Showing 15001 words to 18000 words out of 72572 words

Chapter 6 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

488

" kin yi kyau gaskia "
Hararrar wassa ta yi mishi ta na kauda kai gefe wai ita ta ji kunya

Yar karamar dariya ya yi kafin ya tada motar su ka bar wajen ya na fadin " Baby ina ki ke son mu je "
Dawo da kallon ta ta yi gare shi cikin nitsuwa ta ce mishi " Duk inda ka ke so , amma ya kamata mu koma gida kafin karfe 7 , gobe ina da exams "
Gyada kan shi ya yi ba tare da ya ce mata komai ba
Ita dai kallon shi kawai ta ke ta na sakin murmushi

Cen kuma sai ta bude baki a hankali ta ce mishi " na yi kewar ka sosai in ka tafi "
Wani cool murmushi ya saki kafin ya yi parking din motar shi geffen titi ya juyo da kai ya kale ta , duk yanayin face din ta ya sauya ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka

" ya isa haka kar ki ce za ki yi min kuka , ni ma ba a son rai na ba zan yi tafiyar nan , kuma ai zan dawo "
Shagwabe fuska ta yi ta na kauda kai gefe ta ce " ni na san da ka je za ka manta da ni , ka yi sabuwar Girlfriend a cen "

Maganar ba karamar dariya ta ba shi ba , amma sai ya yi dan karamin murmushi ya zagayo da hannun shi a kugun ta , ya janyo ta jikin shi ya na kallon face din ta ya ce " ke din ma da ya ki ka sace zuciya ta , ba na tunanin bayan ke wata za ta iya "

Yar karamar dariya ta yi ta kara matso da face din ta kusan ta shi " da gaske ba za ka so wata bayan ni ba ? " ta fada cike da shagwaba
Gyada mata kai ya yi allamun eh
" you promise ? "
" I promise Mrs Iqbal " ya fada ya na kashe mata ido guda

Yar karamar dariya ta yi kafin ta kai dan bakin ta ta daura lips din ta saman na shi ta yi mishi kiss
Ta na shirin janye bakin ta ya cabko lips din ta na kassa ya ci gaba da kissing cikin kwarewa , nan take duk wata sigar jikin shi ta mike , ya zagayo da dayan hannun na shi a baya ta ya na shafawa a hankali
Mayar mishi da martani ta shiga yi ita ma , dama ta jima ta na sha'awar shi amma kullum ya ki ba ta dama , yau dai ta samu abun da ta ke so

A hankali ta kai hannu ta riko zip din jacket din shi ta fara yi kassa da shi har ta fida shi , sannan ya sa hannu ta cikin t-shirt din shi , maimakon ta yi sama kawai sai ta yi kassa ta na neman sa hannun ta cikin trouser din shi

Ai ko cak ya damko hannun ta ya na ware idanun shi da su ka yi jazir , sai cikin na ta
Slowly ya zame bakin shi da ga cikin na ta , cikin wata zazzakar murya ya ce mata " me ki ke shirin yi ? "
A hankali ta girgiza mishi kai ta bude ta ce " I'm sorry , ni ma ban san na yi ba "
Bai ce mata komai ya janye hannun ta , ya daura shi saman cinyar sa , sannan ya sa hannu ya Meda zip din jacket din shi , ya tada motar shi su ka bar wajen

Marairaice fuska ta yi kamar za ta kuka ta ce " Baby , i'm sorry "
Slowly ya juyo ya kale ta kafin ya saki wani cool murmushi ya riko hannun ta , ya kai shi saitin bakin shi ya yi mata kiss sannan ya ce " It's okay , za ki je Funfair ? "
Da sauri ta gyada mishi kai ta na murmushi , shi ma murmushi ya yi mata da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har sai da su ka isa wani makeken park , ba sai na fada muku na wanene ba

A haka su ka shiga cikin park din nan , su na rike da hannun juna gwanin burgewa , park din ya na da mugun girma , sai misalin karfe 6 su ka baro shi , a hakan ma ba su hau duk carousel din park din

