Showing 39001 words to 42000 words out of 72572 words

Chapter 14 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

337

kofar su ka ɗaura da ga inda su ka tsaya

duk maganar da su ka yi a kunnen Hayat , dan ta na jin su
sai da ta ji sun ja mata kofa sannan ta saki wani sabon kukan ta na sa hannun ta guda ta toshe bakin ta , hawaye na zubo mata bibiyu

sai da ta yi kukan mai isar ta sannan ta tashi a hankali ta shiga toilet , ta wanke fuskar ta , sannan ta ɗauro da Alwalla , ta fito ta nufi wajen carpet din bakin gadon dan ba ta ga dadduma ba , ta fara Sallat

ta na yi hawaye bibiyu na zubo mata , Haka ta Kamala nafilar ta , ta kai kukan ta ga Allah a kan ya fitar da ita da ga cikin gidan nan , ita ta gwanma ce auren Rabeh da wannan abun da idanun ta su ka yi mata arba da shi
indai irin wannan abun ne Fatima ta ke yi mata magana a kai to tabass dole ta bar gidan a fitowar rana

bayan ta Kamala Sallar ta , ta tashi ta koma bakin gado ta yi zaune ta na ci gaba da kukan ta kassa kassa

cen kuma sai ta dago kai cike da kwarin guyiwa ta kai hannu ta goge hawayen ta , murya kassa kassa ta ce " a'a Shahd , kuka ba na ki ba ne , dole ki bar gidan nan tun lokaci bai ƙure miki ba , in har za ki iya tserewa auren Rabeh wadanan azzaluman ma za ki iya tsere musu "

mikewa tsaye ta yi ta rike kugun ta da duka hannayan ta biyu ta na fadin " ba ke macuciya ba , za ki aiki na , yar iska mazinaciya kawai , annabi a baki , fir'auna a zuciya , wlh Shahd ta fi karfin zama yar iska irin ki , nan gani nan bari wlh na sha tabara na sha lahaula , na sha maganin matsiya ta ma su bakar zuciya , Ni ce nan jikar barbushi , aljannai ma sun gan ni sun kyale bare mutun "

ta na gama fadar haka ta saki wata wata yar siririyar dariya , ta na kallon kofar dakin ta kassan ido
( mu dai mu na jira mu gani abun da zai faru )


▪WASHE GARI ( Misalin karfe 8 )


▪ASH 🔥


a hankali ya bude idanun shi , ba su sauka ko ina ba sai cikin na Vedad , ya na zaune geffen shi ya leko da kan shi ya na kallon face din Ash ya na murmushi

a hankali Ash ya dago Hannu ya dan mari Face din shi cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ya ce mishi " what are you doing here early ? "

yar karamar dariya Vedad ya yi ya na janye kan shi ya na fadin " Big bro it's late not early , karfe 8 fa har da mintina "

a dubu dari Ash ya mike zaune , ya kai hannu ya dauki wayar shi saman bedside drawer , ya kunna ya duba screen din , nan ya ga karfe 8 da mintina 26

meda wayar ya yi ya jingina bayan shi a jikin forehead din gadon sannan ya lumshe idanun shi

a haka ya juya murya Vedad ya na fadin " Big bro , da wani abu cikin Duvet din ka "
a hankali ya bude idanun shi ya kali Vedad ya daga mishi gera guda allamun minene
cikin ko in kula ya kai dan yatsar shi saman Dick din Ash ya na fadin " wannan abun "

ba Shiri Ash ya zaro idanun shi , sannu bai ce ba Vedad ba ya tashi a dubu dari ya nufi toilet da gudu , ya rufo kofar da karfi

ya na shiga ya jingina bayan shi a jikin kofar ya na sauke ajiyar zuciya , a hankali ya dan sunkuyar da kan shi ya kali gaban shi , kafin ya meda kan shi jikin kofar ya na fadin " wai me ya ke shirin faruwa da ni haka , Just for a dream ? " ya na gama fadar haka ya nufi jacuzzi din shi ya tsunduma a cikin ko kayan jikin shi bai cire ba

