayna ta shigo parlourn ta na sallama dan kallo daya na yi mata na gane ta , Anas ne rai da rai babu ta inda ta baro shi sai wajen wadanan ash eyes na Zarah
Cike da fara'a Nihal ta amsa mata sallamar ta kafin ta daura da cewa " ya mijin nawa ya ke ina ki ka baro shi "
Yar karamar dariya Ayna ta yi ta na dan sunkuyar da kai ta ce " ya na nan mummy ya ce ma a gaishe ki "
" Ina amsawa ki ce mishi na yi fushi tun dawowar ku da ga Turkey har yanzu bai zo gani na ba " Nihal ta fada ta na sauke Haleen da ga saman cinyar ta ta zaunar da ita geffen ta
Dai'dai lokacin da Ummi ta fara sauko stair ta na sanye cikin doguwar riga mara nauyi fara kal , ta saki wannan curly hair din ta sak irin na Aylan ya zubo mata har saman shoulder ta na tafe kai a sunkuye ta na latsa wayar hannun ta
Sai da ta karaso cikin parlourn sannan ta jiyo Muryar Ayna ta na fadin " Sannu