Showing 78001 words to 81000 words out of 150731 words
type of hayaniya, bayason damuwa karku, bayason tashin hankali, karku daga mai hankali kark..." bude kofar dakin akayi hakan yasa Dr yadaga kai ya kalli kofan Ahmad ne ya shigo kaman wani abu ya wurgo shi idanunshi sunyi jajir yabi su Mum da yaga fuskarta akumbure da jini da kallo kafin ahankali ya juyo da kanshi ya kalli gadon dayaga an lullube Ya Muhsin da bargo harkai.
Tsaki Dr yayi cikin bacin rai yace "da girman ku, da girman ku, manya daku xakuzo kuna dambe agaban danku mara lafiya, a hospital for dat matter, ku yarane? You guys are very very selfish my God, anyways the damage has been done already, kuzo kuyi clearing komi kokuma nan da 10min zan aiko awuce dashi mutuary" yajuya yabi ta gefen Ahmad dako motsi yakasa yana kallon Muhsin dake alullube, fita Dr yayi hakan yasa Ahmad yadaga kafa ahankali kaman mai matsala a kafa yakarasa jikin gadon ya tsaya chak kafin ya mika hannunshi dake rawa sosai ya daura akan bargon yaja kasa nan yaga fuskar Muhsin da zufa kekan goshinshi idanunshi a lumshe, wani irin faduwa yayi akan guiwowinshi kaman mara lafiya ya fashe dawani irin kuka ya daura kanshi akan gadon yace "innalillahi wa inna ilahi raji'un, Ya Muhsin! Ya Muhsin! dan Allah karka tafi ka barni ni kadai dawayanan mutanen we called our parents, Ya Muhsin you are my strength, my support system, my guardian please wake up, am sorry is my fault, is all my fault, na fita nikadai na barka tareda mutanen nan, Ya Muhsin dina!" yawani irin tashi yana jijjigashi amma ko gezau, fashewa yay dawani irin kuka yama kasa magana da kyar ya iya dago dakai ahankali hawayen dayake suna diga ajikin Ya Muhsin yaja bargon yarufe shi back yana tofamai addu'a kafin yawani irin juyowa cikin fushi yatako har zuwa gaban Abba dake kallonshi jiki asake yace "Alhaji Naseer Aluminum!" saida zuciyar Abba tawani irin girgiza sabida yanda dan cikin shi ya kira sunanshi kai tsaye haka, wani irin kuka kecin Ahmad da kyar cikin kuka ya iya yay magana. "karka, never in your life call me your son, kaiba mahaifina bane, I regret ranan danazo duniyan nan amatsayin danka, na tsanake na tsaneka sosai, I hate you, and kaje sai Allah yamana hisabi dakai kashemin dan uwana dakayi bazan taba yafema ba!" zaro ido Abba yayi yana kallonshi idanunshi sunyi jajir yarasa ta cewa, yajuya ya kalli Mum dake wani irin kuka kanta akasa yace "and you Mum, am so so disappointed in you, kome Mutumin nan zai miki saiki biye mai? I tried talking to you but kince namiki shiru nabarki kiyi magana and vent out your anger, that you are tired, so yanzu you've vented your anger kinyi son ranki danki kuma yarasu kun kasheshi da bakin cikin ku are you happy now? Are you happy Mum? Are you satisfy? Kozaki cigaba ne?" yay maganan yana kuka sosai, girgiza mai kai Mum tayi cikin kuka sosai kaman zata mutu, hannu Ahmad ya daga yana musu clapping yana hawaye yace "wow, wow, wow you guys deserve an award na kashe danku" yajuya dawani irin sauri cikin fushi yafita daga dakin dan zuwa clearing everything ya tafi da wanshi gida, da kyar cikin kuka Mum tadago kanta ta kalli Abba da shima ita yake kallo da idanunshi dasukayi kaman an jijjiga bera a buta tsabagen fitowa, atare sukai wurin gadon suka tsaya, cikin kuka sosai Mum ta kalli Abba tace "Alhaji danmu, Alhaji Muhsin, my son da gaske ya mutu Alhaji?" tai maganan kaman zararra tana janye