Showing 87001 words to 90000 words out of 150731 words

Chapter 30 - Boyayyen Mutun Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

23 Nov 2024

795

aka tafi dashi anje yanko likafani sai amai wanka" gyadamata kai Mum tayi tace "kaini wajen bana gani sosai" gyadama Mum kai Maman fauzy tayi taja hanun Mum ta kaita shashin su Muhsin ta tura kofan suka shiga da sallama ta kurama gawan Muhsin ido ga Ahmad zaune agefe idanun nan sunyi jajir yana kallon gawan shima, sai Abba dake gefen Ahmad kadan shima yana kallon gawan, ahankali Mum tawani irin zube agaban Muhsin tana wani irin kuka tahade hannayenta biyu alamun roko tana kuka tama kasa fadin abinda takeso tace, tai nadama tai nadama tai nadama biyema Abba, maima yasameta? Ya akayi tabari shaidan yaci galaba akanta? Itace ke dambe da namiji? Meya sameta? sosai Ahmad yaji tawani irin bashi tausayi dan yanda take kuka tana nishi saika zata suma zatayi, ahankali ya mike tsaye yaje inda take ya dagata murya chan kasa yace "Mummy is okay, kidena kuka haka is not good for your health, addu'a zakimai" rungume Ahmad tayi tana kuka shima hawaye ya goge da sauri batare daya rabata da jikinshi ba yajata yakoma chan gefe ya zaunar da ita man dogon kujeran falon su ya dago ta ya cirota daga jikinshi, hannunshi yasa ya goge mata hawayen datake yi dasuka kasa dena zuba, Abba da jikinshi yay sanyi sosai sai wani irin kallonsu yake, murya chan kasa Ahmad yace "Mum kinfada ma Nadeera? Yakamata ta sani, yakamata tazo taga Yayanta tamai addu'a kafin akaishi, kin kirata? Because I know kinada masaniyar inda take? Yanzu rasuwa akayi mu manta komi, kin kirata?" da kyar ta iya girgiza kai cikin kuka in a low tone tace "nafada ma mijinta Muhsin ya rasu" ahankali yasake kai hanunshi kan fuskarta yana goge mata hawayen yace "nace kidena kuka be strong, don't break my heart Mum" gyadamai kai tayi tana wani irin kuka, ahankali yamata kiss a goshi yace "is okay Mum" gyadamai kai tasake yi murya chan kasa yace "give me your phone ban number mijin nata lemme call him nace yakawota" gyadamai kai tasake yi tana kuka sosai ta ciro wayar tabude tabashi number, karba yayi yace "stay here am coming" fita yayi daga dakin yafita waje jiri na dibanshi daurewa kawai yake yakira wayar ringing daya Marwan dake mota rungume da Nadeera dayasamu bacci ya fizgeta yay picking ganin number Mum, ahankali Ahmad yace "this is Ahmad yayan Nadeera I hope ina magana da mijin tane?" ahankali Marwan yace "yea" Ahmad da muryanshi tadan fara rawa yace "please i have a request Yayan mu Muhsin yarasu, dan Allah ka kawo Nadeera let her bid farewell to Ya Muhsin please" shiru Marwan yayi hakanan yaji yana relating to the guy's pain yasan ciwon mutuwan your love one, yasan zafin da dacin abin, baka taba gane ya mutuwa take sai wani naka ya mutu, dan ajiyan zuciya yayi yace "we are on our way mun kusa isowa ma" da sauri Ahmad yace "thank you" yay maza ya share hawayen daya zubomai jiyake kaman ya kurma ihu but he's sure ya Muhsin bazai so hakaba, he has to be strong for him, share fuskanshi yayi daidai lokacin Bello ya shigo gidan dasu likafani da sauran su aleda karba yayi suka koma shashin nasu tare.


