Showing 33001 words to 36000 words out of 72572 words
▪HAYAT 💦
Misalin karfe 3 na yamma motar su ta shigo Garin kaduna wani ikon Allah kuma cikin unguwar da su Nihal su ka sauka , Hayat har ta yi barci cikin motar
ta na tsaka da barcin ta ta jiyo Muryar matar nan ta na fadin " Daughter sauko mun iso "
a razane Hayat ta farka ta na fadin " eh eh "
yar karamar dariya matar nan ta yi ta na fadin " ke cewa na yi mun iso sauko "
sai a lokacin da dawo cikin hayacin ta , ta sauko da ga cikin motar a hankali ta fara bin gidan da kallo
gida ne mai girma gaskiya dai'dai mutun biyu da ga gani ita kadai ce cikin gidan nan dan ko ina a rufe ya ke
" mu tafi ko " Matar nan ta fada ta na yin gaba
da sauri Hayat ta bi bayan matar nan su ka nufi door din da za ta sada ka da parlourn gidan
su na isowa matar nan ta bude bag din ta ta fido keys ta saka cikin kofar ta bude ta tura ta, ta na yin sallama
wasu yawu Hayat ta hadiye kafin ta daga kafa ta bi bayan matar nan su ka shiga cikin parlourn , sai dai duk duhu ne cak ta tsaya waje guda zuciyar ta na duka uku uku
ta na a haka ta ga wajen ya É—auki haske har sai da ta dan lumshe idanun ta , ta na bude su a hankali
parlourn ya na da dan Girma komai na cikin shi Milk colour ne , an kawata shi da wasu Royal sofa Milk colour ma su ratsin Gold sun yi bala'in kyau
idan ka shigo a geffen dama akwai wata yar dining room me dauke da wata Dining table fara kal mai chair shidda, sai wata yar door a bayan su allamun ta kitchen ce
geffen Dama kuma Stair ne da ga kassan shi akwai wasu door guda uku allamun bedroom ne
ta yi nisa cikin tunanin ta , ta jiyo Muryar matar nan ta na fadin " Shigo ki zauna mana " ta kai karshen ta na nufar Dining room ta shiga kitchen
fara bin wajen da kallo Hayat ta yi kafin ta tako a hankali ta karaso cikin parlourn ta zauna a kassa saman tiles ta na rungume da buhun kayan ta
fitowa matar nan ta yi da ga dining room ta na rike da tray dauke da Glass biyu da gorar ruwa biyu ta dawo cikin parlourn ta ajiye saman table sannan ta zauna saman sofa three seaters ta na murmushi ta ce " haba daughter tashi ki hau sofa mana kin zauna a kassa "
ba musu Hayat ta taso da ga wajen da ta ke , ta karaso wajen wata sofar maimakon ta zauna saman ta sai ta zauna a kassa
murmushi mai dan sauti matar nan ta yi ba tare da ta ce komai ba , ta bude gorar ruwa guda ta zuba mata ruwan cikin glass din biyu sannan ta dauki gudan ta mikawa Hayat ta na yi mata bismillah
girgiza mata kai Hayat ta yi ba tare da ta ce komai ba
" kar ki ji tsoro ki saki jikin ki , kin ji ko ? "
a hankali Hayat ta taso ta mika hannun ta ta karbi glass din ruwan ta koma inda ta taso ta na fadin " na gode "
murmushi kadan matar nan ta yi ta na fadin " never mind , Na san za ki so ki san ko ni wacece "
a hankali Hayat ta gyada mata kai allamun e
dan jinkirtawa matar nan ta yi kafin ta ce " Suna na Hajiyah Basira , amma za ki iya kira na da Hajiyah , Ni kadai na ke zaune cikin gidan nan sai yaro na da ke zuwa a kai a kai , miji na ya rasu da jimawa , ina safarar kaya da ga kassashe daban daban , ko yanzu wani aiki ne ya kai ni Kano har na hadu da ke "
shiru Hayat ta yi ba ta ce komai ita dai kallon matar nan kawai ta ke yi
" Sha ruwan ki mana , da ga nan sai ki tashi ki shiga daki ki yi wanka ki cire kayan nan sai ki konta ki huta , kar ki damu mai aiki na ta na kan hanya an jima za ta zo "