blanket din daga fuskarshi tana wani irin kallon shi tana kuka, kallon Muhsin din Abba yayi gabaki daya kanshi ya kwance yakasa furta komi sai zaro ido dayake yi gabanshi na faduwa, bude kofan dakin akayi Ahmad da idanunshi sukai jajir ya shigo dawani abokinshi Bello dauke da makara dakuma babban tabarma, wani irin nishi Abba yafara yi yana kallon Ahmad din dako kallon inda Abban yake baiyiba suka ajiye komi akasa yazo ta gaban gadon shida abokinshi zasu dagashi da sauri Abba ya mika hannu zai dagashi Ahmad yamai wani irin kallon da idanunshi dasukai mugun jajir saida gaban Abba yafadi ahankali ya janye hanunshi ya maida kirji kaman mai shirin yin salla yana kallon Ahmad din, Ahmad da abokin nashi sukadau Ya Muhsin suka sakashi a tabarman suka sakashi a makara suka dauka suka fita daga dakin Mum nawani irin kuka tabisu da gudu Abba ma yabisu da sauri ko kallon su Ahmad baiyiba suka sakashi cikin motan ambulance din asibitin dasukai haya suka shiga kafin Mum dake kuka sosai da Abba su iso yawani irin rufe motan yacema direban su tafi suka fita daga asibitin, Mum ta tsugunna a wurin tana wani irin kuka kaman zata mutu bama tasan meke mata dadiba, Abba ya tsaya akanta yana kallonta ahankali yace "H...Ha..Hajara, tashi mutafi, kinji tashi muje" ahankali Mum tamike kaman tababba tace "a'a ina zani dakai wajen Muhsin zani shi kadai muka bari adaki" da sauri ta juya zata koma cikin hospital din Abba yarike hanunta da sauri yace "Hajara dubi, kalleni" cikin kuka sosai ta kalli Abba, Abba yace "Allah yafi nida ke son danmu, dama kuma shiya bamu shiko?" yatambayi Mum ahankali, da sauri ta girgiza mai kai hawaye na bulbulowa Abba yace "to Allah yama Muhsin rasuwa, addu'a zamumai ba kukaba kinji, yanzu zomu tafi gida naga banga motar ki a parking space ba, bakizo dashi bane" gyadamai kai Mum tayi tana wani irin kuka, juyawa yayi ahankali rike da hanunta ganin bata hayyacinta yay bakin gate da ita, yatare musu taxi suka shiga suka zauna yaciro wayarshi yafara kiraye kirayen abokan arziki da abokan business.
***
Dan shiru tayi tai dan murmushi kadan ta dauke kai batare datace komiba tadan matsa gefe sabida yanda suke kusa kusa da Marwan daketa daddanna system abinshi kamshin shi na fizganta, dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Abdallah daketa kallonta hoping zatace wani abu again, dan hararan shi tayi tana wasa da yatsun ta tana turo baki tana kukkuni kasa kasa tace "ni banason ana kallona fa" "lalalala" Abdallah yafada yana saukar da kafanshi kasa, da sauri ta kallai murmushi yay escaping bakinta, ta wutsiyar ido Marwan keta kallonta, Abdallah ya kalli Ya
Marwan yace "Ya Marwan wlh kama amaryan ka magana ba kaga tanamin kukkuni ba" murmushi sosai tayi, hakanan batasan mesa she always find the guy funny ba, kamanYa Ahmad haka yake mata, ahankali Marwan ya janye system din yana wani irin kallon ta kaman yahadiyeta yakasa magana, turo baki Abdallah yayi kaman zaiyi kuka yace "Ya Marwan bakace komiba kagama dariya takemini" murmushi tayi sosai harda daura hanunta akan fuskarta, daidai lokacin aka bude kofa Omari ya shigo dakin dauke da sallama shima idanunshi akan kanwar tasu da sauri Abdallah ya kalleshi kaman zaiyi kuka yace "Ya Omari kaga amaryan Ya Marwan na tsokanana ko, wlh this nurse ko she's so tsokanacious" fashewa tai da dariya hartana bige kafan ya Marwan, dukansu tsayawa sukayi suna kallonta barin ma Ya Marwan