Showing 27001 words to 30000 words out of 72572 words
raba su gidan nan
sai da ya dauki wajen good ten minutes ya na frop jump ko sannu Ash bai ce mishi ba
su na a haka Vedad ya turo kofar Parlourn ya shigo ya na sallama
ya na ganin Iqbal na frop jump ya bushe da wata shegiyar dariya , ya nufi sofar da Ash ke zaune ya zauna geffen shi ya na ci gaba da dariyar shi har da dafe ciki
wata muguwar Hararra Iqbal ya wurga mishi cikin zuciyar shi ya na fadin " za mu hadu waje "
kamar ko Ash ya san abun da ya fada cikin zuciyar shi sai ya ce mishi " Babu inda za ku hadu , ka na taba shi sai na yi maka dukan kawo ruwa "
turo dan bakin shi Iqbal ya yi wai shi ya ji haushi
a hankali ya mike tsaye ya na kallon Ash ba tare da ya ce komai ba
daga mishi gera Ash ya yi allamun minene ?
murguna mishi baki Iqbal ya yi kafin ya nufi hanyar fita parlourn da gudu
a dubu dari Ash da Vedad su ka mike a tare su ka bi bayan shi
da gudu Iqbal ya shige part din shi ya wuce bedroom , ya turo kofar ya na shirin rufe ta Ash ya damko ta da hannun shi , Vedad ya shigo cikin dakin ya rungumo shi ta baya ya na fadin " Big bro , ga shi na riko shi "
sakin kofar Ash ya yi ya shigo bedroom din sannan ya tura kofar ta rufe kan ta sannan ya danna wani button a jikin ta , a hankali ya juyo ya bai ce ma Iqbal komai ba , ya nufi bed din shi ya dauko pillow guda biyu sannan ya dawo ya ce ma Vedad " sake shi " ya kai karshen ya na mika mishi pillow guda
cike da mugun ta Vedad ya riko pillow su ka fara bugun Iqbal da shi
bawan Allah sai kara ya ke ya na fadin su kyale shi , amma ina Vedad an samu mugun ta , shi dama Ash ina ruwan shi bai san ragowa ba ko kadan
da gudu Iqbal ya nufi bed din shi su na biye da shi su na bugun shi ya dauki dayan pillow shi ba ya shiga ramawa , ya na yar dariya shi da Vedad
Ash kuma ya na ganin su na dariya shi da Vedad ya daina bugun Iqbal ya koma saman bed din ya zauna ya na ci gaba da kallon su , su na wassan su kamar kananan yara
sai da su ka yi mai isar su sannan su ka Haye saman bed din su ka konta su na ci gaba da dariyar su , har ga Allah Ash ba karamin dadi ya ke ji ba cikin zuciyar shi duk lokacin da ya gan su cikin wannan yanayin
a hankali Ash ya mike ya nufi door ya danna wani button din da ya danna da farko , sannan ya bude kofar ya kai ya fice
ya na fita Iqbal da Vedad su ka mike zaune , su ka kali juna
" My Cutie pie , wai ka San abun da ke damun big bro ne , kwana biyu ya zama wani haka haka " Iqbal ya fada , dan ya lura wani abu ya sauya a tattare da dan uwan na shi
daga mishi gera guda Vedad ya yi ya na fadin " kamar ya kenan , ni ban ga komai ba "
hannu Iqbal ya kai ya dunguri kan Vedad ya na fadin " dama ya za a yi ka gane , bayan wassa ba abun da ke cikin wannan kan na ka "
murguna mishi baki Vedad ya yi ya na hararrar shi kafin ya sauko da ga saman gadon ya nufi hanyar fita gidan ya fice ya koma na shi bedroom wai shi ya ji haushin maganar Iqbal
da ido Iqbal ya raka shi har sai da ya fita sannan ya yi yar karamar dariya ya koma ya konta ya lumshe idanun shi ya saki wani cool murmushi har da cije lips din shi na kassa
▪NIHAL 🥀
zaune su ke cikin parlourn gidan ita da Ummi , su na kallon Tv amma da ga gani hankalin su ba ya kan Tv din