da to kawai ta Amsa mata sannan ta kai glass din hannun ta a baki ta sha ruwan kadan sannan ta tashi ta mayar da shi saman tray din
mikewa tsaye matar nan ta yi ta na fadin " taso mu je ki yi wanka " ta kai karshen ta na juyawa
da sauri Hayat ta mike ta dauki dan kumshin kayan ta , ta bi bayan matar nan su ka nufi daya da ga cikin door din kassan stair ta bude ta shiga ta na yi wa Hayat bismillah
da sallama a bakin ta ta shigo dakin ta na bin shi da kallo
daki ne dai'dai mutun daya , komai na cikin shi da ga white sai brown colours
nuna mata wata door matar ta yi ta na fadin " shiga ga toilet nan ki yi wanka yanzu ina kawo miki kayan sakawa "
ta na gama fadar haka ta juya ta fice bedroom din ta bar Hayat nan tsaye
a hankali Hayat ta karaso cikin dakin ta ajiye kumshin kayan ta saman gadon sannan ta nufi toilet , ta shiga ta janyo kofar ta rufe
tsaya wa kawai ta yi ta na bin wajen da kallo , cen ta hango wasu bucket biyu cike da ruwa kassan wani dan Fanfo
a hankali ta fara cire kayan jikin ta , sannan ta nufi wadanan bucket din
Bayan wasu mintina ta fito da ga cikin toilet din ta na daure da towel a kirjin ta , amma towel din ba wani mai girma ba ne , wadanan santala santalan cinyoyin na ta su na a waje
gaskia ta wanku sai yau ta yi wankan kirki , har wani Haske ta kara , Color din skin din ta Chocolate ya fito paro paro gwanin burgewa
ta na fitowa ta ga wata Gown Pink color saman bed din dakin da wani dan karamin hijab fari geffen ta
a hankali ta karaso gaban gadon ta kai hannu ta dauki Gown din , nan ta ga pant da bra ajiye a kassan ta
sai da ta ƙare wa gown din kallo da kyau sannan ya ajiye ta , ta dauki pant din nan da bra ta saka
sannan ta saka Gown din , kamar an dai'dai ta da ita , ta zauna ma ta cip cip a jiki , breast din ta da hips din ta sun fito gwanin burgewa
ta na shirin daukar hijab din Hajiyah ta shigo ta na sallama ta na rike da wani perfume
a hankali Hayat ta dago kai ta na amsa mata sallamar ta kassa kassa
cak matar nan ta tsaya ta na ƙare wa Hayat kallo cikin zuciyar ta ta na fadin " Masha Allah , Allahuma barik , Dole na gyara yarinyar nan ba kananan kudade zan samu a kan wannan kyawon na ta ba "
wani cool murmushi ta yi kafin ta karaso cikin dakin ta na fadin " wacece wanan kuma ina Hayat ta yi "
dan karamin murmushi Hayat ta yi ta na sunkuyar da kai wai ita ta ji kunya
dariya sosai Hajiyah ta yi , sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " wai kunya ta ki ka ji , Shikenan ga perfume ki Feshe jikin ki da shi , sannan ki fito ki ci abinci na san ki na jin yunwa " ta na gama fadar haka ta ajiye perfume din saman bedside drawer sannan ta juya ta fice
ta na fita Hayat ta dauki karamin hijab din nan ta saka sannan ta dauki perfume ta feshe jikin ta da shi
maimakon ta fita sai ta nufi dressing mirror a hankali , ta tsaya ta na kallon kan ta
ba ta san lokacin da ta saki wani cool murmushi , ita da kan ta sai da ta ji ta burge kan ta ba karamin kyau ta yi ba , kamar ba yar Ƙauyen nan ba
a hankali ta juyo ta nufi kofar dakin ta fice , ta fito parlourn nan ta isko Hajiyah zaune saman sofa ita da wani kyakyawan saurayi , kamanin su daya da Hajiyah sai dai ta fi shi haske saboda bliching
karaso wa cikin parlourn Hayat ta yi ta na sallama cen kassan makoshi
slowly saurayin nan ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta a ra'rabe