dake gefenta dayakeji kaman ya tsaga jinin shi ya sata ciki, Ahankali Omari daya kasa dena kallonta ya shigo dakin ya zauna gefen Abdallah gani yayi dariyanta kaman na Momma su, da kyar tai shiru tana murmushin data dade batai irinshi ba dimples dinta nawani irin lotsawa, dukan cinyan Omari Abdallah yayi yace "ehen nurse zokiga Ya Omari yaji ciwo a hannu dama dazu yabige da table ko Ya Omari?" kallon Abdallah Omari yayi, Abdallah ya kannemai ido hakan yasa Omari ya kalleta suka hada ido yace "y..y..uhm" da sauri Abdallah ya fizge hanunshi yaja hanun riganshi sama yace "zoki gani nurse" make kafada tayi ahankali tana leken hanun nashi daga inda take zaune tace "aini banga ciwo a hanunba, in bigewa ne jamai kawai za'ayi zai dena zafi, kajamai" da sauri Abdallah ya kwalalo ido yace "ni? Wai bakiga katon hanun Ya Omari bane kaman na Ya Marwan" murmushi yayi ya kalli hanun ya Marwan din dayay kaman baya jinsu nanko kunenshi nakan duk abinda suke cewa, juyowa yayi ya kalli Nadeera itama shitake kallo ya nuna mata hanun Ya Marwan yana cemata look yana nuna mata manyan muscles dinshi Yana nuna mata ta kalla, makemai kafada tayi taki kallo, turo mata baki Abdallah yayi hakan yasa kaman daga sama tace "wlh kacika shagwaba" hararanta yayi shima harsaida tai murmushi yace "nakai ki?" da sauri tace "ni? Ni ai banda shagwaba" tabe baki yayi yace "wai talle kema audi gori" kama baki tayi tace "wai a ina kaji hausa? You don't look like a hausa man" murmushi yayi yace "kema u don't look like a hausa girl shagwababbiya kawai" makemai kafada tayi ta kalli Omari daketa kallon su kaman yasami film yanajin son kanin nashi aranshi tace "dan Allah waini shagwababbiya ce?" girgiza mata kai yayi ya tallabe keyan Abdallah yace "don't mind him lil sis keba shagwababbiya bace" dan murmushi tayi tana komawa jikin kujera dudda she found yanda yakirata da lil sis a little bit weird amma saita basar tajingina da kujeran tareda lumshe ido kaman mai shirin yin bacci, wani irin faduwa gabanta yayi harsaida taidan ihu tareda bude ido a firgice tana numfashi da sauri da sauri, kallo dukansu suka bita dashi, ahankali Marwan dake gefenta yataso ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "menene?" baki ta tabe tana wani irin nishi tana kallonshi tana shirin yimai kuka, girgiza mata kai yayi tareda daura yatsan shi akan lips dinta yana wani irin kallon ta murya chan kasa danko su Abdallah bazasu iyajin abinda yace ba yace "don't cry for me, menene?" yay maganan yana janye yatsan daga kan lips dinta yamata wani irin kallon ban amsa, ahankali hawaye nacika idanunta ta dafa zuciyarta tace "My heart" ahankali ya kalli kirjin nata kaman mai nazarin abu kafin ya mika hanunshi ya janye nata ya daura nashi akai koshi yaji yanda yake bugu fast fast, fashemai tayi da kuka sosai tace "please kiramin Mum, zanyi magana da ita something is wrong" tafara wani irin nishi bakinta ya bushe sosai, dan juyo da kai yayi ya kalli Abdallah dake kallonsu yace "get me water Abdallah" dasauri Abdallah yatashi yana waigenta yaje kitchen ya dauko bottle water yadawo ya mikamai, budewa yayi ya kai bakinta da kyar ta sha tana fashemai da kuka tace "dan Allah Mummy na" yanda take kukan tana wani irin nishi yasa yajata jikinshi ya rungumeta yana buga bayanta hanunshi daya kuma yana kokarin ciro wayarshi dake bayan wando ya ciro yadawo dashi ta gaba ya bude wayan yay dailing number Mum.
