Showing 33001 words to 36000 words out of 150731 words

Chapter 12 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

775

yarda da maganan yayan nasuba sunsan kawai fadi yake shi kanshi baisan irin son dayake ma Nurse bane yace "kai dalla bazaka dena dariyan ba malam" sauka yayi daga kan gadon yakai bakinshi saitin kunen Omari yana kallon Ya Marwan da wutsiyar ido yace "Ya Omari wlh mugun sonta yake fa shi kanshi bai saniba but kasan wani abu we will teach him" ta wutsiyar ido ya hango shi ya mike hakan yasa Abdallah yafita daga dakin da gudu yana dan daga murya yace "get dress fa kasa white shadda yayan mu angoo" goge hanci Omari yayi yana hadiye tashi dariyar yadan saci kallonshi yaga shi yake kallo ya juya yafita daga daki yana sosa kai yana murmushi, ahankali ya koma ya zauna ya daura kafa daya kan daya tareda lumshe ido yana ganin fuskarta wani irin abu na fizgar shi yadan sauke ajiyan zuciya tareda furta "am not in luv inaso na taimaketa ne kawai".


Abdallah da Kamal ne suka rufe fuska su sukaje suka taho da Abba daga dakin dayake a kulle suka fito dashi sukayo masallacin dashi sai bin mutane yake da kallo suka shigo dashi masallacin aka zazzauna, nan limamin dayake abokin baban kamal ya daura aure tsakanin Marwan Muhammad Sani da Nadeera Naseer Aluminum akan sadaki dubu dari biyu, inda baban kamal ya wakilci ango Marwan da baima zo masallacin ba, aka rufe daurin aure da salatin annabi, sai wani irin murna Abdallah da Omari suke, suka kara daukan Abba suka maidashi dakin dayake rike da kudin sadakin da aka bashi na Nadeera wanan karan basu kulleshi ba ajiyeshi kawai sukai akan kujera sai binsu kawai yake da kallo suka fice daga dakin suka rufomai kofa, Omari ne kawai yawuce sama Abdallah da Kamal sun tsaya wurin yan abokanen su da basufi uku dasuka gayyato ba. Ahankali Omari ya turo kofar dakin nashi yana waigen kofar dakin da Nadeera ke ciki, kafin ya juyo ya kalli Ya Marwan dake gaban study dinsu yana aiki da system, maida kofar yayi yarufe ya shigo ya tsaya abayanshi yana kallon abinda yakeyi da system yace "latest ango in town, an daura fa, you are officially a married man now" ahankali ya ture system din dayake aiki dashi ya dago kai yana kallon Abdallah kafin chan ya juyo saikuma ya kasa magana sabida wani irin farin ciki da baisan na meba ya lullube shi ya mayad da kanshi kan system din yacigaba da danne danne dan ya danne farin cikin daya rasa na mene, fizge system din Omari yayi yace "dalla chan computer man katashi kaje kaga matarka ko an daura, give her that kind kiss irin na forehead dinin, daurin aure kiss ka iya?" "kai! Ina wasa dakai? are you mad?" tashi yayi ya yunkuro zai kamoshi da sauri ya juya yafita daga dakin saikuma ya dawo da sauri ya bude kofan yadan leko da kanshi yana kallon shi yace "please kasa native kagadai yau daurin auren, and ur wife yakamata tasan.." kasa karasa maganan yayi yafice da sauri, yadade tsaye yana kallon kofan yarasa takaimaimai meyakeji shi kawai he's just happy ne, to kodai na yay aure ne? Ya tambayi kanshi, komawa yayi ya zauna kafin ahankali ya tashi yay gaban wardrobe din dakinsu dan yanada wasu kaya adakin, wani hadadden farin shadda ya dauko ya wuce bathroom, wani sabon wanka yasake yo wa ya shirya tsaf kafin yafito sai uban kamshi yakeyi cikin wani bakin hermes covershoe dake shining ya saka kafarshi dake cikin black sock, juyawa yayi yafita daga dakin yana kallon kofar dakin datake dake facing wanda yafito.

