Showing 57001 words to 60000 words out of 72572 words

Chapter 20 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

348

gama fadar haka ya ajiye wayar Ash saman bedside drawer ya sauko da ga saman gadon ya nufi door ya ficewar shi
shi dai Ash da kallo kawai ya raka shi har sai da ya fita sannan ya kai hannu ya dauki wata remote saman bedside drawer
ya danna wasu button , nan take kofar dakin ta meda kan ta , ya saka mata security , sannan ya kashe lamps din dakin sannan ya meda remote din saman bedside drawer , ya kai hannu ida janyo duvet din shi har kai ya rufe jikin shi ya ci gaba da barcin shi , da allamun kwana biyun nan General na samun hutu


โ–ชHAYAT ๐Ÿ’ฆ


konce ta ke tsakiyar Gadon ta , ta na kallon ceiling , tun wajen karfe 6 ta farka da ga barcin ta , amma ta kassa motsi kawai ta tsaya ta na kallon ceiling din

ta na a haka Ummi ta turo kofar dakin ta shigo ta na sallama
a hankali Hayat ta juyo kan ta ta kali saitin kofar ta na amsa mata sallamar , sannan ta mike zaune ta na fadin " Ina kwana Aunty "

cike da fara'a Ummi ta amsa mata gaisuwar ta sannan ta ce " na ษ—auka har yanzu ba ki tashi ba "
dan sunkuyar da kai Hayat ta yi ta na murmushi ba ta ce komai ba
dan karamin murmushi Ummi ta yi kafin ta ce " Shikenan yanzu tashi mu tafi ki yi wanka , Zuwa gobe kayan ki za su iso "

cike da rudu Hayat ta ce " Wane kaya Aunty ? "
" kar ki damu , yanzu tashi mu je ki yi wanka "
" Aunty ba sai kin raka ni , na iya wanka " Hayat ta fada ta na saukowa da ga saman gadon

yar karamar dariya Ummi ta yi kafin ta ce " kar ki damu , zan gwada miki yadda a ke yin brush , na kuma wanke miki gashin kan ki , sai ki yi wankan ki "
murmushi kadan Hayat ta yi ta na gyada mata kai sannan ta nufi toilet , Ummi na biye da bayan ta , su ka shiga toilet din tare


โ–ชAFTER SOME MINUTES


Sai da su ka dauki wajen good one hour a cikin toilet din , har wanka sai da Ummi ta yi wa Hayat kun san fa turawan nan ba kunya su ka sani ba , Ita Ummi ko a jikin ta , ta yi wa Hayat Wanka da kyau ta gwada mata yadda a ke yin brush , ta wanke ma ta gashi , tubarikallah ta na da gashi sosai har tsakiyar bayan ta , Baki da shi amma ya yi wani russet da ga tsakiya gwanin burgewa ga sulbi kuma

bayan sun fito da ga cikin toilet din , Ummi ta zaunar da Hayat saman chair din gaban dressing mirror , ta je dakin ta ta dauko hairdryer ta bushe mata gashin ta , Ta daure mata shi a baya

" bara na dauko miki kayan da za ki saka " Ummi ta fada ta na juyawa ta fice dakin

ita dai Da ido kawai ta ke bin Ummi , sai da ta fita sannan Ta kali mirror din gaban ta
kamar ba ita ba , har wani haske ta kara , ta kara kyau , color din nan na chocolate ya fito da kyau , kawai sai ta tsargu da kallon kan ta cikin mirror din babu ko kiftawa

ta na a haka Ummi ta dawo cikin dakin ta na sallama ta na rike da wata gown Sky blue
a haka ta karaso ta tsaya bayan Ummi ta mika mata Rigar ta ce " tashi ki shiga dressing room sai ki saka su , akwai pant amma banda Bra din da za ta miki shi ya sa na dauko miki Vest din nan " ta fada ta na mika mata kayan

da to kawai Hayat ta amsa mata sannan ta mike da ga saman chair din nan ta karaso gaban Ummi ta kai hannu ta karbi kayan sannan ta juya ta shiga dressing room

da kallo Ummi ta raka ta har sai da ta shiga sannan ta zauna bakin gadon

sannu sannu har sai da Ummi ta share wajen ten minutes zaune bakin gadon Hayat ba ta fito ba

