Showing 21001 words to 24000 words out of 72572 words

Chapter 8 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

332

bari idan mun dawo sai ka tafi , ka ga Ash sai ya kula da office din shugaban kassa " Nihal ta fada ta na murmushi

" mummy ni fa ba zan iya aiki shugaban kassa ba , ko shi his excellency da ya ya ke yi " Ash ya fada ya na kallon Rayan

Yar dariya Rayan ya yi kafin ya ce " General , wlh aikin shugaban kassa babu sauki , ni har na fara nadamar hawa na wannan kujerar "

" To sai a ci gaba da rikewa dan babu wanda zai hau ta cikin gidan nan " Ash ya fada ya na mikewa
Da sauri Nihal ta taro shi ta na fadin " Ash ina za ka je haka "
" zan koma na yi barci , dama My angel ne ya tada ni wai fruits zai sha " ya fada ya na sa kafa ya fice part din

Da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan Rayan ya juyo ya kali Nihal ya ce " Sister ya kamata mu kawo karshen gwaurancin General & Marshal , dubi ki ga yadda ya sangar ta Vedad , ki na fa ji cewa ya yi My angel , gaskiya ya kamata a nemo mishi mata "

Yar dariya Nihal ta yi kafin ta ce " kar ka damu Yaya Rayan , kai dai ka roki Allah , ya hada ni da kyakyawar yarinya , mai tarbiya , da adini , wlh ko sun ki , ko sun so sai sun yi aure "
Hararrar wassa Rayan ya yi mata ya na fadin " ke dai , ke dai sister yaushe ki ka koyi mugun ta haka "

Dariya sosai Nihal ta yi kafin ta ce " yaya Rayan ba wata mugun ta , ai mu ma haka a ka yi mana kuma ga shi , yanzu har da yaran mu hudu , ka ga hakan shi ne hanya ma fi sauki da za mu aurar da su , in mu ka ce mu bi ta ra'ayin su wlh ba za su yi auren nan ba "

" Gaskiya ki ka fada , amma sai mun yi a hankali "
" kai dai yaya Rayan ka bar maganar nan a hannu na za ka sha mamaki " ta fada cikin gwarin guyiwa
Dan karamin murmushi Rayan ya yi kafin ya ce " shikenan , ki dai kula min da kan ki sister Allah ya kiyaye hanya ya dawo min da ku lafiya , ya dawo da ku lafiya sister di na "
Ita dai Nihal da amine ta ke amsa mishi da ga haka su ka yi sallama ya fice part din ya tafi na shi , ita kuma Nihal ta tashi ta shiga bedroom din ta ta wuce toilet ta yi wanka sannan ta shirya cikin kayan barcin ta , ta konta asuba ta gari


▪WASHE GARI


Misalin karfe 8 dai'dai na safe duk mutanan gidan su ka shirya har da Rayan su ka fice gidan su ka kama hanyar international airport of Washington-Dulles

Duk wasu shirye shirye da za a yi an riga da an yi su , Ash kadai a ke jira
Airport din cike ya ke jibga jibgan sojoji da dankara dankaran motoci ma su nunfashi , ban ma yi kokarin kilga su ba dan na san ba zan iya ba wlh

A haka su ka wuce kai tsaye cikin Jet din Ash , su na shiga ya daga ko , ya kama hanyar Nigeria , his excellency Rayan kuma ya kama hanyar white house kamar yadda su ka yi da Ash , sai dai mu ce Allah ya tsare ku , ya kai ku lafiya
Bari mu leko su Hayat na san kafin nan jirgin su ya sauka


▪NIGERIA ( KANO STATE )


▪HAYAT 💦


Misalin karfe 7 na safe bus din su ya shigo cikin garin Kano ,
Ta na tsaka da barcin ta mai mugun dadi driver ya tada ta , ya na ce mata ta tashi sun iso
A rude ta tashi ta na bin wajen da kallo , ta na tambayar in sun iso
" eh min iso , sai ki sauka ki tafi wajen dan uwan na ki , Allah ya kiyaye hanya " Driver ya fada mata