Vedad kuma ya na ganin Ash ya shiga toilet , sai ya dauki wayar shi ya shiga latsawa dan mintina , sannan ya tashi abin shi ya fice part din


▪NIHAL 🥀


zaune ta ke saman Sofa , ta na rike da wayar ta , ta na latsa wa cikin konciyar hankali
ta na a haka kawai ta jiyo Muryar Vedad ya na kwalla mata kira
a hankali ta dago kai ta kali saitin stair , nan ta gan shi , ya na sauko stair din da tsale kamar karamin yaro

ita dai ba ta ce mishi komai ba har ya karasa sauko stair din , ya karaso cikin parlourn ya nufi sofar da Nihal ke zaune ya zauna geffen ta

dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " wa kuma ya taba min Angel di na , ko ba ka yi breakfast ba "

girgiza mata kai ya yi cikin shagwaba ya ce " no na yi breakfast , big bro ne sai yanzu ya tashi da ga barcin shi , ki cewa chef su shirya mishi na shi breakfast "

" Ash sai yanzu ya tashi " ta maimaita kassa kassa , a iya sannin ta ko da su ke US , kiran Asubahi na farko da Ash a ke yin shi , ko ya Kamala sallar ba ya komawa barci , sai dai ya shiga Gym motsa jiki har sai karfe 7 ta yi , yau kuma ya tashi har 9 ba dan mintina , gaskiya akwai wata a ƙassa

a hankali ta mike tsaye ta na ce ma Vedad ya jira ta ta na zuwa da ga haka ta Haye stair
kai tsaye part din Ash ta nufa ta wuce kai bedroom din shi
bakin ta da sallama ta shigo bedroom din dai'dai lokacin da Ash ya bude kofar toilet ya fito daure da towel a kugunshi ya na rike da wani karamin a hannun shi

cen kassan makoshi ya amsa mata sallamar ta sannan ya nufi dressing mirror ya tsaya ya ba ta baya

a hankali ta karaso ta tsaya tsakiyar dakin ta ce " Little wai me ya ke damun ka ne , Yanzu Vedad ke ce min wai yanzu ka tashi da ga barci , ko ba ka da lafiya ne "

ba tare da ya juyo ba ya ce " i'm fine mummy "
ya na gama fadar haka ya ji saukar hannun ta saman shoulder din shi , a hankali ya dago kai ya kale ta , ta cikin mirror

hannun shi ta kamo ta jawo shi , ta zaunar da shi bakin gadon shi sannan ta zauna geffen shi , shi dai da ido kawai ya ke bin ta

marairaice fuska ta yi kamar karamar yarinya ta ce " Alyasat ni fa na haife ka , na san akwai wani abun da ba ka son fada min , tun ka na karami ba ka taba boye min abun da ke damun ka ba sai yanzu , ko ka na tunanin yanzu ka yi girman da ba za ka iya fadamin ba ? "

a hankali ya dan lumshe idanun shi kamar mai jin barci ya sake bude su a kan ta murya cen kassan makoshi ya ce " please mummy ki fahimce ni mana , na ce miki ba komai "

mikewa tsaye ta yi ta na fadin " shikenan kar ka fadi , Ni kuma na yi maka alkawari ba zan saka komai a baki na ko ruwa ba zan sha ba , har sai ka fada min abun da ke damun ka " ta na gama fadar haka ta fara takawa za ta bar wajen a fusace

da sauri Ash ya riko hannun ta , ya na fadin " please mummy kar ki min haka "
juyo wa ta yi ta kale shi cikin tsare gida ta ce " little , ni fa mahaifiyar ka ce , Idan ba ka fada min damuwar ka wa za ka fadawa "

sakin hannun ta ya yi a hankali ya sunkuyar da kai ya na fadin " ko na fada miki ba za ki gane ba ne "

a hankali ta dawo geffen shi ta zauna ta na dafa shoulder din shi ta ce " just Tell me , i will understand you "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya dago kai ba , murya cen kassan makoshi kamar ba ya son maganar ya ce " I don't know how it happened you know I never had these kinds of desire , I raped a girl and she died , I couldn't control myself I killed her mom, I arrested Rapists more than a hundred times and today I myself raped a girl who didn't even reach 15 years old and she died because of me " ya kai karshen ya na sunkuyar da kai

