Showing 60001 words to 63000 words out of 72572 words
wajen lilon ya na musu Sallama
amsa mishi sallamar shi su ka yi sannan Vedad ya ce " yawwa gwara da ka zo , ce mata na yi dan uwa na Musician ne , amma ta ki yarda "
hararrar shi Iqbal ya yi ya na fadin " yaushe na zama musician ban sani ba " ya kai karshen ya na zama saman lilon da ke fuskantar nasu
juyowa Vedad ya yi ya kali Iqbal ya ce " Iqbal ka na tune da song din nan da Daddy je yawwan yi wa mummy ? "
wani cool murmushi Iqbal ya saki kafin ya ce " yeah ina tune da shi "
marairaice fuska Vedad ya yi kafin ya ce " please yi min shi " ya kai karshen kamar zai yi kuka
gyada mishi kai Iqbal ya yi kafin ya dan jinkirta ya fara rero mishi waka ya na fadin
" PICTURE PERFECT YOU DON'T NEED NO FILTER
GEORGEOUS MAKE EM DROP DEAD YU'RE A KILLER
SHOWER YOU WITH ALL MY ATTENTION , YEAH THESE ARE MY ONLY INTENTIONS
STAY IN THE KITCHEN COOKING UP GOT YOUR OWN BREAD , HEART FULL OF EQUITY YOU'RE AN ASSET
MAKE SURE THAT YOU DON'T NEED NO MENTIONS , YEAH THESE ARE MY ONLY INTENTIONS "
ya na gama fadar haka ya yi shiru ya na kallon Vedad
yar karamar dariya Vedad ya yi kafin ya ce " Your voice look like Daddy's voice , specially when you sing "
cikin sanyin Hayat ta ce mishi " ni fa ban san abun da ku ke cewa ! "
yar karamar dariya Vedad da Iqbal su ka yi a tare , sun ma manta da turanci su ke magana
" sister , sai na koya miki turanci Gaskiya " Iqbal ya fada da hausa
dan karamin murmushi Hayat ta yi kafin ta ce " Duk da ban san abun da ka ke cewa ba , Muryar ka na da dadin sauraro idan ka na waka "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " Da gaske ki ke ? "
a hankali ta gyada mishi kai ta na fadin " amma kai da gaske mawakin ne ko ? "
wani cool murmushi Iqbal ya saki kafin ya girgiza mata kai ya ce " no , amma ya na daya da ga cikin abubuwan da su ke burge ni a rayuwa , kuma na rubuta wokoki na kaina har guda biyu , bari watarana zan rera miki su ki ji , Kafin nan zan koya miki turanci dan ki gane su "
da sauri Vedad ya katse shi da cewa " amma ni kuma idan na ce ka min sai ka ki yarda " ya kai karshen cikin shagwaba
yar karamar dariya Iqbal ya yi kafin ya ce " Don't worry My Cutie pie , zan yi maka very soon , bari ina yin order din Guitar online kafin mu koma US zan yi maka "
wani kyawatencen murmushi Vedad ya saki ya na juyawa ya kali Hayat
โชNIHAL ๐ฅ
zaune ta ke saman sofa , Ummi na geffen Junior kuma ya na Fuskantar su , duk su na rike da wayoyin su su na latsawa har Nihal
su na a haka Ash ya shigo parlourn babu ko sallama ya nufi Stair
a tare duk su ka dago kai jin takun mutum
da sauri Nihal ta tseda shi da cewa " Ash , come here please "
cak ya tsaya dai'dai ya daga kafa zai taka Stair na Farko
Slowly ya janye kafar shi ya juya ya kali Nihal
wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Ash , dawo ka zauna please ! "
" Mummy yi maganar ki don Allah , Sauri na ke "
" okay , za ka iya tafiya idan ka samu lokaci mun yi maganar "
bai ce mata komai ba ya juya ya Haye Stair
har ya kai tsakiyar Stair din ya ce ma Junior " Marshal , come with me " ya fada dai'dai lokacin da ya ida Hayewa Stair din
ba musu Junior ya tashi ya Haye Stair din ya bi bayan Ash
ya na ida Hayewa Ita ma Ummi ta mike ta ce wa Nihal " mummy ina zuwa "
da ga haka ita ma ta nufi stair ta Haye