Mum dake zaune cukin mota kuka take sosai ko mutum daya takasa kira saima kallon wayar nata da Abba yaciro daga purse dinta yasamata a hannu take, shidai Abba sai kiran mutane yake da limamai, ringing wayan Mum din tayi tabi wayar da kallo dudda tagane number Marwan ne amma takasa picking, sai uban kuka take akaro na uku sanan Abba yace "amsa mana Hajara hakuri zakiyi kinji" da kyar ta iya tai picking call din ta kara akunenta tana kuka sosai takasa magana, daga tachan bangaren saida gaban Marwan yafadi a yanda yaji Mum na kuka da sauri Nadeera dake jikinshi ta dago kai tafashe dawani kukan tana kallonshi, cikin kuka tace "Mummy na ta dauka?" jin maganan Nadeera yasa Mum ta katse wayar da sauri tarushe da kuka sosai, sakinta yay ahankali ya mike tsaye dan jikinshi yabashi wani abu matsawa yayi chan bangaren dining ya tsaya yay dailing number da kyar Mum ta iya picking call din ahankali Marwan yace "why are you crying Mum? Did dat man hurt you?" cikin wani irin murya raunanniya Mum tace "d'ana Muhsin dake kwance a asibiti ya rasu yanzun nan" sosai maganan ta dakai harsaida kirjinshi ya buga yadago kai ya kalli Nadeera dake zaune akan kujeran daya barta tana goge kwalla tana kallonshi jira kawai take taji mezaice, dan murmushi yamata danya kwabtar mata da hankali, kafin ya kalli wayar ahankali yace "may his soul rest in peace, and may Allah forgive his short comings" ahankali cikin kuka Mum tace "Ameen" tareda katse wayan, ahankali ya shigo falon yana kallon su Abdallah da sun riga sun karanci something is wrong daga fuskan shi, kafin ma yakaraso cikin dakin ta tashi da sauri ta karaso tana numfashi sama sama ta rike mai hannu tace "uhmm meya sami Mummy na? Metace? Wlh inaji ajikina something is wrong, please kafadamin gaskiya kaji please" ta karashe maganan tana fashemai da kuka, hanunta ya rike ahankali ya kakalo murmushi yace "come" stairs yay da ita tana kuka sosai ya shiga dakinsu da ita, fashewa tai da kuka sosai tana sake kallon fuskanshi tace "kafadamin dan Allah meya sami Mummy na" rungumeta yayi very tight tanamai kuka sosai kafin ahankali ya cirota daga jikinshi ya jata ya bude kofa suka suka tsaya agaban closet wani doguwan fine rigan abaya yaciro mata sai binshi da kallo take tafashe dawani irin kuka tace "ina zamu?" ahankali ya zage zip din bayan riganta batare daya bata amsaba yacire mata rigan tana kallon fuskanshi tana kuka, ajiye rigan yayi yana kallon fuskarta itama asanyaye, cikin kuka ta dafa hanunshi tace "ina zamu meya sami Mummy na?" yana zage zip din bayan skirt dinta yace "nothing, Mum is fine wife" jan skirt din yayi kasa tsabagen rudewa bama tadamu ba yabi santala santala cinyoyin ta da kallo, doguwan rigan ya dauka ya samata da hijabi. Cikin kuka sosai tace "I.. I want to change" gyada mata kai yayi ahankali yasaketa tadau pad dinta ta shiga bayi da gudu tana kuka, wayarshi ya ciro yatura ma su Omari text su shirya d'an Mum na hospital ya rasu yanzun nan, shiryawa yayi shima yasaka wani light blue yadi mai taushi dayamai bala'in kyau ya fesa turare yana jiran tafito, fitowa tayi tana hawaye sosai ta karaso gabanshi tace "am ready" takalmin ta ya nuna mata ta zura flat shoe jikinta na rawa yarike hanunta suka fito daga dakin, akasa suka samu Omari da Abdallah sunci manyan kaya suma sunyi kyau kaman zasuje gasan kyau sai kallonta suke duk suka fice suka shiga babban jeep din Marwan, Omari na mazaunin driver Abdallah na gefe sai shi da ita abaya suka rufo sanan Omari yatada motar yaja suka fita daga gidan, ahankali ya kwanto da ita jikinshi, dago kai tayi ta kalleshi bakinta na rawa sosai cikin kuka tace "are you sure my Mummy is fine?" gyada mata kai yayi tareda lumshe mata ido yana sake kwanto da ita tai lamo ajikinshi tana sauke ajiyan zuciya.