Parking sukayi ata gefen anguwan sabida mutane da maza dasuka cikashi fam, ana parking tabude ido rass tafashe da sabon kuka tana kallon anguwan nasu, kashe motar Omari yayi suka bude suka fito tana kallon mutane ta kalli Marwan tace "na shiga uku maiya faru?" shiru yayi ta kalli Omari da Abdallah dasuka fito daga motar tace "dan Allah kufadamin meya faru maiya sami Mummy na eh?" hanunta yarike suka fara tafiya suna sallama da mutane sai kallon su ake anga larabawa har zuwa gaban gate din gidan, yanayin yanda take yasa yabude kofan gate din suka shiga ciki tana kallon mazan dake compound din duk yan office din Ya Muhsin da Ahmad ne mata na bangaren Mum, gaban shashin su suka tsaya daidai lokacin fauzy tafito itama idanunta sunyi jajir rike da buta ahanunta zata bama baban su dake tsaye cikin wani irin kuka tace "ina Mummy na Fauzy?" kallonta fauzy tayi cike da mamaki kafin ahankali tai pointing shashin su Ya Muhsin, wani irin fizge hanunta tayi daga na Marwan taruga dawani irin gudu tana kuka tafada babban falon nasu ta tsaya chak tanabin kowa da kallo tana kuka, da Abba tafara hada ido daya kafeta da ido kaman yau yafara ganinta kafin ta kalli Mum daketa uban kuka kanta akasa sai Ya Ahmad zaune kusa da Mum da shima kallonta yake da idanunshi dasukai jajir kafin ta sauke idanunta akan gawan data gani akasa a lullube, bakinta har rawa yake kirjinta nawani irin bugawa, ta daura hanunta akan kirjinta dake wani irin gudu, miyan bakinta ya kafe, da kyar ta iya bude lebbanta dataji sun wani irin manne kaman ansa gum tace "Y..Ya..M..Ya..Muh...Muhsin?" baya tayi luuuu asume wani irin ihu Abba yayi yazabura yamike yace "My Princess!".
[10/17, 6:01 PM] Aishat Muhammad: *karki karanta in baki biyaba, kisani idan kin karanta ina binki bashi*

*Zaki iya samin access to karanta labarin nan akan kudi naira Dari 300 kacal*

*3107021073 first bank aisha Muhammad*
*07012181461 watsapp min tanan for any enquiry*


*BOYAYYEN MUTUN*


*A6*

Da kyar Abba ya mike tsaye yana dan dingishi yana nishin azaba sosai dan wani irin tafarfasa kwanyarshi takemai yana wani irin kallon hanun nashi yace "wayyo Allah na shiga uku ya kashe ni, Princess please ki dawo gareni" da kyar ya iya yafita daga dakin yana kwalama Adamu driver kira awahale. "Adamu, Adamu, wayyo Allah na Adamu zoka kaini asibiti hakika yau bakar rana ce agareni" arude Adamu yafito daga dakinsu yana salati ganin yanda hanun Abba yayi kafin yay magana ma Abba yace "kaini asibiti kai, kaini asibiti kafin narasa hannuna" jan kafadar Abba yayi yabude mota ya sakashi ya shiga gaba da gudu ya rufe yaja da sauri suka fita daga gidan, private asibitin daya bari dazu ya koma yana zuwa suka karbeshi da gudu.


