Showing 12001 words to 15000 words out of 150731 words

Chapter 5 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

766

karyane ni white belly ce, kuma ni kabani kudin break" hararan ta yayi yana son ya wuce yace "sabida kina tayani zuwa banki muna aikin tareko" hanunshi tarike tai kaman zatai kuka tace "ai wlh saika bani, accountant kun cika mako, naira daya dazaku bama mutum kun gwammace kuyi tunanin yanda zaku juyata ta koma miliyan, wlh saika bani ni" tai maganan harda bubbuga kafa akasa, tsaki yayi ya ciro wallet dinshi daga aljihu yabude gayan dubu daidai sai ya zaro wata naira dari biyu sabuwa ya mika mata yace "gashi beggy beggy" turo baki tayi dake kara mata kyau tace "eh naji dai inaso" sakin shi tayi ta mika hannu zata karbi kudin ya daga hanun sama, bin hanun tayi da kallo hakan yasa tai tsalle zata karba yakara dage hannun sama sosai, buga kafa tai akasa tace "kaga kabani kudina" "kai kajimin yarinya kudinki ko kudina? Oya gashinan ai yi tsalle ki karba, ai duk beggy beggy haka ake musu" hararan hanunshi tayi tasake yin tsalle zata chapko kudin yay dage kudin yay sama sosai juyawa tayi tadau after dress dinta kaman zatai kuka tace "banaso" tai hanyar fita da sauri yariketa yana dariya sosai yace "haba emmatan Mum, oya gashi" make kafada tayi taki juyowa tace "banaso" "yakuri to ga dubu daya" da sauri ta juyo tana murmushi, dubu dayan ya ciro daga wallet ya mika mata da sauri ta fizge dan azatonta zai kara kaiwa sama ne dariya yayi sosai yace "beggy beggy gashinan dai kinyi latti" dariya tayi tajuya tafita daga dakin da gudu ta shiga mota Adamu yaja suka tafi.