Akofar gida da already mutane sun cika Abba yasa mai taxi yay parking, fitowa yayi yabiya kudi ya zagayo ta bangaren Mum yabude mata ya riko hanunta tafito daga motan da kyar mutane suka karaso wajen yan anguwa anata musu gaisuwa ana tambayan karfe nawane jana'izar dan ga magrib ta kusa yau za'a kaishi ko sai gobe?" Eh yace musu yace "da isha'i za'ai jana'izar" yamusu godiya yaja hanun Mum dake binshi luu suka shiga cikin gidan, kawayen ta tagani yan kwararu agaban barander su, da sauri Maman fauzy da Abba ya kira ma Mum ta tashi tafito ta rungume Mum tana lallashin Mum data fashe dawani irin kuka Abba kuma yawuce shashin su Muhsin, Mum Fauzy tace "ki daure, ki daure Hajiya, nasan abin da ciwo, I know how painful it's to lose a Son, ki daure kinji, kici wanan jarabawan, ubangiji Allah yafimu son Muhsin, yaro mai kirki, shiru shiru, mara hayaniya, baida magana ga kunya, ga kyauta ga yawan sadaka da kyautatama mabukata, me kuma kike nema? Share hawayen ki" tashare ma Mum hawaye, ahankali Mum tace "ina Muhsin ina Ahmad?" shashin su Muhsin ta nuna mata tace "chan aka tafi dashi anje yanko likafani sai amai wanka" gyadamata kai Mum tayi tace "kaini wajen bana gani sosai" gyadama Mum kai Maman fauzy tayi taja hanun Mum ta kaita shashin su Muhsin ta tura kofan suka shiga da sallama ta kurama gawan Muhsin ido ga Ahmad zaune agefe idanun nan sunyi jajir yana kallon gawan shima, sai Abba dake gefen Ahmad kadan shima yana kallon gawan, ahankali Mum tawani irin zube agaban Muhsin tana wani irin kuka tahade hannayenta biyu alamun roko tana kuka tama kasa fadin abinda takeso tace, tai nadama tai nadama tai nadama biyema Abba, maima yasameta? Ya akayi tabari shaidan yaci galaba akanta? Itace ke dambe da namiji? Meya sameta? sosai Ahmad yaji tawani irin bashi tausayi dan yanda take kuka tana nishi saika zata suma zatayi, ahankali ya mike tsaye yaje inda take ya dagata murya chan kasa yace "Mummy is okay, kidena kuka haka is not good for your health, addu'a zakimai" rungume Ahmad tayi tana kuka shima hawaye ya goge da sauri batare daya rabata da jikinshi ba yajata yakoma chan gefe ya zaunar da ita man dogon kujeran falon su ya dago ta ya cirota daga jikinshi, hannunshi yasa ya goge mata hawayen datake yi dasuka kasa dena zuba, Abba da jikinshi yay sanyi sosai sai wani irin kallonsu yake, murya chan kasa Ahmad yace "Mum kinfada ma Nadeera? Yakamata ta sani, yakamata tazo taga Yayanta tamai addu'a kafin akaishi, kin kirata? Because I know kinada masaniyar inda take? Yanzu rasuwa akayi mu manta komi, kin kirata?" da kyar ta iya girgiza kai cikin kuka in a low tone tace "nafada ma mijinta Muhsin ya rasu" ahankali yasake kai hanunshi kan fuskarta yana goge mata hawayen yace "nace kidena kuka be strong, don't break my heart Mum" gyadamai kai tayi tana wani irin kuka, ahankali yamata kiss a goshi yace "is okay Mum" gyadamai kai tasake yi murya chan kasa yace "give me your phone ban number mijin nata lemme call him nace yakawota" gyadamai kai tasake yi tana kuka sosai ta ciro wayar tabude tabashi number, karba yayi yace "stay here am coming" fita yayi daga dakin yafita waje jiri na dibanshi daurewa kawai yake yakira wayar ringing daya Marwan dake mota rungume da Nadeera dayasamu bacci ya fizgeta yay picking ganin number Mum, ahankali Ahmad yace