Yadade tsaye gaban dakin kafin ahankali yakai hanunshi jikin kofan yay knocking ya saukar da hanunshi kasa, jin shiru yasa yabude dakin ya shiga yana kallon gadon ganin bai ganta akaiba alamun ta tashi kenan, zama yayi kan kujeran dakin ya daura kafa daya kan daya yakai kusan 20min a zaune amma shiru bata fitoba hakan yasa ya mike da sauri ya bude kofar dazai sadashi data bathroom ya shiga tsayawa yayi a wurin batare daya bude kofar bathroom dinba jin yanda take kuka daga ciki, yakai kusan 1min tsaye yana sauraron yanda take kukan, kasa daurewa yayi yasa yasa hannu yabude kofar bayin ya shiga, a mugun firgice ta mike tsaye daga kan kujeran data zauna tana jan towel din data daura kasa dan tun dazu tagama wanka bayan ta tashi daga bacci tazo bayi dan kafarta tai sauki sosai shine taketa kuka Mum kawai takeson gani, wani irin rawa da jikinta yafara yasa tafara waige waige tana neman inda zata boye amma babu wani irin nishi tayi tana kuka sosai tana kallonshi yanda yay folding hannu a kirji yana kallonta, ahankali tadau doguwan bakin rigan data cire tanason ta warware tasa amma ta kasa tsabagen yanda hanunta ke rawa, rike doguwan rigan taji anyi ya karbe daga hanunta ahankali, kasa tai da idanunta tasa bayan hannu tana goge kwalla dake zubo wa jikinta na rawa, hanunta taji yarike batare dayay magana ba yajata hakan yasa tabishi luuuu tanadan dingishi kamshin dayake yi yana wani irin shiga hancinta, zaunar da ita yay akan gado ya tsaya akanta, kulle hanunta tayi a kirjinta tana kuka tana tsoron kar ya mata abinda Abba ke mata. "why are you crying now" dan dago kai tayi ta kalleshi kafin ta maida kanta kasa da sauri sabida yanda yawani irin cika mata ido, muryanta na rawa tace "n..ni..Mummy, uhn..ni wurin Mumy z..zan..zani pleaseee zan tafiii" takara she maganan tana sakin mai wani sabon kuka.


Please manage.
Gobe zan muku da shegen yawa in sha Allah
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *Idan kika karanta baki biyaba keda Allah*!!!



