Showing 72001 words to 72572 words out of 72572 words
su na ganin yaunin kiran sunan saboda sunan mahaifiyar mama ta ne shi ya sa su ke kira na Barira "
gyada kan ta Nihal ta yi kafin ta ce " Ni gaskia Barira bai min ba dan haka da Meriem zan dinga kiran ki "
dan karamin murmushi Barira ta saki kafin ta ce " Shikenan Aunty ba laifi "
( 😴😴😴kun dai ji yanzu Barira sunan ta Meriem dan haka kar ku ga na saka Meriem ku ce wacece duk Barira ce )
Meriem na gama rufe bakin ta Hayat ta dago da ga jikin ta , ta ce " inna idan mun isa Fada don Allah ina son na je na ga Hawa , tun da gidan su kusa ne "
Meriem na shirin magana Nihal ta riga ta cewa " Wacece Hawa kuma ? "
da sauri Hayat ta ce " Abokiya ta ce , a tare mu ka tasso ina son na je na gan ta don Allah " ta kai karshen ta na marairaice fuska
murmushi Nihal ta saki kafin ta gyada mata kai dai'dai lokacin da motar ta tsaya
juyowa Felix ya yi kafin ya ce " Sorry madam motocin ba za su iya wucewa ba sai dai mu tafi da kafa "
" Shikenan ku sauko mu tafi , Hayat za ki iya tafiya wajen Abokiyar ki , Iqbal zai raka ki amma kar ki dade ki dawo kin ji ko ? " Nihal ta fada ta na kallon Hayat
gyada mata kai Hayat ta yi ta na murmushi
da sauri Felix ya sauko ya budewa Nihal kofa ta sauko ta nufi motar su Iqbal
da sauri Felix ya sha gaban ta , ya bude mata kofar baya inda su Iqbal ke zaune
nan ta ga Vedad har ya yi barci ya tada kai da cinyar Iqbal
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Iqbal don Allah ka raka Hayat wajen wata Abokiyar ta za mu je wajen mai garin ba za mu dade ba "
dan karamin tsaki Iqbal ya yi ya na fadin " mummy wai yaushe za mu bar kauyen nan , i'm tired "
hannu ta kai saman kumatun shi ta shafa a hankali ta ce " sorry my baby boy , sauko ku je ka ji ? " ta kai karshen ta na janye hannun ta
da to ya amsa mata kafin ya janye kan Vedad a hankali ya sauko da ga cikin motar
dawowa wajen motar su Nihal ta yi inda Meriem da Hayat ke tsaye ta ce ma Hayat " wuce ku tafi kar ku jima "
gyada mata kai Hayat ta yi kafin ta nufi Iqbal
Nihal kuwa ta yi gaba ita da Meriem Felix da wani guard na biye da bayan su
Hayat kuma ita da Iqbal kadai su ka nufi hanyar gidan su Hawa , su na tafe Hayat na ba shi labarin abotar ta da Hawa
shi dai kawai ya na sauraron ta ya na sakin murmushi gaskiya abotar su ta tuno mishi ta shi da Vedad , dan duk duniya ba shi da Aboki kamar Vedad karewar zance Vedad ne kadai abokin shi a duniya , duk wani siririn shi Vedad kadai ya ke iya fadawa , duk wata hira da zai yi da Vedad ya ke yin ta ko da kuwa ya san abu me wuya ne ya gane abun da ya ke Fada mishi