Suna kaiwa hospital din tafito ta wuce ciki da sauri dan tai latti, sosai gabanta ya fadi tunawa da jiya, ahankali ta daga kafa ta shiga ciki kaman wacce kwai yafashewa a ciki sai kallonta ake bata damuba tai kaman bata gansu ba, office din dasuke signing in tawuce, registrar dake zaune a wurin tace "sai yanzu kike zuwa" ahankali tace "am sorry Ma" attendance book din tabata hakan yasa ta karba tabude taje wajen sunanta tai signing karba matan tayi tana dubawa tace "okay kece Nadeera Naseer kenen?" gyadakai tayi tace "eh nice" "alright kije office din HOD tana nemanki, tace inkinzo ace kije" gyadakai tayi tajuya tafice kirjinta na bugawa sosai, students da medical personnel dake kaikawo sai kallonta suke dauke kai tayi tana tafiya hartakai office din, knocking office din HOD tayi aka bata iziznin shiga ta shiga, hadadden office ne dayaji komi, ga wasu uban award data cika gaban table dinta dasu,glasses din idonta ta gyara ta nunama ta kujera batare datai magana ba hakan yasa ta zauna, gama rubuce rubucenn datakeyi tayi ta matsar dasu gefe sanan ta fuskanci Nadeera da kirjinta ke bugawa sosai tace "Nadeera dudda tun jiya muka samu labarin da anyi bailing dinki but what am about to say must shock you" gyada kai tayi idanunta na farfar sabida hawayen dasuke shirin yi, dan bubbuga table din tayi da yatsun sanan tace "for now Nadeera you've been suspended till further notice" adan tsorace ta kalli HOD dan bata zaci irin punishment din daza'a bata kenan ba, tasan definitely za'a mata punishment and she came prepared but bata zaci suspending dinta za'ayi ba, bakinta har rawa yake sabida kuka dake neman kufce mata tace "a..am am sorry Ma please don't suspend me, i wasn't the one that injected that patient I've explained everything to the police yesterday please don't suspend me, wanan shine last practical dina daga shi sai 2nd semester which is my final semester, dan Allah dont suspend me Ma, please please" ta karshe maganan tana kuka, ajiyan zuciya HOD ta sauke tace "hakane the police man explained everything and yes za'ayi investigating case din further, but there's nothing i can do to help you my dear, order dinan daga sama yake ba daga niba, we have to set an example our reputation is at stake here, we will not allow or tolerate any negligence act dat will temper with patients that are under our supervision, our care, we are care givers tayaya zamuyi accepting wanan misconduct din? So my dear am sorry there's nothing i can do you, for now you've been suspended leave my office am going out" tai maganan tana nuna mata kofa, sosai take kuka da kyar ta mike tsaye tafice daga office din, ko takan neman fauzy batabi ba tawuce tafita tai gate din hospital din da sauri tana kuka, zama tayi akan wani dakali dake gefe taci kukanta sosai, gashi bata zuwa da waya balle takira su Abba tafada musu, da kyar ta lallashi kanta ta share hawayen ta, murmushi tayi tana goge kwallan dake zubowa tace "no Nadeera, no Nadeera don't cry" murmushi tayi irin murmushin nan mai ciwo tana girgixa kai hawaye na rolling tace "am..am not gonna cry, but this is unfair, wanan shine 3rd year danake tare dasu every semester saimunyi practical a hospital dinan basu sanni bane basusan mezan iya bane, why why why" da sauri ta goge hawayen daya zubo tace "no don't cry Nadeera lallashi kanki dama ance sai aski yazo gaban goshi yafi zafi sai yanzu dana kusa karake school dinne zasuyi suspending dina that's not fair now haaa" tafashe da wani kukan, after dress dinta tasa ta share fuskarta tana kuka da kyar tai shiru tana taking deep breath tace "today is a good day Mum zata dawo so i should be happy, be Happy Nadeera and chill, wanan is one phase of life that i must face, koma wanene dat set me up shida Allah, shida Allah" tai maganan tana goge kwalla da hanunta tana fifita fuskarta da hannu tana girgixa kai tace "i will not cry, i will not cry, chill okay, school of nursing ba shine karshen rayuwa ba, smile princess, smile" murmushi tayi saikuma ta mike ta cire jakarta ta ijiye kan dakalin after dress din tasaka ta goya jakan akai sanan tafara tafiya yan keke napep sai mata magana suke ko tafiya ne amma ta sharesu idanunta sunyi jajir hawaye ya ciccika su.


