Showing 9001 words to 12000 words out of 150731 words

Chapter 4 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

771

agabana suka karya ma wani hannu, wani kuma kafa" takara she maganan tana wani irin nishi zata sake suman hakan yasa yace "Nadeera look" bottle water ya kafa mata abaki dan yanda lips dinta suka bushe shows she's dehydrated da kyar tasha ruwan sanan ya ijiye yasa kanta akan kafadarshi yana shafa kanta hakan yasa tasomajin natsuwa sunfi 2min ahaka sanan ya saketa ya kamo habarta yace "fadamin maiya faru no more cry babu abinda zasu miki am here" gyadamai kai tayi kafin ta shiga bashi labarin komi. "Ya Muhsin BOYAYYEN MUTUN dinan ne, i have nothing to do with all wat they're saying wlh" "is okay tashi muje" dagata yayi yadau hijabin ta yasaka mata ya kamo hanunta yarike ganin yanda kafafunta ke rawa suka tafi office din inspecta, kafesu da ido Inspector Aliyu yayi harsuka karaso gaban table din ya zaunar da ita akan kujeran gefenshi, kallonta yayi yace "tell him wat you saw" gyadamai kai tayi tana kokarin hana kanta hawayen dake shirin zubowa ya juyo ta kalli Inspecta dake kallonta tafada mai duka abinda yafaru, murmushi yamusu yace "to tayaya BOYAYYEN MUTUN din dakike cewa yawuce 2 security dake bakin passage din yaje dakin? And how did he get out batare da kowa ya ganshi ba? Koshi aljani ne?" hawaye ta share tace "wlh am saying d truth ba karya nakeyiba" ganin yanda takeyi yasa Ya Muhsin yace "since the patient is still alive inaso nai bailing dinta" hulan kanshi yacire yace "okay fine amma with the condition duk lokacin da muka bukace ta zaka bayyanata, anytime her presence is required she will appear" jiyayi kaman ya buge bakin dan iskan inspecta, cije lips yayi yace "fine!" bail documents yatashi ya dauko yabashi yace "sign" byro yaciro Nadeera na binshi da kallo yay signing sanan ya mikamai takardan mikewa yayi ya dagata yarike hannunta sukai kofa. "bye queen of suma" wani irin kallo Ya Muhsin yamai itako ko juyowa batayi ba hakan yasa Inspecta yay dariya yace "Yayan mu zaka bani ai ko dan gaskiya ina ciki" wanan kara juyowa Muhsin yayi completely yana rike da hanunta ya kalleshi nakusan 2min fuskarshi babu alamun wasa yace "stay within ur limit" yaja hanunta tareda bude kofan suka fice a kanta suka hadu da Abba da Ya Ahmad dake tsaye suna jiran Muhsin dan police din wajen yace musu lawyer ta yariga yazo hakan yasa suka gane Fauziya ta kira Muhsin kenan shima, kafinma su karaso Abba da Ya Ahmad sukai wurinsu hankali tashe suna kallon yanda Nadeera tadawo mara lpy mara lpy, fadawa jikin Abba tayi ta fashe dawani kukan, Ahmad ya kalleta sanan Ya kalli Ya Muhsin yace "what happen bro Fauziya ce dukta kiramu tace anyi arresting dinta" yatsine fuska yayi yana kokarin ciro phone dinshi daga aljihu yace "is a long story muje gida kawai, Abba mutafi" "kagama komine?" Abba yay maganan yana share mata fuska tareda rike mata hannu, ahankali yace "eh nagama kuwuce da ita gida am going to the hospital now" fita duk sukayi atare Abba da ita suka shiga bayan motar Ya Ahmad ya Ahmad kuma ya zauna a mazaunin driver shikuma Ya Muhsin yay wurin motarshi ya shige yaja yay dan zuwa hospital dinsu.
[8/26, 8:26 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳




*Maman Abd Shakur*

7⃣

Wuraren shida na yamma yatashi awahale sai atishawa yake, addu'an tashi daga bacci yayi kafin ahankali ya sauko daga gadon yana atishawa juyawa yayi ya kalli ac yaga ko akunne ne amma akashe hakan yasa yajuya ya bude kofan bathroom ya shiga, wani irin hadadden babban bathroom ne mai hade da closet an raba wajen part biyu bangaren dama wani irin hadadden closet ne komi na wajen blue, ga kaya kala kala dake jikin hanga ga kuma yar stool a tsakiyar wajen sai bangaren haggun kuma koface wacce bayi ke ciki bude kofan yayi ya shiga.