Direct bedroom dinta Mum ta shiga tana share kwalla tabude wardrobe taciro manyan manyan akwatinan ta tana kwaso kayanta tana hadawa ciki tana hawaye sosai, wani irin bakin ciki takeji sama dana kullun, ahankali Muhsin yatura kofan dakin ya shigo Ahmad biye dashi duk suka tsaya suna kallon yanda Mum ke kuka tana hada kaya inka ganta saika tausaya mata kaman wacce take fama da wata cuta, ahankali Muhsin yataka yakaraso gaban wardrobe inda take yasa hannu ya karbi kayan dake hanunta ya ijiye akan gado kafin yabata wani irin hug yana bubbuga bayanta, fashewa tai da wani irin kuka da tuntuni takeso tayi irinshi takasa, sosai take kukan tana shesheka tace "am sorry Muhsin, am sorry, Muhsin kaya kuri okay" ahankali Ahmad ya shigo shima ya rungumeta tabaya suka sata atsakiya suka rungumeta tsamtsam, sosai take kuka tana rokon su gafara, tace "am sorry, kuyafemin, kuyafemin, komi daya faru ayau laifina ne, nice silan komi, ninaja komi, Abban ku batun yau yake nunamin bayason tafiye tafiye naba, nazauna a Nigeria nai business bazai hananiba amma bayison tafiye tafiye, nai kunen uwar shegu, nakiji, gani nake tunda ya yarda tun kafin muyi aure da business dina baida right akaina, baida right yacemin ga yanda zanyi game zanyi, gashinan yau naga illan hakan, na tarwatsa family na dakaina, nabata komi, yakuma sakeni, am sorry Muhsin and Ahmad kuyafemin dan Allah, is all my fault, am the root to all that's happening, kunsha kirana bana dauka, baban ku ma haka ya kira ya kira bazan sami time din dauka ba, princess ma haka, wlh duk laifina ne, ninaja komi, kuyafemin dan Allah" tahade hannayenta biyu tana wani irin kuka mai taba rai, ahankali Muhsin ya saketa ya sanya hannu ya saukar da hanunta kasa yasa hannu ya goge mata fuskan da hawaye yagama wankewa yace "is okay Mum, stop crying, sit" ya zaunar da ita abakin gado ahankali ya kalli Ahmad dake tsaye yana kallon Mum cikin tausayawa yace "jeka mana parking kayanmu Ahmad, lemme park Mum's own" gyadamai kai Ahmad yayi yajuya yafita daga dakin shikuma yacigaba da kwashe na Mum kayan yana zubawa a box, daurewa kawai yake daga Mum har Ahmad need him, so he has to be strong for them,
Nadeera is not his and yay accepting dis faith, yariga yaga yanda guy din yake sonta, so koma wanene shi he don't care, Alhamdulillah tunda tasamu wanda ke sonta haka, Allah ubangiji yacire min sonta araina yabani wata tagari and make me strong enough nasamu na kula da mahaifiyata da kanina, tass yahada ma Mum kayanta ya zage jakan yana dagasu tsaye yaja ya fitar dasu waje ya ijiye gaban motan shi sanan yadawo ciki yafito da Mum dake tafiya ahankali yabude bayan mota yasata yarufe daidai lokacin Ahmad yafito daga shashin su yana gunguro akwatinan su, a boot duka yahada yasa sanan yabama Ahmad key dan bazai iya driving ba ya shiga baya ya zauna kusa da Mum dahar lokacin ke kuka yana sharemata hawaye suka fita daga gidan, saida suka tsaya a hanya sukai magrib da isha'i kafin suje wani babban hotel suyi lodging, yabiya musu kudin komi suka kai Mum dakinta suka zauna a wurin dan suyi keeping dinta company sai wuraren 12 sanan suka fito suka tafi nasu dakin dan bacci dan gobe da safe sukeso subar garin.


**
Dawani irin gudu Marwan ke tuki har kaman mahaukaci har saida ta kankame kanta cikin tsananin tsoro tana kuka sosai, tsayawa dataji anyi yasa tadago kai ahankali tasa hannu tana share kwalla dake zubo mata daga ido, wani irin kashe motan yayi yabude kofa yafita batare daya kallesu ba, fashewa tayi da kuka sosai tana goge kwallan da bayan hijabi, ahankali Omari da Abdallah suka bude kofa suka fito zagayo wa ta bangaren ta Abdallah yayi yabude side dinta ahankali ya mika mata hannu cike da tausayin ta dan yanda take kuka na mugun tabashi yace "come" gyadamai kai tayi cikin kuka kafin ta mikamai hanunta dake rawa sosai ya rike, da taimakon shi tafito daga motar dan kafafunta sun mata wani irin sanyi sosai, rufe kofan Abdallah yayi yana rike da ita Omari a gefenta sukai shashin nasu suka bude kofa babu kowa a falo sukai hanyar stairs tirjewa tayi Abdallah yajuyo ya kalleta yace "menene?" girgiza mai kai tayi cikin kuka sosai tace "am afraid of him, zai dakeni" takarasa fizge hanunta ta koma ahankali ta zauna cikin daya daga cikin kujerun falon tana goge kwallan dasuka kasa dena zuba da bakin hijabin ta, ahankali yake saukowa daga stairs fuskarshi da danshi ruwa alamun alwala yayo yana tattare hanun riganshi yana tafiya ko daya daga cikin su bai kalla ba yawuce yabude kofa yafita daga falon yay masallaci.