a hankali ta juya ta kali kofar dressing room ta na fadin " kar a je ta kassa saka rigar " ta kai karshen ta na tashi ta nufi kofar dressing room

ba ta yi taku biyu ba ta tsaya cak ta na kallon kofar dressing room
a hankali Hayat ta bude kofar ta fito ta na sunkuyar da kai
Allahuma barik , Baki na ya yi kadan ya fada muku irin kyawon da idanu na su ke gani , kamar a jikin ta a ka yi rigar nan , ta zauna mata dai'dai a jiki , Shape din ta sun fito gwanin burgewa
rigar da kan ta abun kallo ce , da kadan ta wuce mata guyiwowi , ta na da dogayen hannu , ta sha Stone da ga tsakiya kamar belt gaskiya na kassa fada muku irin kyawon rigar da ma wadda ke sanye da rigar

a hankali ta ke takowa ta karaso gaban Ummi ta tsaya sannan ta dago kan ta ta saki wani cool murmushi






MY BOOK IS ONLY โ‚ฆ300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753







TAแƒฆRIN ZแƒฆCIYA ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’




( RETแƒฆRN )









(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐Ÿ’‹๐Ÿ”ฅ







โค๐Ÿ‘‘ ๊ช‘๊ช–๊ชถ๊ชถ๊ช–ฦ™แป‰แญข แฉ๊ชนแป‰แญขแจถ๊ซ€เฐ•เฐ• ๊ช‘๊ซ€๊ซ€๊ชน๊ช–๊ซ ๐Ÿ‘‘โค

๐Ÿ•Š๐Ÿ’ž


Wattpad : @bennybite







Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )











FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐Ÿ‘๐Ÿ’•






ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ๏ธ







DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb










๐—ง๐—”๐—ฃ ๐—ง๐—›๐—œ๐—ฆ ๐—Ÿ๐—œ๐—ž๐—˜ ๐—ง๐—ข ๐—๐—ข๐—œ๐—ก ๐— ๐—ฌ ๐—ฃ๐—ข๐—ฆ๐—ง๐—œ๐—ก๐—š ๐—ฅ๐—ข๐—ข๐— 

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i















_________________โœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆ__________________










PAGE ............13.........โค๐Ÿฅ‚





Baki sake Ummi ke kallon ta , ba karamin kyau ta yi mata ba , kamar ta sace ta ta gudu
" la la la , wacece wanan , ina Hayat di ta ta shiga " Ummi ta fada cike da zolaya
murmushi mai dan sauti Hayat ta yi kafin ta ce " Aunty , ni ce fa , ba ki gane ni ba "
" Masha Allah , Mu je mu yi breakfast to na San ki na jin yunwa " Ummi ta fada ta na kamo hannun Hayat su ka fice dakin

a tare su ka fito part din kai tsaye su ka nufi parlour
duk mutanan gidan su na nan zaune Banda Ash da ke part din shi , har junior ya na nan zaune su na hirar su Vedad na aikin da ya saba na zuba musu shagwaba

su na a haka Ummi da Hayat su ka fito shigo parlourn Ummi na sallama
a tare duk mutanan wajen su ka kai kallon su kan Ummi su na amsa mata sallamar ta
su na sauke idanu kan Hayat amsar ta makale ta kassa fitowa , kowa ya tsare Hayat da ido baki sake

Hayat kuwa duk ta bi ta tsargu , ta takure waje guda saboda irin wannan kallon da su ke yi mata
su na a haka ta jiyo Muryar Junior ya na fadin " mummy wacece wanan kuma ? "

Nihal na shirin magana Vedad ya riga ta cewa " Marshal ba ka gane ta ba , yarinyar da Iqbal ya buge ce jiya " ya kai karshen ya na mikewa tsaye ya nufo in da su Ummi ke tsaye ya kai hannu ya kamo hannun Hayat ya na fadin " mu je ki yi breakfast "
da ga haka ya juya su ka nufi dining room , ya janyo mata chair da kan shi ta zauna shi ma ja ta geffen ta ya zauna ya kai hannu ya dauko plate din Pancakes da ke gaban shi ya kawo gaban ta ya na fadin " ke na ajiye wa , ci ya na da dadi sosai "

ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Iqbal ya na fadin " yanzu Vedad na ce ka ba ni Pancakes din nan ka hana ! "

" eh na hana ai ba kai na ajiye wa ba " Vedad ya fada cikin shagwaba ya na murguna mishi baki
sannan ya kali Hayat da ta tsare shi da ido ya ce " Ki ci abin ki tun Iqbal bai saka miki ido ba " ya kai karshen ya na daukar fork ya mika mata
ba musu ta karba ta tsaya ta na kallon Pancakes din ta ma rasa ta ina za ta fara ita ba ta ma san ko minene ba

ta na a haka kawai sai ji ta yi Vedad ya kwace fork din hannun ta ya na fadin " bari na ba ki a baki " ya fada ya na kokarin yanko Pancakes din ya kai mata a baki

ba musu ba bude baki ta karba a hankali ta fara taunawa
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " akwai dadi ? "
da sauri ta gyada mishi kai allamun eh
yar karamar dariya Vedad ya yi ya na ci gaba da ba ta a baki

Nihal kuwa sai kallon su ta ke ta na murmushi , Allah kadai ya san abun da ta ke tunani dan idanun ta sun ciko da ruwa

kallon Iqbal Ummi ta yi ta na fadin " kai Iqbal , wai ina General ya yi , tun jiya rabo na da shi "
daga kafadun shi Iqbal ya yi allamun ban sani dan shi rabon shi da Ash tun shekaran jiya ba ma jiya ba

" Ummi tashi ki dibo shi , ina ga ba shi da lafiya " Nihal ta fada ta na kallon Ummi
gyada mata kai Ummi ta yi kafin ta tashi ta nufi stair ta Haye
kai tsaye part din Ash ta nufa , da sallama a bakin ta ta shigo parlourn shi , ta ga babu kowa a ciki , sai ta wuce bedroom din shi
har ta tura kofar a tunanin ta bude ta ke sai ta ga akasin hakan

a hankali ta sa hannu ta fara yi mishi Knocking ta na fadin " General Bude Kofar nan Ummi ce "
shiru ba a bude mata kofar ba , haka ta tsaya ta na ta bubuga ta


โ–ช'ASH ๐Ÿ”ฅ


tun bugun farkon da ta yi ya juyo ta amma ya kyale ta
sai da ta yi wajen bugawa biyar sannan ya fido hannun shi da ga cikin duvet din , ya kai saman bedside drawer ya dauki remote ya danna wani button kofar dakin ta bude sannan ya saki remote din ya bar hannun nan saman bedside drawer

kofar na budewa Ummi ta shigo dakin ta na yi mishi sallama
nan ta gan shi konce saman gadon shi ya rufe duk jikin shi da duvet ga hannun shi nan saman bedside drawer

a hankali ta karaso bakin gadon ta zauna , ta kai hannu ta kunna lamps din dakin sannan ta janye mishi duvet din nan

idanun shi su na bude , ya kurewa waje guda ido har ta janye mishi duvet din shi bai motsa ba
a hankali ta daura hannun ta saman neck din shi ta ji temperature din shi dai'dai ta ke
" My Twins wai me ke damun ka ne , a sani na ba ka taba kai karfe 8 ka na kwana , yau har karfe goma ta yi ba ka motsa ba " ta fada cikin nuna damuwa

a hankali ya motsa lips din shi ya ce mata " hutu na ke "
ba ta san lokacin da wata yar karamar dariya ta kubce mata ba har ta daura hannun ta guda saman bayan shi ta na fadin " The General of American Army Staff Ash , yau da kan ka ke fadin hutu ka ke yi , fada min gaskia wane abu a ka yi "

dan karamin tsaki Ash ya yi kafin ya sauko da kafafun shi kassa , ya mike tsaye bai ce mata komai ba ya fara takawa ya nufi toilet ya shiga ya bar ta nan