Ash kuma kai tsaye part din shi ya nufa
ya na isa ya zauna a parlour saman sofa ya fido wayar shi ya fara latsawa
ya na a haka Junior ya shigo parlourn ya na sallama ya nufi sofar da Ash ke zaune ya zauna shi ma ya na kallon Ash ya ce " Ya ? ka kamo su ne ? ko kuma mun yi batan kai ? "
ba tare da ya dago kai ba ya ce " No ! " a takaice
cikin rudu Junior ya tambaye shi " ya kuma a ka yi ka dawo kai kadai ? "
dan jinkirtawa Ash ya yi kafin ya ce " She is die "
" Die ! How ? When ? wanene ya kashe ta "
ajiye wayar shi Ash ya yi kafin ya juya ya kali junior ya ce " i don't know too , but duk wanda ya kashe ta ya kamata mu gano inda ya ke "
" Wait , ta a ka yi ta mutu ma tukunna , ka ga gawar ta ne ? "
a hankali Ash ya girgiza mishi kai kafin ya ce " babu wanda ya ga gawar ta saboda gidan ta baki daya su ka kona da ita a ciki , amma kuma mota biyu na gani cikin gidan kenan ba ita kadai ba ce akwai wani a tare da ita a lokacin "
" Yanzu shikenan hanyar da ta rage mana mun rasa ta ? "
" no ba mu rasa ta ba , yanzu dai mu fara kama wanda ya kashe ta , ta hanyar shi ne kadai za mu iya gano inda kungiyar ta ke "
" okay , yanzu bari na duba CCTV din unguwar may be mu samu wani abu a kai " ya kai karshen ya na shirin tashi
cikin nitsuwa Ash ya tseda shi da cewa " ko ka duba ba za ka komai ba , saboda tun jiya a ka kashe ta "
slowly Junior ya koma ya zauna ya na tunanin wani abu
kamar da ga saman su ka jiyo Muryar Ummi ta na fadin " ni na san wadda ya kashe ta "
a tare Ash da junior su ka juya su ka kali Kofar dakin
ta na tsaye ta na kallon su , tun farkon maganar su ashe ta na nan Tsaye ta na sauraron su
a hankali ta karaso cikin dakin ta zauna saman sofa one seater ta na kallon Ash ta ce " General ina ga Matar da ku ke neman Hayat ta kashe ta "
" who is Hayat ? " Ash ya fada
cikin nitsuwa Ummi ta shiga ba shi labarin da Hayat ta ba su tun da ga Farko har kona gidan Hajiya da ta yi
ba ta kai ga rufe bakin ta ba ta ga Ash ya ce mata ta kiro mishi yarinyar ya na son ya mata wasu tambayoyi
ba musu Ummi ta tashi ta bar dakin
ta na fita Ash ya mike shi ma ya shiga bedroom din shi
After some minutes
bai wuce five minutes ba Ummi ta dawo cikin dakin ta na rike da hannun Hayat
sai ta ga Junior ne kadai zaune cikin parlourn
" where is General " Ummi ta tambayeshi
ba tare da ya ce komai ba ya nuna mata bedroom din Ash
ta na rike da hannun Hayat ta nufi bedroom din ta tura kofar ta shiga ta na sallama
sai dai babu Ash a ciki , Ita dai Hayat da ido kawai ta ke bin Ummi , da bedroom din dan tun da ta ke a duniya ba ta taba shigowa irin wannan Bedroom ba
su na a haka Ash ya fito da ga cikin dressing kai a sunkuye ya na latsa wayar shi , ya karaso gaban gadon ya zauna
ya na zama ba tare da ya dago kai ba ya ce " Ko za ki iya kawo min Fruits "
da to Ummi ta amsa mishi kafin ta saki hannun Hayat ta juya ta fice ba tare da ta kawo komai a ran ta ba
shi kuma ya na lure da ita har ta fice part din baki daya , sannan ya tashi a hankali ya raba ta geffen Hayat ya nufi door ta zata fita zai yi sai ta ga ya tura kofar ya rufe ta , ya juyo slowly ya dago kai
" Inallillahi " ta fada cikin zuciyar dan ba karamin razana ta yi ba ganin wadanan sexy blue eyes din na shi
a hankali ya tako ya tsaya gaban ta cikin sanyin murya ya ce mata " who are you ? "
