Showing 45001 words to 48000 words out of 72572 words
hannun shi saman bedside drawer ya dauki wayar shi sannan ya ce " a binciken da na yi , da sunnan aiki a ke kai yaran nan US , da na bi didigin wanda ke kai su US nan na gano cewa akwai wani seat na kungiyar a nan cikin kaduna "
da karfi Junior ya ce " what , da gaske ? yanzu ka samo inda seat din ya ke , ta yadda za mu kai musu hari cikin duhu "
shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba
shi ma dai junior shiru ya yi bai ce komai ba , ya san Ash ba ya son a na maimaita mishi tambaya , shi ya sa ya yi shiru har lokacin da ya ga dama ya ba shi amsa
sai da ya dauki lokaci kafin Ash ya bude baki a hankali ya ce " Je ka kawo min fruits "
yar karamar dariya Junior ya yi kafin ya ce " ashe dai General ba ya supporting yunwa " ya na gama fadar haka ya tashi ya fice dakin
โชHAYAT ๐ฆ
Misalin karfe 8 cib ta farka da ga barcin ta , ko da ta farka ta shiga ta yi wanka , ta meda gown din ta , da hijab din ta fari sannan ta fito dakin ko lotion ba ta shafa ba
ta na shigowa parlourn ta ji gaban ta ya yi wata mumunar faduwa
amma haka ta ci gaba da takowa ta karaso ta na sallama
a tare Hajiyah da wannan mutun su ka amsa mata sallamar ta
sai washe baki ya ki cikin zuciyar shi ya na fadin " an ya zan iya kai musu yarinyar nan haka kawai , ya kamata na dan taba gaskiya "
ya yi nisa cikin tunanin shi ya jiyo Muryar Hajiyah ta na fadin " Ta na gaishe ka ba ka ji ba ? "
a razane ya dawo cikin hayacin shi ya na fadin " eh eh , yawwa sannun ki yarinya "
dan sunkuyar da kai Hayat ta yi cikin zuciyar kuma ta na tsara shirin da ta yi musu
a haka Hajiyah ta ce mata " Hayat wannan abokin aiki na ne , yau din nan ya dawo da ga Dubaรฏ "
a hankali Hayat ta dago kai ta mishi kallon kassan ido murya cen kassa kassa ta ce mishi " sannu da zuwa , "
wani cool murmushi ya saki ya na gyada kan shi kafin ya kali Hajiyah ya ce " Ina kuma ki ka samu kyakyawar yarinya haka , a sani na dai yaron ki guda "
yar karamar dariya Hajiyah ta yi kafin ta ce " ษiyar din wata abokiya ta ce wlh "
a dubu dari Hayat ta dago kai ta na kallon Hajiyah ta na zaro idanu cikin zuciyar ta ta na fadin " ku ji shegiyar mata yaushe na zama ษiyar abokiyar ki kuma "
ta na a haka ta jiyo Muryar mutumin nan ya na fadin " oh ki ce hutu a ka zo miki , ya yi kyau gaskia , sannu fa daughter "
a hankali Hayat ta meda kan ta ta sunkuyar cikin zuciyar ta kuma ta na fadin " munafiki kai ka san minene Dauda din da ka ke cewa "
ganin ba ta ce komai ba ya sa mutuman nan cewa " Hajiyah yarinyar ta ki fa akwai ta da kunya , shikenan , yau dai ina da aiki sosai wlh da ga nan ma Abuja na yi , amma in sha Allah jibi zan dawo mu tafi shan ice cream "
kamar Hajiyah ba ta san da maganar ba kawai sai ta ce " kar ka wahalar da kan ka , na san aikin ka ba ka samun isashen lokacin ka , dan haka mun yahe maka "
" no kar ki damu ai ba wata matsala ba ce , jibi ina dawowa da ga Abuja sai mu tafi har shopping ma sai mu wuce ko ba haka ba daughter na " ya kai karshen ya na kallon face din Hayat
[29/12 ร 11:23] ๐ชท๐ฉท: MY BOOK IS ONLY โฆ300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753
โค๐ MALLAKIN MEERAH ๐โค
ุงููููููู
ูู ุตูููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุตููููููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูุ ุงููููููู