slowly Nihal ta juyo ta kali Ummi cikin sanyin murya ta ce " Ummi wai yaushe za ki fitar da mijin aure ni fa...... "
da sauri Ummi ta katse ta da cewa " mummyyyyy , za ki fara ko , ni fa na fada miki ba na sha'awar yin aure "
" Ummi idan ba ki yi aure ba me ki ke son yi ? so ki ke kullum ki dinga jera kafada da ni , Mutuncin ɗiya mace ya na gidan mijin ta , why ba ki so , ba ki son ganin babys din ki ? "
" ba na son kasancewa cikin irin halin da ki ke ciki a yanzu , kullum sai kin yi wa rasuwar Daddy kuka , your happyness is incomplete without him , ba na zan iya jure rashin mutumin da na fi so a rayuwa ta ba kamar ke , mummy i'm not strong like you , please ki daina yi min wannan maganar ba na so " Ummi ta fada da dan karfi kamar za ta yi kuka
wani cool murmushi Nihal ta saki kafin ta taso da ga saman sofar ta , ta dawo geffen Ummi ta zauna cikin sanyin murya ta ce " na sani shi ma da za a ba shi dama da ya dawo gare mu zai dawo ko da ta rana guda ce , na san duk inda ya ke a yanzu ya na mutuwar kewar ummin shi , amma kin sani mutanan da mu ke so tsakani da Allah ba su mutuwa , kullum su na rayuwa a cikin zuciyoyin mu , kullum mu na tunanin su kuma mu na yi musu adu'a , Gaskiya ki ka fada ina kewar Daddyn ku , kuma har ga Allah Farin ciki na ba zai taba cika babu shi , amma ba ki san dalilin da ya sa na ke yin kuka ba duk lokacin da na tuna da shi "
cikin nitsuwa Ummi ta katse ta da cewa " In har da gaske ya na raye cikin zuciyar ki , why kullum sai kin yi kuka ? "
dan karamin murmushi Nihal ta yi kafin ta ce " ni fa ba dan ya tafi ya bar ni ba ne na ke yin kuka , kawai ina tuno labarin soyayyar mu ne "
yar karamar dariya Ummi ta yi ta na fadin " His maid "
yar karamar dariya ita ma Nihal ta yi ta kai hannu ta dan bugi Damtsen ta , ta na fadin " ni ki kira da Maid ? "
" no mummy ni fa cewa na yi His maid "
hararrar wassa Nihal ta yi mata kafin ta ce " Gaskiya ne da Farko kallon yar aikin shi ya ke min , ni kuma ina mishi kallon sadauki na , har yanzu ina tina haduwa ta ta farko da shi , kallo guda na yi mishi na ji babu wanda na ke so a duniyar nan sama da shi , hmmm shi kuma ya shiga yi min jan aji "
a tare ita da Ummi su ka yi dariya
cikin dariyar ta ta Ummi ta ce " da gaske Daddy jan aji ya yi miki ? ai mata a ka sani da jan aji " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya
" hmmm , The General of American Army Staff guda ki ce ba zai yi jan aji ba , mutumin da bude baki ma ya yi min magana wuya ta ke yi mishi ko gaishe shi na yi ba ya amsawa , sai dai in na yi mishi laifi ya shiga sa ni frog jump , Daddyn ku fa sam ba ya da sakin fuska , ko papi da ya haife shi ba zai iya kallon cikin idanun shi ya fadi wata maganar ba , ko murmushi ba ya yi , sai ya zauna cikin waje shi bai muku magana ba kuma ba ku da izinin yin magana "
" hai fa mummy , Daddy fa ya na murmushi , har da dariya ma "
" eh ya na yi , amma bai taba yin su ba gaban mutanan gidan , bayan haihuwar Iqbal ne ya fara yin murmushi gaban yan gidan , ina tine first time da su His excellency su ka ga murmushin shi har party sai da su ka yi mishi ranar nan "
" party ? just for a smile "