Yay kusan 15 minutes kafin yafito daga bathroom din sanye dawani maroon hoodie da aka rubuta gifted agaban daya daura hulanta akai sai dogon bakin wando da bakin safa akafanshi sai uban kamshi yake, jinginar da kanshi yay ajikin bangon dakin kafin ya dago kai ya dunkule hannu ya daki bangon dakin da karfin bala'i yana tsaki ganin hoton fuskar Nadeera yakara flashing aranshi, dadduma ya shimfida yay sallan la'asar koda ya idar akan dadduman ya zauna ya daura kanshi akan gwuiwanshi, tsaki yaja yace "damn it" fuskar mace bai taba tsayamai arai kaman na yarinyar nanba but why?! Kiran sallan dayaji daga masallacin gidansu yasa ya mike tsaye, slippers ya zira da sauri yana atishawa yana hamdala yabude kofa yafita daga dakin, sauka yayi yafice yay masallaci danyin sallan magrib. Ko amasallacin magrib da isha'i aka hada sabida hadarin daya hadu sosai yana idar da azkar ya mike yafice daga masallacin kafin su Abdallah su rikeshi da magana dan ko kadan bayaji magana, stairs yahau ya bude kofa ya shiga dakinshi mayar da kofan yayi ya rufe harda saka key ya jingina da kofar yana sauke ajiyan zuciya, atishawa yayi yay hamdala kafin ahankali ya daura hannunshi kan heart dinshi da duk single beat remains him of her in his arms, ahankali ya daga kai ya kalli plain white chiffon curtains din dake jikin babban window dakinshi dake kadawa sosai sakamakon iskan da akeyi na shirin ruwa, garin yay duhu sosai kaman irin tsakar dare dinan sabida hadari sai walkiya sama take, ahankali yatashi daga jikin kofan yafara tafiya kaman kwai yafashe mai aciki yay wurin window ya tsaya ahankali ya mika hannunshi ya shafa labule slowly kafin yakai dayan hanunshi yasa duka hannayen shi ya raba curtains din kowanne yatafi bangare daya hakan ya bayyana window daya dan budu kadan, hannu yatura ya bude window duka waaa, yadaga kai yana kallon sama, bai damu da ko sauro ko wasu kwarin su shigo mai dakiba, shiru yayi yana kallon sama iska da kamshin kasa dana trees yawani irin blowing suna ratsa duka jikinshi suna karasashi jin wani iri da baitaba jin kanshi aciki ba, ahankali ya mika hanunshi ya fitar dashi waje ta window yana feeling yanda iska ke dukan hannu dan yayyafin da ake na zuba akan hannun, hanun ya kafe da ido jikinshi namai wani iri ahankali yace "what is happening to me?".