*Maman Abd Shakur*

*AH*

Da sauri suke tafiya har suka kai gida, wani dan daki dake nan kwara daya gaban part dinsu sukayi bude dakin sukayi suka shiga desktop guda biyu ne akan table da sauri Muhsin ya zagaya ya zauna akan kujeran roban wajen, Ya Ahmad ya zagayo ya tsaya ta bayanshi ya dafashi yana kallon system din, da keyboard ya Muhsin ya dinga operating computer sanu dawo da footage din baya har suka kai daidai inda Nadeera tafito daga barander dakinsu da gudu ya danna play tare da daura yatsunshi akan baki yana kallo kirjinshi na bugawa sosai, aguje tafito tanajan rigan baccin ta kasa tana kuka sosai tana kallon baya tana waigen baya tayo shashinsu, saiga Abba shima yafito aguje gaban rigan shi a mike da sauri Muhsin ya kawad da fuska zuciyarshi kaman ta tarwatse, sake juyo dakai yayi idanunshi sunyi mugun ja daidai takawo kofar dakinsu tanaso ta buga saiga Abba magana Abba yafara hakan yasa Muhsin yay pursing ya danna kara sanan ya komar dashi baya yay playing, Abba yana kawo wurin yace zai tsine mata inta buga kofan, har zai tsine saikuma tazo da sauri yawani jata yasa ajikinshi yana shafa mata baya, da sauri ya Muhsin yasake kawad dakai ya kai hannu ya goge kwallar daya zubomai yasake juyo dakai ya kalla daidai inda tafara tutturjewa Abba naso ya shiga da ita ciki kafin yasaketa yafara gyara hannun riga itakuma ta juya da gudu tana kuka tabude gate tafice Abba ma yabita da gudu saiga gateman yafito ya leko ya rufe gate din da kyau yakoma daki.
Sosai Muhsin ke goge hawayen dake zubo mai yama rasa mai zaice, ahankali ya mike tsaye ya kalli Ahmad da shima jikinshi yay wani irin sanyi kanshi ya kwance baima san mezaiyiba yajuya yafita daga dakin yabar Ahmad kadai a wurin a tsaye, fadawa kan kujeran Ahmad yayi ya wani irin zama kaman wanda akama mutuwa da sauri ya tura hannunshi cikin aljihun jallabiyar shi ya ciro wayarshi cikin kunan rai yay dailing number Mum, ringing uku ta dauka da dan dariya tace "Ahmadudu dont tell me kai mafarkina ne dan nasan yanzu naija kaman uku da hamsin ne ko na dare, ya kake my boy" cikin wani irin kunan rai yace "ki kira mijinki ki tambayeshi ina ya kai mana kanwar mu Mum" da sauri Mum tace "Ahmadudu wat is it? Me haka kake maganan baban ka kaman wani mate dinka, wat is going on?" akufule yace "Mum!" da sauri tace "Naam Ahmad dina menene?" "Nadeera ta bace ki shigo hanya kidawo gidan nan" da sauri Mum ta buga salati tace "innalillahi ta bace, garin yaya? How? Na shiga uku na lalace, Ahmad kun sanar da police? Ina Muhsin? Gashi wlh I have one last meeting to attend yau nai finalizing deal dina da burj al arab in sha Allah next tommorow zan dawo" akufule Ahmad yace "ki mutu achan ma mtsww" ya katse wayar tareda wurgar da wayan akasa ta tarwatse, yay wani ihu, wanan wani irin iyaye Allah ya bashi ne, Uwa business tasani tun suna yara nani ke kula dasu, tun basu sababa harsunzo sun saba ma da rashin ta, Uba kuma yanzu ya dawo dan iska, bama dole ya dawo haka ba, all Mum does is travel, business, business, ko Micheal Zuckerberg bazai nunama matarnan tafiye tafiyen business ba, meeting, meeting kaman itace ta hallici meeting a duniya, wani irin ihu yayi yace "i hate dem" fita yayi ya banko kofar ko takan shashin su baibi ba yawuce masallaci, anan ya zauna oo har akai asuba ana idarwa tareda Ya Muhsin da idanunshi sukai jajir suka dawo gida kaman an musu mutuwa inda ace Abba ba Abba bane ayanda zukeji zasu iya kasheshi, wanan ranan shine bakin rana a rayuwan su. Koda suka shigo Abba suka gani sanye da white jallabiyar yana magana da wani ma'aikacin gidan talabijin din AIT yana mika hoton Nadeera, wuce su sukayi batare da sun kalli uban nasu ba sukai shashin su, duk wanka sukayi suka shirya cikin suit bakake, ko wanan su jiyake kaman yamutu, suka fito tsakar gida lokacin gari yay haske sosai suka fito atare, Abba suka gani sanye da fararen shadda riga da wando ya rako Dr Bello dayazo duba shi rike da cikinshi yanadan murmushi, bin yaran nashi yay da kallo yanda sukai kyau sunci bakaken suit gwanin ban sha'awa, Muhsin yakafa bakar glass a ido, suka dumfaro wajen, wucesu sukayi batare da sun gaida Abban ko abokin nashiba kowanen su ya shiga motar shi suka danna wani uban horn mai gadi ya bude musu gate suka fita, bakaramin tsinkewa zuciyar Abba yayiba all he sees a fuskar yaranshi is tsantsar tsana dawani irin mugun hatred, sosai yaji he's heart broken dan yana mugun son yaranshi, he's 3 children are his life. Maganan Dr Bello ne yadawo dashi daga dogon tunanin dayaje yace "nabarka lpy Alhaji, please ka kula da kanka fa, banda yawan tunani karka sami hawan jini, sanan kasha magungunan sosai nan da kwana biyu cikin zai sakeka da izinin Allah" murmushin yake yayi yace "thank you Dr, agaida iyali" jan Motar Dr yayi yabar gidan, Abba yajuya yakoma cikin gida yana dan duka wa jikinshi yay sanyi sosai, akan kujera ya zauna yana dan kara ya jawo wayarshi daga kan table yay dailing number commissioner.