Dum Nihal ta ji zuciyar ta ta buga a dubu dari ta mike tsaye ta na fadin " inallillahi wa'ina illaihi raji'un , Alyasat ta ya za ka yi irin wannan abun , na shiga uku yau ni Nihal , amma Alyasat ba ka rike amanar aikin ka ba , ka san ka na sha'awar mace ba za ka iya fada min ba na samu yarinya na aura maka , shi ne za ka je ka kashe ɗiyar mutane , ka cuce ni Alyasat , Yanzu fada min ina gawar ta ta ke "

" yo ai mummy ke ki ka tashe ni kafin na San yadda zan yi da gawar ta "
cike da rudu Nihal ta ce " ban gane abun da ka ke cewa ba "

kauda kan shi dayan geffen ya yi ya na fadin " ina tsaka da mafarkin ki ka zuba min ruwa a fuska na tashi "

nan take Nihal ta yi sumar tsaye lips din ta har kerma su ke yi ta bude ta ce " mafarki ? "
a hankali ya gyada mata kai kafin ya ce " yeah a dream "
" Ash , ba dai cikin mafarkin ka ba ka yi wannan abun da ka fada min "
a hankali ya dago kai ya kale ta ya ce " it's just a dream mummy , ke fa ki ka ce na fada miki abun da ke damu na , sai da na ce miki baza ki gane ba , Hope dai ba tunanin ki ke ba hakan ta faru da gaske ? "

nan take Nihal ta zube kassa ta yi irin zaman bokaye ta daura hannayan ta duka biyu saman kai kamar za ta yi kuka ta ce " Wayoooooo ni Allah , Abban Ummi ina ka shiga yau Alyasat zai sa zuciya ta ta buga "

MY BOOK IS ONLY ₦300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753






اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM










FREE PAGE ............9.........❤🥂






cikin konciyar hankali Ash ya ce mata " mummy ke fa ki ka ce na fada miki abun da ke damu na "

mikewa tsaye Nihal ta yi ta nufi hanyar fita dakin ta na fadin " Wlh Ash ka ci uwar raina min hankali sama da Vedad ma , amma bar ka , zai yi maganin ka " ta na gama fadar haka ta fice dakin

Da kallo ya raka ta har sai da ta fice dakin sannan ya tashi a hankali ya shige dressing room

Nihal kuwa kai tsaye parlourn kassa ta sauko , nan ta isko Vedad da Iqbal su na zaune abin su
Vedad na ganin Nihal ya tashi da sauri ya nufe ta ya na fadin " mummy mu tafi shan ice cream please , tun da mu ka zo har yanzu ba mu fita ba , kuma ni ina son mu fita na ga gidan da ku ka zaune ka da Daddy " ya kai karshen cikin shagwaba

dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " shikenan je ka cewa Felix ya shirya za mu fita " ba ta gama rufe bakin ta ba ya juya da gudu ya fice parlourn , a hankali shi ma Iqbal ya mike ya bi bayan shi , dan ya gaji da zama cikin gidan

su na fita Nihal ta ci gaba da takawar ta , ta nufi corridor ta shiga part din ta
ba ta yi five minutes ba ta fito rike da wata yar bag , da face mask ta fice parlourn
ta na fitowa sai saman wata dankareriar mota fara kal mai mugun kyau an yi parking din ta dai'dai kofar shigowa parlourn , Iqbal na mazaunin driver , Vedad na geffen shi
dan karamin murmushi ta saki kafin ta karaso wajen motar ta shiga gidan baya ta na fadin " Ba tare da Felix za mu tafi ba ? "

tada motar Iqbal ya yi su ka bar wajen ya na fadin " no mummy , ni na ce ya yi zaman shi "
da okay kawai Nihal ta amsa mishi , da ga haka ya danna hanci motar waje ya na tambayar Nihal ina za su yi , nan ta ke ce mishi ya yi dama , ba musu ya yi dama su ka bar wajen


