Showing 54001 words to 57000 words out of 72572 words
ki ya warke da sauri "
a hankali Hayat ta gyada mata kai ta kai hannu ta ta karbi durgs din ta kai a baki sannan ta kai gorar ruwa a baki dama Ummi ta cire murfin ta shanye maganin sannan ta sauko gorar ruwan ta mikawa Ummi
karba Ummi ta yi ta ajiye saman bedside drawer sannan ta juyo da kyau ta kali Hayat ta ce " yanzu fada min shekarun ki nawa ? "
Dan karamin murmushi Hayat ta yi kafin ta ce " 14 " a takaice
" wow , kin san fa na yi ɗiya da ke , ni na kusa cika shekara 30 , da a ce na yi aure a shekara 16 , da yanzu ina da daughter dai'dai ke "
dan karamin murmushi Hayat ta yi kafin ta ce " Inna ta 33 gare ta "
" ki ce yarinya ce kamar ni " Ummi ta fada cike da zolaya
dariya sosai Hayat ta yi , cikin dariyar ta ta ke fadin " Yanzu ke ce yarinyar , Tab kenan har yanzu ni jaririya ce , Yanzu yaran ki nawa "
girgiza mata kai Ummi ta yi ta na fadin " ko daya , ko saurayi ban taba yi bare aure "
" laaa a shekarun ki , kuma ba ki da aure Tab , kin ji dadin ki gaskiya "
" Haka ki ke gani ? " Ummi ta fada ta na daga mata gera guda
cike da zamudi Hayat ta ce mata " eh mana kin ga ba wanda ke ce miki ki yi abu kaza , ki daina wannan abun , babu wanda za ki kula da shi sai kan ki , Ki ci abin da ki ke so , ki sha abin da ki ke so , ki saka abin da ki ke so , Ki na rayuwar ki cikin konciyar hankali , Ko ni da zan samu irin wannan damar , sai na zagaye duniya baki daya ina sha'ani na " ta fada ta yar karamar har da ware mata hanayan ta
Dariya sosai Ummi ta yi , dan maganar ba karamar dariya ta ba ta ba
ganin yadda Ummi ke wannan dariyar ne ya sa Hayat yin shiru ta koma ta na sunkuyar da kan ta ta ce " ki yi hakuri "
" no kar ki damu , Ina jin dadin ganin ki ki na dariya ba karamin kyau ki ke yi ba , gaskiya bari na yi wa mummy magana ta yi wa General kamu " Ummi ta fada ta na kai hannu ta ja kumatun Hayat
" uhm uhm ni gaskia ban shirya aure ba har yanzu ni jaririya ce , kuma ni ban ma san wanda ki ke cewa , kuma , kuma inna ta ba...... "
cikin nitsuwa Ummi ta katse ta da cewa " kontar da hankalin ki babu wanda zai yi miki auren dole , ke da kan ki idan ki ga General za ki ji ki na son kasance wa tare da shi , Kin ga ai ina da kyau ko "
a hankali Hayat ta gyada mata kai allamun eh
" to yadda na ke haka shi ma General ya ke , saboda Tawaye na ne , ya na da kirki sosai , sai dai ba ya son raini , idan ka ce za ka raina shi , zai yi wa mutum dukan mutuwa , kuma ba izinin ramawa , shi fa bai taba kallon mace ba ya ce ya na son ta , matan ke biyar shi , su na cewa su na son shi , bai cika yawwan magana , kin ga tun zuwan mu Nigeria ko so guda bai sauko da ga dakin shi ya zo ya zauna tare da mu , ya yi hira , kullum ya na cikin dakin shi , sai dai me son magana da shi ya tarda shi dakin shi , mutum ne shi da ba ya son hayaniya sam "
" To ni na minene za ki fada min wannan abun dukka ? " Hayat ta fada dan ba ta gane inda Ummi ta nufa
wani cool murmushi Ummi ta yi kafin ta ce " ina son ki zama matar sa , ban san dalilin da ya sa na ke jin mugun son ki raina kamar yarinyar da na haifa , Dan uwa na mutum ne me kirki da kyakyawar zuciya , Ya kamata a ce ya samu matar da za ta kula da shi a yanzu , wadda za ta kontar mishi da hankali , dan kullum cikin damuwa ya ke , rabon da na dan uwa na ya yi ko dan karamin murmushi yanzu an yi shekara 20 , bayan ni da mummy , babu mace a cikin gidan nan , lokaci guda na ji dadin zama da ke a gidan nan kuma gaskia ba na son ki tafi ki bar mu "