ita Hayat ba ta ma san ya na yi ba ta karaso cikin parlourn ta zauna saman carpet ta na sunkuyar da kai
sai bin ta da kallo saurayin nan ya ke yi har sai da ta zauna sannan ya janye idanun shi ya kali Hajiyah ya ce " Hajiyah wacece wanan kuma ? "
wani dan karamin murmushi Hajiyah ta yi ta na fadin " she's my guest yarinyar wata friend's di ta ce "
gyada kan shi kadan sauran yin nan ya yi kafin ya kali Hayat ya ce " what's your name " ya fada da turanci
shiru Hayat ta yi ba ta dago kan ta ba allamun ba ta ji abun da ya ce ba
" ohhhh Ba ta jin turanci kai ma " ta fada dan ta san da wuya ne a ce ta na jin turanci dan ba ta yi kama da yaran da ke zuwa school ba
kallon Hayat ta yi sannan ta ce " Hayat ! "
a hankali Hayat ta dago kai ta na amsa mata da " na'am "
nuna mata saurayin nan Hajiyah ta yi ta na fadin " Hayat wannan shi ne yaro na Razak , ki gaishe da yayan ki mana "
gyada mata kai Hayat ta yi kafin ta juya ta kali Razak murya kassa kassa ta ce mishi " ina wuni ? "
murmushi ya yi ya na fadin " lafiya lau , ya ki ke ? "
" Lafiya " ta fada a takaice ta na sunkuyar da kan ta
kallon Hajiyah ya yi cikin harshen turanci ya ce " Hajiyah ba za ki neman min auren ta ba gaskiya ta konta min a rai "
hararrar wassa Hajiyah ta yi mishi ta na fadin " ba na son shirme da ga ganin yarinya sai ka ce ta kon ta ma ka a rai ? to tun wuri ka cire ta , nan gani nan bari "
marairaice fuska ya yi ya na fadin " please Mum , why za ki yi min haka , ni gaskiya ina son ta "
wani mugun kallo ta wurga mishi cikin zuciyar ta ta na fadin " ka ga dan iskan yaro ka na neman ka bata min shiri "
cen kuma sai ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " shikenan zan yi magana da mamar ta , in ba a fitar mata da miji ba "
wani kyawatencen murmushi Razak ya saki kafin ya ce " yawwa mummy na shi ya sa na ke mugun son ki "
murmushi kadai Hajiyah ta yi ba tare da ce komai ba
ita dai Hayat kamar babu ita a wajen , ga shi da turanci su ka yi maganar su ita kuma ba jin turanci ta ke yi ba
su na a haka wata yarinya ta fito da ga cikin Kitchen ta na rike da wani tray dauke da wani plate rufe da wani plate din
bakin ta da sallama ta shigo parlourn
sai da Hajiyah ta amsa mata sallamar ta sannan ta ce " ajiye mata " ta kai karshen ta na nuna Hayat
ba musu yarinyar nan ta ajiye tray din gaban Hayat sannan ta mike ta komawar ta kitchen
ta na barin wajen Hajiyah ta ce ma Hayat " bude ki ci mana , na san ki na jin yunwa "
gyada mata kai kawai Hayat ta yi kafin ta kai hannu ta bude plate din , ta sa hannu har za ta fara ci Hajiyah ta tsaida ta da cewa " a'a dauki spoon mana "
a hankali Hayat ta gyada mata kai sannan ta kai hannu ta dauki spoon din da ke geffen plate din , a haka dai ta ka'kama duk da ba ta taba cin abincin da spoon ba amma sai da ta cinye jollof rice din nan tasss , sannan ta kora da ruwa , dama yunwa ta ke ji
su dai Hajiyah da razak kallon ta kawai su ke yi su na murmushi har sai da ta gama sannan ta dauki tray din ta mike tsaye
da sauri Hajiyah ta taro ta ta na fadin " zauna war ki , za ta dawo ta dauke shi "
girgiza mata kai Hayat ta yi ta na fadin " zan kai mata "
da to kawai Hajiyah ta amsa mata , da ga haka ta juya ta na rike da tray din ta nufi dining room
bakin ta dauke da sallama ta shigo kitchen din
nan ta isko yarinyar nan tsaye gaban gas cooker , slowly ta juyo ta na amsa mata sallamar ta