Omari ne yadawo inda take yace "let's go, bazai miki komiba, kinga yama tafi mosque" tashi tayi ahankali tabi bayansu tana waigen kofan suka kaita dakin ta zauna abakin gado ahankali, Abdallah ya kalleta yace "are you hungry? Meza kici" ahankali tace "I want yogurt zansha maganina" "alright yanzu zan kawo miki da abinci but stop crying okay" hannu tasa tana goge kwalla, ahankali Omari ya zauna kusa da ita yakama hanunta yarike batare dayace mata komiba yana kallon fuskarta, he just wanna hug his little sis, ya lallasheta, he want to shower her with love, ahankali yace "Rahma, my little sister" ahankali ta dago kai ta kalleshi hawaye sun cika idanunta shima haka hawaye suka cika idanunshi gam, ahankali yana kara matse hanunta yace "baki yarda, we are your brothers ba ko? ranan da Momma ta haifeki aranan ta rasu, we've went through hell in this life but munyi enduring sabida ke muke nema, don't worry bit by bit I will tell you everything, I will show you our file and your file kigani, but for now kidena kuka okay, we will always protect you, we really need you in our lives, I love you so much Rahma" wani irin fadawa jikinshi tayi tafashe da kuka sosai hakanan all maganganun dayake mata tana feeling dinsu har cikin ranta, and tunba yauba barin ma Abdallah dataji she feels so connected to the guy tun ranan dasuka fara haduwa a super market saisa ma bata manta da fuskan shi ba, dan idan normal person ne da tuni ta manta dashi, bude kofan Abdallah yayi ya shigo dauke da tray dake dauke da abinci chicken rice dakuma farm fresh yogurt da cup da spoon, ganin yanda ta rungume Omari tana kuka yana bubbuga bayanta shima hawaye na zuba daga idanunshi yasa yaji kukan shima yazo mai, da kyar ya ijiye tray a gefe ya zauna agefen su yanadan murmushi, ahankali Omari ya saketa ta juyo ta kalli Abdallah daya kafeta da idanu dasuka chanza kala, murmushi tayi hawaye na bulbulowa daga ido kafin tawani irin bashi emotional hug tace "Ya Abdallah" kankameshi tayi shima haka yana kuka yace "My shagwababbiya Sister" makemai kafada tayi tace "uhm uhm" cirota yayi daga jikinshi yanaji kaman ya cinye ta yamata kiss a forehead yakara rungumeta very tight da kyar ya iya sakinta shida Omari suka sata a tsakiya hakanan taji tamanta da duk wani bakin cikinta, wani irin farin ciki da batasan daga ina yakeba taji yawani irin lallubeta, duk sukai shiru sun tasata agaba sunata kallonta, Omari ne yay breaking silence din yace "zokici abincin ki, muje muyi salla Abdallah" kaman zaiyi kuka Abdallah yatashi suka fita daga dakin yana mata bye itama haka tanata kallon su kafin taja tray din chicken rice dayakawo mata da yogurt da spoon, hada maganin da Mum takawo mata tunda dama safe da dare ne tasha da kyar sanan taci abincin da sauri sabida yanda yabata mata baki taci kusan rabin abincin sanan taji ya isheta tasha tsimin da acewanta shiyafi dadi tasha sosai sanan ta maida tray kasa ta jingina da gado tareda lumshe ido tai shiru tana tunanin komi da kowa na rayuwata, barin ma Abba da agabanta Marwan ya ballamai hannu, wasu hawaye masu zafi ta share. Takusan bata one hour ahaka sanan ta tashi da kyar ta shiga bayi tayo wanka da brush ta shirya ta saka wani cotton rigan bacci white iya guwiwa tafito ta zauna akan gado tai tagumi tana kallon kofa ita kanta batasan metake jira ba takai kusan 30min tana kallon kofan kafin bacci yay nasaran awon gaba da ita.