***

Gida suka wuce suna shiga har dakinta Abba ya kaita yace "jekiyo wanka ki chanza kayan nan kici abinci zai aika Ahmad ya siyo miki magani karki damu everything will be fine" gyadama Abba kai tayi ta wuce bayi tana atishawa tanajin wani irin sanyi ajikinta hakan yasa ta shiga bayi da sauri, wanka tayo da ruwan zafi ta dauro alwala kanta nawani irin ciwo tafito, gaban wardrobe dinta taje tajawo wani dogon riganta baki ta zira ta saka hijabi tahau kan dadduma da kyar tai sallan la'asar dan sosai kanta ke mata ciwo gashi sanyi takeji sosai tana idarwa tacire hajabin tafada gado ta lullube da bargo tana godema Allah da ya tsareta yau bata mutu ba da wanan BOYAYYEN MUTUN dinan fa ya harbe ta, atishawa tafarayi tayi sunkai biyar ajere hakan yasa takara jan banrgo ta dukunkune ahaka bacci yay gaba da ita koda Abba ya shigo dan kiranta taci abinci bacci yaga tanayi hakan yasa ya kashe mata wuta yafita da Ya Ahmad sukaci karo shima zaizo dubata hakan yasa yace "tai bacci son" gyada kai yayi yajuya yay falo shikuma Abba ya wuce dakinshi dake nan corridor zama yay akan daya daga cikin kujerun falon ya zauna wayanshi yaciro daga aljihu number dayay saving da Sweetheart yaciro yay dailing har yagama ringing ba'a dagaba, nabiyu ma haka ana uku ne aka dauka daga ta chan bangaren Mum tai magana ahankali tace "Alhajina please ina meeting da some investors ne, i will call you back i promise Alhajina" ta katse wayar dip, wayar Abba yacire daga kunenshi yabi wayan da kallo yanajin wani irin haushi a ranshi, ajiye wayar yayi ya gyara zama yana kallon news, saida aka kira magrib sanan yatashi ya shiga bayi dakenan falon shi ya dauro alwala ya chanza kayan jikinshi zuwa jallabiya brown sanan ya fito, dakinta yafara shiga har lokacin bacci take tadata yayi ta tashi sanan ya wuce masallaci, da kyar ta lallaba ta shiga bayi alwala ta dauro ta fito tasaka hijabi tai magrib rashin karfin datake dashi yasa bata iya karanta Al Qur'ani yauba, tashi tayi ta bude kofa tafito tayi falo kitchen ta shiga ahankali ta jona ruwa a heater kettle yana tafasa ta hada tea mai kauri ta dawo dining ta zauna tana juya spoon a cup din tana kallon tea, wani irin kewan Mum takeyi bana wasaba sokawai take ta rungume Mum taji dumin mahaifiyar ta kotaji natsuwar datake nema, ahankali ta cire spoon din ta ijiye ta dau cup din takai baki tafara sha sanan ta sauke cup din tana kallon tea dako kadan baya mata dadi, sake kafawa abaki tayi ta kwalkwale sanan tadau spoon din tasaka acikin cup din tamike ahankali ta shiga kitchen din tsayawa tayi awajen tap din tana dauraye kofin tana kallon window kitchen din yanda gari yay duhu sosai sakamakon hadarin daya hadu sai walkiya ake, wani irin abu taji yana fizgar ta hakan yasa ta ijiye kofin ahankali tai wajen kofan dazai sadata da backyard tabude wani irin iska ne ya hurata hakan yasa tadan lumshe ido kafin ahankali ta budesu, kallon sama tayi yanda ko ina yay bakinkirin hazo sai tafiya yake wani irin iska mai dadi dake kamshin kasa na shiga hancinta, sosai take kallon sama jikinta nawani iri, lumshe ido tayi sakamakon yayyafin da aka fara wani iska dayazo ne ya feso da yayyafin akan fuskarta runtse ido tayi sosai kafin ta bude idon ahankali tana kallon sama tace "maisa nakeji kaman wani abu zai faru da rayuwata? Why do I feel as if something is about to happen? Ya Allah please protect me, am very very scared of him, ko rufe ido nayi saina ganshi, i can't get his face out of my head, Ya Allah am afraid of this mask man, ya Allah ka kareni ka tsareni" jinkinta ta rungume yayyafin na feso mata tana kallon saman da wanan karan yay duhu sosai, tai nisa acikin tunani, hannu taji akan kafadarta hakan yasa tasaki wani irin ihu tajuyo afirgice Ya Muhsin tagani tsaye abayanta yana mata wani irin kallo yace "Ke mehaka wai mekikeyi anan bakiga ana yayyafi bane jibi yanda ruwa ya jikaki" yanda ta kwalalo ido tana kallonshi fuskan shi na rikadan mata zuwa fuskan boyayyen mutum, runtse ido tayi da sauri ta kankame jikinta breath dinta na neman daukewa, jijiga kafadunta yayi yace "Nadeera" ahankali ta bude ido ta kalleshi ta lankwasa kai ahankali tace "Na'am" matsar da ita gefe yayi ya kullo kofar kitchen din sanan yajuyo ya kalleta yace "are you okay? Me matsalar ki?" girgixa kai tayi hawaye na taruwa a idonta ahankali tace "am just missing Mum" "don't worry takusa dawowa, Ahmad yakai miki magani daki jeki sha" gyadamai kai tayi tabi gefenshi tafice daga kitchen din da sauri, bin kofar databi yayi da kallo kafin ya bude fridge yadau cold maltina yafita daga kitchen din yay dakin Abba.
[8/27, 4:44 PM] Aishat Muhammad: 🕳🕳🕳🕳🕳