dan karamin murmushi Hayat ta yi kafin ta ce " da ga gani ki na son dan uwan ki "
gyada mata kai Ummi ta yi ta na fadin " sosai ma , ina son shi fiye da komai na wa , shi kadai na ke kallo na ji dadi cikin zuciya ta , ina son ya ji wannan dadin cikin zuciyar shi shi ma , ba ki san irin abubuwan da ya yi na al'hairi a rayuwar shi , kullum cikin yi mishi adu'a da Fatan Al'hairi mutane ke yi mishi , shi ya sa na ga ya dace a ce yanzu ya na da na shi familyn "
" to ke me ya hana ki yin auren kema , na ga ai shekarun ki daya "
girgiza mata kai Ummi ta yi kafin ta ce " ki yi hakuri ba zan iya fada miki ba , yanzu dai konta ki huta nan da kwana biyu idan kin samu sauki za mu meda ki gidan ku " ta kai karshen ta na mikewa , ta riko kafadun Hayat ta kontar da ita sannan ta janyo duvet ta rufe ta har zuwa kirji sannan ta ce mata sai da safe , da ga haka ta kai sannu ta kashe lamps din dakin ta kunna bedside lamps , sannan ta fice dakin ta koma na ta
Ummi na fitowa ta ci karo da Nihal zaune saman sofa
kallon ta da kyau Ummi ta yi kafin ta karaso geffen ta ta zauna ta na fadin " Mummy kin jima a nan ne " abun da ba ta sani ba tun lokacin da su ka fara maganar nan da Hayat Nihal ta shigo dakin , dama ta zo ta duba in Ummi ta ba ta maganin ta shi ne ta jiyo su su na magana , duk hirar nan da su Ummi su ka yi Nihal ta ji su
dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " ban jima ba yanzu na shigo "
" okay ni zan shiga na konta " Ummi ta fada ta na kokarin mikewa
da sauri Nihal ta ce mata " zauna ina son mu yi wata magana "
ba tare da ta zauna ba ta ce " mummy in dai maganar aure na ce to ki bar ta kawai sai da safe " ta fada ta na fara takawa
ko taku biyu ba ta yi ba Nihal ta riko hannun ta ta ce " no ba maganar auren ki ba ce , maganar auren Ash ce , ina son na ji ra'ayin ki a kai , ina son na nema mishi auren yarinyar nan Hayat "
da sauri Ummi ta dawo ta zauna geffen Nihal ta na washe baki ta ce " kin ga ko mummy ni ma maganar nan ta na cikin rai na sosai , Yarinyar nan za ta dace da General "
hararrar wassa Nihal ta yi mata ta na fadin " to sannu madam , to ke yaushe za ki samu wanda zai dace da ke , kar ki manta ce min ki ka yi duk ranar da Ash ya yi aure ke ma za ki yi , to ki shirya ki fido da mijin aure dan Ash ya samu mata "
yar karamar dariya Ummi ta yi kafin ta ce " mummy kar ki damu in har General ya yi ni ma zan yi in sha Allah "
" to na ji shikenan , yanzu ya ki ke so mu yi ? "
" nothing , kawai mu bari yarinyar nan ta kwana biyu tare da mu , mu ga yanayin ta , mu ga halayan ta , mu koya mata wasu abubuwa da ga baya sai mu meda ta gidan su , da ga nan a nema mishi auren ta , idan iyayen ta sun yarda , sai a yi auren nan wajen ki dawo da ita mu koya mata yadda za zauna da shi , abun da ya ke so , abun ba ya so da ga nan sai mu sakawa ikon Allah ido "
" shikenan to yadda ki ka ce haka za a yi " ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi kofar fita
da kallo Ummi ta raka ta har sai da ta fita sannan ta tashi ta shiga bedroom din ta ita ma