**
Abba kam hanunshi a machine din hoto aka fara sawa kafin aciro amai dauri, bakaramin wuya yasha ba, ihu babu kalan wanda baiyiba, kai karaya da zafi, take wani mugun zazzabi ya turke shi akai admitting dinshi aka samai ruwa, da kyar bacci yay awon gaba dashi yana kiran sunan Princess ahankali ahankali yana nishi kaman zai mutu yay baccin.


**
5:30 na safe tama su Mum da Muhsin da Ahmad a airport, basu wani bata lokaci ba suka biya wani extra kudi akan kudin tickets din flight dinsu dasukai missing na jiya aka basu New tickets, karfe bakwai jirgin su ya daga sukai bye bye da Nigeria.


***
Knocking mata kofa da akayi yasa tabude ido ahankali taga rana tayi gari yay haske sosai, ga kanta dataji yana mata wani irin ciwo, daga tachan waje Abdallah ya daga murya yace "hope kin tashi babysis? Good morning, oya stand up and get ready we are going to New house, yeeee excited right?" yay wani irin kara, murmushi tayi ahankali ta sauko daga kan gadon tana kallon dakin ganin ko alamunshi bata ganiba, tashi tayi ta shiga bayi tai brush tayo wanka tsaf tafito ta shirya cikin wani skinny Jean dayabi shape din jikinta sosai black, dawani yellow t-shirt daya kamata shima, wani black kimono ta dauko cikin kayan da Mum ta kawo mata ta daura akai ta yane kanta da gyalen kimonon kafin ta fesa turarenta da Mum ta kawo mata twilly, dudda babu makeup a fuskarta but tai wani irin inviting kyau ta zira flat shoe dinta tafito.



Kaman wata matsoraciya tabude kofan dakin tafito kirjinta na faduwa daidai lokacin shima ya bude kofan dakin Omari yafito yana sanye da white shirt daya kamashi da fadadden kirjinshi yafito sosai sai dogon Jean sai baki, yasaka wani black Prada sandal daya kara haska farin kafarshi yay kyau ciki, sai kamshi yake kallo daya yamata ya dauke kai yacigaba da tafiya abinshi yay kasa, wani irin mummuna faduwa gabanta yayi takasa koda motsin kirki balle tai tafiya, Omari ne yafito daga dakin nasu yana gunguro wani babban hadadden akwati yana ganinta ya sakin mata murmushi, murmushi itama ta sakin mai tace "ina kwana" hanunta ya kama yarike yace "how was your night Kinga yanda kikai kyau kuwa, muje Ahmad zaizo ya dauko jakan ki" gyadamai kai kawai tayi tabishi suka sauka gabanta na faduwa har zuwa compound din, tsaye tahango shi dawani tsoho baban Kamal yana magana yana dan murmushi wurin motan Omari ya kaita ya bude baya ya sata kafin yabude boot yasaka jakan shi aciki yakoma cikin gida, yakai kusan 2min yana magana da baban kamal sanan ya juyo ya dawo motan yanadan Satan kallonta yanda kanta ke kasa tana wasa da yatsun ta, bude gaban motan yayi ya zauna a mazaunin driver, ahankali ta dago kai tadan saci kallonshi miyan bakinta nawani irin bushewa da kyar ta daddage kaman zatai kuka tace "good morning" ko alamun amsawa baiyiba balle tasaran zai amsa, sake mayarda da kanta kasa tayi daidai lokacin kuma Omari da Abdallah suka karaso wajen jakunkunan su da nata suka zuba a boot din suka rufe sanan suka bude motan Abdallah ya bude baya ya shiga yana daura mata file din adoption dinta a cinya na wurin Mum yana rufo kofa shikuma Omari ya shiga gaba ya rufo kofan. Kunna motan yayi suka fita daga gidan Abdallah yace "shagwabatu open it and see" gyadamai kai tayi duk jinta wani irin take takeji, tabude ahankali tafara karantawa na wurin, hoton ta natun tana jaririya tafara cin karo dashi dan Mum ta nuna mata hoton dama saikuma sunan ta data gani baby R, saikuma motherless home din da akai adopting dinta dagashi a Egypt, sanan saiga hoton su Mum da Abba da Muhsin ranan da akai adopting dinta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login