Showing 51001 words to 54000 words out of 72572 words
sa'a , a dawo lafiya " inna ta fada cikin sanyin murya
da Amine ya amsa mata kafin ya fara takawa ya fice gidan
sai da ya fita ita ma ta tashi ta nufi dakin da Barira ta shiga ta na fadin " ya Allah ka tsare mana Hayat duk inda ta ke " ta kai karshen ta na shiga dakin
▪KADUNA ( GIDAN SU NIHAL )
▪MISALIN KARFE 8 NA DARE
▪HAYAT 💦
A hankali ta fara kokarin bude idanun ta , ta na bude su sai saman ceiling
shiru ta yi ba ta motsa ba kallon ceiling kawai ta ke yi ta na kifta idanun ta a hankali
sai da ta dauki wajen good ten minutes a haka kafin ta mike zaune a hankali
da sauri ta kai hannu ta dafe kan ta na fadin " wayooo Allah kai na " dan ba karamar sara mata ya yi ba
nan ta ji Bandejin da ke a le wajen , a hankali ta sauko da hannun ta , ta fara bin dakin da kallo
sam bai mata kama da gidan Hajiyah ba , wannan ya yi biyun dakin da ta sauka a gidan Hajiyah
a hankali ta matso bakin gadon ta sauko da kafafun kassa sannan ta mike tsaye
ba shiri ta koma ta zauna , dan jikin ta ba kwari sam
amma a haka ta aro duk jarumtar ta , ta mike tsaye ta nufi kofar fita dakin
ta kai hannu ta kama handle din kofar ta jayo ta sa kafa ta fice dakin , ta fito cikin corridor din
sai da ta kali damar ta , ta kali hagu sannan ta yi damar ta dan nan wajen ya fi haske sosai
a haka ta biyo corridor din nan ta na tafe ta na dafe da bango , a haka har ta fito corridor din
duk mutanan gidan ko su na nan Banda Ash da Junior , Vedad na faman zuba musu shagwaba , su kuma su na biye mishi su na dariya
ita dai Hayat tsaya wa ta yi ta zuba musu ido ta kassa cewa komai
su na a haka kawai Iqbal ya juyo ya kali wajen corridor din , kawai sai ya gan ta tsaye
su na yin ido hudu da shi , ta baya kadan ta na sunkuyar da kai
dan karamin murmushi ya yi kafin ya kali Nihal ya ce " Mummy "
dawo da kallon ta ta yi gare shi ta na fadin lafiya
da kai ya mata allamun ta kali corridor
a hankali ta juya da kan ta , ta na murmushi
nan ta ga Hayat tsaye ta na dafe da bango ta sunkuyar da kai
kara fadada murmushin ta Nihal ta yi kafin ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi Hayat
a tare Vedad da Ummi su ka juya su ka kali Hayat
wani dan karamin murmushi Ummi ta yi ta na fadin " Har kin tashi ? "
( kar fa ku manta fa duk maganar nan da su ke yi da turanci su ke yin ta "
Hayat kuma ta na tsaye sai ji ta yi an kamo hannun ta
sai da ta razana ta dan ja da baya
" calm down ba abun da zan yi miki , mu je ko ? " Nihal ta fada ta na janyo Hayat
ba musu ta biyo bayan Nihal ta na tafiya a hankali kai a sunkuye
har sai da su ka karaso sofar da Nihal ta ke zaune , ta zauna sannan ta zaunar da Hayat geffen ta
ta dago kai ta kali Iqbal ta ce " Je ka ce ma chef ya shirya mata jollof Rice , na san ba za ta iya cin abincin mu ba , sannan ka kawo mata fruits "
da to Iqbal ya amsa mata kafin ya tashi ya nufi dining room ya shiga kitchen
ya na barin wajen Nihal ta kai hannu ta dago habar Hayat ta na murmushi ta ce " Sannu ya jikin na ki "
shiru Hayat ta yi ta zuba mata idanu , ita fa sam ba ta gane abun da ta ke fada
ganin yadda ta yi shiru ta tsare ta da idanu ya sa Nihal gane cewar ba ta jin turanci