Wasu yawu ta hadiye kafin ta ce mishi " dan Allah , dan uwa zan iya samun wani abu na ci wlh yunwa na ke ji " ta fada ta na marairaice fuska

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya kai ya dauki bread din da a ka sayo mishi da gorar ruwa guda ya mika mata
Da sauri ta kai hannu ta karba ta na washe baki ta shiga jero mishi aduo'in godiya har sai da ya ce mata ta tafi ya isa haka
Ba musu ta sauka da ga cikin motar , shi dai da kallo ya raka ta har sai da ta bacewa ganin shi sannan ya saki wani cool murmushi , har ga Allah yarinyar nan ta kon ta mishi a rai , ya ji tausayin ta sosai , sam yanayin idanun ta bai sa ya ji kyamar ta ba , sai ma burge shi da su ka yi , ya so ya raka ta har gidan su amma ba zai iya ba , dama saboda ita ya ba da kudi a ka amso mishi bread din nan , ko da ba ta tambaya ba , shi da kan shi zai ba , Sai dai na ce Allah ya biya ka , dan a wannan zamanin ba kowa ba zai yi irin wannan taimakon da ka yi

▪KADUNA


▪ KADUNA INTERNATIONAL AIRPORT


Misalin karfe daya na yamma jirgin su Nihal ya sauka a cikin international airport na kaduna , allamun a kaduna za su sauka

Airport din cike ya ke da manya manyan motoci ma su nufashi ma su bala'in kyau da tsada ni kassa kilga su ma na yi , ga ubanin sojoji cike da airport din kowane rike da gun , ba fa sojojin Nigeria , sojojin US ko shugaban kassar Nigeria da kan shi ba zai samu irin wannan tarbar ba , tun cikin daren jiya Rayan ya ba su umarni su taho , tare da wannan manyan motocin , musaman dan shirya zuwan familyn shi , har gidan da za su zauna sojojin nan sun riga da sun gyara komai

Kai tsaye wajen motocin nan su ka nufa , Ash da junior su ka shiga mota guda , Ummi da Nihal su ka shiga mota guda , sai Iqbal da Vedad su ka shiga mota guda , a jere motocin su ka bar airport din nan da mugun gudu su na jiniya kamar wanda za su tashi sama

Ba su dauki wani lokaci ba su ka iso cikin unguwar Nassarawa ,
Tun kafin su iso bakin kofar gidan , sojojin da ke cikin gidan su ka wangale musu kofar , su ka yi cikin gidan da mugun gudu
Kai tsaye parking space su ka nufa , su ka yi parking din motocin su , sannan sojojin nan su ka fara dirowa da ga cikin motocin su da sauri sauri kawai ji ka ke dib dib dib
Da gudu su ka nufi motocin mutanan gidan su ka bubude mu su kofa , su na sarawa Ash da junior

Ash bai tsaya bin ta kan kowa ba ya daga kafa da sauri ya nufi cikin gidan
Gidan ya na da girma sosai , Two floor ne sai wani dan balcony da ke hawa na biyun , an saka mishi wasu chair kamar na kaba , ma su mugun kyau

Ya na shigowa parlourn ko tsaya wa bai yi ba ya nufi stair da sauri ya Haye abun shi
Ya na hawa ko su Nihal su ka shigo cikin parlourn gidan , sai da su ka kare wa parlourn kallo da kyau sannan Nihal ta kale su ta ce " ku je ku dan huta " ta kai karshen ta na nufar wani corridor ta shiga part din kassa ita

Ta na shiga junior, Iqbal da Vedad su ka Haye sama abin su , Ummi kuma ta bi bayan Nihal ta shiga part din da ke geffen na ta

Kar ku tambaye ni ina kayan su , na ce muku tun daren jiya his excellency ya turo sojoji su ka gyara gidan , to tare da kayan su su ka taho , kowane su ka gyara mishi part din shi , shiga kawai za su yi
Duk part 7 din bedroom biyu ne a ciki da parlour guda , part guda ke da bedroom daya sai parlour , shi ne kuma na Ash , wannan karan Iqbal da Vedad part guda su ka shiga , junior ma ya kama part din da ke kusa da na Ash