*BOYAYYEN MUTUN*🕳 🕳 🕳 🕳



*Maman Abd Shakur*

8⃣ - 9⃣

Sallama yayi Abba yabashi izinin shigowa hakan yasa ya shiga yana shan malt din dake hanunshi ya maida kofar yarufe yakaraso nan kusa da Abba a kasan carpet ya zauna yace "sannu da hutawa Abba" alamu Abba yamai dakai na yauwa dan ranshi abace yake har yanzu Mum bata sake kiraba, ajiye malt din hanunshi gefe yayi yace "Abba I've been calling Mum yafi sau uku she's not answering, gaskiya Abba tadawo this girl need her mana, she looks lonely gatanan duk kalan tausayi tausayi, yanda zatai feeling taji tamanta da matsalolinta a jikin Mum bahaka zataji a wurin muba, please Abba Mum should come back kace tadawo." "and kana tunanin bance mata tadawon bane?" Abba yay maganan yana raising ma Ya Muhsin voice ranshi abace, yanda Ya Muhsin ya tsaya kallonshi da mamaki ne dan da wuya kaga Abba yay fushi hakan yasa ya dafa kanshi nayan sakannni kafin ya shafa fuskarshi ya sassauta muryanshi yace "Muhsin lemme advice akan wani abu, inhar lokacin auren ka yatashi karka sake ka yarda da any conditions da wacce zaka aura zata kawoma na zata dinga tafiye tafiye tana business, Mum dinku ko hmm" sai kuma yay shiru kawai batare daya kara wata maganan ba, ganin yanda Abba is so pained ne yasa shima yaji ranshi dukya baci, haba mana Mum kullum tana wanan garin tana wanchan garin sabida Abba na sonta and he's too soft towards her saisa take abinda taga dama, maganan Abba ne ya katse mai tunani yace "kaga Son i have meeting daya kamata naje, gobe ne meeting din a japan amma dole nafasa tafiyan zamu barkune ba baba ba Mama?" girgixa mai kai Muhsin yayi yace "kayakuri Abba" "is okay, i know what to do, yaya kukayi da kaje asibitin?" yatsine fuskarshi yayi yace "bansami HOD dinsu ba, so i will be going their tommorow i need her permission ne sabida nai gaining access to their CCTV footage, dudda nasan thousands of people suna shiga da fita daga asibiti daily but i want to take my time and watch it, dan inhar Nadeera tace taga boyayyen mutum taganshi ne, inhar am able to see him that shows that she's innocent kaga koda wani abu eventually happen to d patient baza ai holding dinta responsible ba in anyway" gyadakai Abba yayi alamun gamsuwa da maganan da Ya Muhsin yayi, ahankali yace "to ubangiji Allah ya fitar da ita, ya maganar mu Son? Sabida banason takura muku saisa ka banzantar da ita ko? Wlh fa zan maka auren nan babu abinda ya shafan koma wacece saidai nahada ka da ita" lumshe ido yayi ahankali yace "my heart, soul, system and my nerves only belong to her Abba" "mekace banajinka" bude ido yayi ya kalli Abba yana murmushi yace "Abba in sha Allah very soon zan fito da mata, ka karamin lokacin kadan" gyadakai Abba yayi yace "is okay take your time amma banason ka wuce dis year kaga kana 29 yanzu at least by 30 ko yaron kirki?" maltinan shi ya dauka yasha sanan yace "yes Abbana" zama ya gyara suna kallon news din tare, ba'a wani dadeba Ya Ahmad ma yashigo suna hira kasa kasa suna labarai sai wuraren eleven na dare suka baro dakin Abba koda zasu tafi su kwanta saida suka bude kofar dakinta amma hartai bacci ta lulluba da bargo, hakan yasa suka kashe mata wutan dakin suka rufo kofan sukai part dinsu.