" hmmm , murmushin daddyn ku karshe ne , ko namiji ne ya ga murmushin Daddyn ku wlh sai ya burge shi , ina kuma ga mata , har yanzu ban ga mai murmushi irin na Daddyn ku ba "
" that's why you love him " Ummi ta fada ta na kashewa Nihal gera guda
Girgiza mata kai Nihal ta yi kafin ta ce " ko ɗaya , lokacin da na kamu da son shi ban ga wannan murmushin ba , lokaci guda na kamu da son shi , kuma har yanzu son nan ya na cikin zuciya ta bai sauya ba , a duk lokacin da na kale ku , ke da brothers din ki , sai in ji kamar ya na a kusa da ni , musaman idan na kali Ash , yadda ki ka ga Ash haka daddyn ku ya ke , kamar an tsaga kara , sai dai fa ina ga Ash sai ya fi daddyn ku miskilanci " ta kai karshen ta na dariya ita da Ummi
kamar da ga sama su ka jiyo a na yi musu gyaran murya da ga bayan su
a tare Ummi da Nihal su ka zaro idanu , a razane su ka juya idanun su ba su sauka ko ina ba sai saman Ash da ke tsaye tsakiyar stair ya nade hanayan shi a kirji ya zuba musu wadanan sexy blue eyes din na shi
a hankali ya daga ya fara sauko stair din ya karaso bayan sofar su ya tsaya ya ce " gulmar mutane ku ke yi ko ? "
kallon kassan ido Nihal ta yi mishi kafin ta ce " kai kuma labe ka ke yi wa mutane "
shiru ya yi bai ce komai ya na ci gaba da kallon su
sai da ya ƙare musu kallo da kyau sannan ya daga kafa ya nufi kofar fita
da kallo Nihal da Ummi su ka raka shi sai da ya fita sannan su ka bushe da dariya a tare
sai da ta tsagaita dariyar ta sannan Nihal ta ce wa Ummi " please Ummi ki fitar da mijin aure "
" mummy ni fa ba auren ne ba na so ba , har yanzu ban ga wanda ya yi min ba "
gyada kan ta Nihal ta yi kafin ta ce " sannun ki , to yanzu a ka je wanda ya yi miki , ke ba ki yi mishi ba "
" sai na hakura " ta fada a takaice
dan girgiza kai Nihal tayi ta na fadin " Ummi rayuwa fa ba haka ta ke ba , ka yi aiki da abun da ka samu "
cikin nitsuwa Ummi ta katse ta da cewa " mummyyyyy , ni ma nawa sadaukin na ke jira , I want to be with a man like my dad, a man who could sacrifice his life for me, a man who will cherish me and make me his priority, a man who will accept me as I am with all my qualities and my faults "
murmushi mai dan sauti Nihal ta yi kafin ta ce " a takaice dai you just want the perfect man ? "
" Daddy was perfect ? "
gyada mata kai Nihal ta yi ta na fadin " yes ! but in his own way "
Dan karamin murmushi Ummi ta yi ba tare da ta ce komai ba
mikewa tsaye Nihal ta yi ta daura hannun ta saman kumatun Ummi ta na murmushi ta ce " no man is perfect my darling, it's you who will make sure that he becomes perfect as you wish " ta na gama fadar haka ta juya ta nufi corridor
da kallo Ummi ta raka ta , ta na murmushi murya kassa kassa ta ce " I love you mummy "
▪ASH 🔥
Bayan ya fito Parlourn kai tsaye Boys quarter ya nufa ya na neman junior
duk Sojojin wajen su na ganin shi su ka mike da sauri su na sara mishi , bai bi ta kan gaisuwar su ba ya ce " Where is Marshal ? "
" Ya Fita sir " Felix ya fada cikin girmamawa
" shi kaɗai ya fita ? "
" Yes sir "
Ya na jin hakan ya juya cikin konciyar hankali ya koma cikin gidan ,
Kai tsaye part din shi ya wuce , ya shiga bedroom din shi ya dauki laptop din shi sannan ya dawo parlour ya zauna ya fara latsawa
Dan zaro wadanan sexy blue eyes din nan na shi ya yi cike da rudu ya ke fadin " How can it be possible "