▪ASH 🔥


bayan ya Fitar Nihal da ga Bedroom din ya tashi ya shiga dressing room

jim kadan ya fito sanye da Trouser black color da T-shirt white color , ya daure wanan curly hair din na shi a baya , Kafafun shi babu takalmi a ciki sai tashin fitinannan kamshi yake yi

ya na fitowa ya nufi bed din shi ya zauna ya dauki laptop din shi ya shiga aikin shi

bai yi five minutes ba da Zama Ummi ta shigo ta na sallama kassa kassa , ta sanye da kayan barcin ta , Duk gashin ta a tirje ya ke , da allamun ko wanka ba ta yi ba

ba tare da ya dago kan shi ba ya amsa mata sallamar ta cen kassan makoshi

a hankali ta karaso geffen shi ta zauna sannan ta yi baya ta konta
a hankali ya bude bakin shi ya ce " What's wrong ? "
wani dogon nunfashi ta yi kafin ta ce " nothing ! " ta fada a takaice

da ya ke ya san yar uwar ta shi , ya san ba karamin abu ba zai kawo ta wajen shi tun da safe haka ko wanka ba ta yi ba

a hankali ya ajiye laptop din shi saman bedside drawer , ya juyo kai a hankali ya kale ta ya ce " Oya stand Up , tell me what's wrong with you ? "

dan karamin gunguni ta yi kafin ta mike zaune ta na sunkuyar da kai ta ce " ta ya ka san da akwai wani abu ? "

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " don't forget you are my twins , Idan wani abu na damun ki , ina iya jin shi a jiki na "

dan karamin murmushi ta yi ta na fadin " It's true , ka na iya jin abun da ke damu na , ni ma ina iya jin abun da ke damun ka , kuma tun jiya da dadare na ke jin kamar wani abu ya faru da kai , shi ya sa na taho na duba in ka na lafiya "

a hankali ya dan sunkuyar da kan shi ya na fadin " i'm fine , mummy ma sai da ta tambaye ni , kuma na fada mata ni lafiya ta qlau "

" really you're fine ? "
a hankali ya gyada mata kai kafin ya dago ya kale ta ya ce " Tell me what's wrong with you too "

wani dogon nunfashi ta ja kafin ta koma baya ta konta
murya cike da rauni ta ce " Mafarkin Daddy na yi "
" and ! "
" I really missed him , Har yanzu ba kassa yarda ya tafi ya bar mu , ko ganin karshe ban yi mishi ba "

" I missed him too " ya fada cen kassa kassa

mikewa zaune ta yi ta na marairaice fuska ta ce " yanzu da gaske ya tafi ba zan sake ganin shi ba , Ash ka tabbata Daddy na cikin motar nan lokacin da ta watse , kar a je ya fice kafin Explosion din "

a hankali ya juyo ya kale ta ya dan girgiza mata kai kafin ya ce " Ki yi hakuri Ummi , amma Daddy ya na cikin motar , gaban ido na ya shiga cikin motar , kafin ma ya fita da ga cikin Headquater motar ta yi exploded , na duba ko ina amma ba mu samu komai ba da ga cikin gawar shi , Har yanzu wannan abun na cikin zuciya ta "

wasu hawaye ne su ka fara zubo wa Ummi kamar za ta yi kuka ta ce " Shikenan yanzu ba za sake ganin Daddy na ba , why Daddy ? why za ka tafi ka barni , ni fa har yanzu ina da bukatar ka , ya ka ke so na yi yanzu "

da sauri Ash ya sa hannayan shi biyu ya janyo ta jikin shi ya rungume ta ya na fadin " It's okay , ya isa haka please ki daina kukan nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login