cike da tsoro ta ce mishi " ba na jin turanci " ta fada Muryar ta har kerma ta ke yi
a hankali ya lumshe idanun shi kafin ya sake bude su slowly
cikin zafin nama ya kai hannu ya damko wuyan ta ya shake ta ya na cewa " kar ki raina min hankali , su wanene su ka turo ki , kin zo ki kashe ni nima ko "
wata razananiyar kara ce Hayat ta saki tare da kuka lokacin guda
murya a shake ta ke cewa " ni ban san abun da ka ke cewa ba "
wata gigitaciyar tsawa ya daka mata ya na cewa " shut up ! kar ki kuskura ki sake bude min wannan bakin naki , me ki ke yi a cikin gidan nan " ya fada da hausa wannan karan
a hankali ta bude baki za ta yi magana ta kassa fitowa saboda shakar da ya yi mata
a hankali ya fara ganin idanun ta sun koma jazir ta na lumshe su a hankali
dan karamin tsaki ya ja kafin ya sake ta
nan take ta sulale a kassa sumamiya
MY BOOK IS ONLY โฆ300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753
TAแฆRIN ZแฆCIYA ๐๐บ๐
( RETแฆRN )
(๏ผฒ๏ผฏ๏ผญ๏ผก๏ผฎ๏ผด๏ผฉ๏ผฃ ๏ผฌ๏ผต๏ผถ ๏ผณ๏ผด๏ผฏ๏ผฒ๏ผน )๐๐ฅ
โค๐ ๊ช๊ช๊ชถ๊ชถ๊ชฦแปแญข แฉ๊ชนแปแญขแจถ๊ซเฐเฐ ๊ช๊ซ๊ซ๊ชน๊ช๊ซ ๐โค
๐๐
Wattpad : @bennybite
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks ๐๐
ุงููููููู
ูู ุตูููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุตููููููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูุ ุงููููููู
ูู ุจูุงุฑููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุจูุงุฑูููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏู๏ธ
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
๐๐๐๐๐๐
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
๏ผด๏ผก๏ผฐ ๏ผด๏ผจ๏ผฉ๏ผณ ๏ผฌ๏ผฉ๏ผฎ๏ผซ ๏ผด๏ผฏ ๏ผช๏ผฏ๏ผฉ๏ผฎ ๏ผญ๏ผน ๏ผท๏ผจ๏ผก๏ผด๏ผณ๏ผก๏ผฐ๏ผฐ ๏ผง๏ผฒ๏ผฏ๏ผต๏ผฐ ๏ผฃ๏ผฏ๏ผญ๏ผญ๏ผฅ๏ผด๏ผณ ๏ผณ๏ผฅ๏ผฃ๏ผด๏ผฉ๏ผฏ๏ผฎ
๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
๐ง๐๐ฃ ๐ง๐๐๐ฆ ๐๐๐๐ ๐ง๐ข ๐๐ข๐๐ก ๐ ๐ฌ ๐ฃ๐ข๐ฆ๐ง๐๐ก๐ ๐ฅ๐ข๐ข๐
๐๐๐๐๐๐๐
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
_________________โฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆโฆ__________________
PAGE ............14.........โค๐ฅ
bakin gadon ya nufa ya zauna ya fara latsa wayar shi
bai fi two minutes da zama ba , Ummi ta turo kofar dakin ta shigo ta na sallama ta na rike da tray din Fruits
ta na ganin Hayat a kassa , ta zaro idanu ta na kiran sunan ta da karfi ta nufi table din gaban Sofa ta ajiye tray din hannun ta
ta dawo wajen Hayat ta Zube saman guyiwowin ta ta talabo kan ta ta na kiran sunan ta
amma shiru Hayat ba ta motsa ba
" Ash me ya same ta " ta tambayi Ash ta na dago kai ta kaleshi
sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce mata " i don't know , kawai tambayar ta na yi , sai na ga ta fadi "
kare mishi kallo da kyau Ummi ta yi kafin ta ce mishi " Ash tell me the truth "
ba tare da ya dago kai ba ya ce mata " karya zan miki ne , please ni fidda min ita da ga cikin daki "
ba ta ce mishi komai ba ta tashi ta fito parlour nan ta tardo Junior ko motsi bai yi ba da ga wajen shi
" please Marshal ko za ka iya dauko Hayat ka kai ta bedroom di na " ta fada mishi cikin sanyin murya
" why ? me ya same ta ne ? " ya fada
dan lumshe idanun ta ta yi a hankali kafin ta ce " please ka je ka dauko ta kawai "
ba musu ya tashi ya nufi bedroom din Ash , ya na shiga ya ga Hayat konce kamar gawa
bai tsaya bin ta kan Ash ba ya tsuguna ya sa hannu ya dauki Hayat cak kamar baby , ya juya ya fice bedroom din