Da Asuba Abba ya shigo yatada ta saida ya tabbatar ta tashi sanan ya fice, saukowa tai daga kan gadon ahankali ta shiga bayi, bata wani jimaba ta fito daure da alwala, rakatanil fajiri tafara yi, sanan tai sallan asuba tana gamawa tai azkar sanan tajawo Al Qur'ani tafara karatu da qira'anta mai dadin gaske saida gari yasoma haske ta rufe Qur'anin ta ijiye ta linke dadduma ta ijiye sanan ta wuce kitchen ruwan tea tadafa takai shashin su Ya Ahmad babu ma kowa falon alamun basu dawoba hakan yasa ta wuce part dinsu tray ta dauka takai part din Abba, sanan tafito tai dakinta tattare dakin tayi sanan ta wuce ta shiga wanka bata wani dadeba tafito daure da pink towel gaban wardrobe taje ta dauko wasu gogaggun uniform dinta ta shirya tsaf, gaban mirror ta tsaya tadan shafa hoda tasaka kwalli bakaramin kyau tayiba dudda idanunta da dan ragowan kumburin jiya na kuka, addu'a tayi Allah yasa kar amata komi a practical yau, ajiye hijabin tayi akan gado ta zira silifas ta fita, kitchen taje tahada tea tai soya egg tafito dining ta zauna tana ci, Ya Muhsin ne ya shigo sanye da black suit sai kamshi yake, kallo daya yamata ya dauke kai hadiye egg din bakinta tayi tace "ina kwana Yaya" corridor yayi dan zuwa ciki ya gaida Abba batare daya kalleta ba yace "kin tashi lpy", agurguje ta shanye tea tadau komi takai kitchen sanan tafito tai corridorn itama ta shiga dakinta, black cover shoe dinta ta dauko ta saka sanan tadau hijabin tasaka shima, tadau jakarta ta goya ta rike hadadden after dress dinta a hannu tafita daga dakin sai kamshin turaren ta twilly takeyi tafice tai dakin Abba sallama tayi ta shiga Abba da Ya Muhsin ke zaune kusa dashi suna wani abu da system ta kalla tace "good morning Abba" "morning princess, zakije anya ba matsala kuwa?" yay maganan yana kallon fuskar Ya Muhsin, jingina yay da jikin kujeran yace "no taje Abba anjima i will go to the hospital anjima" gyada kai Abba yayi yace "okay to shikenan, Allah bada sa'a" Ameen tace tana murmushi yaciro dubu uku ya mikamata karba tayi tace "thank you Abbana bye, bye Ya Muhsin" batare daya dago kai daga abinda yakeyiba yace "bye" fita tayi da sauri ta wuce waje da Ya Ahmad sukaci karo kunenta ya rike ta hijabi yace "ke kin gaisheni dis morning" kaman zatai kuka tace "tona shigo side dinku lokacin baku dawo daga mosque ba, good morning ya Ahmad" "morning princess kinsan wani abu?" yay maganan yana mika mata red necktie din dake hanunshi, karba tayi ta ijiye after dress dinta akan kujera tace "saika fada" tai magana tana dage kafa dan ta sakamai necktie din dan yafita tsawo, duko da kanshi yayi hakan yasa ta hau dauramai yace "tommorow ki shirya zamuje amusement park, zaki rakani tadi wurin My Deejay, a park din zamu hadu" dan dariya tayi saikuma ta harareshi tace "wlh in nine Khadeeja bazan bari kana cemin My Deejay ba chabdi" tai maganan daidai tagama dauramai tie din, hakan yasa ya dungure mata kai yace "sunanta dai yafi naki dadi black belly" "wlh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login