Kai tsaye apartments din ta ya meda ta , a wannan karan sai da ya sauko ya raka ta har apartments din ta , su ka yi sallama ta masoya sannan ya baro building din ya koma gida kai tsaye

Ya na komawa a ka fara kiran Sallar magriba , kai tsaye part din shi ya wuce dan babu kowa a parlourn , ya na shiga ya wuce toilet ya yi wanka ya fito ya shirya sannan ya yi sallat


▪AFTER SOME HOURS

▪ASH 🔥

Zaune ya ke saman bed din shi da ga shi sai short da singlet , ya rike da laptop din shi ya na faman aiki , allamun tun bayan fitar Iqbal bai je ko ina ba

Ya na a haka Vedad ya shigo Dakin ya na sallama , ya na sanye da kayan barcin shi white color sai tashin kamshi ya ke yi , ya na rungume da wani pillow a kirjin shi , kai tsaye bed din Ash ya nufa ya Haye ya yi rub da ciki

Sarai Ash ya lura da shi amma bai ce mishi komai ba
Sai da ya Kamala aikin shi sannan ya ajiye laptop din saman bedside drawer , ya kali Vedad ya daura hannun shi saman kan shi ya shiga shafa lalawsan gashin kan shi ya na fadin " My angel , what's wrong ? "

" Let me , ni ba na son yi maka magana yau " ya fada ba tare da ya dago kan shi ba
Ci gaba da shafa kan shi Ash ya yi ya na fadin " Why ? Laifin me kuma na yi ? "
Bai gama rufe bakin shi ba rufe bakin shi ba Iqbal ya shigo bedroom din ya na sallama ya nufi Sofar da ke fuskantar bed din ya zauna ya na kallon su Vedad

Ya na zama ya saki wata yar karamar dariya ya ce " Cutie pie , yau yan shagwabar ne ke sama ? " ya fada cike da tsokana

Da sauri Vedad ya dago ya mike zaune ya tila wa Iqbal pillown hannun shi ya na fadin " Stop calling me Cutie pie "
Da sauri Iqbal ya cabko pillown ya na dariya

" ya isa in wassan ku , ku ke son yi , ku tashi ku fice min daki " Ash ya fada cikin tsare gida
Turo dan bakin nan na shi Vedad ya yi cike da shagwaba ya ce " ni babu inda zan je a nan zan kwana ma " ya kai karshen ya na komawa geffen Ash ya zauna ya kontar da kan shi saman shoulder din Ash

Shi dai Iqbal dan karamin murmushi ya yi kafin ya jingina bayan shi a jikin sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi ya tafi duniyar tunanin shi

Ash na ganin hakan ya kai hannu ya dauki laptop din shi zai ci gaba da aikin shi
Vedad na ganin wallpaper din shi ya kai hannu ya kwace mishi laptop din ya na ci gaba da kallon wallpaper din ya saki wani kyawatencen murmushi
" My angel are you okay ? " Ash ya fada dan ya ji kamar Vedad ya yi sanyi

Girgiza mishi kai Vedad ya yi allamun ba komai ya na kashe laptop din ya mikawa Ash kayan shi
Karba ya yi ya meda ta saman bedside drawer sannan ya kai hannayan shi ya talabo face din Vedad nan ya ga hawayen da ke konce cikin idanun shi

Cikin konciyar hankali Ash ya ce mishi " My angel , why did you cry ? You know i don't like see you crying "
A hankali Vedad ya sunkuyar da kan shi ya fada jikin Ash ya rungume shi da kyau murya kassa kassa kamar me kuka ya ce " Big bro , wlh ina kewar Daddy over , kullum da dadare sai na jira shi , ya zo ya yi min adu'ar barci , amma kullum ba ya zowa har barci ya dauke ni "

" it's enough now , kar ka yi min kuka , ai ina nan , kuma Mummy ta na nan , ga Ummi and your best friend Iqbal , we are all here with you "

" i know but ....... "
Cikin nitsuwa Ash ya katse shi da cewa " But what , ko duk ba mu ishe ka ba ? "
Nan take kuka ya kubce wa Vedad , cikin kukan ya ke fadin " but i want to see my Daddy , I missed him "