▪ASH 🔥

Bayan ya shiga part din shi , kai tsaye bedroom din ya wuce , ya na shiga ya wuce toilet dan ya yi wanka , ba su yi 30 minutes ba da shigowa Nigeria amma shi har ya fara jin zafin garin

Sai da ya dauki wajen good one hour kafin ya fito da ga cikin toilet din daure da towel a kirjin shi

Ya na shigowa bedroom din idanun shi su ka sauka kan Vedad ya na zaune tsakiyar bed din shi ya na rike da wayar shi ya na latsawa , ya na faman turo dan bakin nan na shi

Ash bai bi ta kan shi ba ya wuce dressing room , jim kadan ya fito da ga shi sai short da singlet farare kal , ya saki wannan curly bakin gashin shi , sai tashin kamshi ya ke

A hankali ya karaso bakin gadon ya zauna , ya kai hannu ya kwace wayar shi a hannun Vedad sannan ya ce " My angel tashi ka kawo min fruits "

Noke kafada Vedad ya yi ya na kauda kai gefe
Cikin nitsuwa Ash ya tambaye shi " me ya ke faruwa kuma ? "
" Big bro wai me mu ka zo yi cikin garin nan mai mugun zafi , dubi tun dazu sai zufa na ke yi " ya fada cikin shagwaba
Cikin ko in kula Ash ya ce mishi " mu je na yi maka wanka "
" ni na yi wanka kafin na taho "
" ka yi breakfast ? "
" eh na yi " ya ba shi amsa a takaice

Gyada kan shi Ash ya yi kafin ya ce " to minene matsalar ? "
A hankali Vedad ya juyo kan shi ya na shirin magana Iqbal ya shigo bedroom din ya na sallama kassa kassa sai yamutse fuska ya ke yi
Da Ash har Vedad duk kassan makoshi su ka amsa mishi sallamar shi

Shi kuma ya na shigowa ya nufi bed din Ash ya Haye ya yi rub da ciki
Mikewa tsaye Ash ya yi ya dauki laptop din shi da wayar shi , ya juya ya nufi wani glass da ke fuskantar door din shigowa bedroom din , Gadon na tsakiyar su

Ya na isa kofar ta bude kan ta , ya daga kafa ya shiga dan balconyn , ya bar Iqbal da Vedad nan dan ya san in ya ce zai biye musu ba zai yi aikin da ya kawo shi ba

Su kuma da kallo su ka raka shi har sai da ya shiga sannan Iqbal ya mike zaune ya na kallon Vedad ya ce " My Cutie pie , me ya faru na ga sai turo baki ka ke , ko dai big bro ya dake ka ? "

Girgiza mishi kai Vedad ya yi kafin ya sauko da kafafun shi kassa ya mike tsaye ya mikawa Iqbal hannu ya na fadin " mu je ka raka ni wajen mummy "

Hararrar shi Iqbal ya yi kafin ya ce " ba ka san hanya ba ne "
Kukan shagwaba Vedad ya fara yi mishi har da bubuga kafafu a kassa ya na fadin " ni ban san inda ta ke ba "
Mikewa tsaye shi Iqbal ya yi ya riko hannun shi ya na fadin " it's okay my Cutie pie , mu je ni ma wajen ta zan je " ya kai karshen ya na yin gaba

Dan karamin murmushi Vedad ya yi ya na bin bayan Iqbal kamar rakumi da akala su ka fice part din baki daya
Kai tsaye stair su ka sauko , su na shigowa parlourn su ka tardo Nihal da Ummi su na zaune

Da sauri Vedad ya kwace hannun shi da ga cikin na Iqbal ya nufi Nihal da gudu ya fada jikin ta ya na fadin " mummy tashi mu koma gida ni ba zan zauna nan ba " ya fada cikin shagwaba dai'dai lokacin da Iqbal ya karaso cikin parlourn ya zauna geffen Ummi sannan ya ciro wayar shi da ga cikin trouser din shi ya shiga harkar gaban shi

Nihal na shirin magana Ummi ta riga ta cewa " Vedad tashi da ga nan ko kunya ba ka ji ba , kai fa ba yaro ba ne "