( MISALIN KARFE 12 NA DARE )
▪ASH 🔥
A hankali ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya ya na juyawa ya koma saman bayan shi
slowly ya fara ware idanun shi ya na fuskantar ceiling , sun koma Farare kal kamar da farko
mike hanayan shi ya yi ya na yar mika da allamun barcin ya yi mishi dadi
sai da ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune da ga haka ya mike tsaye ya nufi Toilet ko rufe kofar bai yi ba
After some minutes ya fito sanye da bathrobe ya wuce kai tsaye dressing room
jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi farare kal , ya saki wani wannan black curly hair din na shi , sai tashin kamshi ya ke yi
wajen bedside drawer ya nufa ya dauki wayar shi ya saka cikin aljihu sannan ya nufi kofar fita dakin ya daura hannun shi saman finger print , nan take kofar ta saki wata yar karamar kara sannan ta yo baya ta bude kan ta
ta na budewa ya sa kafa ya fito parlour , nan ya ga tray din fruits da junior da ya ajiye mishi
doguwar sofar ya nufa ya zauna , sannan ya kai hannu ya matso da table din ya fara shan Fruits din , dan tun jiya rabon shi da ya wani abu a bakin shi , shi dama ba wani ma'abocin ciye² ba ne
ko rabin fruits din bai sha ya tashi ya dauki tray din ya fito part din , kai tsaye stair ya sauko ya nufi dining room ya ajiye tray din saman dining table , sannan ya juya ya nufi parlour ya zauna
ya kai hannu cikin aljihun shi ya ciro wayar shi , ya sunkuyar da kai ya fara latsawa
nan take duk jelar shi ta zubo mishi ta rufe mishi fuska , sam bai damu ba ya ci gaba da aikin shi
bai yi one minute ba da zama wani jibgegen soja ya shigo parlourn , Sai da ya nufi Ash ya sara mishi sannan ya nufi stair ya Haye
▪HAYAT 💦
A hankali ta fara kokarin bude idanun ta ta na karanto adu'ar tashi da ga barci
ware idanun ta ta yi ta na fuskantar ceiling , a hankali ta kai hannun saman cikin ta , kafin ta sauko da kafafun ta kassa ta mike zaune sannan ta mike tsaye ta nufi kofar fita , ta fito parlour
a hankali ta fara bin parlourn da kallo , cen ta hango wata yar karamar fridge kusan Kofar bedroom din Ummi
da sauri ta nufi Fridge din nan , ta kai hannu ta bude a tunanin ta za ta samu wani abu
sai dai ba komai ciki da ga ruwa sai juice
dan karamin tsaki Hayat ta yi kamar ta yi kuka ta ce " ya zan yi ni yanzu yunwa na ke ji "
a hankali ta juya ta kali kofar fita part din sannan ta juyo ta kali kofar dakin Ummi , cije lips din ta na kassa ta yi sannan ta juya ta nufi kofar fita part din
a hankali ta ke tafiya cikin corridor din kamar barauniya
a haka har ta fito ta nufi dining room , ta na zuwa ta ga tray din Fruits saman dining table
dan karamin murmushi ta saki kafin ta nufi dining table din ta janyo chair guda ta zauna ta janyo tray din gaban ta , ta fara shan Fruits din cikin konciyar hankali
sai da ta ji ta koshi cikin ta ya cika sannan ta mike ta meda chair din wajen ta sannan ta juya za ta koma cikin corridor din idanun ta su ka sauka saman shi
ya na nan zaune ko motsawa bai yi ba ya na faman latsa wayar shi , tun fitowar ta da ga cikin corridor ya jiyo ta amma bai dago kan shi ba , asali ma a tunanin shi Ummi ce , shi ya sa bai dago kai ba
tsare shi da idanu Hayat ta yi cikin zuciyar ta ta na fadin " Aunty fa ce min ta yi su biyu ne mata cikin gidan , wagga kuma fa "