" ina zan ajiye " Hayat ta fada cen kassa kassa
wani desk yarinyar nan ta nuna mata ba tare da ta ce komai ba
desk din Hayat ta nufa ta ajiye tray din sannan ta karaso geffen yarinyar nan ta tsaya ta na fadin " minene sunan ki ? "
dan karamin murmushi yarinyar nan ta saki kafin ta ce " duk cikin yaran da Hajiyah ke kawowa gidan nan ke ce ta farko da ki ka yi min wannan tambayar , suna na Fatima "
" kennan bayan ni akwai yaran da su ka sha zuwa gidan nan " Hayat ta fada cike da mamaki dan Hajiyah ta fada mata ita kadai ce a gidan bayan yaron ta ba me zuwa
gyada mata kai Fatima ta yi ta na fadin " eh mana , ki na nufin ba aiki za ta samo miki ba "
girgiza mata kai Hayat ta yi kafin ta ce " a'a kawai mun hadu da ita saman hanya shi ne ta kawo ni gidan ta "
wani murmushi mai dan sauti Fatima ta yi kafin ta ce " ban cika shiga cikin harkar da ba tawa ba , amma da zan ba ki shawara tun wuri ki bar gidan nan , kafin ki yi nadamar shigowa cikin shi "
cike da rudu Hayat ta tambaye ta " me ki ke nufi ? "
dan karamin murmushin geffen fuska Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da aikin ta
ita dai Hayat ta rasa me ta ke nufi da maganar ta , jin yadda ta yi shiru ba ta amsa mata ba kawai sai ta juya ta bar wajen ta fice kitchen din
bayan ta fito kitchen din kai tsaye ta dawo parlour , har za ta wuce bedroom din ta , ta jiyo Muryar Razak ya na fadin " Sister ba za ki zo mu yi sallama ba , tafiya zan yi "
cak ta tsaya ta juyo a hankali ta dawo cikin parlourn ta zuba mishi ido ta kassa cewa komai
daga mata gera guda ya yi allamun minene
girgiza mishi kai ta yi murya kassa kassa ta ce " Allah kiyaye hanya "
ta na gama fadar haka ta juya da sauri sauri ta koma bedroom din da ta fito
da ido ya raka ta har sai da ta shiga dakin ya na kallon bayan ta ,ya na lashe lips
sai da ta shiga dakin sannan ya mike tsaye ya na fadin " Mum ni zan tafi may be nan da two days na dawo "
mikewa tsaye ita ma Hajiyah ta yi ta na fadin " Okay , Allah ya kiyaye hanya Baby na , sai ka dawo "
sai da ya kai bakin kofar sannan ya juyo a hankali ya ce " please mum kar ki manta magana ta " ya fada kamar zai yi kuka
gyada mishi kai ta yi ta na fadin " shikenan Baby na , zan fada mata , sai ka dawo "
ta na gama fadar haka ya sa kai ya fice gidan
da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta ce " Gaskiya sai dai ka yi hakuri , amma ba zan aura maka yarinyar nan ba , akwai shiri na musaman da na yi a kan ta , wannan kyawon na ta ba kananan kudade zai kawo min ba "
ta na gama fadar haka wayar ta da ke saman table , ta fara ringing
hannu ta kai ta dauki wayar ta na kallon screen din
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Alhajin Allah , yanzu ko na ke shirin kiran ka ! "
shiru ta yi ta na sauraron abun da mutuman ke fada dan ni ba na iya jiyo abun da ya ke cewa
shiru ta yi na dan lokaci kafin ta saki wata shegiyar dariya ta na fadin " Alhaji Alhaji , ban jima da dawowa ba , yanzu haka ina gida kai kadai ne ke jira , ka zo Aljihu cike dan na yi sabon kamu yau "
yanzu ma dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " shikenan sai ka Zo Alhaji na " ta kai karshen ta na yar karamar dariya kafin ta sauke wayar da ga kunne ta katse kiran ta tashi ta Haye stair
â–ªZINDER ( KAUYEN NAWACH KALE )
â–ªBARIRA
misalin karfe 8 na dare
zaune su ke cikin harabar