ูู ุจูุงุฑููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุจูุงุฑูููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูโค๏ธ
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
PAGE ............10.........โค๐ฅ
a hankali Hayat ta gyada mishi kai ba tare da ta dago ba
murmushi mai dan sauti Hajiyah ta yi kafin ta ce " to shikenan Allah ya kai mu jibin "
" hmmm , ai ku da ga nan sai lahira , gobe ma ba za ku gan ta ba " Hayat ta fada cikin zuciyar ta
ta na gama fadar haka ta mike tsaye ba tare da ta ce komai ba ta nufi hanyar dining room
da sauri Hajiyah ta ce mata " Hayat ina kuma za ki je "
a hankali Hayat ta juyo ta saki wani cool murmushi ta ce " Ruwa ne zan sha "
da to kawai Hajiyah ta amsa mata , ita kuma Hayat ta juya ta ci gaba da tafiyar ta ta shige kitchen
ta na shiga ta fara bin wajen da kallo , a hankali ta fara takawa kamar barauniya , ta dinga bude duk closet din kitchen din , a hankali da allamun akwai abun da ta ke nema
ta bude wajen closet uku kafin ta saki wani kyawatencen murmushi ta kai hannu ta dauki kwalin match din da ta gani
da sauri ta juya bayan ta , ta na kallo kar a je Hajiyah ta taho , amma sai ta ga ba kowa
da sauri ta ci gaba da bude sauran closet din har sai da bude su duka ba ta samu abun da ta ke so ba , kamar za ta yi kuka
cen ta hango wani dan karamin Space tsakanin fridge da wani closet
a hankali ta karaso wajen ta na rokon Allah ya sa ta samu abun da ta ke nema
ai ko cikin sa'a tun kafin ta duba idanun ta su ka hango mata wani Jug fari , da wani abu cikin me color blue
da sauri ta karaso wajen ta dauki Jug din , ta daura saman closet ta sa hannu ta bude murfin da sauri sauri ta kai hancin ta ta shinshina
da sauri ta janye ta na sakin wani cool murmushi , tabass gasoline ne
( To fa me ta ke shirin yi da Essence har da ashana ๐ค๐ค )
ko rufe bidon ba ta yi ba ta dauke shi ta nufi door ta baya ta fice kitchen din ta fito bayan gidan
ta na fitowa ta fara zazzaga gasoline din a wajen , ta na tafiya ya na zuba kamar igiya , haka har ta karaso wajen motocin Hajiyah da ta mutumin nan
su ma sai da ta dan watsa musu kadan , sannan ta nufi hanyar fita gidan
dai'dai ko ta kawo bakin kofar gasoline din ya ida
ta na ganin ya ida ta tila bido din gefe
ta riko kwallin ashanar nan ta bude ta ciro guda , ta fara gyasta wa amma ta ki kamawa , har ta yadda ta , ta ciro wata ita ma ta ki kamawa
kamar za ta yi kuka ta ce " haba don Allah kar ki yi min haka " ta kai karshen ta na yadda ta hannun ta ta ciro uku lokaci guda
kamar da ga sama ta jiyo Muryar mutumin nan ya na fadin " ke , ke me ki ke yi haka ? " ya fada da dan karfi ,ya na fara takawa ya nufe ta , dan ya karaso bakin kofar parlourn zai fito ya jiyo warin gasoline din
a dubu dari Hayat ta shiga gyasta ashanar nan , har kuka ya kubce mata
cikin sa'a ko , ko taku uku na kirki bai yi ba ashanar nan ta kama
wani cool murmushi Hayat ta saki hawaye na zubo mata , ta tila Ashanar nan saman Gasoline din da ta zuba
nan take ko ya kama da wuta , ya bi hanyar da ta zuba shi har saman motocin nan
ta na ganin ya kama ta juya da gudu ta bude kofar gidan ta fice , ta janyo kofar ta rufe ta ta baya ta na fadin " Allah ya isa la'anannu , mazinata kawai , ku kone baki daya " ta fada da karfi ta na barin wajen da gudu ko hanjar da za ta bi ba ta sani ba ita kawai ta tafi
