Showing 69001 words to 72000 words out of 72572 words

Chapter 24 - Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel

Anish   

02 Feb 2025

347

Inna in ba za su iya tafiya neman ta ba , ku bar ni na je neman ta da kai na , don Allah Inna "

hannu inna ta ja ta rungume Barira ta ce " Ki yi hakuri Barira ta , haba Diyar malam , jikar barbushi guda ko aljanu sun kyale ta bare mutum " inna ta fada cikin zolaya

yar karamar dariya Barira ta yi kafin ta ce " Inna , wace jikar barbushi kuma , ku kyale min Hayat di ta da wasu aljanai , ni da ma zan iya yi musu magana da zan ce su je su kawo min Hayat di ta "

yar karamar dariya inna ta yi ta na kai hannu ta buge ta kadan a baya ta na fadin " sannu mara kunya , ni za ki fadawa Haka ? sai na yi maganin ki "

" Uhm uhm ni ki kyale ni mun ma bata , da ga ina yi miki wassa "

hannu inna ta kai ta ja mata kumatu ta na fadin " na ji shikenan , ya kamata ki je ki yi sallat ki yi wa Hayat adu'a , a duk inda ta ke Allah ya kare miki ita , ya dawo miki da ita cikin koshin lafya "

wani cool murmushi Barira ta saki ta ce " In sha Allah za ta dawo min lafiya , na san Hayat di ta jaruma ce , za ta iya kula da kan ta a duk inda ta ke , duk wani mugun abu da ya tunkaro ta Allah ba zai bari ya cutar da ita ba , Zan ci gaba da yin adu'a Allah ya tsareta a duk inda ta ke , ya medo min ita lafiya "

da Ameen Inna ta amsa ma ta


MY BOOK IS ONLY โ‚ฆ300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753







TAแƒฆRIN ZแƒฆCIYA ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’




( RETแƒฆRN )









(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐Ÿ’‹๐Ÿ”ฅ







โค๐Ÿ‘‘ ๊ช‘๊ช–๊ชถ๊ชถ๊ช–ฦ™แป‰แญข แฉ๊ชนแป‰แญขแจถ๊ซ€เฐ•เฐ• ๊ช‘๊ซ€๊ซ€๊ชน๊ช–๊ซ ๐Ÿ‘‘โค

๐Ÿ•Š๐Ÿ’ž


Wattpad : @bennybite







Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )











FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐Ÿ‘๐Ÿ’•






ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒ๏ธ







DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i







๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb










๐—ง๐—”๐—ฃ ๐—ง๐—›๐—œ๐—ฆ ๐—Ÿ๐—œ๐—ž๐—˜ ๐—ง๐—ข ๐—๐—ข๐—œ๐—ก ๐— ๐—ฌ ๐—ฃ๐—ข๐—ฆ๐—ง๐—œ๐—ก๐—š ๐—ฅ๐—ข๐—ข๐— 

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡


https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i















_________________โœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆโœฆ__________________






PAGE ______16_____ ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฆ




Inna na gama rufe bakin ta wani yaro ya shigo da gudu cikin gidan babu ko sallama ya nufi gaban su Inna ya na faman haki ya ce " Inna Barira , ga wasu jibga jibgan sojoji tsaye bakin kofar gidan ki "

kallon juna Barira da Inna su ka yi kafin Barira ta juyo ta kali yaron ta ce " Sojoji kuma baba Idi ? a kofar gida na , cewa su ka yi su na nema na ? "

girgiza mata kai yaron nan ya yi kafin ya ce " Inna Barira ban sani ba , ni ma mu na wassa ne na gan su shi ya sa na taho na fada miki , kuma kuma na ga wata yarinya mai kama da Hayat a tare da su "

dum Barira ta ji gaban ta ya fadi da sauri ta mike tsaye ta na zaro idanu ta ce " Baba Idi Hayat di ta ka gani tare da su ? "