a haka ya fito part din dauke da Hayat Ummi na biye da bayan shi su ka sauko stair
Nihal na ganin Junior dauke da Hayat ta mike ta na fadin " junior me ya same ta kuma ? "
da sauri Ummi ta ce mata " kar ki damu mummy ina ga tsorata ta yi da ganin Ash " ta fada dan ta san abun da dan uwan ta ya aikata , sarai ta ga shatin hannun shi saman wuyan ta amma ta kyale shi
sai da ta raka junior har bedroom din Hayat , ya kontar da ita saman bed din ta sannan su ka juyo a tare su ka baro part din su ka dawo parlour su ka zauna saman sofa guda
su na zama Vedad ya ce ma Ummi " Big Sister , me ya same ta wai ? "
dan karamin murmushi Ummi ta yi kafin ta ce " nothing my angel "
da sauri Nihal ta katse ta da cewa " ki fadi gaskia dai , na san halin ki ba ki son abun da ya taba dan uwan ki "
yar dariya Ummi ta yi kafin ta ce " Really mummy ba abun da ya same ta "
" ni fa mummy ina ga Big bro ya fada soyayyar yarinyar nan " Iqbal ya fada cikin zolaya ya na yar karamar dariya
dariya sosai junior ya yi kafin ya ce " wanene ? General da soyayya ? Kam ai duk wadda ta bude baki ta ce ta na son General sai ta mutu lokacin ta bai yi ba , wannan mai Taurin zuciyar bai san minene so ba "
hararrar shi Ummi ta yi kafin ta ce " Junior kar fa ya jiyo ka "
da sauri Junior ya kumshe dariyar shi , dan ya san indai Ash ya jiyo abun da ya ce yau sai ya kwana a word room
" Mummy ni fa akwai wani abu da ban gane ba har yanzu ! " Iqbal ya fada ya na kallon Nihal
daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " minene abun kuma ? "
" mummy why big bro ya ki duba Hayat jiya , ki na gani har da A box ya taho amma kuma ya ce ba zai iya duba ta ba bayan kuma har ya sauko , in da ba shi da niyar duba ta da ba zai sauko ba "
gyara zaman shi Junior ya yi kafin ya ce " ka sani ko , wlh ni ma wannan abun ya tsaya min a rai , ban taba ganin Razana a cikin idanun General ba sai a lokacin "
kallon shi Ummi ta yi kafin ta ce " Ban gane ba kenan sai da ya gan ta sannan ya ce ba zai duba ta ba ? "
a tare junior da Iqbal su ka gyada mata kai allamun eh
shiru ta yi ba ta ce komai ba , ita sai yanzu ta tuno a ranar dai'dai ta fito da ga cikin part din ta , ta ji zuciyar ta ta buga da karfi har sai da ta tsaya ta na karanto kalmar shahada ta rasa dalilin haka , kenan zuciyar Ash ce ta buga da karfi haka
ta yi nisa cikin tunanin ta ta jiyo Muryar Iqbal ya na fadin " May be shi ma love at first sight ne ya ji "
a tare shi da junior su ka bushe da dariya
hannu Nihal ta kai ta buge Iqbal dama geffen ta ya ke
juya wa ya yi ya kali Nihal ya ce " mummy why za ki bugu na , ni fa gaskiya ce na fada "
" Mummy , Iqbal fa ya yi gaskiya , ita fa soyayya ba ka san lokacin da ta ke kama ka ba , ko ni haka na ji lokacin da na kamu da soyayya " Junior ya fada ya na yar karamar dariya
yar karamar dariya Nihal ta yi kafin ta ce " Ku dai ku na son takurawa Ash , me ya yi muku ? "
Ummi na shirin magana Vedad ya riga ta cewa " uhm uhm ni ku yi shiru don Allah kun hana ni kallon film di na " ya fada cike da shagwaba
yar karamar dariya Iqbal ya yi kafin ya ce " Cutie Pie , Daddy once said ? "
" Mummyn ku wayo ta ke min wlh " Vedad ya fada ya na dariya
dariya Nihal ta yi kafin ta ce " Yanzu tsakani da Allah ni da Daddyn ku , wa ke yi wa wani wayo ? "
" Gaskiya mummy ke ki ke