shi dai mutumin nan ya kassa motsi wutar duk ta zagaye hanyar fita gidan
da gudu Hajiyah ta fito ta na fadin " Lafiya me ke faruwa "
cike da bacin rai mutumin nan ya ce " ban sani ba , ba ki da idanu ne , yarinyar nan da ki ka kawo ita ce ta saka wa gidan wuta kuma ta gudu "
da gudu Hajiyah ta nufi kofar fita gidan , sai dai ina wutar har ta yi karfi ta mamaye ko ina , ga kuma Hayat ta rufe kofar gidan ta baya , babu yadda za a yi su tsira , sai dai na ce Allah ya cece ku dan gaskia ba ku da hanyar tsira a nan , ga gidan kuma da motoci har biyu , su ma sun kama da wuta , ga kuma gas a kitchen , to fa
โชNIHAL ๐ฅ
Tafiyar su su ke yi cikin konciyar hankali saman hanyar , har yanzu ba su yi kwana ko guda ba
a hankali Iqbal ya dan juyo da kan shi ya kali Nihal ya ce " mummy wai har yanzu ba za mu yi kwana ba ? "
yar karamar dariya Nihal ta yi kafin ta ce " To , ni ma ban sani ba , kun san fa yanzu shekara 30 rabo na da kaduna ka san ba komai zai tsaye a yadda na bar shi ba "
da sauri Vedad ya juyo ya na fadin " mummy ba dai ba ki san hanya ba , kar mu bace fa " ya kai karshen kamar zai yi kuka
girgiza mishi kai Nihal tayi ta na fadin " no ba za mu bace ba , mu da mu ke da Ash , ko mun bace zai samo mu , bare ma ba za mu bace ba , Iqbal yi kwanar cen ta biyu "
gyada mata kai ya yi ya na fadin " to mummy Allah dai ya sa ba bacewa mu ka yi ba "
yar karamar dariya Nihal ta yi , dai'dai lokacin da su ka yi kwanar
ba shiri Iqbal ya ja wani wawan burki samakon mutumin da ya buge , har sai kan Vedad ya bugu a gaban motar
a razane Nihal ta ke kallon Iqbal ta ce " Iqbal lafiya za ka yi irin wannan burki "
sai zaro idanu Iqbal ya ke yi a rude ya ke fadin " mummy mutun na buge , wlh ban gan ta ba , kawai sai ganin na yi ta fada saman motar mummy wlh ban gan ta ba " ya kai karshen kamar zai yi kuka
" inallillahi " Nihal ta fada da dan karfi ta na zame belt din ta ta bude kofar motar ta sauko da gudu ta nufi Hayat da ke konce wanwar gaban motar
ta bugu sosai a kai har jini ta ke zubar wa
a rude Nihal ta Zube saman guyiwowin ta gaban Hayat ta na ฦare mata kallo
dago kai ta yi ta kali Iqbal ta ce " sauko ka sa ta cikin mota , mu tafi gida Ummi ta duba ta "
a dubu dari Iqbal ya sauko da ga cikin motar ya nufi Hayat da ke konce a kassa ya sa hannayan shi duka biyu ya dauke ta cak , sannan ya juya ya nufi motar
da sauri Nihal ta sha gaban shi ta bude mishi gidan baya , ya kontar da ita a ciki sannan Nihal ta rufe kofar ta zagayo daya geffen ta bude ta shiga , shi kuma Iqbal ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya juya su ka kama hanyar komawa gida
a hankali Nihal ta sa hannu ta janyo Hayat ta kontar da kan ta saman cinyar ta ta na kallon face din ta
" mummy i'm so sorry wlh ban gan ta ba , ni ban ma san da ga ina ta fado ba " Iqbal ya fada kamar zai yi kuka
mika hannun ta ta yi ta dafa shoulder din shi cikin sigar rarrashi ta ce " don't worry , ba abun da zai faru "
ta na gama rufe bakin ta Vedad ya ce " mummy duba kar a je ta mutu "
" no kar ka damu , ba ta mutu ba kawai ta dan ji rauni ne a kai "
kallon dawo da kallon shi kan Iqbal ya ce " kar ka damu big bro punishment kawai zai ba ka , ba zai sa a rufe ka ba "
wata muguwar hararra ta kassan ido Iqbal ya wurga ma Vedad , ya na neman ya saka shi cikin wata sabuwar matsalar