" Inna Barira , na ce miki mai kama da ita yarinyar nan fa yar burni ce idan ki ka gan sam ba ta yi kama da Hayat ba , idanun su ne kawai su ka yi kama "

da sauri Barira ta nufi kofar fita gidan ta na rokon Allah ya sa Hayat din ta ce

ta na kawo tsakiyar harabar gidan ta tsaya cak ta na kallon Hayat da ta nufo ta da gudu ta na hawaye

da sauri Barira ta nufe ta ta rungume ta , ta na sakin kuka kamar karamar yarinya ta na fadin " Hayat ! Da gaske ke ce ? Allah na gode maka , Allah na gode maka da ka dawo min da Shahd di ta cikin koshin lafya "

cikin kuka Hayat ta fadin " ni ce Inna , na yi kewar ki sosai Inna "

Barira na shirin magana Nihal ta shigo gidan ta na sallama , Vedad da Iqbal na biye da ta

da sauri Hayat ta raba jikin ta da Barira ta koma wajen Nihal ta riko hannun ta ta na fadin " Inna kin ga mummy , ita ce ta dawo da ni gida , mummy wannan ita ce Inna ta " ta kai karshen ta na nuna wa Nihal Barira

a hankali Barira ta karaso gaban Nihal ta rike hannayan ta dukka biyu kamar za ta yi kuka ta ce " na gode da ku ka medo min ita , Ita kadai na mallaka a duniya "

cikin nitsuwa Nihal ta katse ta da cewa " Shikenan ya isa haka , kar ki saka ni kuka ni ma "

ta na gama rufe bakin ta Vedad ya karaso geffen Nihal ya marairaice murya ya ce " mummy please mu tafi , ba na jin dadin tsayuwa a wajen nan "

cikin harshen Turanci Nihal ta ce mishi " My angel please calm down , ba za mu jima ba za mu koma "

ta na gama rufe bakin ta su ka jiyo Muryar Inna ta na fadin " Barira sai ki bar su a tsaye ? ku karaso mana "

da sauri Barira ta ce " don Allah mu je ku zauna , ko da ruwa ne ku sha na san kun debo hanya " ta kai karshen ta na nuna musu tabbarmar da Inna ke zaune

ba musu Nihal ta tako a hankali ta na rike da hannun Hayat su ka karaso wajen Tabarmar su ka zauna
dan karamin tsaki Vedad ya yi kafin ya juya ya fice , da sauri Iqbal shi ma ya juya ya bi bayan shi su ka koma cikin motar su

su na barin wajen Barira ta juya ta nufi tulunan gidan ta debowa Nihal ruwa cikin girmamawa ta mika mata

wani cool murmushi Nihal ta saki kafin ta kai hannu ta karbi cup din ruwan ta kai bakin ta , ta kurbi kadan sannan ta ajiye shi ta na yi wa Barira godiya

zama Barira ta yi ta kai hannu ta janyo Hayat ta na bin ta da kallo ta ce " Hayat ina ki ka samo irin wadanan kayan , dubi yadda ki ka sauya lokaci guda haka , ba dai Shafe shafe ki ka yi a cen ba "

yar karamar dariya Hayat ta yi kafin ta ce " Inna ba wani shafe shafe da na yi , kuma Aunty Ummi ta ba ni kayan nan , sun yi min kyau ? "

wani kyawatencen murmushi Barira ta saki kafin ta ce " Sosai ma kuwa ni da farko kassa gane ki na yi , sai ka ce irin Gimbiyoyin nan da mu ke gani a cikin Tv kin gane su ai ? "

dariya sosai Hayat ta yi har ga Allah ta yi kewar Innar ta , kuma ta godewa Allah da ya sa su Nihal ba kamar Hajiya ta ke ba , ga shi ta cika Alkawari ta medo ta wajen innar ta

" oun don Allah ina son na yi magana da mahaifiyar ta " Nihal ta fada cikin sanyi murya

gyada mata kai Barira ta yi kafin ta ce " Ina sauraron ki , wace magana kuma ? "

wani cool murmushi Nihal ta saki kafin ta juya ta kali Hayat ta ce " don Allah ina son wata Alfarma a wajen ki "

kallon Hayat ita ma ta yi cikin rudu ta ce
" wace irin Alfarma kuma ? "