da hausa ta ce mata " Sannu ya jikin na ki "
a hankali Hayat ta gyada mata kai
murmushi mai dan sauti Nihal ta yi kafin ta ce " bude baki ki yi magana ba cinye ki zan yi ba , ya sunan ki "
Nihal na gama rufe bakin ta Ummi ta matso bakin sofar da ta ke zaune , da ya ke duk cikin su babu wanda bai iya hausa ba , kawai dai ba su son yin magana da ita ne , sun saba sosai da Turanci saboda shi ne a ke yi a US
cikin wani kwarbaban harshen hausar ta ta ce " sannu ya jikin na ki , kan ki ba ya miki ciwo "
a hankali Hayat ta gyada mata kai allamun eh , dai'dai lokacin da Iqbal ya fito da ga cikin dining room ya na rike da tray shake da Fruits
kai tsaye saman table ya ajiye shi sannan ya matsa table din gaban sofar su Nihal shi ma ya koma dayan geffen Hayat , da harshen turanci ya ce mata " Hi ! ya jikin na ki ba ki dai ji ciwo ba sosai , ko akwai wani wajen da ke yi miki ciwo "
sai da ya Kamala maganar shi sannan Ummi ta ce mishi " ba ta jin turanci yi mata da hausa "
" okay , san...nu ya jikin na ke " Iqbal ya fada a rarabe allamun bai gware da yin magana da hausa ba
ita dai Hayat da ido kawai ta ke bin su ta kassa cewa komai zuciyar ta sai duka uku uku ta ke yi ta na rokon Allah ya sa ba irin su Hajiyah ne ba
a hankali Nihal ta kai hannu ta dauki barin Apple guda ta kai bakin Hayat ta na fadin " bude baki "
ba musu Hayat ta bude baki a hankali Nihal ta saka mata Apple din nan
Vedad na ganin haka ya saki dan karamin kukan shagwaba har da bubuga kafafun shi a kassa
da sauri duk mutanan wajen su ka kale shi , har Iqbal da Ummi su na hada baki su na tambayar shi lafya
cike da shagwaba ya ke musu " Why mummy za ta ba ta a baki , ni wlh ba na so "
dan karamin murmushi Nihal ta yi sannan ta ce " Haba my angel ba ka ga ba ta da lafiya ne "
" uhm uhm ni ki daina ba ta a baki ta sa hannun ta , ni kadai za ki dinga ba wa a baki , ni na ma tafi na fadawa big bro " Vedad ya fada ya na turo dan bakin nan na shi kafin ya tashi ya nufi stair ya Haye
da kallo duka su ka raka shi har sai da ya Haye sannan Nihal da Ummi su ka yi yar karamar dariya Nihal ta kai hannu ta dauki wani Apple din ta kai wa Hayat a baki ta na fadin " rabu da shi ci abin ki , Ba ki dai jin wani ciwon a jikin ki ? "
a hankali Hayat ta gyada mata kai allamun eh
Iqbal da ke bayan ta ne ya ce " Ki saki jikin ki kin ji , ba abun da zai faru da ke "
cike da zolaya Ummi ta ce " ko dan kin gan mu jajaye ba mu yi kama da Hausawa ba " ta kai karshen ta na daga mata gera guda
yar karamar dariya Hayat ta yi murya kassa kassa ta ce " Haske ne kawai gare ku amma da ga gani an san jinin hausawa ne ku "
" Ashe dai ba kurma ba ce " Iqbal ya fada ya na yar dariya
dariya ita ma Nihal ta yi kafin ta ce " Kai ya isa haka , ku bar ta , ta sha fruits din ta da ga baya kun yi magana "
Shiru su ka yi ba wanda ya sake cewa komai su na kallon Hayat
sannu sannu har ta fara sakin jiki ta na karbar Fruits din da Nihal ke ba ta
su na a haka daya da ga cikin Chef ya fito da ga dining room ya na rike da tray dauke da wani plate an rufe shi da wani , da glass biyu daya na ruwa daya na juice
a haka ya karaso cikin parlourn ya ajiye tray din saman table gaban Su Nihal sannan ya juya ya koma inda ya fito