" ke kuma wa ya miki magana " ya fada ya na murguna ma ta baki
Da sauri ta tasso ta na shirin bugun shi , da sauri Nihal ta tare ta ta na fadin " Ummi wlh ki kiyaye ni , me baby na ya yi miki da za ki buge shi "

" mummy wlh duk ke ki ka ba ta wannan yaron , sai in ya yi wa mutun laifi ki ce ba za a taba shi ba " Ummi ta fada ta na komawa wajen ta ta zauna

Yar karamar dariya Vedad ya yi ya na yi mata gwalo , abun ba karamar dariya ya ba ta ba ita da kan ta , ba ta san lokacin da ta yi mishi hararrar wassa ta na fadin " dube shi don Allah Big baby kawai "

Yar karamar dariya ya yi kafin ya konta ya daura kan shi saman cinyar Nihal , sannan ya ce " Mummy , a cikin gidan nan ku ka zauna ke da Daddy ko ? "

Girgiza mishi kai ta yi ta na daura hannun ta saman kan shi ba ce " no ba wannan ba ne , in ka na so zan kai ka "
" eh mummy ina so , ina son na ga inda labarin soyayyar ku ya fara "
Yar karamar dariya Ummi ta yi kafin ta ce " kai yanzu har ka san soyayya "
" na sani mana , ga Iqbal nan ya na yi "
A hankali Ummi ta juyo ta kali Iqbal , sai faman latsa wayar shi ya ke , ba ya ma tare da su
Dawo da kallon ta ta yi kan Vedad ta na daga mishi gera guda ta ce " da wa ya ke soyayya ne ? "
" ni ma ban sani ba , tambayi big bro "

Mikewa tsaye Ummi ta yi ta nufi stair ta Haye
Ta na hawa Vedad ya na dawo da kallon shi kan Nihal ya ce " mummy wai minene soyayya ? "
Murmushi mai dan sauti Nihal ta yi kafin ta ce " My angel , ba ni da amsar da zan ba ka gaskiya , amma ka bari duk ranar da ka ji ka fada za ka san minene "
" mummy ni fa babu inda zan fada "
" haka shi ma Daddyn ka ya ce , amma duba ga ka nan zaune ka na zuba min shagwaba " ta kai karshen ta na ja mishi hanci
" Kennan sai a na soyayya , a ke samun baby "
" kai , Vedad tashi fice min da ga nan , so ka ke na fadi abun da ya fi karfin baki na , tashi ban waje "

Ta na gama fadar haka ta ture kan shi , ta tashi ta shige corridor ta koma part din ta
Dan karamin gunguni Vedad ya yi kafin ya tashi ya Haye stair ya koma part din shi
Iqbal kuwa babu ma shi a wajen Allah kadai ya san abun da ya ke yi cikin wayar nan


▪ASH 🔥


Ya na zaune saman chair ya na aiki cikin laptop din shi kamar da ga sama ya ji ummi ta soko kai tsakanin shoulder din shi ta na fadin " kai ma soyayyar ce ka ke ? " ta kai karshen ta na janye kan ta , ta janyo chair ta zauna geffen shi

Shi dai bai ce mata komai ba , ya ci gaba da aikin shi
Dan karamin tsaki Ummi ta yi kafin ta kai ta kwace laptop din shi ta na fadin " ka ga dalilin da ya sa ba ni son yi maka magana, sai ka kyale mutun ni kuma ba ni son hakan "

Slowly ya juyo da kan shi ya zuba mata wadanan sexy blue eyes din na shi ya ce " What happening ? "
" nothing , kawai na zo na duba in kai ma ba ka fara soyayya ba ne " ta fada ta na duba laptop din shi , nan ta ga pics din yan mata dayawa a killa duk ba za su wuce 16 years ba , kuma da ga gani ba yan Turawa ba

Dawo da kallon ta ta yi kan Ash cike da rudu ta ke fadin " Ash , wannan pics din na miye ? Ko matar auren ce ka ke nema haka " ta fada cikin zolaya ta na yar dariya
Hannu ya sa ya karbi laptop din shi cikin ruwan sanyi ya ce mata " no , aikin da ya kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login