dan sunkuyar da kai Nihal ta yi kafin ta dago ta kali Barira ta ce " na san ba za ki fahimce ni ba , amma ina jin Hayat sosai a ciki zuciya ta , ba na jin zan iya rabuwa da ita gaskiya , don Allah don son annabi Muhammad ( S.A.W ) ki bari na koma da Hayat , da na yi niyya ba abun da zai hana ni wucewa da ita america kai tsaye , amma kin ga sai da na medo miki ita saboda ni ma uwa ce , na san irin zafin da ki ka ji cikin zuciyar ki lokacin da ba ta nan , shi ya sa na medo miki ita dan ki san ta na cikin koshin lafya kuma ta fado a hannun mutanan kwarai , don Allah ki bari na koma da ita wlh ban jin zan iya rabuwa da ita "

dan zaro idanu Hayat ta yi ta na kallon Nihal ai ko abun da zai raba ta da innar ta a yanzu sai dai mutuwa , ta dawo kenan babu inda za ta je bare kuma ta ga Ash a cikin gidan ta san wannan babu tsoro a cikin idanun shi tabas zai iya kashe ta watarana

nan take ta fashe da kuka ta kankame Barira ta na fadin " Ni wlh babu inda zan je , ba zan bi ki ba , ni wajen Inna ta zan zauna "

rungume ta da kyau Barira ta yi idanun ta na kawo ruwa ta ce " Haba baiwar Allah , ya za ki min haka , ni ina godewa Allah Hayat di ta , ta dawo , ke kuma ki na neman ki raba ni da ita har abada ? idan ta tafi America ina zan samu damar ganin ta , ita kadai ce Allah ya ba ni ya zan rabu da ita "

cikin sigar rarrashi Nihal ta ce " za ta dinga dawowa , don Allah ki yi min wannan Alfarma ba dan na girme ki ba ? "

da sauri Barira ta girgiza mata kai ta ce " a'a ba zan iya rabuwa da Hayat di ta ba gaskiya ki yi hakuri malama "

har Nihal ta bude baki za ta yi magana wata zuciyar ta ce mata " ke tsaya , me zai hana ki tafi da su baki daya , kin ga Barira ba mumuna ba ce , da ta sha wanka za ta fito fess abun ta , ni da na ke da dan uwa zaune ba mata , lokacin kawo karshen gwaurancin yaya Rayan ne ya zo ba ki sani ba "

wani kyawatencen murmushi Nihal ta saki kafin ta ce " me zai hana mu tafi tare har da ke ? "

cak Barira ta tsaya ta na zaro idanu ta kali Nihal
ta na shirin magana Nihal ta riga ta cewa " don Allah , tun da kun ce ba za ki iya rabuwa da ita ba , me zai hana mu tafi tare da ku baki daya "

slowly Barira ta juya ta kali Inna , dan karamin murmushi inna ta saki kafin ta dafa shoulder din Barira ta ce " Barira ki yarda ku tafi tare da yarinyar ki , tun da har ta amince za ta tafi da ku ki yarda kawai "
Inna ta fada don har ga Allah za ta so Barira ta tafi , ga shi cikin kauyen ba ta da koya sai ita da malam , su kuma shekaru sun ja ba za su iya kula da ita ga kuma Hayat , ga shi ba wasu gonaki gare su da za su ci albarkacin ta , Idan har Barira ta tafi da Nihal hankalin su zai fi konciya da sanin ko bayan rayuwar su akwai wanda zai kula musu da ita , da su bar ta cikin wannan duniyar babu dangin uwa bare na uba gwara su bar ta a hannu mutunan kirki da su ka yarda da kan su za su karbe ta cikin ahalin su

Sunkuyar da kan ta Barira ta yi , kamar mai tunanin wani abu
cen kuma ta dago kai ta ce " amma Inna ki na ganin malam zai yarda "