Tafiya ta dinga yi tana mikan titi iska na kadata, dudda gidansu da asibitin da nisa sosai bata damuba, daga kai tayi taga wani babban super market mai suna time & tide super market hakan yasa tai dan murmushi ta wuce ta shiga ciki, ahankali take tafiya a super market din dan bama tasan mezata siyaba kawai ta shigo ne kotadanji sanyi aranta, hakan yasa kawai ta cigaba da tafiya abinta tanabin cleaners din dake mopping tiles din kasan wurin da kallo inda suka ajiye caution sign da aka rubuta careful slippery floor ajiki, murmushi tayi tai bangaren book tana dubawa wani english novel mai suna "the noisy neighbor" ta dauka tana dan budewa ganin yamata yasa ta dauka tabude tana dubawa tana tafiya, zwiiiiiiiii!! taji santsin kasan ya kwasheta hakan yasa tai ihu tana kokarin hana kanta faduwa amma ina daidai lokacin kuma wani guy yataho rike da leda supermarket din dan yariga yabiya kudin abubuwan daya siya zaiyi kofa yafita, fadawa tayi kanshi dudda she tried her best not to hakan yasa shima yatafi zwiiii da ita a jikinshi wani irin ihu yasaki dayama fi nata yay kasa tana kanshi, ihu yayi sosai ledan hanunshi yay gefe ya zube akasa, kaman zaiyi kuka yace "wayyo Allah na kwankwasona Ya Marwan zata karyani" da sauri ta dagashi tana komawa gefenshi adan tsorace, security supermarket din yazo da sauri ya mikamai hannu cike da respect yanason dagashi yace "we are sorry Sir, we apologize for the inconvenience, we had an issue da cleaners dinmu ne saisa yau basuzo dawuri ba" ihu Abdallah yasake yi daga kwancen yace "please leave me dawanan long essay dakake karanto min, i can't feel my kwankwaso, wai wacece ma tafado kaina ne? wash Allah na Ya Marwan Ya Omari, kai duba kagani are you sure kwankwaso na nanan i can't feel it?" bilhakki yake ihun shi ga mutane duk antaru akanshi, ahankali ta mike tsaye tadau book dinta tana gyara zaman jakan bayanta ta tsaya akanshi tareda dan duko da kanta tana dan murmushi da idanunta dahar yanzu basu washeba tace "sorry santsi ne ya kwasheni" wani irin zakin murya daya ratsa mishi tundaga kunne har zuwa kwankwason dayake mai ciwo dayaji yasa ya bude ido ba shiri, murmushi ta sakin mai daya karamata wani irin kyau, lumshe ido yayi yasake budewa ya daurasu akansu, ahankali tace "to katashi nagani if u are fine kokuma akwai abinda zaisa namaka allura ne ko admission" tai maganan tana kara kallonshi, kaman wanda akama magani ya mike tsaye yanadan yatsine fuska yana kakkabe jeans din jikinshi, murmushi tayi tace "bama wani abu bane dazaran kaje gida kawai kai wanka da ruwan zafi zakaji bayan ya mike yadena" yatsine fuska yayi yace "this nurse kin kusa kasheni yau" hannu tamai waving tace "sorry" murmushi yayi yadau ledan shopping dinshi yace "am Abdallah and you?" da sauri ta juya tace "just call me nurse kaman yanda kace" binta yayi da kallo harta wuce, juyowa yayi ya kalli mutanen dake kallonshi ya daure fuska yace "lpy banason sa ido" watsewa sukayi hakan yasa yajuya yafita yana dan dingishi yay wajen parking motoci, bude kofan gaban wata bakar jeep yayi ya shiga ya zauna ya rufo kofan yana lumshe ido yana cije baki ya wurga ledan dayan kujeran yana nishi. "menene?" aka mai tambaya dawata irin husky voice, ahankali ya juyo da kanshi ya kalli Ya Marwan dake zaune abaya a owners sit yana danne danne a MacBook dake kan cinyarshi, kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan wata nurse ce zata karyamin bayana, d floor was wet so she slipped tafado kaina nima i slipped nafadi akasa na bugu sosai, kuma zafi wayyo Allah na" dan tsaki yayi awahale ya kalli yanda yake shafa bayan yace "sorry, lazy Nigeria youth" "kai dan Allah ya Marwan, dazafi fa" yay maganan a shagwabe, dago kai yayi dan yamai magana daidai lokacin security ya bude mata kofa tafito daga super market din rike da dan leda, ko numfashin kirki bai karayi ba yaji wani irin sanyi na shiga jikinshi, bin inda yake kallo Abdallah yayi da sauri yace "Ya Marwan kaga nurse din data bugenin chan tana fitow..." kasa karasa maganan yayi ganin yanda Marwan ke kallonta yana binta da kallo hartai titi ya juya ta baya yana lekata ta glass din wajejen booth.
[8/27, 7:10 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳



*Maman Abd Shakur*


1⃣0⃣

Laptop din dake kan cinyarshi ne yazo zai fadi tsabagen yanda yake juyawa yana kallonta da sauri Abdallah ya mika hannu ya dauke laptop din daga kan cinyarshi yace "Ya Marwan" dan juyowa yayi ya kalleshi kafin yakara juyawa yana kallonta tana tsaye akan titi kana ganinta kasan abin hawa take jira, dan sanyi jikin Abdallah yayi, asanyaye yace "itace yesterday nurse from St. Edward?" ahankali ya juyo ya kalli Abdallah, shima Abdallah kallonshi yake ganin ko alamun zai bashi amsa baiyiba yasa yay dan murmushi yabude kofa ya fita daga motan, kalle kallen kasan wajen ya shiga yi kaman mai neman abu, hango wani kusa yayi akasan nan kusa da motarsu kadan hakan yasa yay wurin da sauri saida yafara daga kai ya kalli titin, ganin har lokacin tana nan kan titi bata sami abin hawaba yasa ya cire takalmin kafar shi ya tsugunna ya juyar da kusan yataka nail din tareda runtse ido dan zafi saida tadan bula kafan sanan yay maza ya janye kafar data fara jini, jini na bulbulowa, zama yay akasan wajen ya kwala ihu. "wayyo Allah nurse, nurse" daidai lokacin ta tare wani keke napep tana shirin shiga bama tajishi ba hankalin ta yay nisa gida tana tunanin hala Mum ta dawo yanzu, nuna mata bayanta mai napep din yayi yace "hajiya bake wancan dayaji ciwo ke kiraba?" ahankali ta juya dan ganin mai kiranta, hakan yasa Abdallah ya nunata da hannu kaman zaiyi kuka yace "nurse nataka wani abu, wayyo Allah am bleeding karna mutu, zoo ki dubani" gyara zama tai a keke napep din ta dauke kai saikuma ta sake kallonshi tace "this is a minor injury kacika raki, kaje kai alluran tetanus a any nearby pharmacy" ta kalli mai napep tace "muje malam" kaman zaiyi kuka ya rike kafan yana kallo yace "Nurse wlh karma kifara kisa nai bleeding to death, kinyi nightingale pladge fa zakuyi best dinku for patients, dan haka my life is in your hands now, kizo ko Allah ya kamaki" murmushi tayi daya kara mata kyau, oh yau Allah yahadata da namiji mai halin Ya Ahmad, dan bazan surutu bala'i, fitowa tayi daga keken tace "malam yi tafiyar ka karna batama lokaci" sanan tajuya, karasowa tayi ahankali inda yake tana kallon kafan nashi. Marwan da gabaki daya ya kafeta da ido any step datai taking har cikin kasakasan ranshi yakeji, namomin jikinshi nawani irin amsawa, blood stream dinshi nawani irin freezing. Tsayawa tai agaban shi tana kallon kafan, ahankali ta sauke jakan bayanta ta tsugunna batare data kalli fuskarshi ba, zage zip din jakar tayi ta fito da yar karaman first aid kit din dake ciki ta ijiye a gefe, handglove tazaro daga kwalinsu tasaka a hannu hakan yasa ya kwalalo ido yace "Nurse tiyata zakimin ne wai? kai!" wlh batasan lokacin data fara dariya ba, hannu tadaura akan fuskarta ta rufe tana dariya sosai dan maganan shi ya mugun bata dariya, ahankali Marwan yay wining down tinted glass din motar kasa kadan danya kalleta da kyau, yanda take dariyan da hannayenta data daura akan fuskarta yakara mata wani irin kyau, wani irin tafiyan butterfly yaji acikin cikinshi hakan yasa ya daura hannunshi akan cikin dayaji kaman ma yana murdawa yana kallonta still. Kasa daina kallonta Abdallah yayi yace "wai bazaki dena dariyan ba sai jinin jikina yakare, jibi yanda jini ke fita daga fine kafana fa" janye hanun tayi daga fuskarta ahankali batare data kalleshi ba ta bude kit din ta ciro spirit ta bude ta kwara mai akan ciwon dake jinin, dan kara yayi yace "auuch, me wanan kikasa min? Gaskiya u are a wicked nurse ba kya petting patient" murmushi tayi batare datace komiba tadau cotton wool tana sharewa tace "kaiko kacika raki, ga surutu kaman yayana Ya Ahmad, inyaji ciwo ko haka yake kaman kai" tai maganan daidai tagama cleaning ciwon tana kokarin cire handglove din hanunta sai kallonta yake, ahankali yace "and I know inda ace my sister na nan she would've been just like you" dago manyan idanunta tayi ta kallai daidai tagama cire handglove din, shima ita yake kallo, daukan kit dinta tayi ta maida cikin jakan tace "make sure kaje an maka tetanus injection, Allah sawake" daukan jakanta tayi ta goya zata juya wani irin sanyi ne ya shiga jikinta sosai hakan yasa ta tsaya chak tareda juyowa ta kalli motar su, da sauri Marwan yay wining glass din up tun kafin ta lura, atishawa tayi tai hamdala, mikewa Abdallah yayi yace "inane asibitin ku anan zanje nai alluran" batare data juyoba tace "St. Edward teaching hospital" tai gaba da sauri tai titi daidai lokacin wani keke napep ya tsaya ta tare ta shiga.