Murya cike da rauni Ash ya ce mishi " please My angel stop crying , ni ma ina kewar Daddy over , kullum cikin yi mishi adu'a na ke , kai ma adu'a ya kamata ka dinga yi mishi duk lokacin da ka tuno da shi , ba kuka ba "

Slowly Vedad ya dago da ga jikin Ash ya na fadin " Da gaske ka na kewar Daddy ? " ya fada ya kallon Ash cikin ido

Gyada mishi kai Ash ya yi kafin ya kai hannayan shi ya fara goge wa Vedad hawayen shi ya na fadin " ina kewar shi mana , kawai dai na san adu'a ta ita ya fi bukata a yanzu , shi ya sa na shanye abun da ke cikin zuciya ta , ina yi mishi adu'a duk lokacin da na yi sallat "

Dan karamin murmushi Vedad ya yi ya na fadin " Ni ma kullum in na yi sallat sai na yi mishi Adu'a "

" Haka ya kamata ka dinga yi duk lokacin da ka tuno da shi my Angel " ya fada ya na kai hannu ya shafi geffen fuskar Vedad
Daga kan shi sama Vedad ya yi ya na fadin " Daddy ! You know i really missed you everyday ,Allah ya jikan kan , ya yi maka rahama , Allah ya sa ka huta , kai da dukanin al'umar musulmi da su ka riga mu gidan gaskia , ina rokon Allah ya sa wannan adu'ar ta tarda ka duk inda ka ke , I love you my Superman " ya kai karshen ya na sakin wani kyawatencen murmushi

A hankali Ash ya sa hannu ya janyo shi jikin shi ya rungume ya na fadin " na gwada maka wani abu ? "

Da sauri Vedad ya dago da ga jikin Ash ya na fadin eh
A hankali Ash ya koma ya jingina a jikin forehead din bed din shi sannan ya sa hannu ya dauki laptop din shi ya nuna wa Vedad geffen shi sannan ya shiga latsa laptop din
Da sauri Vedad ya dawo geffen shi ya zauna ya na murmushi

Ya na zama Ash ya mika mishi laptop din dai'dai wata video ta kama
Wani kyawatencen murmushi Vedad ya saki lokacin da idanun shi su ka sauka kan abun da ke cikin videon

Ba komai ba ne face Aylan shi da Vedad tun ya na karami ba zai wuce 3 years ba haka
Su na zaune saman Lillo cikin Garden din nan na Gidan Aylan na farko
Vedad sai tura fruits ya ke yi a baki Aylan na kallon shi ya na murmushi
Su na a haka Kawai su ka jiyo Muryar Nihal ta na kwallawa Vedad kira
Da sauri Aylan ya dauki Vedad ya bude jacket din shi ya saka shi a ciki sannan ya meda zip din kassa kassa ya ce " My angel yi shiru kar mummy ta jiyo ka , ta tafi da kai "
Yar karamar dariya Vedad ya yi ya na cikin jacket din Aylan

Dai'dai lokacin da Nihal ta karaso wajen lillon ta yi sallama sannan ta ce " Abban Ummi ina Vedad ya yi , tun safe na ke neman shi yaron na tsere ya buya "

Cikin ko in kula Aylan ya ce " Duba wajen Khaled may be Ya na cen shi da Iqbal "
Tsuke fuska Nihal ta yi ta ce " Abban Ummi minene ke motsi cikin jacket din ka "
Yar karamar dariya Ummi da ke rike da wayar Aylan ta yi ta na toshe bakin ta

Hararrar wassa Aylan ya yi mata kafin ya ce " Baby na ne , you don't know i'm Pregnant "
Wata muguwar harara Nihal ta wurga ma Aylan , da sauri ya sa hannu ya zuge zip din jacket din shi

Wani cool murmushi ta saki kafin ta koma geffen shi ta zauna ta daura hannun ta saman face din Vedad , har ya yi barci a jikin Aylan " Duba duk ya bata maka kaya " ta fada cikin sanyi

Rungume Vedad tsam Aylan ya yi ya na fadin " ba komai" ya kai karshen ya na kai dan bakin shi ya sumbaci forehead din Vedad da ga haka videon ta kai end