" na san zai yarda , amma ku je na san ya na a fada yanzu sai ki tambaye shi "

inna na gama rufe bakin ta Nihal ta dora da cewa " eh , eh zai yarda ma , don Allah kar ki ce a'a ki tashi mu je mu tambaye shi idan ya amince sai mu wuce "

dan jinkirtawa Inna ta yi kafin ta raba jikin ta da Hayat ta ce " shikenan bari na hada kaya na " ta kai karshen ta na kokarin mikewa dan ta je ta gado kayan ta

da sauri Nihal ta taro ta ta na cewa " kar ki damu , za mu saya miki kaya a cen idan mun je , kawai ki tashi mu tafi , ba na son mu kai dare ba isa cikin gari ba "

kallon Inna Barira ta yi kamar za ta yi kuka ta rasa yadda za ta yi , ba za ta iya rabuwa Da Hayat ba , kuma ta na jin zafin rabuwa da inna matar nan ita ta kula da ita tun ta na yar shekara bakwai , har ta kai munzalin mutane su ka ba ta tarbiya me kyau , su ka shayar da ita , su ka tufatar da ita , su ka kai ta islamya , ta koyo sunnonin Sallat , karatun kur'ani su ka yi mata aure cikin amincin Allah ta samu Hayat , yanzu kuma ta rabu da su may be rabuwa ta har abada dan ba ta san yadda rayuwar su za ta kasance ba bayan tafiyar ta , kamar kar ta tafi kamar ta zauna tare da su , amma inna da kan ta ta ce ta tafi may be ta ga abun da ita ba ta gani ba

kamar Inna ta san abun da ta ke tunani sai ta ce mata " don Allah Meriem tashi ku tafi tun dare bai yi ba , kin san hanyoyin nan ba su da kyau musaman cikin dare "

gyada mata kai Barira ta yi hawaye na zubo mata , ta rungume Inna kamar za ta yi kuka ta ce " zan yi kewar ki sosai Inna , don Allah ki kula min da kan ki "

Rungume ta ita ma Inna ta yi ta na fadin " ni ma zan yi kewar ki Barira , ki kula min da kan ki don Allah , kar ki yi abun da zai janyo miki matsala kin ga mutanan nan sun ce za su tafi da ke , dan haka ki kiyaye ki ba su girmamawa ko ba komai ta girme ki , dan haka ki ba ta girman ta kin ji ko Meriem ? Allah ya tsare min ki , Allah ya kiyaye hanya ya kare min ke duk inda ki ke " ta kai karshen cikin raunin murya

" Inna kenan kin yarda za ki bi mummy , mu koma da ita ? " Hayat ta fada cikin rudu

a hankali Barira ta dago da ga jikin Inna ta saki murmushin karfin hali ta ce " Eh za mu bi ta "

dan zaro Hayat ta yi ta na fadin " Inna ni ba zan koma ba , wlh cikin gidan akwai wani mai idanun mage , ba shi da kirki ko kadan har shake ni ya yi kuma ya ce zai kashe ni "

ba ta gama rufe bakin ta ba Nihal ta bushe da dariya ta na fadin " Hayat , yanzu yaron nawa guda ki ke ce ma mai idanun Mage ? haba sai na aura miki shi ma , ki zama matar mai idanun mage " ta kai karshen ta na sakin yar karamar dariya

tsuke fuska Hayat ta yi ta na fadin " ai mummy ba karya na yi ba " ta kai karshen ta na kauda kai gefe kamar ba ita ta yi maganar ba

yar karamar dariya Nihal ta yi kafin ta mike tsaye ta na fadin " Shikenan ku tashi mu je , bari idan mu je gida ki tambayi Vedad wanene wannan , na san da ga ranar ko hanya ya bi ba za ki sake bin hanyar ba "

mikewa tsaye Barira ta yi , ta riko hannun Hayat ta mike tsaye , su ka yi wa Inna sallama sannan Nihal ta zuba mata godiya da makudan kudade na Franc CFA wanda su ke aiki da shi a Niger sannan su ka baro gidan

Barira na fitowa ta ga manyan motocin da Nihal ke tafe da su , ita duk duniya ba ta taba ganin irin su yau a ce ita za ta shiga wannan motar

a haka su ka shiga cikin motar Nihal da Hayat da Barira su ka shiga mota guda Already dama Vedad da Iqbal su na cikin motar a haka su ka tada motar su ka nufi fadar mai gari

kafin Barira Nihal ta yi kafin ta ce " Na ce , na ji wannan tsohuwar ta kira da Meriem kuma Barira , wane ne sunan ki na gaskiya "

wani cool murmushi Barira da ke rungume da Hayat ta saki kafin ta ce " Meriem ne suna na , Kawai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login