Nihal kuwa a hankali ta sa hannu ta zare mata dan karamin hijab din ta , ta daura a wajen da ke zubar da jini , ta toshe
da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har su ka iso gida
ko da su ka shiga gidan ba nufi parking space ba , kai tsaye bakin kofar parlourn ya nufa da motar ya yi parking din ta
sannan ya bude kofar shi zai sauka ya ce ma Vedad " yi sauri je ka kira Ummi ta fito " ya na gama fadar haka ya sauko da ga cikin motar
shi ma Vedad sauka ya yi da ga cikin motar ya nufi cikin gidan da gudu
Iqbal kuwa ya bude gidan baya ya sa hannayan shi duka biyu ya dauko Hayat ya nufi cikin gidan
ita ma Nihal saukowa ta yi ta bi bayan shi da sauri ta su ka shiga cikin gidan
su na shiga ya kontar da Hayat saman Sofa three seaters
sannan ya koma gefe ya tsaya ya na kallon ta
Nihal na shirin magana , Vedad ya fito da gudu da ga cikin corridor ya na fadin " mummy , Ummi ta na cikin wanka "
dafe kan ta Nihal ta yi ta na zama saman sofa ta na fadin " Wayoooooo ni Allah , yanzu ya za mu yi , kar ta zubar da jini dayawa , mu je ta samu matsala "
shi dai Iqbal tsaye ya yi ya na kallon Hayat
Nihal na Kamala maganar ta , ta ga Iqbal ya juya da gudu ya nufi stair ya Haye ,
ya na Hayewa ko Junior ya fito da ga cikin dining room ya na rike da tray din fruits
ya na ganin Hayat ya ajiye tray din hannun shi saman dining table din ya nufi parlourn da sauri ya na fadin " mummy me ya faru ne "
cikin ko in kula Vedad ya ce " ba Iqbal ba ne ya buge ta da mota "
shiru Junior ya yi ya na kallon Hayat ba tare da ya ce komai ba , Nihal dai ta na dafe da kai ta lumshe idanun ta
bangaran Iqbal kuwa ya na Hayewa stair ya nufi part din Ash kai tsaye
tun da ga parlourn shi ya fara kwalla mishi kira har sai da ya shigo cikin bedroom din babu ko sallama
tun kiran farko da ya yi Ash ya ji shi amma bai yi ko motsi ba , ya na nan zaune yadda junior ya bar shi ya na rike da wayar shi
da sauri Iqbal ya karaso gaban shi ya na fadin " Big bro don Allah taso mu tafi "
cikin nitsuwa Ash ya ajiye wayar shi saman bedside drawer ya dago kai ya kali Iqbal ya ce " What happening ? "
" Vedad ya je kiran Ummi ta shiga wanka , kuma ta na zubar da jini dayawa , please tashi mu tafi ka duba ta " Iqbal ya fada duk ya bi ya rude
" okay calm down your mind , Fada min me ke faruwa "
a hankali Iqbal ya ja wani dogon nunfashi ya na saukewa kafin ya ce " mun fita ne tare da mummy da Vedad , shi ne na zo zan yin kwana na buge wata yarinya , kuma ta ji ciwo a kan ta , yanzu haka ta na parlour ta na zubar jini sosai , shi ne Vedad ya je kiran Ummi amma ta shiga wanka , mu je ka duba ta please " ya kai karshen ya na marairaice fuska
a hankali Ash ya kai hannu ya bude box din bedside drawer ya dauki A box sannan ya mike , cike da nitsuwa ya fara takawar shi kamar ba ran mutun ne ba ke cikin hatsari , ya fice dakin Iqbal na biye da bayan shi
a haka su ka sauko stair su ka karaso cikin parlourn
Nihal na ganin shi ta mike ta na fadin " yawwa Ash don Allah duba mana ita har yanzu ba ta farka ba " ta kai karshen ta na nuna mishi Hayat
da sauri Vedad da Junior su ka koma geffen su ka ba shi waje
a hankali ya karaso ya ajiye A box din hannun shi saman table sannan ya juya ya kali Hayat ta na shirin Dauke mata Hijabin da Nihal ta daure a kai
har ya mika hannun shi ya tsaya cak ya na kallon face din ta
wata irin muguwar Faduwa Gaban shi ya yi