After some minutes ya fito sanye da bathrobe , ta na nan inda ya bar ta , amma ta gyara mishi Bed din , ta na zaune a baki ta na rike da wayar ta

bai ce mata komai ba ya nufi dressing mirror ya dauki lotion din shi ya fara shafawa sannan ya nufi dressing room ya shiga
duk abun da ya ke ta na kallon shi ta kassan ido

jim kadan ya fito sanye da Trouser Black color da T-shirt white color , kafafun shi kuma cikin wasu shagon sneakers farare kal ma su mugun kyau , ya saka wasu gloves bakake a hannayan shi , da wasu glass bakake a idanun shi , ya daure wanan lalawsan curly hair din na shi a baya sai tashin kamshi ya ke kamar companyn perfume abun dai Masha Allah amma dai fuskar nan a daure ta ke tamau kamar hadari , sam babu wassa a ciki

ya na fitowa ya nufi bedside drawer ya dauki wayoyin shi , ko sannu bai ce ma Ummi ba ya nufi hanyar fita gidan
da sauri Ummi ta riko hannun shi ta na fadin " General ina kuma za ka je ka kyale ni "
slowly ya juyo ya kale ta cikin wadanan bakaken glass din shi
cikin wata zazzakar sexy voice din shi ya ce mata " sake min hannu akwai wajen da za ni "
yanayin da ya yi mata maganar ya sa ta sakin hannun shi babu shiri
allamun yau mutanan sun hau , sam ba allamun wassa a tattare da shi yau

ta na sakin hannun shi ya juya ya ci gaba da tafiyar shi
da sauri ita ma ta mike ta bi bayan shi su ka fice part din

tun da ya fara tako stair mutanan gidan su ka tsare shi da idanu , da Allamun yau na mulkin na sama
bai bi ta kan su ya sa kai ya fice parlourn baki daya

ya na fitowa duk sojojin da ke cikin gidan su ka tsaya cak waje guda su na daga kafa sama su na sara mishi amma bai bi ta kan su
ya nufi wajen motar da a ka shirya mishi dan dama ya fada wa Felix ya shirya mota za su fita
ya na isowa bakin motar Felix ya sara mishi ya na fadin " Good morning Sir " ya bude mishi kofar gidan baya
bai bi ta kan gaisuwar shi ba ya shiga motar
ya na shiga cikin motar Felix ya rufe ya zagayo da gudu ya shiga mazaunin driver
ya tada motar , su ka bar gidan da mugun gudu
sai da su ka bar gidan sannan sojojin nan su ka sauko da hannayan su , su ka ci gaba da aikin su , kawai dai su na ta zagaye gidan

a cen cikin gidan kuma
Ummi na sauko stair din ta ga Vedad da Hayat ba su cikin dining room , ba kuma su cikin parlour

kallon Nihal ta yi ta na fadin " mummy ina kuma su Vedad su ka yi ? "
" wai ya tafi ya gwada mata garden " Nihal ta fada ta na dan karamin murmushi
mikewa Iqbal ya yi ya na fadin " bari na je na gani " ya kai karshen ya na fara takawa

sofa Ummi ta nufa ta zauna ta na kallon junior ta ce " a'a Marshal ba tare za ku fita ba kenan ? "

girgiza mata kai junior ya yi ya na murmushi kadan ya ce " no , shi ma ba zai jima ba yanzu ya dawo " ya fada ba tare da ya dago kan shi da ga saman wayar shi ba
shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba ta fara latsa wayar ta ita ma

bangaran Iqbal kuma
kai tsaye cikin corridor ya nufa , ya yi tafiya mai dan nisa kafin ya iso karshen shi
wata door ce ta glass , ya na isowa ta zuge kan ta ya daga kafa ya shiga

wani tanpasheshen garden ne , mai mugun girma , babu abun da babu a cikin shi
akwai filin buga ball , da swimmig pool geffen filin cen karshen garden din

ta ko ina cikin garden din ciyayi ne , da kananan flowers multicolore ma su mugun kyau , ko ina akwai kananan chair Farare irin na shan iska

gefe guda kuma akwai wata Runfa mai dan girma an kawata ta da wasu lilo guda Uku ma su dan girma
biyu na fuskantar juna , guda tsakanin su , da ga tsakiya kuma akwai wata table ta glass mai mugun kyau
runfar duk zagaye ta ke da flowers gwanin burgewa

cen ya hango Vedad da Hayat zaune saman lilo
dan karamin murmush Iqbal ya yi kafin ya karaso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login