***
Afirgice ta farka daga baccin datake yi sakamakon wani irin haske bau dataji akan fuskarta tana kallon dakin cikin shirin yin kuka, yana tsaye jikin window ya yaye labulen dan ta farka, juyo da kai yayi ya kalleta yanda take kokarin tashi daga gadon jikinta na rawa amma takasa sabida kafarta dayay mata tsami sosai, ahankali yafara tafiya ya zagayo wajen ta gaban gadon, kulle idanunta tayi gam kirjinta nawani irin bugawa jin mutum akanta gawani irin kamshi dayake yi mai shegen dadi, daukanta da akayi yasa tasaki kukan datake ji sosai batare data bude idanunta ba jikinta narawa sosai, abayi ya zaunar da ita da sauri ta kifa kanta akan kafafunta tana kama jikinta, juyawa yayi yay wajen kofa yace "15 minutes nabaki, rana tafito u need to pray" yabude kofa yafice yarufo mata, saida taci kukanta ta koshi sanan ta dago kanta ahankali tana kallon inda ya ijiyeta kasan shower ne kaman jiya saita chan gefe kadan kuma babban leda ne da aka rubuta 24 hours super market ajiki ga towel sai toothbrush da toothpaste akai, da kyar ta cire jallabiyar jikinta tai wanka a zaunen tai brush kafin tai alwala, ta share jikinta tana kallon ledan, kaya ta gani ciki yasa tasake fashewa da kuka Mum kawai takeso tagani, wani doguwan riga data gani nasama baki mai stones taja tasaka aiko ya mata kyau ba kadan ba, bakin dan kwalin ta yafa akanta, ahankali ta dafa bango dantaga ko zata iya mikewa da sauri ta koma ta zauna dan kaman kafan ya balle sabida azaban dayake mata, knocking kofan akayi hakan yasa ta kara makurewa a zaunen, bude kofa yayi ya shigo yana tafiya wani irin nishi tayi tanaji kaman tai fitsari ajiki yanda yake tafiya ko ina na jikinta takeji gawani irin sanyi da takeji yana siga kasusuwan ta, daukanta taji kawai anyi hakan yasa tasake fashewa dawani kukan shikenan ita tadawo kaya adauka a ijiye, akan dadduma ya ijiyeta ga hijabi pink akai dake a linke yakoma kan dogon kujeran ya zauna yana danna agogon hanunshi, ahankali tadau hijabin ta saka, azaunen tai sallan ta idar ta daura kanta akan kafafunta, kaman daga sama taji saukan maganan shi. "hey! look up" yafada adake, da sauri ta dago kai takasa kallonshi, "look at me" kaman wata yarinya ta juyo dakai tana wani irin pikipiki da ido ta kalleshi tana sauke ajiyan zuciya ajejjere, yanda yaga tanayi yasa yadan sassauta murya yace "what's your name?" ahankali bakinta na rawa sosai tace "N..a...Nad..Nadeera" tai maganan tana goge kwallan daya zubo mata da bakin hijabin jikinta, innocent face dinta ya kafe da ido sanyi na ratsa jikinshi sosai, murya chan kasa yace "meke miki ciwo yanzu?" gwuiwanta ta nuna mai da yatsa, hakan yasa ya mike daga kan kujeran yazo inda take, wani irin kwalalo ido tayi kaman wacce za'a kashe kirjinta na bugawa tana kallon kafafun shi, hannunshi dake cikin safan hannu ya mika mata yace "give me d leg" wani irin rawa hanunta keyi tadan yaye doguwan rigan da hijabin tabashi kafar jikinta narawa sosai, karban kafan yay ahankali yadan ja rigan ta yanda gwuiwan yafito ya kalli yanda ya kumbura sai shining yake, ahankali yakai hannu zai taba da sauri ta rike hanunshi tana kuka sosai tana kallon gwuiwan cikin kuka tace "dan Allah ka barshi, zai warke ahaka am scareddd" sosai yake kallonta yanda take kukan wani irin abu na fizgarshi, jiyayi kaman butterfly namai yawo aciki, ahankali yace "leave my hand" da sauri ta sakeshi tana hawaye sosai, calmly yace "close your eyes" kulle