ya na barin wajen Nihal ta kai hannu ta bude plate din
shake ya ke da jollof rice ta sha vegetable da fried chicken sai tashin kamshi ta ke har yawu na sai da ya tsinke kamar na kai hannu na debo
a hankali Nihal ta kai hannu ta dauko plate din ta dauki Spoon ta debo ta kai bakin Hayat ta na fadin ta bude baki
ba musu Hayat ta bude baki ta karba , dama ta na daura ido saman abincin ya shiga ran ta , sannu sannu har ta zame ta ci abinci har sai da ta ciye duka
sai da ta cinye sannan Nihal ta ajiye Plate din saman tray sannan ta dauki glass din ruwa ta kai mata a baki ba musu ta bude baki ta shanye ruwan tass sannan ta sauko da glass din
ajiye shi saman tray Nihal ta yi sannan ta dauki na juice ta mika mata ta na fadin " yanzu tun da cikin ya cika an samu bakin magana ko ? "
a hankali Hayat ta gyada mata kai ta na wani dan karamin murmushi
ita ma Nihal murmushi ta yi kafin ta kali Iqbal ta ce "Iqbal meda tray din nan kitchen "
da okay ya amsa mata kafin ya tashi ya dauki tray din biyu duka ya kai dining room ya ajiye saman dining table sannan ya yi wa door din kitchen knocking guda sannan ya juya ya dawo parlour ya zauna geffen Ummi
ya na zama Nihal ta kali Hayat ta ce mata " yanzu fada min ya sunan ki kuma da ga ina kike "
Dan sunkuyar da kai Hayat ta yi sannan ta ce mata " suna na Hayat , ni yar kassar Nijer ce , da ga kauyen NAWACH KALÉ da ke a zinder " da ga haka ta shiga ba su labarin abun da ya faru tun zancen auren ta da Rabeh yadda a ka yi ta tsere har ta shigo kano da hadu da Hajiyah ta kawo ta kaduna har zancen da su ka yi na sayar da ita har kona gidan da ta yi duk ba ta boye musu har lokacin da ta fado gaban motar Su
sumar zaune duk mutanan wajen su ka yi , yanzu da iya shekarun nan na ta har za ta iya kashe mutun
" ki yi hakuri , amma fa nan gidan sojawa ne ki ka fado , dole mu hukun ta ki , kin yi kokarin kashe har mutun biyu , wa ya sani yanzu ko sun mutu , bari ma na kira yan sanda su fido mota mu tafi da ke " Iqbal ya fada cike da zolaya
A razane Hayat ta saki glass din hannun ta ya fadi kassa nan take idanun ta su ka kawo ruwa ta shiga girgiza mishi kai ta na fadin " a'a don Allah ku yi hakuri ni babu inda zan je , ba zan je gidan yari ba , don Allah kar ku kira yan sanda " ta kai karshen kuka na kubce mata
da sauri Nihal ta rungumota ta na fadin " kontar da hankalin ki wassa ya ke miki , da ga nan gidan ku za ki koma , babu inda za ki je kin ji ko ? "
Bushewa da dariya Iqbal ya yi har da dafe ciki
hannu Ummi ta kai ta buge shi ta na fadin " ka ji dadi ko , ka saka ta kuka "
cikin dariyar ta shi ya ce " shikenan , i'm sorry wassa ne fa na ke mata " ya na gama fadar haka ya taso ya tsaya gaban Hayat ya dan sunkuyar da kai ya na fadin " Yi hakuri kin ji wassa na ke miki " ya na gama fadar haka ya nufi stair ya Haye ya na ci gaba da dariyar shi
MY BOOK IS ONLY ₦300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
KU TURA SHAIDAR BIYAN TA WANNAN NUMBER
+22795577612 or +22798999753
TAღRIN ZღCIYA 💖🌺💍
( RETღRN )
(ROMANTIC LUV STORY )💋🔥
❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ᩏꪹỉ᭢ᨶꫀకక ꪑꫀꫀꪹꪖꫝ 👑❤
🕊💞
Wattpad : @bennybite
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )
FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION
👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb
DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK
👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠
👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________
PAGE ............12.........❤🥂
sai da ya Haye stair sannan Nihal ta dago Hayat da ga jikin ta ta ce mata " yi hakuri kin ji ko ? babu inda za ki je , Ummi ! tashi ki kai ta bedroom din ta , ki gwada mata yadda za ta yi aiki da toilet , ta yi wanka , na san cikin kayan ki ba za a rasa kanana ba , ki ba ta ta saka , yanzu ina yi mata online shopping , da ta samu sauki mu maida ta gidan su "
da to Ummi ta amsa mata kafin ta mike ta riko hannun Hayat ta mikar da ita tsaye sannan su ka nufi corridor su ka shiga part din Ummi
ta shiga da ita dayan bedroom , su ka wuce toilet ta gwada mata yadda abubuwan su ke aiki , sannan ta cika mata bath da ruwa sannan ta fice toilet din ta bar bedroom din ta shiga na ta
▪NIHAL 🥀
Ummi ta na barin wajen Vedad ya sauko da ga stair a hankali ya na kuka kamar baby
Da kallo Nihal ta rako shi har sai da ya karaso cikin parlourn ya nufi sofar ta ya Haye ya konta ya tada kan shi da cinyar ta
a hankali ta daura hannun ta kan shi ta fara shafa wannan lalawsan gashin kan shi ta na fadin " wa ya taba min my angel , ba dai Iqbal ya buge ka "
cikin kukan na shi ya ce " Mummy big bro ne , tun dazu da na hau bedroom din shi ta na rufe na yi ta jiran shi har kiran shi na dinga yi amma ya kyale ni "
" oh ni Nihal ! " ta fada cikin zuciyar ta a fili kuma ta ce " haba my angel , may be ya yi kwana , yanzu tashi ka taya ni yi wa Hayat online shopping "
a hankali ya dago kan shi ya na mikewa zaune kamar ba shi ne ba yanzu ke kuka ya ce " amma mummy ni zan zabar mata duka "
dan karamin murmushi Nihal ta yi ta na fadin " shikenan yadda ka ke so haka za a yi " ta kai karshen ta na daukar wayar ta da ke geffen ta saman sofar sannan su ka shiga yi wa Hayat online shopping , kayan da su ka saya mata ko wata amaryar ba za ta same su ba , kamar wadda a ke shirya wa kayan lefe , ba abun da ba su sayo mata ba har underwear da takalmi har da su sneakers duk aikin Vedad ne , duk abun da ya gani sai ya saya har kananan kaya bai bari ba
a takaice sai da su ka kashe wajen one million of dollars ba ma naira ba sai wajen karfe 10 na dare sannan su ka tashi , Vedad ya koma bedroom din shi , Nihal kuma ta nufi bedroom din ta ita ma
▪HAYAT 💦
Bayan Ummi ta fita toilet din ta rufe mata kofa , ta shiga yin wankan ta
cikin nitsuwa ta yi wankan ta , sannan ta dauro towel a kirjin ta ta fito Toilet din
Ta na fitowa ta ga wasu kananan kayan barci shanye saman gadon
a hankali ta nufi kayan ta kai hannu ta dauke su , ko underwear ba ta saka ba , ta saka kayan barcin sannan ta Haye saman gadon
ta na Hayewa Ummi ta turo kofar ta na sallama
a hankali Hayat ta juyo kan ta , ta kali kofar ta na amsa mata ta
karaso cikin dakin Ummi ta yi ta zauna bakin gado ta mikawa Hayat gorar ruwan da ke hannun ta
ba musu Hayat ta kai hannu ta karba
ta na karba Ummi ta mika mata wasu drugs a hannun ta ta na fadin " karba ki sha magani ne zai sa ciwon