Yar karamar dariya Vedad ya yi ya dago kai ya kali Ash ya na mika mishi laptop din shi ya ce " big bro ina ka samo wannan videon ? "

Ajiye laptop din saman bedside drawer Ash ya yi ya na fadin " a lokacin Ummi ta na rike da wayar Daddy ta na game , Ta cikin camera din na ga abun da ku ke yi , ai ni na fadawa mummy ku na garden "

" you , you are wicked big bro " Vedad ya fada ya na kontawa ya rungume kugun Ash dan barci ya ke ji ya lumshe idanun shi

Shi dai Ash bai ce mishi komai ba , sai a lokacin ya tuno da Iqbal da ke zaune saman sofa , duk abun nan da su ka yi bai ce uffan ba allamun ya yi barci ko akasin haka

A hankali Ash ya kai hannu ya dauki pillow ya tila wa Iqbal
A razane Iqbal ya dawo cikin hayacin shi
Da sauri Ash ya ce mishi " Shut up !!!!!!!! Tunanin mi ka ke yi haka ? "
Dan karamin tsaki Iqbal ya ja ya na kauda kai gefe ya na turo dan bakin shi ya ce " ni ba tunanin da na ke "
" oya come here "

Ba musu ya taso ya dawo dayan geffen shi ya zauna ya na ci gaba da turo dan bakin nan na shi
" Fada min gaskia , ba dai wani abu ku ka yi kai da yarinyar nan ba " Ash ya tambaye shi , dan ya lura yadda sigar jikin shi duk ta ke mike

Cikin ko in kula Iqbal ya ce mishi " ni fa ba abun da na yi mata , ai ita ta fara yi min kiss "
" Kai kuma me ka yi mata ? "
" Kiss kadai na yi mata , ni ban ma san ya a ka yi ba kawai sai jin hannun ta na yi , ta na kokarin saka shi cikin trouser di na "
" ka bari ta saka ? "
Da sauri ya girgiza mishi kai ya na fadin " no , ban bari ba "

Okay kawai Ash ya ce kafin ya gyara konciyar shi , ya na rungume da Vedad
Shi ma Iqbal konta wa ya yi su ka saka Ash a tsakiya
" ka san wani abu ? " Iqbal ya fada ya na kallon Ash da ya lumshe idanun shi
Girgiza mishi kai ya yi ba tare da ya bude idanun shi ba

A hankali Iqbal ya matso ya kai bakin shi saitin kunen Ash kassa kassa ya rada mishi " Amma fa big bro , na ji dadin kiss din nan over "

Cikin ko in kula Ash ya ce mishi " Okay bari in mu ka dawo da ga Nigeria , Sai ka yi abun da ya fi hakan ba wanda zai hana ka , but ka ce min Duk familyn ta a New York su ke zaune ko ? "

" eh a NEW York su ke "
" Tun yaushe ku ke tare da ita ? "
" this year , wannan shekarar ce ta shigo university din mu , So za mu kai six to seven months haka "
A hankali Ash ya gyada kan shi kafin ya ce " Kai ka ce ka na son ta "

Yar karamar dariya Iqbal ya yi kafin ya ce " kai da ka san halin brother din ka , ita ta ce ta na so na , amma na ki yarda , Sai da ta matsa har kokarin kashe kan ta ta yi , sannan na hakura na yarda da ga baya na ji na kamu da son ta ni ma "

Shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba " Tabass akwai wani abu a kassa " ya fada cikin zuciyar shi saboda Binciken da ya yi da safe bai samo komai ba a kan ta , ko university din su Iqbal da ya duba register din First year bai ga mai sunan Maya ba , hakan na nufin akwai wani abu a kassa may be aiko ta a ka yi dan cutar da familyn shi ? Ko ma minene ya dauki alwashin sai ya gano shi , dan ba zai bari wani abu ya sami brother din shi ba
Da wannan tunanin har barci ya dauke shi , dan shi ma Iqbal ya jima da yin barcin shi



* NIGER ( ZINDER STATE )

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login