Kakkabe jikinshi yayi yay murmushi yabude kofan motar su ya shiga ya zauna ya rufo ya leko da kanshi ya kalli yayan nashi yana murmushi yace "how was my act?" ahankali yace "kana hauka ko, inba hakaba tayaya zaka taka nail comfortably, wats wrong with you Abdallah" murmushi yayi yana murza key motar yace "because you are in love" "what!" yafada angrily, tada motar yayi yace "Allah Ya Marwan, dudda baka fadamin abinda yafaru jiyaba tace a St. Edward take aiki which was inda mukaje jiya and naga yanda kake kallonta dat wat made me do abinda nayi sabida ka kalleta da kyau, finally kaga wata kanaso, finally you've seen someone, finally kai developing feelings ma someone, finally Ya Marwan zaiyi aure, finally Ya Marwan is in luv" tsaki yayi "something is really wrong with you Abdallah, kai! are you sick upstairs?" yay maganan kaman wani dan daba dinan, tsaki yasake yi ya dau MacBook dinshi yafara danne danne amma bama ya gane komi, sake dago kai yayi ya kalli Abdallah ta madubi yace "karka karamin irin maganan nan, i hate it! am not in luv, i just don't know what is wrong with me, i guess fushi nake kan rashin concluding aikin jiya" murmushi kawai Abdallah yayi yacigaba da tukin shi batare dayace komiba.
[8/28, 6:56 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳



*Maman Abd Shakur*


1⃣1⃣ - 1⃣2⃣



Shi kadai ya dinga jera uban tsaki yafi sau goma, gabaki daya fuskarta yake gani barinma lokacin data daura hannayen ta akan fuskarta tana dariya, tsaki yayi yamaida hankalinshi yacigaba da aikinshi da MacBook yana so ya natsu amma ina ya kasa a screen din MacBook dinma ganinta yayi tanamai murmushi hakan yasa yawani irin jan dogon tsaki yarufe system din da sauri yace "damn it!" sai uban huci yake kaman kumurci yana duddunkule hannu, murmushi Abdallah yayi yacigaba da tukinshi abinshi yace "ari".


Koda takai gida babu kowa duk sun tafi aiki Abba ma bayanan, mai aikinsu ce kawai agidan gaisheta tayi ta wuce daki tai wanka kaya ta chanzo har lokacin tana murmushin rakin Abdallah tafito tai kitchen tana taya yar aikin nasu aiki sukai hadadden girki ma Mum sukai arranging gidan aka share ko ina sai kamshi yake, tafito da kayan wankinta sukai backyard inda washing machine yake ya wanke su ya dauraye ta ciro ta shanya sanan ta dawo dakin lokacin an sakko daga masallacin juma'a hakan yasa tai dakinta taje tai salla, wayarta dake ringing yasa ta mike da sauri ta dauka agaban madubi, Mum data gani yasa tai wani irin tsalle ta zauna akan gado tadau wayar saikuma ta saki kuka tace "Mum tunda kika tafi baki nemeni ba kona kiraki baki dauka why Mum" dan dariya Mum tayi daga ta dayan bangaren tace "sorry my

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login