idanunta tayi gam tana numfarfashi, itadai batasan meyama kafar ba amma wani irin azaba dataji lokaci daya takusa suma ihu tayi sosai tayi tana ture hanunshi da karfi cikin azaba tana kuka, saida yagama sanan ya saki kafar yana kallonta yanda take kukan dayakeji har ranshi, ahankali yace "waye wanan mutumin na jiya?" da sauri ta dago kai ta kalleshi saikuma ta dauke kai da sauri kirjinta na bugawa sosai tana goge hawayen datake yi. "who is he?" da sauri ta matsa baya dan yanda yay maganan kaman zai kasheta, data tonama Abba asiri awaje gwara taga yayyinta ko Mum tafada musu, akaro na uku yasake cewa "waye mutumin nan?" girgiza mai kai tai da sauri tana share kwalla, hannu yasa abayan wandonshi yaciro karaman bindiga, ihu tayi cikin kuka tana kallon bindigar cikin tsoro, saita mata bindigar yayi akai hakan yasa taja wani irin numfashi kaman zata suma tana kwalalo ido, cikin tsananin fushi yace "waye mutumin nan dat was trying to rape you?" a mugun tsorace tace "A..a..Abba na ne" da sauri yace "what? Abba? U mean Ur dad?" gyadamai kai tayi ahankali hawaye nabin kuncinta, ahankali ya maida bindigar bayan wandonshi ya dagata ya daurata kan gado, wani irin tsayuwa yayi agabanta ya daura kafa daya kan gadon yay folding hanunshi a kirji yace "Abban ki?" gyadamai kai tayi ahankali wasu hawaye masu ciwo na zubo mata. "and where is your Mum?" girgiza mai kai tayi tana kokarin hana kanta kuka, muryan ta na rawa sosai tace "bata nan" "ina taje?" yatambayeta da sauri, cikin sheshekan kuka tace "Dubai for business" wani irin fuzar da iska yayi kafin yasake daga kai ya kalleta yanda take kuka mara sauti yace "jiya yafara miki hakan?" dago jajayen idanunta tayi ta kallai saikuma ta girgixa mai kai alamun a'a hakan yasa yace "yaushe yafara?" sosai kuka yaci karfinta, shiru yayi yana kallonta zuciyarshi namai zafi da kyar tace "3days ago" wani irin ajiyan zuciya yayi murya chan kasa yace "yamiki wani abu d first time?" girgiza mai kai tasake yi tana goge kwallan datake yi tace "i ran na shiga toilet na kulle da key" sosai jikinshi yafara rawa hakan yasa ya janye kafarshi ya zauna yana facing dinta yace "kinada siblings?" gyadamai kai tayi tace "Ya Muhsin da Ya Ahmad" cikin fushi yace "to maisa baki fada musu ba?" fashewa tasakeyi da kuka sosai tana goge fuskarta da hijabi da kyar ta iya magana tsabagen yanda kuka yaci karfinta tace "yace zai yankani da wuka inna fada, and zai tsinemin" wani irin juya kanshi yayi with so much anger kafin yasake juyowa ya kalleta yace "ba a compound dinku brothers dinki ke zama ba?" gyadamai kai tayi tace "suna side dinsu, side dinmu is just me Abba and Mum muke a wurin" cikin tsananin kunan rai yace "inane gidan ku, wani anguwa kuke?" cikin kuka tace "Cresent Street no. 16" "ya sunan Abban ki?" batare data kawo komiba tace "Alhaji Naseer Aluminum" tashi yayi yafita daga dakin yana tafiya kaman zaki, saka kanta tai akafafu ta fashe da sabon kuka dan yasa ta sake tuna abubuwan da Abba yamata ne da ko kadan batason tunawa.


Yakai kusan 30min sanan ya shigo dakin dauke da tray kulan abinci da plates da spoon ga ledan magunguna agefe, tunda ya bude kofar fuskarta yake kallo yanda ta dukunkune tana bacci da hijabi ajikinta fuskarnan hawaye duksun bushe, gefen bakinta har yanzu da tabon ciwo wurin marin ne kawai ya sace, ajiye tray din yayi akan side drawer ya juya ya zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login