Kamar da ga sama ya jiyo muryar Junior ya na fadin " na jima ai da na dawo "
A hamkali Ash ya lumshe idanun shi ya bude su , Kafin ya dago kai ya juya ya kali junior
ya na tsaye bakin kofar Parlourn ya jingina a jikin door din ya nade hanayan shi a kirji ya na murmushi
a hankali ya saki hannayan shi ya karaso cikin parlourn ya zauna geffen Ash ya na fadin " ni dama na san sai ka ce za ka yi tracking di na shi ya sa na kashe Tracker din "
dan kashe idanun shi Ash ya yi kafin ya ce " Ina ka je ? "
" nowhere , kawai na fita zagaye garin ne , amma na jima da na dawo da ga nan na wuce garden Felix bai ga dawowa ta ba ne "
gyada kan shi Ash ya yi kafin ya ce " Okay , but ya kamata ka dinga sanar da ni idan za ka fita "
" Ash i'm not a baby please " junior ya fada ya na kauda kai gefe
" it's true , kar ka manta aiki ne ya kawo mu nan , Idan ka san ba za ka iya ba za ka iya komawa US "
" ya isa haka Ash ni fa ba kannen ka ba ne da za ka tsaya ka na yi min magana yadda ka ga dama , na san aiki ya kawo mu , shikenan sai a ce ba ni da izinin fita "
" Marshal Aylan jalaludeen don't forget i'm your general ka san abun da za ka fada min " Ash ya fada da dan karfi dan magaganun Junior sun fara bata mishi rai allamun yau junior ya sha Tabar nan da ya ke sha
dama haka nan ta ke yi mishi duk ranar da ya sha ta sai Rayan ya shiga tsakanin su , Ga Ash dama da zuciya , in ya na cikin fushi bai san abun da yake ba , shi kuma junior ya fadi duk abun da ke cikin zuciyar shi kamar wanda ya sha giya , da ga baya kuma su dawo kamar ba a yi komai ba , shi ya sa Ash ya ke son ya daina shan ta amma ya ki , har company da su ke buga Tabar a US sai da Ash ya sa a ka rufe ta amma ya rasa inda junior ya ke samo ta
mikewa junior ya yi , ya na fadin " Ni kuma Big brother din ka ne , Respect me , na gaji da wannan abun da ka ke min kawai dan ka fi matsayi " ya kai karshen ya na juyawa zai fice parlourn
cak ya ji an damko hannun shi , a dubu dari ya juya ya ga Ash ya riko hannun shi , ya waro wadanan sexy blue eyes din shi kamar su fado , sun yi jazir dan bacin rai
lips din shi har kerma su ke yi ya na fadin " Junior , be careful i don't like that "
bige hannun shi junior ya yi da karfi ya na tsaki ya juya
bai yi taku biyu ba , Ash ya riko hannun shi , ya juyo shi da karfi ya dunkule hannun shi ya kai mishi wani wawan bugu a fuska , har sai da bakin shi ya fashe nan take
a dubu dari Junior ya dago kai ya yi kokarin Kai wa Ash bugu , sai dai bai same shi ba ya gauce , Dama training din da su ka samu ba daya ba , tun Ash na shekara goma Aylan ya fara ba shi training din Soja , shi kuma junior bayan ya shiga Army ne ya fara karbar training kun ga Duk yadda za a yi Ash ya fi shi kwarewa wajen iya fada
riko hannun shi Ash ya yi ya daga sama ya kai mishi wani mugun bugu a ciki har sai da junior ya fice parlourn ya fado cikin corridor din , dama su na kusan door din
duk da ya ji zafin bugun amma bai hakura ba sai da ya tashi da karfi ya nufi Ash Kafin ba ya karaso Ash ya daga kafa ya tura shi baya har sai da ya furzo jini da ga bakin shi dai'dai lokacin da Vedad ya fito da ga part din su
ya na ganin halin da Junior ke ciki