dan zaro idanu ta yi murya kassa kassa ya ce " kar a je aljana ce , dan wannan jikin ta bai yi kama da na mace ba " ta na gama fadar haka ta nufi corridor da gudu ta shige ta nufi part din Ummi ta shige bedroom din ta , ta Haye saman gadon ta janyo bargo ta rufe har kan ta , ta na karanto ayatul kursi
kar a je aljana ce ta gani , ga ta zaune tsakiyar parlour tsakar dare babu me rai ita kadai , ga yanayin jikin ta sam bai yi kama da na mace ba , ita gashin nan da ta gani ya sa ta tunanin mace ce , sam ba ta lura da murdaden jikin shi
Ash kuma ya na jin ta shige corridor ya dago kan shi a hankali ya kali Saitin corridor din
wani dogon nunfashi ya ja kafin ya yi baya ya jingina bayan shi a jikin sofar ya lumshe idanun shi
murya cen kassan makoshi kamar mai rada ya ce " I really miss you Dad "
ya na gama fadar haka wannan sojan ya sauko da ga stair , wannan karan ma sai da ya nufi Ash ya sara mishi sannan ya nufi kofar fita parlourn ya fice
Slowly Ash bude idanun shi sannan ya tashi ya nufi stair ya Haye ya koma part din shi
ya na shiga wani dadaden kamshi ya kai mishi karo , a haka ya karaso ya nufi bedroom din shi
a hankali ya bude kofar ya shiga , wani mugun sanyi mai dadi dakin ya ke , an gyara komai na cikin dakin , an sauya bedsheet , da Duvet din , an saka wasu ma su launin Sky blue , sai mugun kamshi su ke yi , da allamun dai sojan nan gyaran part din ya hayo
ya shigowa ya nufi bed din shi , ya zauna bakin gadon ya kai hannu ya ajiye wayar shi saman bedside drawer sannan ya kashe lamps din dakin duka har da bedside lamps , sannan ya sa hannu ya cire rigar jikin shi ya tila ta saman sofa , ya ida Hayewa bed din ya konta ya janyo duvet ya rufe jikin shi har zuwa kirji sannan ya daura hannun shi saman forehead ya lumshe idanun shi , a hankali ya fara karanto adu'ar barci , da ga haka wani nanauyan barci ya dauke shi , asuba ta gari
▪WASHE GARI ( Misalin karfe 8 )
a hankali lips din shi ke motsi ya na karanto adu'ar tashi da ga barci , kafin ya ware idanun shi ya na fuskantar ceiling
a hankali ya fara jiyo Muryar Vedad cike da nitsuwa ya na wata yar waka
slowly Ash ya juyar da kan shi , nan ya ga Vedad zaune saman bed din ya jingina bayan shi a jikin forehead din gadon , ya na rike da wayar shi ya na latsa wa , ya na motsa lips din shi a hankali
ya na fadin " MIRRORS , THEY NEVER LIE
DON'T SEE MYSELF INSIDE
WHY CAN'T I GET IT RIGHT ?
I DON'T KNOW !
YOU'RE ALWAYS WATCHING ME FALL
SHADOW THEY LIKE MY WALL
WHY DO I FEEL SO SMALL ?
I DON'T KNOW
SO , I WALK INTO THE DEAD OF NIGHT
WHERE MY MONSTERS LIKE TO HIDE
CHAOS FEELS , SO GOOD INSIDE NOW I KNOW
I LOST , I LOST , I LOST CONTROL AGAIN
ALWAYS DO THE SAME AND I'M TO BLAME I LOST CONTROL AGAIN
I DON'T , I DON'T , I DON'T KNOW WHO I AM
ALWAYS DO THE SAME AND I'M TO BLAME I LOST CONTROL AGAIN "
a hankali Ash ya dago hannun shi ya daura saman laps din Vedad
a razane Vedad ya daina wakar shi ya juyo ya kali Ash
wani dan karamin murmushi Vedad ya saki ya na fadin " Good morning Big bro "
dan lumshe idanun shi Ash ya yi kafin ya sake bude su a hankali ya ce " ka ji dadi ka tashe ni ko "
a hankali Vedad ya girgiza mishi kai ya na turo dan bakin nan na shi cikin shagwaba ya ce " no ni ban tashe ka ba , ka ga ma tafiya ta " ya na